Showing 126001 words to 129000 words out of 388641 words

Chapter 43 - KWAI CIKIN KAYA

10 Sep 2025

20693

gata Mummy da kanta ta tisa ƙeyar Aamilah suke gyara ɗakin Shahudah, Aamilah sai tunzura baki take gaba dan bata saba da aikinba.
Jitake tamkar taje ta kira Amina, dan ta fahimci amfaninta sosai a gidan a yau, hakama Bilkisu, dan tasan badan wannan ƙaddararran aikin da Bilkisun keyiba ai da yanzu itace zatai gyaran.
Haka dai suka kammala Mummy ce ƙarfin aikinma, dan danan ɗakin ya ɗauki ƙyau da haske tamkar ba shiba, shima yau yasan maishi zata dawo garesa.
Huɗu nayi Salman ya baro office ya taho gidan domin zuwa tarbar gimbiya Shahudah😝.
Gudun karma a ɓata mata rai huɗu da rabi suka bar gidan, sun gwammaci su suje su jirata, amma ba ita taita jiransu ba.

Zaman da baifi mintuna ashirinba kuwa jirgi ya sauka, fasijoji suka fara fita, sosai idanun su Mummy nakai.
Can sai ga zillaziyya zankaɗaziyya gimbiyoyi mandiyoyin oga Jawaad ta fito cikin takun ƙasaita da gayu.
Sanye take cikin wandon blue da yay masifar kama jikinta, sai riga ruwan hoda an rubuta Beauty da ado mai ƙyalƙyali a gaba, siririn gyalenta data yana a kai shima ruwan wandon, sai rigar sanyi data ɗaura a ƙugu, ta toshe fuska da eyeglasess mai nuna blue a jiki.
Tabbas tayi masifar ƙyau, kuma duk wanda ya gani tilas ya ƙyasa dan ta cancanta.
Aamilah ta tafi da gudu gareta, hakan yasa Shahudah sakin akwatinta da jakkarta ta hannu a ƙasa ta rungume ƴar uwarta, takalman ƙafarta masu masifar tsini badan sunada maɗauri ba babu abinda zai hana su sakata ta faɗi.
Wasu daga cikin mutane sai kallonsu suke, musamman irinmu ƴan ƙauye da bamu waye ba😒, dan harda bakuna muka hangame lokacin da Salman yazo ya rungumeta shima.
Yanda suka ƙanƙame juna lamarin zattakaici, ta sakeshi ta nufi Mummy ta rungume itama, sai kuma suka sake rungumeta baki ɗaya, hakan dai na nuna suna cikin tsantsar farin cikin ganinta duk da sukanje su ganta a can musamman ma Mummy da Aamilah.
A sabuwar motarta da Dad ya saya mata akaje ɗaukarta ita kaɗai, ta kalli Mummy ta kalli motar cikin alamun tambaya.
Dariya duk sukai mata, Aamilah ta sanar mata ƙyautar Dad ce.
Wani ihu Shahudah ta saki tana ɗane Mummy, motar da kullum take nafarkin mallakarta, ta ƙiyasta kuɗinta bazasu kai ta sayaba shiyyasa ta haƙura, ashe Dad zai cika mata burinta.
Yanda take matuƙar murnar ne yasa mutane suka sake maida hankalinsu a kallonsu, wasu zato suke ko daga karatu Shahudah ta dawone akai mata wanna irin tarba da ƙyauta mai tsoka, har dai suka shiga mota zuwa gida idanun mutane na kansu.

Daɗi ya ishi Shahudah sosai, dan Dad yay mata bazata irin wadda bazata taɓa iya mantawa ba, sayen motarnan yay bala'in kai mata ko ina a cikin ƙoƙon ranta, har tana tunaninma wace kalar murna zatai masa yasan taji daɗi.
Murnar motama ta hanata nutsuwa taci abincin kirki a cikinta, duk da tarin abincin da aka shirya matan kuwa.
Wayar Aamilah ta amsa ta kira Dad ɗin, maimakon tai masa godiya da addu'ar fatan alkairi sai kawai taita masa ihun murna da faɗa masa ya cika mata burinta, shi dai yana saurarentane yana murmushi, yanataso yaji ta masa godiya tamkar yanda idan yayma Bilkisu ƙankanin abu take masa amma sai yaji tsit.
Maimakon hakan ya taɓa ransa sai ya danne kawai, yama cigaba da nuna mata farin cikinsa na dawowarta, ya kuma tabbatar mata a satinnan shima zaizo ƙasar kodan ita.

★★★

Duk yanda Mummy taso tai haƙuri Shahudah ta huta sannan suyi zancen Jawaad ta kasa, haka ta zayyane mata halin da ake ciki yanzu na tallar ƴammata da ake masa a cikin family ɗinsu.
Ran Shahudah ya matuƙar dugunzuma, ta shiga masifa da faɗin Jawaad natane ita kaɗai, duk yarinyar datai gigin shigar mata rayuwar miji wlhy sai ta halakata.
Tai shiri akan a daren zataje family house ɗin su Jay, amma sai Mummy ta hanata, ƙin sauraren Mummy tayi, sai da ƙyar, dan ta nuna mata abinfa YAƘIN SUNƘURU yakeso yanzu, dan haka kar tayi gaggawa, ta jira taji abinda suka shirya akan al'amarin............✍🏻


Alhamdullahi ala kulli halin🙏🏻😢.


Anan na kawo ƙarshen littafin ƘWAI CIKIN ƘAYA na ɗaya. Abinda na rubuta daidai ya rabbi ka haɗamu a ladan baki ɗaya, wanda nayi kuskure kuma ALLAH ya yafe mani da ku da kuka karanta🙏🏻😭.

Wannan shine wasa farin girki.

Ga dai Bilkisu ta kafa alƙalamin bincike akan al'amarin da ya faru da Amina. Shin zata dace da gano wanda yayi? Ku fans ma to wa kuke zargine akan wannan al'amari? (Ina jiran amsarku).

Ga Shahudah ta dawo, kuma da burin komawa gidan mijinta, sannan ga burin iyayenta da bamusan manufarsaba sam, shin zatayi nasara kokuwa dai iskace ke wahal da mai kayan kara?🤔🤒.

Ga Bilkisu alamu sun nuna zata koma tawagar Jay, yaya kuke tunanin wasan zai kayane? Faɗuwar gaba da kallon kallo da sukema juna tsakanin ita da Boss ɗin minene manufarsa?😌.

Qaseem ya ɗau zafi da komawar Bilkisu tawagar Jawaad, yaya kuke ganin za'a kwashe, zai bartane? Kokuwa zai canja salon wargaza tafiyar?🤫

Ina Jazuga? Ina Firdausi da iyayenta? Ina labarin gidansu Uwargida? Ina labarin gidan hayar dasu Bilkisu suka rayu da iyayenta? Shin duk Bilkisu zata waiwayesu ne kokuwa dai sun zama labari?🙃

Mahaifiyar Jawaad babu wanda yasan inda take, akwai kuma maganar da ta taɓa shiga tsakanin Jawaad da dattijuwar dake aiki gidan Alhaji kokino ba giyar yaroba, shin kuwa babu lauje a cikin naɗi? Dan zaurancen nasu yayi kama da🤫🤭.

Kenan dai akwai ƙurori da cakwakiyoyi sosai kenan, duk kuma a cikin littafin ƙwai cikin ƙaya kashi na biyu🤓🥱⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀.


BILKEESU IBRAHEEM MUSA
(Bilyn Abdull ce😘🤫)


Typing
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce
Assalamu alaikum, barkanku da wannan lokaci, barkanmu da sake dawowa filin daga, insha ALLAHU zan cigaba da littafin ƘWAI CIKIN ƘAYA kamar yanda na fara, inafatan haɗin kai daga gareku, haɗin kan kuwa shine tsaftataccen Comments da zai iya zaburar dani akan abinda nake rubutawa, masu ɗaukar littafi su ɗaura a youtobe wlhy wlhy na rantse duk wanda ya ɗauramin ƙwai cikin ƙaya a youtobe kar yay kuka dani akan matakin da zan ɗauka yay kuka da kansa. Masu cewa kuma na maida littafin na kuɗi kudaina yimin ƙarya, inda naso hakan da tun a 1 zance na kuɗine. Masoya kumuje zuwa, yanzu za'a fara wasan .
BOOK TWO
(1)
............Kowa yana cike da murnar dawowar aunty Shahudah a gidan amma banda ni, ba komai ya jawo hakanba kuwa sai irin tarbar dana samu daga gareta bayan dawowata aiki a randa ta dawo.
Cikin ɗokin ganinta da kewa na nufeta, amma saita kalleni cikin wani yanayi na wulaƙanci da ƙyama kamar yanda ta sabamin a baya, daga ƙarshe ta koma dariyar aikina. Hakan ba ƙaramin ciwo yayminba, musamman yanda naga harsu Mom sun biye mata suma suna tayata dariyar. Daurewa nai nima na tayasu, dan na ɗaukama kaina alƙawarin insha ALLAHU sun daina ganin raunina a yanzu. Sai da muka gama dariyar sannan na nufi ɗakina nabarsu, su Aunty Aamilah na bata labarin yanda akai nazama dss a yanzu.
Ina shiga ɗakina na faɗa saman gado na fashe da kuka, tabbas wulaƙanci bashida ƙyau sam a rayuwa, ƙasƙanci ga mutum abune mai muni, amma a wannan duniyar babu abinda mutane suke alfahari dashi kamar ƙasƙanta ɗan uwansu musulmi.
“Sai kaga mai dukiya yana ƙasƙanta talaka koda da magana ne, mai ilimi na ƙasƙanta marashi, mai mulki na ƙasƙanta mabiyansa, miji na ƙasƙanta iyalansa, ɗan uwa na ƙasƙanta na ƙasa dashi. koyaya mutum yafi wani saikaga yana hura hanci wajen ganin yayi tozarci ga wanda bai kaisaba, kaicon mutane da wannan ɗabi'a, kamanta ALLAHN daya baka shima bai manta da shiba, sannan badan ka fisaba ya baka shi ya hanashi, ikonsane wannan yabama wani ilimi yayi wani jahili, ya bama wani dukiya yayi wani talaka, ya bama wani haihuwa yayi wani babu ɗa, ya bama wani mulki yayi wani mabiyi, ya bama wani lafiya yayi wani mara lafiya, kowa a rayuwa akwai jarabawarsa, kaine wane bashike nuna kafi kowa ba, kai ka samu kaza ko kake da kaza bashike nuna ALLAH yafi sonka ba, nima ALLAH yana sona, kuma ina sake gode masa da yanda yayini aunty Shahudah.......”
Tun daga wannan ranar na sake jabaya ga kowa da komai na gidan, Dad dama bai dawoba, hakama Yah Qaseem yayi tafiya tun washe garin dawowar aunty Shahudah gidan. ko a wajen aiki bani da wata walwala, Ummie da wasu abokan aikina sai suka danganta rashin walwalar tawa da kewar Yah Qaseem da bayanan, dan zuwa yanzun mutane da yawa sun san alaƙar dake a tsakanina dashi.
Ni kuma a ɓangarena ba damuwar rashin yah Qaseem bane da lamarin gidanmu kawai kecin raina, akwai wani abu daban danaketa ƙoƙarin tureshi a raina, dan bana fatan gaskata zancen zuciyata koda da wasa kuwa.
★★★★★★★★
Yau data kasance juma'a dai-dai da dawowar aunty Shahudah da kwanaki huɗu Dad shima ya dawo, kowa yay murnar dawowarsa tamkar yanda muka saba, ya kuma samu tarba daga matarsa harma da Aunty Shahudah dake ganin wannan dawowar tatace. Nidai ina daga baya-baya dukda jana a jiki da Dad keyi, dan motsi kaɗan ya sako sunana a cikin zancensa, hakan na kula baƙaramin sosa zuciyar Aunty Shahudah ya keyi ba, hakama Mom. Dana kula abin zaiyi tsamari saina zare jikina na gudu ɗaki, dama dai muna zaune ne muna cin abincin dare.
Ban sake yunƙurin fitowaba kuwa har safiyar washe gari domin nima naji a raina yakamata na basu waje su gana da mahaifansu. duk da kasancewar asabar ce babu aiki ban iya komawa barci ba, dan narigada na saba yanzu da yanayin tashin sassafe. Ina zaune akan abin sallah tun bayan idar da sallar asubahi ban tashiba, na lazimci azkar nai karatun Qur'ani, rashin abunyi ya sakani tashi nahau gyaran ɗakina, hakan sai ya jani tsayin lokaci har kusan tara da wasu mintuna.
Sama-sama nake jiyo hayaniya kamar na kuka, kukan kuma yaymin kama da muryar Mom. Nai azamar ajiye tawul ɗin dana ɗauka zan shiga wanka na fita. Sosai gabana ya faɗi saboda cin karo da Mom dake kuka iyakar ƙarfinta, Dad na riƙeta, daƙyar na iya haɗa maganganunsu, daga ƙarshe na fahimci ƙanin Mom ɗine ALLAH yayma rasuwa mai suna Usman, tabbas naji suna yawan faɗar sunan Uncle Usman, sai dai ban sanshiba, ban taɓa ganinsaba, dan duk zamana a gidan ban taɓa zuwa gidansu mom ɗinba, bankuma cika ganin ƴan uwanta suna zuwaba, kowa dai yasan halin wasu ƴan bokon nan da aƙidar rashin son takura.
Nima dai tausayin Mom ya sakani bin sahun masu sharar hawaye, nan dai Dad ya cigaba da lallaɓata, kafin yajata sama, muma yace duk mu shirya domin tafiya can gidan. Hakanne ya saka kowa nufar ɗakinsa mu duka.
______________________________
A daren jiya juma'a misalin ƙarfe sha biyu da wasu mintuna mummunan labari ya iso gidansu Jawaad, cewar Uncle Usman ya samu haɗarin mota a hanyarsa ta dawowa daga tafiyar da yayi ta kwanaki biyu.
Lallai wannan gida sun fuskanci tashin hankali na bazata, dan bayan mahaifin Jawaad basu ƙara rasa ko ɗaya a cikinsuba, kaf ƴaƴan malam Yusif Abdul-aziz ne kawai ALLAH yayma rasuwa. Saiko shi malam Yusif ɗin da matarsa ɗaya sai mama maryam, idan ka cire waɗanan huɗun sauran duk sunada ransu, saima yaɗuwa da suka sake yi saboda haihuwar jikoki harma da tattaɓa kunne.
Ruɗanin da mama Atika ta shigane ya sakata yanke jiki ta faɗi, dan abune da tunaninsu bai taɓa kawo musuba anan kusa duk da sunsan mutuwa tabbacice ga duk mai rai, ba Uncle Usman ba ko ita kanta data tsufa sosai bata tuna mutuwar zata iya ɗaukarta a yanzu balle shi da ayanzune ake ƙara shiryama duniyar filin zama.
Lokacin da gidansu Jawaad ke cikin wannan ruɗanin shi yanacan suna gumurzu da wasu gungun ƴan ta'adda da suke fako tun kusan sati uku da suka shige, sai a yaune ALLAH ya basu nasarar yin fito na fito dasu, sun sami nasarar kama wasu a cikinsu, yayinda wasu suka gudu.
Kusan ƙarfe huɗu na dare suka iso station ɗinsu da waɗanda suka cafko, sunyi tiɓis da gajiya, ga yunwa dake cin hanjinsu ta bala'i ma kuwa, sai dai jarumtarsu da juriya mai haɗe da trianing ɗin da suka gogu a ciki duk ya ɓoye gazawarsu. Rose cema dai kawai ta kasa juriyar kasancewar ƙarfin zuciyar mace dana namiji ba ɗayaba, dukda itama ta cancanci a kirata jarumar kuwa, Jawaad ma baiso akai aikin da itaba, amma ta matsa akan sai taje, badan yasoba ya barta ta bisu.
A station ɗin suka ƙarasa kwanan, washe gari safiyar asabar ana idar da sallar asuba Jawaad ya kira gimba akan yazo ya ɗaukesa. Yanda yaji muryan gimban ne ya bashi mamaki, cikin yanayin gizagonsa yake jefa masa tambayar lafiya?.
Sanin halinsa baya son ɓoye-ɓoye a magana ya saka Gimba faɗa masa gaskiyar tashin hankalin da ake ciki a gidan nasu.
Dukda halin da yake ciki da matsalolin dangin mahaifin nasa hakan bai hanashi shiga ƙololuwar tashin hankaliba, a take ya birkicema su Jabeer, waɗanda suma jin rasuwar tai bala'in sakasu a ruɗani. Basu wani ɓata lokaciba suka nufi gidansu Jawaad ɗin kai tsaye, duk da halin gajiya da buƙatar hutun da suke a ciki. Sun iso gidan ƙarfe kusan bakwai da wasu ƴan mintuna, hankalin Jawaad ya sake tashi sosai ganin halin da ahalinsa ke a ciki, tuni ya manta da gajiyar dake tattare dashi.
Bai zaunaba su Uncle Nasir suka jashi zuwa asibitin da gawar Uncle Usman take domin su amso, abinda yasa ba'aje tun jiyaba saboda ba'a nan cikin gari bane, inda ya baro yafi kusa da inda yay haɗarin, shiyyasa aka maidashi asibitin can garin.
★★★★★★★
Ƙarfe goma da wasu mintuna muka iso gidansu Mom, katafaren gida na alfarma da ƙawa, dukda cikin tashin hankalin mutuwa mukazo hakan bai hanani mamaki da jinjina dukiya irinta wannan ahaliba, lallai dolene su aunty Shahudah suyi wulaƙanci yanda sukeso, kaga gida tamkar ba hannune ya ginashiba, harabar gidan kawai naganimafa kenan, sai mutanen gidan da zakaima kallo ɗaya ka fahinci ƴan bokone na haƙiƙa tun zamanin da boko keda tsada da daraja kuwa......
Ina cikin wannan tunanin ne nafara jiyo ƙarfin koke-koke na ƙaruwa, babu shiri na dawo hayyacina, a sannanne na lura ashe an iso da gawar mamacinne.
Har ciki sosai Ambulance ɗin dake ɗauke da gawar ta shigo, ta tsaya dai-dai sashen danaji wasu na ambata da sashen mama Atika mahaifiyarsu Mom. Zuciyata tai masifar harbawa saboda ganin wanda ya fito daga Ambulance ɗin.
Cikin tsagwaron mamaki na furta “Boss kuma anan?” akan laɓɓana, kamar yanda nakejin zuciyata aduk sanda ta samu kusanci dashi yanzunma bata canja zaniba, dole na shiga karanto addu'a gudun kar nayi abinda zai jawo hankalin mutane a kaina.
Nayi nisa a tunanin da har aka fidda gawar ban saniba, saida suna gab da shiga sashin ne nakai idanuna kansu tare da sauraren koke-koken mutane, su biyune kawai ke ɗauke da gawar a mankara, tana lulluɓe da farin ƙyalle da yay face-face da jini, alamar dai mamacin ya bugu sakamakon Accident ɗin da yayi, nantake sai zuciyata tai rauni saboda tunowa da mutuwar nawa mahaifin, sai kawai na durƙushe a wajen na fashe da kuka mai cin rai da zuciya.
Isowar gawarce ta saka gidan ya kuma cika sosai, koke-koken da akeyi ya sake ƙaruwa, ban kuma ganinsaba kuma har aka sake fitowa da gawar kusan sha biyu na safe, da alama dai yanzu an masa sutura za'a miƙashi gidansa na gaskiyane. Wani da nake ƙyautata zaton ɗansane ya rugo da gudu ya riƙe mankarar da aka ɗakko yana kuka da roƙon su ajiye masa Dadynsa, yarone da bazai gaza shekaru sha uku ba a duniya, sai ƴanmata guda biyu da zasu iya kawai 23 da 20 suma sukazo suka riƙe. Hakan ya kuma tada hankalin jama'a, ni kaina sunyi masifar bani tausayi, suma kenan da suke da gatan dangi dana jin daɗin rayuwa, na tuna sanda baba ya tafi ya barni, har aka binnesa ma ni bansan ina nawa hankalin ya keba.
Na share ƙwallar dake gudu bisa kumatuna, dai-dai isowarsa, wajen da alama yanzune ya fito, shine ya janye yaron ya rungumesa a jikinsa yana bubbuga bayansa, hakan ya saka ƴan matanma sakin mankarar suka durƙushe a wajen suna kuka. Bai saki yaronba har saida aka fita da gawar, ya shafa kansa yana ɗago fuskarsa, babu wanda yasan miya faɗama yaron, amma kowa ya kula magana yay masa kafin ya sakesa ya fice shima zuwa waje inda za'a sallacesa.
Tashin hankalin da ake cikine yasa ban samu damar tunanin alaƙar gidan da boss ba sam, bankuma sake ganinsaba, sai dai ganin nasa da nayi yana nan daram a zuciyata, dan kwanaki kusan shida kenan ban gansaba ko'a office, tun fitar da sukai ranar sai yaune na ganshi. A mamakina sai naji raina sakayau, bakamar yanda na tsinci kaina cikin ƙunci ba a kwanakinan.
★★★★★★
Tun bayan zuwanmu gidan ban sake sanya ƴan gidanmu a idonaba, har zuwa yanzu da aketa hada-hadar sallar azhar da cin abinci, garama dad bayan sun dawo daga binne gawar ya shigo cikin gidan shi da wasu manyan mutane sunyi gaisuwa, daga haka ban sake saka ko ɗaya a cikinsu a idanunaba.
Mutane nata shiga sassan gidan domin gabatar da salla, sai dai ni narasa ina zan dosa koda na tashi, waɗanda nazo dominsu ban sake ganinsuba, ina zan shiga nikan nace zanyi salla? Tunda babu wanda ya sanni babu kuma wanda na sani.
Ina nan zaune ina saƙa mai fishsheni a zuciya budurwar dake zaune a kusa dani ta miƙomin jakkarta da waya akan na riƙe mata tana zuwa, kamar zanyi magana sai kuma na amsa ina maida mata murtanin murmushin da takemin, ina zaune a wajen ban motsaba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login