Showing 162001 words to 165000 words out of 226733 words

Chapter 55 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

7949

mabarata an bi a gagaje komai?"

Fuskantar inda zancen ya nufa ya saka Maman Muhay kaiwa saman kujerar tana fadin" Toh Fah "

Shima MUHAY din sai ya so juyawa ya bar dakin fuskantar da ya yi kamar abin shi ya shafa, sai dai bai kai ga fita ba matar ta Dad ta dora da fadin" Ka duba ka gani yau a cikin gidan nan Madafa ta zame mana abin hange muna ji muna gani ta fi karfinmu, wai ita da uwar matar d'anta sun gaje madafa gaba dayansu sunna ta dafe dafe , an fitar da kayan abinci an yi mana almubaranci a cikin gida an watsar da komai har ana zubawa ana mikawa makota wai su a saudiya haka ake ana sadaka sosai wa makota, mu za'a nunawa sadaka ne ko so ake a nuna mana ba'a san zafin abin ba?, To gaskiya ba zan yarda ba ni kam na gaji walahi na gaji, nan Jet din dake malakinka ne yaron nan ke bulaguro a cikinsa da iyalinsa mu kuma sai dai mu bi mota mu sha wahalar zama, Elhaj kawai ka daidaita darajar kowata mace a gidan nan gaskiya"

Yadda zuciyarsa ke zafi gaba daya sai ya ringa jin har wata zufa na neman keto masa a tsayen da yake yana kallonta

A hankali matarsa ta tsakiya ta budi bakinta ta ce"💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥


*The Hero writer*


*SAJIDA*


_Bismillahir rahamanir rahim_


PAGE:. 5️⃣8️⃣



*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*






*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*


*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*



*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*



*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*


*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618


Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰










A hankali matarsa ta tsakiya ta budi bakinta ta ce" Haba hajia, me yasa kika cika zafafa abu ne wai a rayuwa?, Yanzun wannan ai bai dace ace kece kika yi wannan abin ba kamar wata yarinya karama?, Me ya tauye mu a gidan nan? Ko mu mun ce zamu kawo bakin ne ya mana iyaka da dukan wajen da muka so ajiye su?, Ko ya taba hanna mana abinda zamu dafawa bakinmu ne? Haba hajia kece baba a gidan nan aman kuma kece mai yon wasu abubuwan da basu da dadi, kar ki manta ke ya dace ki koya mana kyawawan dabi'u fa"

Sai da ta bari ta kai karshe ta debeta da ido ta watsawa kasa ta ja uban tsaki tana fadin" Kin san ai ni ba munafuka bace da zan tsaya yin kumbiya kumbiya a kan abinda yake cikin zuciya na ringa munafuntar kaina da kaina sannan na munafurci mutanen dake tare da ni, sai ki rantse da wanda ya busa maki numfashi cewar abin nan baya ci maki tuwo a kwarya, bafa wani abin boye boye bane, abu ne na gaskiya wanda yake abin a duba, ba maganar bakin ciki sai magamar gaskiya, dan haka na kawo kukana idan zaman adalci ake yi a gidan nan a duba min"

CHIEF OF ARMY haka jikinsa ke rawa yana tsaye yana kallonta

Maman Muhay ta girgiza kanta dake kasa a sanyaye ta ce" Allah ya baki hakuri, sai da ya so ya kaisu wani wajen mune muka hanna, bamu san hakan zai hadasa wata matsala ba, aman in sha Allah idan har yayan ya amince sai su koma wani wajen, hakan ba zata kuma faruwa ba"

MUHYIDEEN ya yi dan murmushi mi ciwo yana sada kansa da hayaniyar da ake yi a hankali ya furta" Allah ya sanyaya "
Sannan ya mike ya fice a falon, domin wannan dai ba huruminsa bane, koma menene zasu daidaita kansu ne tsakaninsu

Yana fita CHIEF OF ARMY ya juya ya nufi dakin barcinsa yana fadin" Idan kun fita ku rufe min kofar "

Da wani bakin cikin ta raka shi da kallo hakama sauran
Sosai damuwar yannayinsa ya kama Mama, aman kuma na zata taba yin gigin zuwa a yanzu ba domin wata fitinar take ita hadasawa kanta, dan haka ta mike ta nufi bangarenta tana tunanin sanadiyarta ne ake son saka masa hawan jini ko me? In sha Allah ba zata basu damar su wulakantashi ba, in dai a kan bakin yaronta ne zata je da kanta ta gyara masu wani wajen ta kawata masu yadda zasu ji dadin zaman


MUHYIDEEN na dawowa wucewa ya yi ciki ya rufo kofarsa ya zauna bakin bed hadi da dafe gaban goshinsa

Sai kuma ya tashi yana watsar da tunanin ya dauro alwallah ya dawo ya shiga gabatar da shafa'i da wuturi dan gaba dayama ya manta da Shuwwa da barci ya kwasheta a saman doguwar kujera lulube da bargonsa, yana gamawa ya yi kwonciyarsa ya shiga neman barci

_____________________________________

Da sasafe tun kusan karfe shida Dad ya bar gidan, cikin shirinsu na kaki yau ba tare da ya nemi kowa ba sai sojojinsa masu bashi tsaro

Cen kusan karfe tara kira ya samu MUHYIDEEN daga baban ofishinsu daga shugaban kasa cewar yanzu yanzu ana nemansa, hakan ya sa da gagawa ya diro ya shiga shiryawa a gagauce ya saka kaki dinsa ya fice da mugun sauri yana dan daga mata hannu a lokacin da take fadin" Yalabai ina kwana" ya wuce ya tafi Wajen da ake kiransa

Kusan karfe goma sha daya zuwa sha biyu jiniya ta ringa yi a cikin gidan wanda ko barci kake yi dole ka farka ka fito ka ga abinda yake faruwa a gidan
Kusan kowa yau sai da ya fito a tankamemen balbalin gifan na CHIEF OF ARMY, harda y'ayansa da matayensa da ma'aikatansa baki daya kowa ya fito harda su Malan, wa'inda basu fito ba kawai mahaifin SHUWWA ne da mamanta, summa aban nata ne ya hanna su fitar dan ita ta so ta fito din ya nuna aa gidan sojoji fa suke ko ba komai ai ba za'a rasa jiniya ba

Wuleliyar motar dake parrke ba'a bude ba zagaye da sojoji kowa ya fi kallo, har CHIEF OF ARMY ya fito a motar da yake yana murmushi ya shiga fadawa kowa wanda yake ahalinsa, iyalinsa da bakinsa cewar su karasa baban falonsa da aka bude aka basu damar shiga

Kowa na kallon dan uwansa ne, aman kuma ba damar yin musu ko tambayhar ba'asi, sshigar dai kowa ya yi dan sun fuskanci koma meye abu ne da ya shafe su

Bangaren da iyayenta suke ya je da kansa ya yi salama ya nemi alfarmar su karasa falonsa
Suma din sun karasa din ba tare da musu ba sun kuma zauna a saman kujerun da aka nuna masu kowa ya yi tsuru yana saurare

A hankali Shuwwa ta dunguri Nahidt kasa kasa ta ce" Ke wai me aka yi ne?"

Nahidt ta daga kafadunta itama kasa kasa ta ce" Ko dai am daura min auren ne da Malan za'a mana nasiha? Ko kuma auren ne za'a daura? Baki ga yau Aban naki sai kyalin amarci yake yi ba?"

SHUWWA ta girgiza kai tana janye hijab dinta baki wanda ya kai mata har kasa mai hannaye da zif ta ce" Allah dai ya sa ba wani abu ya samu katona ba gaskiya, dan na fara tsorata ban ganshi ba a hargagin nan, matsalar auren soja kennan , su ko makotaka kake da su zakana gannin fitintinu ne kala daban daban, ni gaba dayama na rikice"

Fausy kasa kasa ta ce" Kin fola ne?"
Shuwa ta girgiza kai ta ce" Ba maganar folawa, munma saka ranar rabuwa, kawai dai katon akoy shiga rai ne, inaga sai abana ya tofe ni da adu'ar dangana"

Dan murmushi ta yi zata bata amsa katuwar muryar wani sojan yake sanar masu *CHIEF OF ARMY* zai shigo

Basu wani damu ba dan sun san ai Dad ne zai shigo kuma an saba yi masu wannan shelar, kowane dai na dan sha'aninsa, aman kuma hankalinsu na kan kofar shigowar

A hankali ya bude kofar ya shigo da salamarsa da kuma muryar nan tasa mai rikita kwonya
Gaba daya idannuwa ne suka sauka a saman kansa
Lokaci daya dukan wani wanda ya gane kalar kakin dake jikinsa da galolin dake kafadarsa da gaban kirjinsa ya mike tsaye yana mai zuba masa ido, har Dad ya bayana a bayansa cike da murmushin farin ciki kafin ya bayana a gabansa da wata chemise blu mai dauke da takardu a hannunsa
Mutanen falon ya sake waigowa yana kallo a lokacin da Shuwwama ta mike tana fadin" Bari dai mu tashi muma kar aje wani abun ne za'a yi" domin ita dai bata san meye ake nufi da hakan ba, aman kuma yannayin MUHYIDEEN ya saka ta kure shi da ido har ya sauke dubansa a kan mahaifiyarsa wace jikinta ke rawa tana kallonsa cike da tsoro da kuma wani irun abu dake ratsa ilahirin jikinta tana son gane me hakan yake nufi, sai dai kallon da ya mata yana mai risinar da idannuwansa ya saka langwabar da kanta da wata murya a sanyaye ta furta" Masha Allah......."

Chief of army ya yi murmushi shima a sanyaye ya furta" Yau dai Allah ya taimake ni na samu ya amshi kujerarsa, Allah ya taimakeni na hada shi da manya sun rarasar min shi ya amshi kujerarsa, domin ni na gaji, shekaruna sun ja, kaina ya dade da dena gane hayaniyar gidan soja, hutu nake da bukata da kulawar iyalina, yau gashi Allah ya nuna min, sai dayar rigimar da nake kwana nake tashi da ita, wace zan roki alfarmarka sannan na kama kafa da iyayenka, da Abanka gayanan zaune, su sake saka baki na miko maka takardun arzikinka baki daya ka rike, ka koyi juyawa domin bana so na mutu da su a hannuna su zamto jayaya ko wani gardama, duda akoy sunnanka a sama aman dan adam a kan arziki babu abinda ba zai iya aikatawa ba, My Son ka yarda ka amshi tarin dukiyar nan ko zan ji nauyin nan ya sauka a kaina"

Idannuwansa ya rintse da karfi yana jin yadda aka kwashi murna masu yin ihun murna na yi masu barka a bayane na yi, haka kuma wa'inda bakinsu ya mutu murus na kallo tamkar wa'inda suka summa a tsaye

Mama ce ta sake kallon mijinta a raunane ta langwabar da kanta ta ce" Aya Abansu, fushi ka yi da mu ne?"

Matarsa ta tsakiyama ta fuskance shi tana fadin" Abansu aikin ka ajiye ne?"

Murmushi ya masu yana girgiza kansa ya ce" ba maganar fushi, dama na yarda na amsa dan a lokacin shekarunsa basu kai daukan wasu lalurorin ba, ya kuma nuna tsoroma yake ace shine da makakar dukiyar nan, aman a yanzun shekarunsa sun kawo wajen da ya dace ya zama jajirtace, Maman Umi kika ce aiki na ajiye? Dama ai inaga kudin gwamnati kawai nake ci, ina aikin? Kulun ina gida ina nishi kuna hade ni, ku kun san na tsufa da aikin nan , sannan maganar da zan fada maku kun ga rabona da aikata maku Wani anfani na gidan nan da aljihuna har naa manta, cinmu, shanmu, wutar lantarkinmu, komai shine a tsaye a kai, kun ga kangon gidan ne kawai na samu na gina aman shine a tsaye a kanmu, daga yau shikenan sai ya shigo a matsayinsa na d'ana ya kawo wanda yake so a lokacin da yake so ba tare da na fuskanci wata rigima ba, kumu yi masa adu'ar fatan alkhairi kun ji? "
Ya juya wajen su Malan dake dubansa gaba daynsu da su Aba ya ce" Ku saka min a adu'a dan Allah"
Sannan ya salami gaba daya y'ayansa na cikinsa da kuma su SHUWWA wa'inda yawanci da murna da tsale suka bar falon domin su a wajensu daya ne sun san ko abansu ko yayansu yake dauke da matsayin du daya ne, wasunsu kuwa kumar zasu saka kuka da ihu , chok din abin ya dake su sosai sun cika da al'ajabin abin nan har cikin kwakwaluwarsu , sai dai rabonsu jin haushin ne dan sun san ba zai taba yiwuwa su bayanar ba, ciki kuwa harma Uma wace aurensu bai fi kwana goma sha daya ba domin ranar da Father ya saka matsowa take yi sosai duda mamanta ita bata shirin komai, aman shi ranar da ya saka tana matsowa da kamar wuya kuma ya kasa aiwatar da abinda ya yi niya, yanzun shikenan ba uba ba mijinta a masu dauke da wannan daraja? Ta tabata abinda mamansu ta yi ne ya saka Father aikata wannan abin, shikennan mamansu ta jaza masu , su shuwwa kam sun so tarewa bangaren Mama, sai dai Nahidht ta nuna ko daya maza SHUWWA ta je ta yi jiran mijinta, idan har ya bata dama su yi magana a kan halin da yake ciki, ta kamanta sanyaya masa zuciyarsa ko yayane
Har ta so ta yi gardama da nata dalilin suka ki bata damar hakan

Jiki a mace ya shigo bangarensa
Dadadan kanshin turaren wutar da yanzu baya rabo da sashinsa ne ke tashi, haka kuma idannuwansa suka sauka a saman wannan kyakyawar budurwa da bata shayinsa, bata kuma jin tsoronsa tanaa tsaye da turaran wutar ga dukan alamu daga dakin barcinsa ta fito da shi

A hankali yake binta da kallo har ta ajiye kafin ta juyo inda yake tsayen nan ta zuba masa idon itama tana tunanin shin tsayuwar nan tasa mai kama da cogiya me yake so ne?, Wai me yake so a cen cikin zuciyarsa ne?

A hankali ta karasa gabansa kadan ta tsaya, ta sauke dubanta a saman galolin dake jikinsa, da irin girman kirjinsa kafin ta dauki hannunta a hankali ta dora saman galolin ta dan shafa sai kuma ta zubawa fuskarsa ido, a hankali ta kuma nufar fuskar tasa da hannun nata dan ta shafa sajen fuskar , aman sai ya dan kauce fuskar tasa kadan Yana lumshe idannuwansa hadi da fatan samun kwarin gwuiwar kin barinta aikata haka, domin zuciyarsa a karairaye take sosai baya tunanin idan ta bashi dama ba zai iya kasa fin karfin zuciyarsa a kanta ba yau
Dan murmushi ta sauke ta sake kallon fuskar tasa da ya kawar a hankali sosai ta furta" Welcm *CHIEF OF ARMY*"

juyowa ya yi saman dan bakin nata da ta furta CHIEF OF ARMY din, wanda ya ji shi daban da furucin sauran, domin nata kamar sai da aka saka shi a studio aka tace shi sosai kafin a ciro shi
A hankali ya dan saki ajiyar zuciya yana kallon fuskarta, sai kuma ya gaa ta juya zata yi tafiyarta , domin a tunabinsa tafiyarta ne zata yi

Da sauri ya saka hannunsa yana sakin abinda ke hannun nasa ya damko nata hannun sannan ya yi saurin janyota ta haka ya hadeta da jikinsa ta bayanta
A hankali ya dora habarsa a saman gashin kanta mai launin baki sannan ya ringa tafiya da ita a jikinsa har ya kai saman kujera ya zauna yana dorata a saman cinyarsa ya rungume bayanta sanann ya yi shiru
Da farko tsorata ta yi sosai, daga baya kuma sai ta lumshe idannuwanta tana jinsa a jikinta irin rungumar da ya yiwa bayanta irin sosai din nan ne

Muryarsa cen ciki sosai ya iya furta kalamai kamar haka yana sake nanukarta yana murza sajensa a doron wuyanta" *TSORO NAKE JIHHHHHHH, YINWA NAKE JIHHHHHHH, ISHRIRWA NAKE JIHHHHHHHHHHHH*"💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥


*The Hero writer*


*SAJIDA*


_Bismillahir rahamanir rahim_


PAGE:. 5️⃣9️⃣



*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*






*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*


*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*



*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*



*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*


*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618


Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰











A hankali ya sake dago jajayen idannuwansa ya dora a saman lebenta da take cicijewa tana tunanin me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login