Showing 30001 words to 33000 words out of 388641 words
boss sun dawo gareshi, tarkon da makiya suka kafa ya buɗe”.
Jawaad da fuskarsa babu walwala ya girgiza kai kawai ba tare da yace komaiba ya buɗe mota yana musu nuni dasu shiga.
Basu ɓata lokaciba suka bar wajen zuwa gidan Jay ɗin dake Empty babu kowa ciki, gidan yayi ƙyau sosai, gashi anguwar da yake babu yawan hayaniya.
Suna shiga gidan dukkan farin cikinsu da suka danne da kewar juna sai ya bayyana, dan sake rungume juna sukai a tare kowa na faɗo yanda yay kewar ɗan uwansa.
Tsawon lokaci suka ɗauka a haka har Gimba ya dawo da ledojin abinci ba tare da sunsan zaiyi wannan ɗawainiyarba.
Godiya sukai masa duk da kuwa yana ƙasansu, ya nuna musu hakan ba komai bane tare dajin daɗinsa na murna da sukai, ya jajanta musu da addu'ar ALLAH ya kiyaye gaba.
Wanka suka shiga su duka a mabanbanta banɗakin dake cikin gidan, sun ɗauki tsawon lokaci, dan Jawaad ma harya fice zuwa wani kiran gaggawa daya samu daga office ya barsu akan kafin ya dawo su tabbatar sunci sunsha sun huta.......
______________________
BILKEESU
______________________
.........Har dare babu labarin bilkisu a cikin anguwar, ga kuma ƴan sanda ta ko'ina an bazasu nemanta, sai kuma yaran Jazuuga dasuma ke aikinsu domin taya ƴan sandan.
Ina cikin mankarar har dare, tun ina kuka da hawaye da murya harna koma na zuciya kawai nake iyawa, hankalina bai gama tashiba sai da na farajin motsin mutane masu shigowa sallar magriba, kuma nutsuwa nayi a wajen duk da ƙarfina ya ƙare, hannuna dafe da bakina gudun kar wani mai ƙarfin ji ya iya jiyo fitar numfashina.
ALLAH ya aramin wannan lokacin har akai sallar magriba aka kammala.
Sosai ƙarfina ya gama ƙarewa, na gaji da tsaiwar, burina kawai na zauna nahutama raina, ƙafafuna sunyi nauyi tamkar ba'a jikina sukeba, gashi wasu suna a massallacin basu gama ficewa ba, sun zauna har sai anyi sallar isha'i.
Haka na cigaba da dauriya a wannan yanayi mai wahalar musaltawa har lokacin sallar isha'i yayi ya wuce, mutane sun fara barin massallacin, inda akabar tsirarun da suka koma fita ɗai-ɗai.
Wani da ya fita na ƙarshe shida abokinsa naji suna faɗin ƙarfe goma da rabi na dare, bana a hayyacina zuwa lokacin sosai, amma bayan fitarsu da wasu mintuna saina leƙo kaina cikin massalacin, babu kowa sai mutum ɗaya dake barci, da gyar na tattaro ɗan sauran ƙarfina na janye mankarar na fito, tafiya nake tamkar bugaggiyar da tayi mankas da kayan maye, ni kaina bansan a ina nake jefa ƙafaba, tafiya kawai nake tamkar bahagon raƙumi.
Ƙwaƙwalwar kaina sam bata aiki da zuciyata, ni kaina na fara manta wacece ni?.
Ƴan sanda biyu dana hango gabana suna tunkaroni yasani firgicewa, nai saurin komawa baya na maƙale jikin bangon wani gida, ta gabana sukazo zasu wuce suna magana wadda na fahimci akainace.
Ɗaya a cikinsu ke faɗin, “Oga kana ganin Alhajin nan zai bamu maƙudan kuɗinnan kuwa daya faɗa inhar aikinnan ya kammala yanda akeso?”.
“Hhhh bayarwa kuwa zaiyi ɗan sambo, bakaga yanda yake a firgiceba, bashi da burin daya wuce akama yarinyar, sannan ɗansa ya kuɓta, shiyyasa nima nace muyi ƙaimi, dan inada tabbacin tana cikin anguwarnan bata fitaba, sai dai idan wani munafikinne ya bata mafaka a gidansa”.
“Shegun ba, ai zamu kamatane, idan kuma har kuɗinan suka tabbata lallai lokacin ƙara aurena yayi kenan, dan wlhy zama da kubra kawai nafi ƙarfinsa”.
“Hhhhhhh!! Wato ɗan sambo shiyyasa nake sonka wlhy, kai abokin neman arziƙine, idan kana abu sainaji daɗi saboda lallai kana kan tsarina, saikace uwa ɗayace ta haifemu”.
Dariya suka kwashe da ita tamkar wasu mahaukata su duka biyun, da wannan mahaukaciyar dariyar suka wuceni batare da ɗayansu ya hankalta dani ba.
Numfashi na sauke cikin gajiyawa, sai da na tabbatar sun ɓacema ganina sannan nacigaba da tafiya ina zirar da hawaye, wace irin ƙasa muke da ita hakane? Masu bada tsaro da kariya sune suka koma masu ɓata tsaro da zalunci?.
Ta yaya har muke tunanin samun shugabanni adalai bayan muma talakawan azzaluman junane?.
Nacigaba da tafiya ba tare da namasan ina nakeba, abinda na sani kawai shine nayi nesa da anguwarmu kam tabbas, sannan ina buƙatar zama na huta, sai dai tsoro da fargabar kar azo a kamani sun hanani damar samun wajen yada zango.
Nayi tafiya mai nisan gaske, wadda sam banida nutsuwar ƙididdigeta koda da ƙiyasine, tun ina gamuwa da mutane da kallon motoci a titi har garin ya fara ɗaukar shiru, bakaji koda ƙarar mashin, ƙafa tafara ɗaukewa, hakama motoci, lokacin da garin ya gama ɗaukar shiru babu abinda kakeji sai haushin karnuka.
Da ƙyar na iya kawo kaina wani wajen da nakeji sautin kiɗa na tashi, duk yanda naso samun dauriyar matsawa daga nan na kasa, cikin rashin kuzari da ƙarewar ƙarfi na zube jikin wata bishiyar mangwaro dake a gaban gidan, mashina ne birjik a wajen duk an faka, sai jefi-jefi na mutane dake fitowa daga wajen mace da namiji ko mata zalla.
Tun ina kallonsu har na gazama hakan, idanuna da sukai nauyi jingim saboda kukan da nasha na lumshe a hankali, badai barci nakeba, bakuma ina tare da duniyar mutane bane sam.
Tsawon lokaci ina a wajennan ba tare dana fargaba, sama-sama naji ana tadani, na buɗe idanu da ƙyar ina saukesu akan ƴanmata biyu da bazasu gaza sa'annina ba, sai namiji dake gefe yana faɗin, “Ƙila tasha abinda kanta ya gaza ɗaukane ko?”.
Ɗaya a cikin ƴanmatan da ke ƙokarin taimakamin na tashi tace, “Anya ma wannan kuwa bamma santa ananba sam, dan inaga baƙuwace”.
Kaɗan ɗayar ta ɗan haskani da fitilar wayarta rakani kashi, ta kautar da hasken daga fuskata tana cewa, “A gaskiya baƙuwace, dan nima bamma taɓa ganintaba a gidan wasannan”.
“Da wannan surutun da kuka tsaya da kamata kukai mukaje da ita gida, dan tabbas tana bukatar taimako” namijinne yay magana cikin nuna kulawa.
Basuce komaiba sai taimakamin da sukayi na miƙe tsaye sosai, ni dai ban iya cemusu uffanba, suka kamani a kafaɗinsu mukabi wani lingu.
Banwani damu da inda suka kawoninba, duk dama gidan tsitt yake alamar duk anyi barci, namijinne yasa key ya buɗe ɗakin suka shiga dani ciki.
Sun kwantar dani a katifar ɗakin wadda halin danake ciki baisa na fahimci komai akantaba.
“Ƴar daɓas kunna risho a dafa mata ruwa tasamu tai wanka, dan a halin da take ciki na fahimci bazata iya jin daɗin barciba”.
Da to wadda aka kira ƴar-daɓas ta amsa, cikin mintuna kalilan aka haɗamin ruwan wanka mai matsakaicin dumi, yanzuma da taimakonsu na shiga banɗakin dake a cikin ɗakin.
Ban cutar da kainaba na daure nayi wankan, naji daɗin hakan sosai, bayan nagama na ɗauki doguwar rigar da aka ajiyemin na saka sanann nayo alwala na fito, dan yin wankan yasa naɗan fara dawowa a hayyacina.
Zaune na iskesu sunacin nama, na ɗan kallesu na duƙar dakai ina faɗin, “Dan ALLAH ku taimakeni da abin salla da hijjab”.
Ganinai sun kalli juna a wani irin yanayi na shakku, ni saima na fara tunanin koba musulmai bane.......
Ɗayar ta katsemin tunani da faɗin, “ƴar uwa samun abin salla a ɗakinnan lallai babban abune, ke ama gidannan gaba ɗaya zance, amma dai ga ɗankwali idan zaki iya maneji dashi, hijjab ma inaga za'a iya samun wanda nazo dashi a farkon zuwa gidanan, tunda kuma na ajiyeshi ban sake waiwayeba”.
Ban fahimci zancen nasuba, bankuma tambaya ba, inadai tsaye aka bani hijjab da ɗankwalin, shinfiɗawa nai na tada salla, sai da nayi sallar la'asar da banyiba da magrib sannan nai isha'i, harma da shafa'i da wutiri, hannuna na ɗaga sama ina addu'a hawaye masu zafi na kwarara saman kumatuna, nakai tsawon lokaci ina kaima ALLAH kukana, kafin na miƙe.
“Wai, wannan salla taki akwai tsawo, zokici abinci muɗan kwanta, dan gari gab yake da wayewa”.
Yunwa nakeji, hakan yasa banyi musuba nai zaman cin naman da sukaci suka ragemin, sai fura mai sanyi wadda naji daɗinta sosai.
Ina kammalawa suka nunamin wajen kwanciya.
Sai a yanzune dana samu nutsuwa komai ke iya dawomin dalla-dalla, wasu hawaye ke sauka saman fuskata a gurguje, koyaya Firdausi take? Inna da baba da sauran ahalin gidanmu, na ɗago hannuna ina kallo zuciyata na wata irin suka, ni Bilkisu yau nice matsayin wadda tai kisan kai, wai ni na kashe mutum?....
Kuka mai ƙarfi ya ƙwacemin, nanfa na shiga rairashi babu mai lallashi, dan masu masaukin nawa bansan ya akai daga kwanciyarsu barcinsu yay nauyi irin hakaba, na daɗe ina kuka har aka kira sallar asubahi a kan kunnena.
Tashi nai cikin layi da nauyin jiki nayo alwala, nazo ina ƙokarin tashinsu amma sam babu wadda tai motsin kirki balle na saka ran zasu tashi, haka na haƙura saboda jin zan rasa sallah.
Koda na idarma na sake gwada tashinsu amma basu tashinba, nanma haka na haƙura, sai dai zuciyata na mamakin irin wannan nauyin barci haka?, nima ban fargaba barcin ya kwasheni a wajen.
★★★★★★
A daren ranar yaran jazuga suka dawo gidan da taimakon ƴan sandan nan, duk wani makami da sukasan sun ajiye gidan harda wanda Bilkisu ta gani da yawa a kwali randa ta kasa masa shara duk suka fitar dasu, kayan shaye-shayensu da duk abinda za'a iya kalubalantarsu dashi saida suka fitar dashi.
Hakama innar Firdausi sun fito da ita, asibiti suka kaita inda baba yake cikin wani yanayi da baki bai iya musaltawa.
Innar Firdausi ta fashe da sabon kuka saboda ganin halin ruɗani da mijinta ke a ciki, gefe yaran Jazuga sukaja baba da inna, suka shinfiɗa musu dokoki tare da gargaɗi mai tsoratarwa.
A tsorace baba da inna suka amince kodan son tsira da ransu.
Alhaji Lado yace, “Zamu baku ƴarku mu canjata da gawa, munaso kuyi nesa da garinanma gaba ɗaya, koda sau ɗaya naga masu kama daku na rantse saikun mutu dukanku, bayan na gama gallaza muku azaba mara musaltuwa, sannan koda wasa kuka taimaki yarinyar data kashemin ɗa wlhy kuma saikun mutu, dan daga yanzu dukkan motsinku zai cigaba da gudana ne a kan idona”.
Cikin kuka baba da inna suka amsa.
A munafurce aka fiddo firdausi da taimakon likita da shima aka toshe bakinsa da kuɗi, tare da yaran Jazuga da ƴansandan nan.
A wata mota aka sakasu harda Firdausi da har yanzuma bata farfadoba, sai dai raunikan jikinta duk sun sami kulawa.
A wannan tsohon daren aka nufi asalin ƙauyen su baban Firdausi dasu, sunaji suna gani, suna kuka da ɗunbin tausayin Bilkisu da tunanin tana cikin wane haline? Wane kuma hali zata iya shiga daga nan zuwa safiyar gobe.............✍🏻
https://www.youtube.com/channel/UCl9IGLUXrqUtta-Tjmhoo7Q
*_MANHA HAUSA NOVEL'S_*
_Maza garzaya domin bada gudunmawarka kaima, dan ALLAH a danna mana subscribing, tare da bibiyar shirye-shiryanmu masu ƙayatarwa a koda yaushe, harma da tsaftatattun littatafan hausa masu ƙayatarwa da zasu dinga zuwa muku a Audio, yanzu haka ƘARAYAR ARZEEƘI ya fara sauka, garzaya kar ayi babu ku😉🥰🥰🤝🏻._
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_**_Typing📲_*
*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_
*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na goma sha biyu_
*______________________________________*
............Tun a farkawar da nai a wannan barcin safe da yay nasarar saceni na fahimci lallai ƙaddarar rayuwa ta sake jefoni wani rukunin ajin karatun, dan kuwa babu tantama gidan nan na karuwaine. Wasu hawaye masu ɗumi suka gangaro saman kumatuna, ban damu da sharewa ba na barsu suna cigaba da kwarara tamkar an buɗe fanfo.....
“Baƙuwarmu kina ganin kuwa kukan nan bai isa hakaba?”.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka taimakeni ta faɗa tana janye hannun da nai tagumi dashi.
Idanu na ɗago na kalleta, ƙyaƙyƙyawace, sannan yarinya shakaf da shekarunta bazasu gaza kamar nawa ba, banbancina da ita kawai jikinta a murje yake alamar akwai jin daɗi tattare da ita, na sauke ajiyar zuciya ina kauda idanuna daga gareta ba tare da na ce uffanba.
Ɗayar data shigoce ta katsemu da faɗin, “Sweet gafa Laran gabas can nayi dake akan wasan jiya”.
Ƴar daɓas ta kwashe da dariya tana zama a bakin katifar, “Bar shegiya kinji Sweet, itadai ai bariki iyawace, kowa kaga yazama wane ya iya allonsa ne, idan ta isa itama ta iya wanke nata”.
“Kamar kuwa kin shiga zuciyata Sweet, dan nima haka nace mata”.
Kusan a tare suka taɓe baki, Nazy ta juyo indomie daga cikin tukunya tana ajiyewa gabana, “Sorry bakuwarmu mun barki da yunwa, kinga abincinki nan tun ɗazun tsumayen tashinki mukeyi, kinfa sha barci, saikace wadda bata samun isashen barci daga inda ta fito?”.
Murmushin yake kawai na mata, sai dai ban iya cemata komaiba itama.
Ƴar daɓas tace, “Nikam badan jiya kinyi magana ba da nace kodai ke kurmace, ki daure ki amsa mana tambayoyinmu kafin Uwargida ta shigo gidan nan, dan in bata fara samun wani bayani daga garemu ba zamu fuskanci matsalane akan kawoki, kodai kema rayuwace ta nuna miki hanyar zaɓar ƴancin kankine?”.
“Neman ƴancin kai kuma?”.
Cikin tsagwaron mamakin daya mamaye fuskata nake jefa musu tambayar tawa.
A tare suka ɗagamin kai, Nazy ta washe haƙora tana cewa, “Ai duk macen da kika gani a gidan nan tazone domin samun ƴancin kanta, sai dai kisamu banbancin dalilan da suka nuna mana hanyar hakance nasararmu”.
“Wata sabuwa kenan”. na faɗa a fili batare dana saniba.
Atare suka maimaita abinda na faɗa ɗin, suka ɗora da faɗin, “Miyasa kikace haka? Kina ganin hanyar da muke bata dace da tsarinkiba kika fito da ga gidanku?”.
Murmushi nayi ina lumshe ido, wasu hawaye suka sake ziraromin, hannu na saka na sharesu a karo na farko, na kallesu sosai cikin matuƙar tausayawa kanmu, “Ni ba wannan harkar nazo yiba, ƙaddarar rayuwace kawai ta kawoni cikin taku ƙaddarar”.
Shiru duk sukayi suna kallona, nima ban sake cewa komaiba na zame na kwanta ina cigaba da kukana, tsawon loakaci muna a haka babu wanda ya sake cewa komai, sai zuwa can ƴar daɓas tace, “To ki daure ki tashi kici abincin, sannan idan bamu shiga rayuwarkiba dan ALLAH ki bamu labarinki”.
Shiru ban motsaba, bankuma iya cewa da ita komaiba, babu abinda ke sukar zuciyata sai halin dana bar ƴar uwata Firdausi a ciki tare dasu Inna, saiko kisan Jazuga danai da hannuna, na ɗago hannuna ina kallo, wasu sabbin hawayen suka sake ziraromin, jinake inama ni Jazuga ya kashe, dana huta, koba komai zan kusantu da iyayena, na rushe da kuka mai sauti ba tare da nasan muryata tayi ƙarfi irin hakanba.
Akusan tare sukai kaina suna tambayata lafiya?, yanzunma dai basu iya samun amsaba daga gareni har wata mata ta shigo.
Barina sukai duk suka juya gareta, cikin matukar ladabi da girmamawa suka shiga gaishe ta.
Amsawa take a dake, yayinda idanunta ke a kaina ko kyaftawa batayi, batare data ce musu komaiba ta nunani da ɗan yatsa.
Nazy ce tai saurin faɗin, “Uwargida baƙuwace da jiya muka taimaka a ƙofar gidan wasa, Babu ne kuma ya bamu ƙwarin gwiwar hakan, yakuma sanar mana zai faɗa miki da safe”.
Shiru bata amsa ma Nazy ba, sai takowa