Showing 93001 words to 96000 words out of 226733 words

Chapter 32 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

8006

tsaye yana fadin tafi ne suka kalla su dukansu

Hannunta ta saka ta kamo nasa tana kallonsa aa sanyaye ta ce" Haba yayanmu, tafia zaka yi min da ita? Dan Allah ka barta tare da ni"

Hannun nasu ya bi da kallo, ya sake kallon wayarsa dake saman cinyarta

Baki ya sake tabewa ya juya ya nufi sama ba tare da ya furta masu ci kanku ba,

Da kyar suka iya daidaita tsakaninsu bayan Hamza ya fahimta sannan ya yarda cewa daga an kwana biyu zata koma wajensa ne ya iya tabo mahaifinsa cewar zai koma ya gama , a nan mahaifinsa ya tabo Number Muhyideen dake saman cinyar SHUWWAR, a kan dole ta mike ta nufi sama tana ta gungunnin barin wayar da ya yi ta nufi dakinsa dan ta kai masa wayar su kuma sunna jira ya amsa dan ya bada damar zai fita a barikin a wannan lokacin a raka shi har cikin gari saboda tsaro

Bugawa ta fara yi kamar sau hudu, kafin ya saka hannunta ta murda ta shiga gaba dayanta tana mai yin salama a dan dage

Ido cikin ido sukai da junna domin tunda ta fara buga masan ya tabata cewar sabuwar tsagerar dake kawowa nutsuwa da kwonciyar hankalinsa farmaki ce, dan kaf cikin barikin nan ko mashaya giya ba zasu sha su nufo nan su aikata mumunan aikin nan ba gaskiya, wannan aiki na bakon gari ne mai son halaka kansa ido rufe

A hankali ta janye idannuwanta a cikin nasa tana sauke ajiyar zuciya hadi da rike gefen rigarta da karfi tana son controlling din abunda take tunanin ko tsoro ne ta ji sanadiyar ido hudun da sukai da wannan mutumen domin gabanta ne ya yanke ya fadi a lokacin da ta kalli fuskarsa wace take cikin yannayi na ba yabo ba falasa

Dan murmushi ta yi tana sake aro jarumta ta shiga fadin" Dama, Dama, Dama kira ne yake shigowa, shine na ce bara na kawo maka wayar ka mantata a cen kasa ne"

Hannun nata dake miko masa wayar ya kurawa ido kafin ya maida dubansa saman fuskarta
Gefe take kallo, ko yace kirjinsa take kallo

A dan nutse ya ce" Waye shi?"

A hankali ta dan dago tana kallon fuskarsa ta ce" Ban sani ba na dai ga an rubuta Father"

Idannuwansa ya maida gefe ya sake maidowa kanta yana girgiza kai da tunanin ta yiwu jaka ce bata da ilimi sam, ta yaya zata yi tunanin zai mata tambayar waye mutumen dake kira a wayarsa bale ta ga sarai me aka rubuta, ko bata iya karantawa ba sai a magana ne ta dan koyi kadan kadan?
"Look, Allah ya sa tare kuka fito duniya kar na kuma gannin kin zaune gabansa ba hijabin dake kare mutuninki na mace, sannan kar na kuma gannin kina magana kina shafarsa ki yi hakurin aikata hakan daga nan har zuwa lokacin da zamu saki hannun junna dan bama so sanadiyar kina karkashin ikona a matsayin wanda ya aureki na fada wutar jahanama dan Annabi ya fada duk mutumen da baya kishin iyalinsa dan wuta ne, bai bambance iyalin naka wanda kake so, ko wanda baka so ba, dan bariki ko tsaftatace ba, cewa dai ya yi duk mutumen da baya kishin iyalinsa dan wuta........bana tunanin kin kai matsayin da zan yi sake na fada wuta saboda ke, game din ba riba......ki kama mutuncin kanki ki iya bambance bariki da gidan aurena!".................................... A kausashe ya yi furucinsa, a hade ya fadi abinda ke cikin tunaninsa, a zafafe ya isar da sakonsa, sannan sai da ya damki damtsen hannunta ya dago da dan karfin da ya saka ta bashi dukan hankalinta harma ta gane cewar furucinsa ba karya yake nufi ba, gaskiyarsa yake nufi yanai mata kashedi ne a kan ta kiyaye kar ta aikata zina da yayanta a cikin gidansa

A hankali ta raka bayansa da kallo, har bayan ya rufo kofar da karfin da ya saka Idannuwanta kirftawa a sekwond daya suka kuma budewa a yan sekwani,

A hankali ta shiga taka kafafuwanta tana nufar Wajen da ya bi ya fita har ta fice a dakin itama ta tsaya daga sama tana kallon lokacin da suka yi gaba da shi da yayunta sukaiwa Hamza rakiya ya fice tana kallon kofar har ta ga an bude an shigi, Nahidt ta nufi dakinta tana yar dariya, cen kuma sai ta ga an bude ya bayana ya shigo kamar yadda ya saba shigowa, wannan karron direct ya nufi wajen kayan abincin nan ya hau ya zauna ga dukan alamu abincin ne zai ci

A hankali ta lumshe idannuwanta da dan karfin da ya sakata jin dumi dumi , danshi danshi na bin kumatunta hakan ya sa a hankali ta saka hannunta na dama ta shafa abin a hannunta ta dauko yatsarta tana kallo

Juyawa ta yi jikinta tamkar babu laka ta nufi dakinta ta murda ta shige a hankali ta nufi bakin bed ta zauna tana kallon kasa
Mayafin abayarta ta saka hannunta tana shafawa wajen goshinta dan ta ji shin rufarta ta yaye a jikinta ne?
Sai dai ta ji a rufe gashinta yake ruffffffffff tun daurin da ta yi a dakin NAHIDT

A hankali ta dora hannunta saman kirjinta tana rintse idannuwanta a sanyaye ta ce" Ban yi tunanin mutun mai ilimi, da girma, da hankali, wanda ke gwagwarmaya da kalolin mararsa jin magana, wanda ya shanye su a cikin kwakwaluwarsa da rashin jinsu da komai zai iya aikata aiki irin wannan ba...................., Kana nufin ka ce min kana hanna ni kokarin kusantar zina da yayana a cikin gidanka???????"

Idannuwanta ta sake rintsewa hakan ya sa wasu zazafan hawaye suka shiga silalo mata a saman kumatunta ta sake cewa" Duka lalacewar tamu ce ta kai haka ko kuma rashin gata ne ya sa ake jifanmu da kazamin tunanin irin haka?, MUHAY me na aikata da zafi haka da har zaka kwatanta irin wannan a kaina?, Me ya saka ka a cikin duhun da har kake neman saka zuciyata mai rauni da sanyi a saman wannan sha'ani, mai saurin kawar da damuwa dan kar tai min ila, mai matukar yin takatsantsan da aikin nan na zina, na rufe ido nake warto aure ido rufe, ba ruwana da yaro ko tsoro ni dai na raya sunnar ma'aiki, na shigo nima a gidanka ba da rokona ko son raina ba, asalima kai din nan ka saka kaki bayan haka kawai masu kaki basu yi min ba a rayuwata, a haka ne ka dangantani da mumunan aiki haka Why?"............................................. Ta idasa maganar ta fitowa da gursheken kukan da ya saka ta dora kanta saman filonta tana yi har kasan zuciyarta kafin ta sake lumshe idannuwanta tana dannar kirjinta a kasan zuciyarta ta ci gaba da maganarta kamar haka' Na san ni ba kowa bace, aman mutun ce ni da ya dace idan za'ai min magana a kiyaye yi min wace zata tarwatsa min farin cikina harma ta sakani zubar da hawaye.....shin kai baka san ba magana mai dadima sadaka ce in ji ma'aikin Allah? Ko kuma a cikin kokarin kaucewa fadawa wutar jahanamar da kake son yi a kan mutun marar mahinmanci irina a rayuwarka kana da zabe ne? Ko ka manta a cikin hakokin da aka wajabta maka wa'inda suke iya kaika wutar idan baka kiyaye ba akoy masu tsaurin da kake takewa hankali kwonce, kai ko dai kai ana baka zabi ne na rayuwa da yadda zaka tafiyar da ita ko dan kana wani kana da damar wulakantani hankali kwonce? Ko so kake ka nuna min dan ina mace an rigaya an yini a cikin wadda maza ke takawa a lokacin da sukai ra'ayi su wulakanta idan hakan ta raya masu?.............'

Sake rukunkume jikinta ta yi tana mamakin irina yadda maganar nan ke neman kasara dukan wani farin cikinta da kwonciyar hankalinta har idannuwanta suka sauka a kan boyayen abin da bata taba ankara cewar akoyshi a dakin barcinta ba

A hankali ta sake kura masa ido, watau an masa wani mahaukacin boyo ne da idan dai kai din kai a duhu ne ba zaka taba gane cewar akoyshi aa wajen ba, dan kuwa an saka wasu irin fitilun kwaliya ne a gefensa shi kuma an masa dabarar da ya dauki kalar fitilun suka laye da junna hakan ya sa da gagawa ba zaka fahimci cewar camera ce a wajen ba

Mikewa ta yi tana kallon camerar a hankali ta karasa wajen kujera ta janyo ta kawo kusa da camerar

Ajiyeta ta yi sannan ta dan duka ta saka hannunta ta cire pant din dake jikinta baki sannan ta haye kujerar ta daga pant din da kyau ta yadda za'a gane meye ta rufa a wajen sannan ta rufe camerar da shi da kyau ta yadda gannin camerar ya dawo duhu rudum domin a yanzun ba'a gannin abinda yake dakin ta sauka tana tsaki a bayane ta ce" Ku dora doka, kuma ku taketa da kanku, to babu wanda zai shiga secret life dina! Kamar yadda kuka dora dokar hanna saka camera a dakin barcin mutun ni babu wanda zai saka min!"

Ta koma bakin gadon ta zauna tana gyara zamanta domin ya rage mata oant daya tak kennan wanda ke rike da audugarta a jikinta ta sake kurawa hannayenta ido a kasa kasa ta shiga furta" Lalle zamu aiwatar da aikin ladan da zai hanna mu shiga wutar jahannama kafin mu saki hannun junna gaba dayanmu MUHAY, nai maoa alkawarin nuna maka menene aikace aikacen kiyaye fadawa wutar jahanama da mace ya dace ta yiwa mijinta in sha Allah......duk rintse sai na bayana maka kafin mu saki hannun junnan da ni da kai domin abinda baka sani ba koda ka ki ka sakeni ba zan rufe wata daya da kai ba sai ka sakeni ta laluma ko na maka ka a kotu!"

Da wannan kuncin ta kwonta barci, hakan ya sa ta yi barcin marar dadi, domin a takure take jikinta a hade yake waje daya tana ta juye juye dan ta samu ta daina mafarkin da batama san na menene take yi ba har garin Allah ya waye

Kusa da kiraye kirayen sallar subahi wayarta ta dauki kuka
Irin kukan wayarta kuwa wakar wata balarabiya ce mai kaudin murya ko a nesa kake kana iya jiyota bale kana barci, hakan ya sa ta farka a zabure tana waige waige da neman wayar, gabanta na yankewa ya fadi ta kai dubanta wajen wayar da kuma agogo tana tunanin mai kiranta a irin wannan lokacin ko waye ba lafia ke tafe da shi ba

A dan birkice ta wawuro wayar tana duba numbobin da zata iya rantsewa bata taba gannin numbobi masu bibiyar junna irinsu ba hakan ya sa ta ki ta daga har sai da wayar ta tsinke, aka sake bugowa

Daga kiran ta yi tana ajiyewa saman bed dinta ta saka a amsa kuwa sannan sannan ta zubawa wayar ido batai magana ba

"Na san kina jina, kuma na san kina cikin bacin rai, kar ki damu yadda ya wulakantaki haka yake wulakanta kowa, ki bani hadin kai mu nuna masa cewar shima ba kowa bane mu bashi abinda yake nema mu nuna masa shi din ashe kaskantace ne a cikin kaskantatu, zan sake kiranki na ji amsar ki a kan haka!"..........muryar da ta kasa fahimtar ta mace ce, ko ta namiji ce, tana ruwa ruwa alamu an saka wani abu a jiki dan kar a gane mai muryar aka fada mata magangannun nan da ta kasa gane inda suka dosa, da kuma tunanin ta yaya aka san ranta a bace da komaima suka sakata yin mutuwar zaune hadi da afkawa a duniyar tunanin da kiran sallah ya sakata zabura dan tsorata ta yi da jin kiran tamkar an matso masalacin yau cikin kunnayenta hakan ya sa ta yi baya da karfi ta hantsila ta..................................









Alkalamin KADARA..................................................................☺️☺️☺️☺️☺️☺️☺️ I'm back na gode da uzuri da akai min🥰🥰🥰🥰🥰🥰*ALKALAMIN KADARRATA*






NA SAJIDA



3️⃣1️⃣



Da karfi ta hantsila ta fado kasa daga saman gadon ta zabura ta mike tana zazaro idannuwanta a bayanne ta furta" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, Innalilahi na shiga ukuna na lalace, ni kuma?"

Sai ta koma ta zauna gwarab saman tiles tana ta haki kamar wace ta yi gudu kafin ta dora hannunta a saman kirjin nata tana kallon waje daya a hankali ta ce" Shi yasa yake tafiyar da rayuwarsa wata iri? Wanene wannan mai tsaurin idon da ya samu number wayata? A ina ya samu number wayata? Yaya aka yi ya san ina cikin bacin rai? Ko me yake faruwa akoy ta hanyar da yake sani!"

A hankali ta karkata kanta wajen camerar da ta rufe da pant dinta dazun da safe, sai ta samu kanta da maido kanta da sauri tana zazaro idannuwanta

Cike da Tsoron haka ta mike da sanda ta fito ta shiga sauka da gudu gudu tana harhada matakalar tana sauka ta yi dakin yar uwarta da gudu ta bude ta fada ta mako kofar

A hankali ya lumshe idannuwansa a zaunen da yake a falo fitila a kashe da yar karamar wayar da ya gama sauraron komai a hannunsa har fitowarta da fadawarta dakin yar uwarta Duka kaf a kan kunnensa da idannuwansa

Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kansa a kasan zuciyarsa ya shiga ayana' An samu kutanen da kudi baya gabansuma bale ke?, Na san har sai kin yi farin ciki kafin ki taya mai son kasheni karni a doron kasa, na rasa me na yi da zafi haka, na rasa gagawar me yake yi, idan har mutuwar ce shin akoy wanda ya taba dorewa a doron kasa ne?........bawa ya cika neman fitina a duniya'

Daga haka ya mike ya saka wayar a aljihunsa ya fice a falon yana mai sake ayana' Aman zan yi asarar girki mai dadi, dan ba laifi abincinsu ya min dadi, na zata za'a bari na dan kwana biyu ina dan ci ko yayane.......'
(🤔)
Watau duk matar da ta amsa sunnan tasa koda ta wuni daya ce sai an masa tracng din numbarta ta yadda ko mesage, ko kira, ko whatsup komanta yana da damar samu da zarar ya bukaci hakan, ya samu wannan dama ne da kyar, domin abu ne da kudinka baya baka sai idan an yarda da abinda ya sa za'a iya yi maka shi da sauki, domin rayuwar mutun ta sirri tana da mahinmanci sosai a kasa ta yadda baka tashi kai tsaye ka yi haye a cikinta

Tunda ta fado dakin take koro mata bayanan nan bata ko tsayawa ta sauke numfashi har sai da ta gama sannan ta tsaya tana wiki wiki da idannuwanta wanda hakan ya saka itama cikinta juyawa tana kallonta ta ce" Kar dai a je wani soja ke son wajensa kin san fa ba karamin mutun bane a sojojin kasar nan gaba daya shine na biyu , kin ga Idan ya kashe mutun fa ba'a masa tambayar dalili an san mutumen ya cencenci kaura ne, mun shiga uku mun shigo tsakiya kar a hada da mu!"

Shuwwar ta kai zaune tana dafe gaban goshinta a sanyaye ta ce" Bama wannan ne damuwata ba, na tabata koma waye sai dai ya bi ta bayan fage ya saka da mu din idan ban masa biyayya ba, babar damuwata da yake na zo na hau kan sawun barawo ne inaa tafia, ina tsoron a kama ni a matsayin mai laifin da ban aikata ba, ina ji a jikina bana so na hau laifin da ba nawa ba Nahidt a kan lamarinsa, Domin camerar dake dakina ban yarda da ita ba sam, na fara kokonta a kan anya shi din nan da iliminsa zai sakawa iyalinsa camerar da ta kai har kuryar dakinsu na kwonciya barci dan yana tsoron kar a kashe shi? Anya kuwa ya san da zamaan camerar da ta wuce wancen ta falonsa a kafe? Nahidt anya ba yana zaune ba tare da ya san da ita bane ba kwata kwata?"

Nahidt ta sauke ajiyar zuciya tana ji ana salame sallar asubahi a sanyaye ta ce" Kin gyara dakinsa kuwa?"

Shuwwar ta girgiza kanta

Nahidt ta ce" Ki tashi ki je ki kwatanta, ki yi kokari ki iya jurewa har ya bar gidan, sannan ki tambaye shi fita ku je wajen Abanki,, ni kam ina cike da tsoron lamarin nan Shuwwa"

Shuwwar ta gyada kanta a hankali ta juya ta fice a dakin da dan hanzari ta nufi dakinta

A nutse ta samu kanta da shiryawa bayan ta kai tufafinta cikin bayi da dukan abinda ta yi niyar yin anfani da shi a yau, domin a jiya bakinsa ne ya yanka wuyansa, ta yi niyar binsa tamkar bawa da uban gidansa , kamar yadda yace yana son kiyaye saka kansa a cikin wuta, zata bashi dama ta kuma nuna masa cewar a duniya gaskiya ba shi daya ke tsoron mutuwa ya koma ya tarda wutar ba, itama a kansa bata tunanin zata yi garagen da za'a tsomata a wuta

A cikin bayin ta gama komai ta fito da wanda zata shanya ta shanya su ta ajiye na ajiyewa sannan ta sake satar kallon wajen camerar nan kafin ta juya ta fice bayan ta sake daukan sansanyan turaran ruwanta ta murza a jikinta,

Tafe take tana dan motsa bakinta da tunanin yaya akai man leben da ta dan murza yake da danko a baki sosai?

A nutse take hawa cikin shiga ta doguwar rigar da ta dan dara gwuiwarta kadan, rigar irin mai fafadan wuyan nan ce sannan hannunta dogo ne ama a yanyanke yake sosai tamkar an yayaga shi da gangan, gashin kanta kuwa ta daure shi ne a tsakiya ta kama shi da ribom ta baza gaban sosai ta yadda ta bada kala domin yana da cika hakan ya sa yai kyau, bata saka bra ba, sai pant kadai ta saka domin rigar daga wajen kirjinta a rike take da kirjin dassss , daga kasa ne ta dan bude take lafewa a jiki da zarar ta motsa
Kafarsa kuwa sanye take da lalausan takalmi mai gashishika sosai wanda gashinsa ya rufe gaban kafar sai bayanta ne a bayane
Tana janye da abin shafa da na guga da ta dauko a kasa ne ta saka hannunta ta dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login