Showing 234001 words to 237000 words out of 388641 words
sonake dai naji abinda ka sani ɗin, ranar juma'a Gimba yazo tashar nan taku?”. Dattijo yace, “Eh to kamar dai yazo”. Jay daketa dannewa bayason ya tsoratashi yace, “Banason ƙwana-ƙwana a magana, ka fitomin a mutum mu wanye lafiya”. Ya ƙare maganar da zare glass ɗin idonsa sukai ido huɗu da Dattijo. Sosai kwarjinin Jawaad ya sake cikama Dattijo idanu dama wajen baki ɗaya. kasa jurar kallon idon da Jay ke masa yayi ya duƙar da kansa. Jawaad yay wani munafukin murmushi yana ɗauke kansa shima, “Yaya zan samu amsar gaskiya?”. Kai Dattijo ya ɗaga batare da ya yarda ya sake kallon Jay ɗinba. “Tabbas yazo nan ranar juma'a nayan an sakko masallaci”. “A motar wa ya tafi gida?”. “Bai shiga motar kowaba ranar a tashar nan”. Cikin ƴar fusata Jay yace, “To motar wa ya shiga?!”. “Ni...ni bansanshi ba Alhaji”. Murmushi Jay ya sakeyi irin na zan lailaya kanka a titi ɗinan ya ɗaga jacket ɗinsa ƙaɗan yace, “Kalli nan”. Koda Dattijo ya ɗago yauy arba da bindiga sai ya waro idanu waje, kafin kace kwabo zufa ta gama jiƙesa. Jawaad yace, “Saika zaɓa, amsata ta gaskiya kokuma rasa numfashi?”. “ALLAH ya baka haƙuri oga, wlhy inada iyali da ƙananun yara a gida, abinne wuya garesa shiyyasa”. “Kai kake ganin wuyarsa”. Cewar Jay yana haɗe fuska fiye da farko. Cikin kakkausan murya yasake faɗin, “A wace mota gimba ya tafi gida ranar juma'a?”. “Tare da ɓaleru” Dattijo ya faɗa da sauri kamar zai haɗiye harshensa.
Jay ya sake zare glass ɗin idonsa a karo na biyu, sun sake kaɗawa sunyi ja da ɓacin rai, “Wanene Ɓaleru?”. Ya faɗa yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya da harɗe hannayensa saman ƙafar yanaɗan juya glasess ɗin hannunsa idanunsa kafe akan dattijon. Kan Dattijo a ƙasa yace, “Shima ɗan garinmu ne, zanma a iya ce maka kamar abokai suke da marigayi gimban, dan duk sa'anni ne kuma unguwarsu ma kusan ɗayane”. “Ina zan samesa yanzun?”. “Wlhy oga ban saniba, kawai dai nasan yana anan birni shima yana aikin drivernci a wani gida”. Miƙewa Jay yayi tsaye da cewar, “Koma ina yake ni zan memosa, ba'a cin kuɗina a matsayin cin hanci, amma ina biya idan na saka aiki, zan baka aiki nakuma biyaka yanzunan, ya rage naka kaimin da gaskiya kokaci amanata idan anzo an biyaka abinda yafi nawa, biyoni”.
Jiki a saɓule dattijo yabi bayan Jay har zuwa isa inda ya faka motarsa. Jawaad ya buɗe motar ya shiga ya zauna batare daya rufeba, ƙafafunsa duka a waje, takarda ya ciro da pen ya kalli Dattijo dake tsaye, “Ka iya karatu ne?”. Da sauri Dattijo yace, “Eh nayi sakandire Oga”. Jay baice komaiba ya maida kansa yay rubutu da hausa a takardan sannan ya miƙa dattijon tare da kuɗi bandir ɗin ɗari biyar. “Wannan aikin zakaimin, ga kuɗin aikinka nan”. Daga haka ya shige motar sosai ya rufe abinsa yaymata key tare dayin reverse yabar wajen.
Ganin lokacin sallar zuhur yayi sai ya tsaya yay sallah kafin ya ƙarisa station, tunkan ya shiga office ɗinsa ya samu kira daga sir Ahmad, fasa shiga nasa office ɗin yay ya nufi na Sir Ahmad ɗin. Ba'a masa iso dan zai shiga office ɗin sir Ahmad, knocking kawai yakeyi a bashi iznin shiga. Yanzunma kansa tsaye ya isa yay knocking ɗin, daga ciki sir Ahmad ya bashi izinin shiga dan yana kallonsa.
Cikin girmama ya gaishesa, Sir Ahmad ya rufe file ɗin gabansa yana kallon Jay ɗin dake zaune, “Ina ka shige hakane tun ɗazun nake aike a kiramin kai?”. “Am sorry sir na fitane”. “Okey to ya ƙarin haƙuri?”. “Alhmdllh sir”. “To ALLAH ya gafarta masa, ya raya abinda ya bari. Na kiraka ne dama akan Qaseem, wai yau kwana biyu yana hannun police”. Cike da mamaki Jay yace, “Police kuma? Basusan shiɗin wanene ba?”. Murmushi Sir Ahmad yayi yana kwantar da bayansa jikin kujera, “Sun sani sarai, gabace da gabanta, ya mari wani Doctor ne a General hospital shekaranjiya lahadi harya fidda masa jini, to Doctor ɗin ɗan Alhaji ɗan-iya warzu ne, shinefa yakai maganar hukumar lafiya ta ƙasa baki ɗaya, sukuma suka saka aka kama Qaseem ɗin”. Huci Jawaad ya furzar , shi shaf yama manta yabar Qaseem ranar a asibiti, yaso ya koma amma sai aka samu akasi, ya tabbata dalilin abinda ya faru ranarne Qaseem ya mazge Doctor, shi baisan yaushe Qaseem zai daina halin ƴan danbe ba ya rage baƙar zuciya. Yace, “Yanzu miya faru to Sir?”. Sir Ahmad yace, “I.G ne ya kirani da safen nan yake sanar min cewar shi Warzu yace sai anje kotu, shikuma yaga ɗaya daga cikin yaranane shiyyasa ya kira ya sanarmin dan anrma lauya, kuma ko babansa ma bai saniba”. Murmushi ne ya kufcema Jay, dan kuwa dai yasan lallai da Dad yaji da ba'a zauna lafiyaba, dan inma ɓakin son ƴaƴane Dad yatake Warzun ya shanye. “Miya baka dariya?” Sir Ahmad ya faɗa yana tsatstsare Jay da idanu. Kai Jawaad ya shafa yana ƙara sakin wani murmushin, “Sir abinne nasu ne ai, ni nasan Dad da yasan Qaseem na cell da yanzu garinan ya fara yawo a gajimare dan rikicinsa, kafaɗamin wane station ne? zanje na fiddosa yanzun insha ALLAH”. “To aini banƙi in baka damar cirosanba, kaima rikicin naka nake tsoro ai, dan baka da maraba da Dadyn naku, ta wani wajenma ka fisa zama ɗan ƙunar baƙin wake, nikuma banason ka haɗa harƙalla da Warzu dan shaiɗanin mutumne da kake ganinsa kullum cikin manyan kaya”. “Karka damu Sir salin alin zamu dawo”. “To shikenan gashi, saika nema lauyan Qaseem ɗin kuje tare”.
Sallama Jay yaymasa ya fita.
Bai koma office ba ya sake ficewa, harga ALLAH bazai iya jurar tuƙiba, haka yake shi baison tuƙi saita kama dole, dolene yasan mafita, to amma shikam ‘Wane driver ne zai iya maye masa gurbin Ginbansa?’ yay maganar cikin rai zuciyarsa na masa zafi. Office ɗin Jabeer ya shiga, babu jimawa suka fito tare. Jabeer ɗinne ya jasu, sai da suka fara tafiya yaɗan dubi Jay ɗin daketa faman danne-danne a tab ya ɗauke kansa ya maida ga titi “Na zatafa wajen rasuwarnan ka koma?”. Jay da bai ɗagoba bai kuma fasa abinda yakeba yace, “A'a, dama sonake sai gobe idan ALLAH ya kaimu mu koma mu duka”. “Okey ALLAH ya kaimu” cewar Jabeer yana maida hankalinsa ga tuƙin.
Asibiti suka fara zuwa wajen Doctor Ballo Warzu, cikin girmama ya tarisu yana tambayar jikin Bilkisu?, mafi yawan amsarsa Jabeer ne ya bashi ita, sai da suka gama gaishe-gaishensu sannan Jay yay masa magana akan abinda ya kawosu, da tambayar miya faru bayan tafiyarsa?. Labarin komai Dr Bello ya basu, Jay ya dafe kai cikin takaici.
Shi dai Dr Bello haka kawai komai Jay yayi ƙyau yake masa da burgesa, haka ALLAH ke sakama bawa ƙaunar wani batare da wata manufa ba, yay murmushi yana kallonsa, “Karka damu abokina na haƙura indai nine, bansan ɗan uwanka bane dana barsa tun a ranarma baza'a kai hakaba saboda kai, naga rashin hankalin nasa ne yayi yawa shiyyasa naga gara aɗau mataki, amma yanzu kam yaci darajar mai daraja”.
Fuskar Jay ɗauke da guntun murmushi yace, “Nagode Doctor ALLAH yabar zuminci”. Shima Doctor godiya yaymusu, ya kuma rakosu har inda motarsu take, sai da yaga fitarsu sannan ya koma office yana kiran babansa a waya.
★★★★★
Tunda suka shigo police station ɗin aketa basu girma, kai tsaye office ɗin d.p.o suka nufa, inda acan ɗinma dai suka tarbi juna da girmamawa kafin a ɗaura da gaisuwar mutunci. Jay da kansa yayma d.p.o bayanin abinda ya kawosa, ya kuma nuna masa lawyer'n Qaseem ɗin da ya shigo a bayansu dan shi isowarsa kenan. A take anan aka kashe magana babu zancen zuwa kotu sannan aka kawo musu Qaseem. Babu abinda akai masa, dan ko hararsa babu wanda yayi tunda aka kawosa gurin saima girmamawa, ko kayansa ba'a cire masaba, sannan ba'a haɗashi da kowaba a cell.
Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Jay, kowa ya ɗauke nasa fuska a tamke, Jay ya fara miƙewa ya fice abinsa, hakan yasa Qaseem jan tsaki, rai a ɓace ya kalli d.p.o yace su maidashi cikin cell ɗin. Duk kallon mamaki suke masa, Jabeer da yasan wasan ya dafa Qaseem ɗin yana magana a hankali, kamar Qaseem ɗin bazai yardaba sai kuma miya tuna oho masa ya nufi hanyar fita Jabeer da lawyer ɗinsa suka take masa baya.
A jikin mota suka iske Jay tsaye yana magana da Engineer ɗin da zai masa gyaran gidansa da Bilkisu zata zauna. Suna isowa yana ajiye wayar dan sungama. Sake ma juna kallon ido cikin ido sukai shi da Qaseem, cikin ɗacin rai Qaseem yace, “Miyasa ka cironi? Minene haɗina da kai?”. Murmushin rainin wayeo Jay yay masa yana lasar lip ɗinsa na ƙasa, yaɗan ɗage gira cike da salo dukda idanunsa na cikin glass ne, hannayensa duka cikin aljihun wandonsa suke, Yace, “Inada business da kaine shiyyasa”. Wani kallon banza Qaseem yayma Jay shima, yace, “A kasuwa ka ganni?”. Jay ya sake murmusawa tare da ciro hannunsa yaɗan sosa gefen girarsa da ɗan yatsa yana karyar da wuya, “Karkai taurin kai, akwai tagomashi mai yawa da riba”. Qaseem yaja tsaki ya motsa zaibar wajen yana faɗin, “Zanyi maganin tsagerancinka ne yaro kwanan nan”. Cike da rainin hankali Jay yace, “Ai zuru batacin zuru, sai dai a haɗu ai zuru-zuru. Nabaka nanda kwanaki bakwai kacal zaka nemeni da kuɗinka ma”. Qaseem yay wata dariyar kai banzane ya wuce motar lawyer ɗinsa batare da yabama Jay amsaba....
Jawaad yay wani lalataccen murmushi yana zare gilashin idonsa, sai da Qaseem ya shiga motar sannan ya maida glasess ɗinsa yay salute ɗin motar da faɗin, “YANZUN MUKA FARA”. (Bari na ƙarasa maka jikan Yusufa🤣. WASAN😉).
____________________________________
Ƙarfe sha biyu da wasu mintuna na farka, ni kaɗaice a ɗakin, na sauka daga gadon ina addu'a da miƙa, naji daɗin jikina sosai gaskiya, rashin barci ai masifane. Wanka na shigayi, amma abin mamaki sai nai karo da Jini, cikin mamaki nace, “Jini kuma? To duka yaushe ma nai wankan tsarki? Kofa sati biyu banyiba”. Mamaki tamkar zai kasheni nai wanka na fito. Ina shiri ina juya al'amarin cikin raina. Shigowar Amaturrahman ne ya sakani juyawa na kalleta. Tai murmushi da faɗin, “Amarya saifa wani Shining kikeyi miye sirrin ne?”. Murmushin yaƙe na mata kawai bance komaiba, itama tai dariya kaɗan, “Kefa tuni na lura irin Marwah ce, muskilanci ya muku yawa, idanma an zauna hira daku daga eh sai uhm sai a'a kuka ƙware yi, badai haka za'aje anama Yayan namu dunɗun dunkum ba kamar hadarin maraice?”. Bansan sanda na ƙyalƙyale da dariya ba babu shiri, dan harga ALLAH taban dariya musamman yanda tayi da fuska sanda zatai maganar. Ta ɗagamin gira da cewar, “Ko kefa, gashi na sakaki kin dara, ki shirya muje Ummu na jiranki, yau dai tace sai taga ƴarta”. Naji daɗi a raina, sai dai ina ɗanjin tsoro-tsoro, nice yau zan gamu da Sarauniyar gagara badau gaba ɗaya, ni Bilkisu ɗiyar baba makaho da Asiya gurguwa, ALLAH sarki duniya, duk abinda kaga ba'a gani saboda ƙanƙantarsa wataran zai fito kowa ya gansa saboda girmansa, wataran kuma sai tsufa ya sakayashi, a ƙarshe mutuwa ta ɓoyesa. Tsaf na shirya da taimakon Amaturrahman cikin siket da riga na atanfa da sukaimin ɗas a jiki, dukda dai basu kama jikina ba, duk yanda tasi hanani na saka gyale kasawa nai saida na saka sannan muka fito.................✍
Barkanmu da dawowa, ina fatan kunyi weekend cikin ƙoshin lafiya😉😘😘😍😍😍😍.
Masu kira akan zasu sayi ƘWAI CIKIN ƘAYA!! bafa shi ake tallaba, muna tallar buks ɗinmune guda goma na zafafa gasunan, duk wanda bai sayaba ya motso ya saya karya bari romon daɗi ya wucesa🤗🤗🚴🏼
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[12/22/2020, 6:53 PM] HASNA✍🏻: ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO
Page 34
...................Katafaren falone daya amsa sunansa falo, komai yaji iyakar ji fiye da tunanin mai hasashe, ga wani sassanyan ƙamshi mai kashe lakkar jiki da tsaida gudun jini na tashi, lallai wannan baiwa ta isa a kirata sarauniya, ta haɗu tama gaji da haɗuwar, ga kwarjini irin wanda kowa yasan masu mulki dashi. Tana kishingiɗe ne amintacciyar baiwarta na gefenta da alama hira sukeyi, dan fuskokinsu dukansu ɗauke suke da murmushi, sai bayi biyu kawai a falon, ɗaya na tausa mata ƙafafu ɗaya na yanka mata tufa a ƙaramin filet. Sallamarmu ta sakata maido fararen idanunta kanmu, da sauri Amaturrahman ta tareni tana faɗin, “Gaskiya Ummu sai kin biya”. Murmushi Gimbiya Munaya tayi mai ƙayatarwa, cikin nutsatstsiyar muryarta tace, “Amaturrahman kin maidani kakarki a gidannan, nakula kema auren kikeso”. Da sauri Amaturrahman ta matsa gefe tana tura baki gaba da faɗin, “Ni ALLAH banason aure ina tare dake da Abbu da Mommah”. Dariya hadiman sukayi, nima dai murmushi nike, dan saita tunomin da Nabeelah. Gimbiya Munaya dake murmushi ta miƙomin hannunta da yasha adon jan lalle, “Kinga ɗiyata manta da wannan zo naji ɗuminki kinji”. Jikina har rawa yake saboda yanda tamin tamkar mahaifiya, na taka a sannu cikin nutsuwa gareta, durƙusawa nai kaina a ƙasa, ina faɗin, “Barka da rana Ummu”. Ina jiyo fitar sautin murmushinta, ta ɗora yatsunta saman haɓata ta ɗago kaina, “Nagode da wannan girmama ɗiyata, ALLAH yay miki albarka kinji, kiyi haƙuri da rashin ganina tun zuwanki”. Murmushi na mata ina ƙasa-ƙasa da idanu, dan bazan iya kallonta kamar yanda take kallona ba, nace, “Babu komai Ummu”. Murmushi ta sake yi, tare da zaunar dani sosai, ta sallami bayinta guda biyu, daga ni sai Amintacciyar baiwarta da kuma Amaturrahman data koma can cikin kujera tana kumbura wai ance za'a mata aure. itafa ta rantse bazatai aure tabar Ummu da Abbu ba. (Kujimin ƴa, to itama munayar ai sunƙumota Galadima yay daga gabansu hajiya innaro😂).
Cikin nutsuwa da hikima Gimbiya Munaya kejan Bilkisu da hira, abin gwanin sha'awa, babu wani nuna ƙyara ko izzar mulkin kasancewarta ƙasan ƙasa da ita, haka gimbiya Munaya take, bata yarda ƙasƙantar da waniba a rayuwarta, tace tasan ciwon ƙasƙanci, bazataso yima waniba, ita tasan wahalar da zuciyarta tasha lokacin da suke ƙarƙashin mulkin mallakar Innaro a gidansu. (hajiya innaronmu ta mutumci kwanciyarki lafiya cikin ƙasa matar Faruku😂🤗, karkimin fatalwa da daddare kuma yasin😤).
Yanda Sarauniya ta iya hira har bansan sanda nake bata duk amsar data buƙata daga gareni ba, har takai munyi zurfi sosai a hirar fiye dazaton mai hasashe, kiran sallar zuhur ne ya tashemu, muka koma ɗakinmu domin yi, nidai banyi yunƙurin yiba tunda naga jini a jikina dukda dai kaina a ƙulle yake.
Muna cin abinci kira ya shigo wayar Amaturrahman, ɗaukata cike da zumuɗi tana faɗin “Meenal kun tahone?” bansan mi akace mata daga canba naji cike da murna ta sake cewa, “Wlhy da gaske nake tana nan har sai lokacin tarewarta”. Daga inda nake ina jiyo ihunsu, itama ta miƙe tana rawa da ihu. Nikam mamaki suke ban, Amaturrahman irin tsagwaron izza da mulkinan na ƴaƴan sarakuna sam batayi, ko kiga tana wulaƙanta bayi tana takasu yanda takeso, abinda kawai na fahimta tarbiyyace daga iyayensu hakan, An nuna musu bayin gidansu mutanene tamkarsu masu daraja da mutunci, shiyyasa sam basa tozartasu.
Ban tambayeta su wayeba muka cigaba da ƴar hirarmu, dukda nifa dauriya kawai nake hankalina ya rabune kashi-kashi. Ba'afi mintuna talatinba saiga ƴammatan ranar da muka taɓa haɗuwa a Saloon tare da su Amaturrahman ɗin, Meenal da Amatullah, ashe tafiya sukayi shiyyasa ban gansuba tunda nazo. Suka rungumeni cike da murna, ni harma mamaki suka bani, gasu suma da shegen kauɗi, aiko yinin yau dai kaina har ciwo yake saboda surutunsu, amma zamana dasu ya ɗeben kewa sosai, sai nake ganinsu kamar su Ummie. Muna tare Zuhrah ta kira waya, yanda sukaji muna waya da ita tana tsokanata Amatullah ɗiyar Buzaye mai cike da sirrin ƙyau ta fige wayar ta saka a hansfree kowa yanaji, a cewarta suma yanzu ai ƙawayen Zuhrah ne, duk ƙawayena sun zama nasu suma.
Abin mamaki da daddare saina nema jini na rasa, baƙaramin ɗaure kaina al'amarin ya sake yiba, ni a ƴan kwanakinnan sam bama na ganema kaina, daga wannan al'amari ya wuce sai wannan, ALLAH na gode maka da wannan jarabawa, ya rabbi ka bani ikon cinyeta, ka ƙaramin haƙuri da juriya.
(Amin Sakwara🚴🏼)
____________________________________
“Nifa wannan wasan naku dariya yake bani kaida Qaseem Boss, gashi yanzu Mami ta sake tunzura komai ya ɗau zafi, shi bazai yarda da ƙaddara bane ba?”. Murmushi Jay yayi baice komaiba, sai ƙoƙarin saka waya da yake a kunne. Daga can Abbati yay sallama. Amsawa Jay yay suka gaisa. Yace, “Ina fatan yau zaka tashi aiki da wuri dan inason ganinka, banason kuma a wuce yau saboda muhimmancin zaman”. Daga can Abbati yace, “Babu damuwa, ai kama yanka akan gaɓa, dan inason na shigo namaka ta'aziyya dama, zan shigo bayan magriba da safe sai na wuce”. Jay yace, “Kai malam nifa yanzun ƙattai sun daina kwanarmin a gida inada iyali”. Ba Abbati ba hatta da Jabeer dariya ya kwashe da ita harda ƙyaƙyƙyewa, Jay ya mangarema Jabeer kai tareda ranƙwashi mai zafi, yace, “Kaima ɗan iska na wayar zan kamaka ne, masu zuwa lahira da ido ɗai-ɗai”. Bai jira amsar abbati ba ya yanke wayarsa. Jabeer dake sosa inda Jay ya ranƙwashesa yana tuƙi yace, “Oho dai, ai sa idon namu mai lasisi ne, ni nama taɓa ganin munafukin soyayya irinka?, ALLAH zan cema sarauniya karta bar Mami ta tare har sai kazo da kanka ka furta kana SO da hawaye”. Taɓe baki Jay yayi da kwantar da kansa jikin sit ya lumshe idanunsa, a hankali yace, “Idan namata ciki a waje saiku barta ta tare ɗin, koku bari