Showing 30001 words to 33000 words out of 226733 words

Chapter 11 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

7957

fada fada hakan ya sakata kikifta ido tana kallonsa

Watau tunda aka kawota gidan nan aka nuna mata dakinta rabonta da wani abun mutunci ya hadata da mutanen gidan
Wanu gani gani suke yi mata a bayane kuma sukan yada mata magangannun da ta ajiye haka aa matsayin dama tana iya fuskantar irin haka ko yayane, ta share kowa ta ringa farin cikin gannin ta waye a gidan miji itama
A hankali awani dake shigewa ya saka ta fara damuwa da rashin gannin mijin nata a bangarenta
Ba dan ta saba ko ta matsu da wani abu ya shiga tsakaninta da SUDAIS ba, ko daya , hasalima ita ba taba yi ta yi ba sannan bata cikin jinsin yan matan dake kwalafa ransu da abin nan , kai tanama iya cewa ita halitarta ba ta d'a namiji bace sam, aman kuma sai ta ringa jin ya dace ace mijin nata ya zo inda take ko dan ya ji yaya ta kwana yaya ta tashi

Kwanon abinci daya ne ake miko mata tun na safe sai wata safiyar wanda ta ajiye haka a matsayin sunna tunanin tana girki da kanta ne kila, bata san mutanen gidan na girki sau biyu ne kadai a wuni, lokacin dorin na biyu kuwa ba'a kawo mata sam!
Bai neme ta ba, bai nemi inda take ba, sai dai ta hango giftawarsa ko ta ga wata yar budurwa mai yawan zama da zumbulelen hijab har kamar ya kayar da ita na ajiyewa SUDAIS abinci shi kuma ya dauka ya ci
Bata taba sannin cewa SUDAIS yana cikin jerin mazan da suke dauke da fushin rayuwa ba dare ba rana ba'ai masu komau bama bale irin abubuwan da matar malamin da ya daura aurensu ta fada wanda ya sake bincikawa ya ga eh gaskiya ne ya saka shi kulatarta a zuciyarsa sannan ya yi niyar yi mata kishiya kwana kusa dan ya horata kuma ya dauki budurwa da fari koda zai iya kusantarta

"Ki bani amsa mana ina maki magana" ya sake fada a harzuke hakan ya sakata mikewa tsaye tana kallonsa ta ce" Ka ga, ka sasauta fushinka ka saurareni mana SUDAIS, eh na taba yin aure wannan gaskiya ne"

"Kin taba yin aure ko kin yi aure aure ana sakinki daga an daura maki?, Kennan gaskiya ne matsalar biye biyen mazan ne kema ke damunki ake sakinki aure? Idan wanu ya sake ki dan ra'ayi wani ba zai sake ki ba dan jin dadi, SHUWWAR kin ha'inceni kin rufe ni kin saka da aureki a rufe ko?"

Gabanta ne ya fara faduwa gannin kamar abun na nema ya zama baba, hakan ya sa a birkice ta shiga kokarin ganar da shi abubuwan da sula faru tana mai sasauta muryarta a kan rasa tana mayyar da fushinta gefe ta ce" Haba my SUDAIS, ban kawo maka maganar auren da na yi a baya bane dan babu wanda na tare a cikinsu, babu wanda na je na dora tukunya a cikinsu, SUDAIS hasalima auren kawai ake daura min *ALK'ALAMIN K'ADARRARTA* na datse igiyoyin auren nawa ba tare da na kasance mace a gidan miji ba, ka yi hakuri dan Allah idan hakan ya bata maka rai, maganar auntynama gaskiya ne, idan ka kula fitarta da dawowarta kan sakani a hali na bacin rai da tashin hankali, aman duka wannan baa matsala bane tunda ni bana aikatawa"

SUDAIS dake kallonta yana dane wayarsa dake ringin ya ce" Me zai tabatar min da kema ba hakan bane SHUWWAR?"

SHUWWAR ta sauke ajiyar zuciya tana fadin" Domin ni budurwa ce SUDAIS...." ta idasa fada tana sada kanta cike da jin kunyar furucinta

Shima sai ya samu kansa da kureta da kallo, maganar da ta fada na neman yin tasiri a kwakwaluwarsa ya ce" Kina nufin, baki taba wata mu'amala da wani namiji ba a duniya?, SHUWWAR ina iya ganewa fa da zarar na kusanceki"

Kunya ta hanna mata amsa shi, tana ra karra sada kanta aka kuma doko masa wani kiran, hakan ya sa ya amsa yana dubawa da dan sauri domin mahaifinsa ne

Abinda baban nasa ya fada ya saka shi mikewa tsaye a rikice tana fadin" camp din sojoji kuma? Aba kuma SHUWWAR SHUWWAR tawa aka ce? Me ta aikata da har za'a turo daukanta zuwa camp din sojoji?"

Cikinta ne ya juya a zaunen da take hakan ya sa ta kafeshi da ido tana son fahimtar abinda ake fada masa a cikin wayar nan tasa

Wayar ya kashe yana kafeta da ido ya ce" SHUWWAR me ya hada ki da motar sojoji aka zo daukanki har cikin gidanmu? SHUWWAR kin kuwa san darajar mahaifina a garin nan? Motar sojoji du irin yadda yake kare mutuncin kansa da ta iyalinsa yau a zo nemanki me kika aikata?"

SHUWWAR ta mike a rikice tana kikifta manyan idannuwanta ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une motar motoci kuma? Me mes na aikata dan Allah?"

Gannin kamar raini irin na Shuwwar karra ci gaba yake yi a wajensa ya saka shi miko mata hijab dinta yana fadin" wuce mu tafi domin Aba ya tafi ba yau ba ya kuma nemi alfarmar kar a dauke ki a bayan mota zan kaiki, wuce mu je idan wata jarabar kika janyowa kanki cen ki karata, SHUWWAR ba zan boye maki ba na fara tsintar dana sani a aurenki da na yi"

Sosai magangannun suka soketa aman kuma sai ta hadiye ta bi bayansa cikinta na ta kukan tsoro da tunanin uban me ta yiwa soja kuma ita?

Ido ido ake yi a dakin bayan jin magangannun da suka bayana masu ga kuma wanda ya saka aka dauko sun yana zaune a hakimce tamkar wani sarki yana kallon su

Takaici, bakin ciki, tsana bata taba tunanin zata ji a kan wata halita irin yadda lokaci daya ta ji a kan wannan bawan Allahn

A rikice ABDUL Mutalab ya ce" SHUWWAR da gaske wannan mijinki ne?, Aman ai aunty ta bani wata uku ta ce zaki gama ida hankalinki ya kwonta sai mu je mu yi tambaya idan har kin halata a gareni na aureki ko? Shine kika yi aure ban sani ba?, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une"
Ya karashe yana mai fashewa da kuka lokaci daya mahaifinsa da Mahaifin Sudais suka kwashi salalami sunna kallonsa
Mai shinkafa ya kai masa rankwashi yana fadin" Kai dan ubanka ni fa na aureta, muhadu rasululahi sallalahu alaihi wa salam dama ana haka aa hausa?"

Mahaifin Sudais ya ce" Elhaj Mustafa dama itace na halarci daurin aurenta a kofar gidansu da kai?"

Mai shinkafa ya gyada kansa yana fadin" Allah ya taimaki malan ai wannan da kake gani nine na aureta , a lokacin da na fuskanci wacece marikiyarta na saketa dan ba zan iya hada zuria da ita ba, shine ta min dibar albarka da maganar kudin nan da yalabai Maman sani ya yi bayani a kansu ta dauko su a dakina a gidana , ni kuma sai na ba yaron nan salahun ya maka min ita a wajen sojoji a amso min hakina kar ta kashe, ashe ka ga yaron nan daya da na malaka ya hadu da sharin mace wai ya taimaka mata kar a rufeta ya ce matarsa ce? Ka ji yadda aka yi, a ranar da aka daura mana aure......................." Baki daya abinda ya faru mai shinkafa ya kwashe ya sanar dala dala wanda hakan ya saka MUHYIDEEN dake sauraro jin takaici a zuciyarsa domin shi du a tunaninsa sato kudin ta yi shi yasa ya sake bi ta kanta dan idan har satowa ta yi ya tabata ba ita kadai bace barauniyar ba zara rasa yan tayata aikata satar ba, da ya samu reshensu kennan da ya more ya ringa kamo su daya bayan daya, aman abin takaici sai yake jin wannan tsohon shi ya dauko mata kudin da kansa dan bashi da gaskiya ba wani dan yana tsoron taa masa shari ba

Da wani takaicin ya mike yana daukan wayarsa ya kalli Lieutenant Maman Sani da ya sara masa yana fadin" Ashe bata lokaci ne, ka bata takardarta ka salame su, bara na shiga cikin gari"

Daga haka ya zagaye ya yi tafiyarsa ya bar Lieutenant Maman Sani da alkakai domin a lokacin Shuwwar ta yi saurin matsawa kusa da mijinta tana doke hannun Abdul da ya matso yana rike hijabinta yana fadin" Ki ce ya sake ki ni kike so ba shi ba"
Ta ce" Elhaj yanzu saboda kudin da ban ci ko ficika a cikinsu bane ka saka aka daukoni aka kawoni nan a gaban mijina da mahaifinsa kana neman wulakanta min aurena? An fada maka duniya irinka ce da banda san kanka babu abinda ka iya?, Allah sai ya saka min fadan da ka hadani da mijina a kan shirme"

Da dan karfi ya ce" To rasa kunya, to uwar mararsa kunya, an fada maki ni na neme ki ne? Wanda ya fitan nan shi ya sa aka kawo mu baki dayanmu nan ba wani ba, ni na neme ki? Haba SHUWWAR ko a hanya ai bana tunanin fatan haduwa da ke, Kai abdul idan ka kuma tabata zan tsine maka albarka, hala hauka make zan hada jinni da wannan yarinyar?"

SUDAIS kam wata ajiyar zuciya yake saukewa saboda jin abinda ya faru, shi fa dadima ya ji cewar da gaske ne ashe da ta ce maza babu abinda ya shiga tsakaninta da mazan da take aure duda matar Malan ta ce barinta hudu

A sanyaye ya ce" Allah dai ya sanyaya, in sha Allah zan kawo maka kudin da kaina a yi hakuri Sir mu koma gida"

Mahaifinsa da mamaki ya ce" Ku koma gida? Ku koma gida da wa SUDAIS? Kana nufin nima zan ga kashi da rana da dare na zo na saka kafa ne? Kana ganni dai a gabanka komai yake faruwa ba wai fada maka aka yi ba, a gaskiya wannan ba uwar jikokina bace, nima kai daya ne namijin ba zan iya wannan saken ba, ka bata takardarta ka dawo gida, idan ka ki aikata haka zan yafeka duniya dan na kula bata yiwa maza da sauki ga Elhaj da dansa ana kace nace bayan mu da muke abokanan kasuwanci mun san irin biyayar da ABDUL Mutalab ke yiwa mahaifinsa?"
Yana gama ya mike tsayinsa yana yiwa sir salama ya fice a office din

A haka Mai shinkafa yaa tisa keyar nasa Dan dake tirjewa suka fice suka bar SUDAIS da matarsa da sukai mutsuwar tsaye

Yana juyowa gabanta ta zube gwuiwoyinta kasa tana hada hannayenta bibiyu ta ce" Dan Allah, dan Allah kar ka yi, kar ka sake ni, kar ka yi mugun aikin nan, ka bari mu fadawa malan su hadu da datijawan anguwarmu su je su ba Aba hakuri na tabata zai dangana ya barmu mu yi aurenmu, SUDAIS ina sonka kar ka sakeni, kar ka mayar da ji bazawara dan Allah"

Tana fada hawayenta na barkewa a saman fuskarta, hannayenta a hade wahe daya ta yada suke bari ba ji ba gani

Dukawar ya yi shima yana mai janyota jikinsa da karfi ya rukunkumeta ta yadda har sai da ta ji kamar numfashinta zai dauke
Muryarsa na rawa ya ce" SHUWWAR, dan Allah ki yafe min, mahaifina ne, idan ya yafeni duniya ba zan ga da kyau ba, SHUWWAR saki halal ne sannan a kan dalilin da ya dora kalmar sakinma abin dubawa ne , Shuwwar ina son ki, sonki ya sa du irin abinda matar Abanki ta fada na jure na so zama da ke , SHUWWAR aman abana fa?"

Kai take girgizawa hakan ya sa Lieutenant Maman Sani cire kansa a kansu cike da jin tausayinsu baki dayansu domin a lokacin SUDAIS sake riketa ya yi a jikinsa sosai daidai MUHYIDEEN ya shigo office din dan daukan takardar da aka fitar masa ta GPS din garin

Turus ya yi yana kallon wani sabon salo a office dinsa daidai lokacin da SUDAIS ya furta mata kalmar saki daya tak sannan ya janye jikinsa ya fice da mugun sauri har kamar ya kifa a kasa

Idasa faduwa ta yi a kasan tana mai dora hannayenta bibiyu a saman kanta zara kuma rushewa da wani kukan ta hadiye sakamakon Lieutenant Maman Sani da ya matso yana neman taimaka mata ta tashi ta tafi domin Sir ya dawo office din kar ya yi fada duda yakan hukunta ne a maimakun fada

Da karfi ta janye jikinta har tana doka bayanta a jikin table din tana sauke masa dukan kallon tsana a saman fuskarsa a kausashe ta ce" Dont tuch me!"

Lokaci daya kuma ta kama ta mike tanaa cire hijab din jikinta domin ji take ya shake mata wuyanta bata ita numfashi

Kudin daje ajiye wanda cenji ne aka dawowa da MUHYIDEEN da ya yi aika wanda baima san an dawo masa da cenjin ba ta mika hannunta ta dauka ita kanta bata san ko nawa bane ta juyo da jiyar ficewa a office din sukai ido hudu da Muhyideen dake sake kallon iKon Allah

Kallon sama da kasa ta masa wata wutar tsanarsa na sake ruruwa a zuciyarta taa budi bakinta ta ce" Ka sa an sake ni, Me na yi maka ne?, Shi yasa na tsani soja a duniya, bawan Allah da zan ga kana ci da wuta sai dai na karra petur ! Ka ga sai nake ji na tsaneka har kasan raina!, Walahi i hate u so much!"

Maganar da take yi a sanyaye ne, haka kuma tana yi ne wasu hawaye na zubowa a saman kyakyawar fuskarta da ta fara rinewa da ja

Da sauri Maman Sani ya so tsawatar mata aman sai ya dakata sanadiyar daga masa hannu da LIEUTENANT GANARAL ya yi yana kallonta har ta gama ta fice da slifas dinta bakake ta fita a office din sannan ya kalli Maman Sani sai kuma ya cire dubansa ya karasa ya dauki takardarsa ya juya ya fice yana tunai kamar haka' Me na yi mata ta tsane ni ita kuma wannan?, Ko bayan sata, karya, kuma mahaukaciya ce?......kai Allah ka shirya matan garin nan"


A kafarta take tafia tana langui bayan babu abinda ta sha

Tafia ta yi mai tsayin gaske kafin take samun kanta a bakin titi

Tsalakawa ta yi ta dauki wata hanyar tana tafia har ta karaso daidai wani babam waje da aka rubuta *BAR* a jikin katon plake din dake kafe

Samun kafafuwanta ta yi da janta suka sakata cikin wajen duda irin mutanen da take ganni da shiga irin ta shirme bata wani ankara ba har ta karasa gaban teburin masu siyar da abubuwan da ake siyarwa a wajen

Kudin nan na hannunta ta ajiye a saman wajen tana yin dadage ta haye saman doguwar kujera tana kallon Barmans din ta ce" *GIYA NAKE SO* "







😭😭😭😭😭😭😭😭 YA SALAM, MENENE LAIFIN IBTISAM NE? ME YASA IYAYE SUKE MANTA KALMAR JIN KAI SUKA RIKI SON KAI? ME YASA BA ZA'A FUSKANCI RAYUWAR BAYIN ALLAHN NAN DA DUBA NA FAHIMTA BA? SHIN IDAN SUN ZAMTO KARIN BATA GARI MAIMAKUN GYARA GARI FADUWAR IYA SU TA SHAFA? TO BARI KU JI YA KU YAN UWANA, FADUWAR TA SHAFE MU NE MU DUKANMU, DOMIN IDAN KARUWANCIN SUKA AFKA Y'AYANMU NE, MAZAJENMU NE, YAYUMU NE, MAHAIFANMU NE ZASU FADA A TARKONSU SU , SAI WANDA ALLAH YA TSALAKE, IDAN SHAYE SHAYEN SUKA FADA Y'AYANMU NE, MU KANMU NE ZAMU IYA FADAWA A KOWANI LOKACI, SHIN BAMA JIN KUNYA NE? BAMA JIN TSORON ALLAH NE? KO MU MUN FI KARFIN *ALKALAMIN KADARRA* YA BI TA KANMU NE? ........YA LILAHIN SAMAWATI WAR ARDI WAMA BAINA HUMU RAHAMAN, YA JILJALALI WAL IKHRAM, KAA DATAR DA MU DA SAMUN DACEWA A CIKIN DATATUN BAYINKA 😭👏👏👏👏








tuntubeni ta number wayata +22793811618 dan samun naki hajiata😍😍😍😍😍😍😍Numfashi ta sauke tana fadin"kar kanwarta ta ce"💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥


*The Hero writer*


*SAJIDA*


_Bismillahir rahamanir rahim_


PAGE:. 1️⃣2️⃣



*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*






*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*


*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*



*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*



*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*





Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.


*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login