Showing 198001 words to 201000 words out of 226733 words

Chapter 67 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

8005

bashi da lafiya sai ya zauna

Kusan minti tara tsakani aka zo aka sake gyara kujerar dake gefensa na dama, wace shi du a tunaninsa shugaban kasa aka tanadarwa ita Kuma sai bai zo ba, domin an bambabtata sosai an kuma kawatata sosai da shinfida irin ta kilishi a saman kanta

Da ido ya sake raka sojan da ya gama gyaran , yana bacewa ganninsa sai ga murya, murya ce irin ta baban bafade, duda muryar a yanzu bata da kaifi irin ta da kuma bata da zaudi irin ta da aman murya ce wace tun sunna yara suke jiyota a fadar gidansu, domin bafaden dan uwansa ne wanda bayan nadi aka neme shi aka rasa
Hakan ya saka shi zubawa tsohon da ya shigo da rawani irin na sarautar gidansu da kuma rankwafa ta tsohuntaka ga kuma karfin hali na kirari uwa uba abinda baakinsa ke fadi kirari ne ziryan na dan uwansa wanda ya goge ya dora nasa

A kausashe, gabansa na neman faduwa ya ringa karfafawa kansa gwuiwa da ture tunanin dake shigo masa, domin kuwa ya tabata ko a mafarki abu ne da aka yiwa tufka hanci aka lula nesa, ba dai mutun ba walahi

Wata muryar mai iso da shigowar sarakin ta saka shi sake maida dubansa kyam a kan wanda zai shigo
A tarihin masarautun kasar nan, masarautar gidansu ce kadai aka yiwa zamanin iso da mai shigowa, a zamanin sarautar dan uwansa ya goge wannan, bayan ya rasu shi ya dawo da ita aman kuma ta wata siga daban, sai ga tsohuwar sanarwar tana shiga dodon kunnensa, wanda hakan ya saka shi sake neman zurmuwa a wani tunani daban
Shin wani karamin kwaron sarki ne ya dauki wannan sanarwa ya maida ita kasarsa? Da kuwa ya ga ikon Allah domin idan takamar kasar cewa an dade da juya babin yaki da kuwa sun tsogalo rigima da aljani, dan kuwa shi da kansa zai dauki takobi ya sare kan tsageran sarkin da ya dauki busa da kuma kida irin na masarautarsu!

Hanya aka buda, sandarsa ta fara bayana a wajen a hannunsa, sanda mai ruwan ta mahaifinsa sak, wace take da ado irin ta mahaifinsa
Mutane da yawa wa'inda suka rayu da mahaifinsa suka kuma san adon rawani irin na mahaifinsa ne suka mike hankali tashe sunna zuba idannuwansu a saman mutumen da ya bayana a lokaci daya da tsayuwa da mayar da kai gefe tak irin na sarkin garinsu marigayi Allah ya jikan rai

Da kakarfar muryar wannan tsoho jikinsa na daukan tsuma ya bude bakinsa yana fadin" GYARA KIMTSI MUTANEN GARINA, GYARA KIMTSI GA NADIN ALLAH, GYARA KIMTSI BANDA HAYANIYA, GYARA KIMTSI GA JINNI NA SARAUTA, SARKIN GARINA MAI TAUSAYINMU, MAI KAUNARMU, KAWUNNANKU A KASA DOMIN MAGABACINMU NE TAKAWARKA LAFIYA SARKI DAN SARKI JIKAN SARKI *UMAR ABDULAHI BINE MUTALAB*, Ga da a wajen IBRAHIMA DA KHAMISSSSSS, ........"
Watau tunda aka ambaci sunnan nan sarki Khamisss ya daina fahimtar abinda yake faruwa, haka kuma idannuwansa suka dawo kallon gabansa tarrrr ya ringa fitar da numfashi ta bakinsa, har sai da UMAR ABDULAHI BINE MUTALAB ya zauna a kujerar dake hade da tasa, sannan CHIEF OF ARMY MUHYIDEEN MUHAY ya zauna a dayan barin da a da wani ne a sama aman a yanzu ya tashi

Yana zama ya sauke ajiyar zuciya hadi da sake ambaton sunnan Allah da fatan Allah ya bashi dama kar ya fashe da kuka a zaunen nan da yake a gaban mutumen nan da ya wulakantar da rayuwarsa, yana fata yadda ya ga dare ya ga rana to ya jure wannan moment din

Dogaren da suka zube a gabansa, datijai wa'inda suka yo zamani da mahaifinsa ne yake kallo, da kallo irin na soyaya mai tarra kwala a cikin idannuwa
Sai kuma a hankali ya daga masu kai dake nuni da ya amsa gaisuwarsu baki daya

A zabure sarki KHAMIS ya juyo a lokacin da baban shehin limamin Yah sheik ya amsa wannan gayata da dumbin kauna bayan an masa bayani a boye ya kuma zo da dukan kwarin gwuiwarsa duda matarsa bata jima da haihuwa ba ya zamto shine wanda zai daura auren a wannan lokaci ya yi gyaran murya a nutse ya shiga gabatar da dukkan abinda ya dace , ga kuma mai amsa kuwa a gefe yana fadin komai a cikin amsa kuwar ta yadda yan cikon gida ke ji da kunnayensu haka kuma yan nesa da nesa

Cikin kankanin lokaci aka daura auren MUHAMMAD da NAHIDT UMAR ABDULAHI BINE MUTALAB bisa sadaki kwakwara mai motsi wanda ana gama sanarwar daurin auren mai amsa kuwa ya sanar da babar murya sannan ya sake buda muryarsa ya sanar da sako kamar haka" SUGABAN Sojojin kasar nan watau MUHYIDEEN MUHAY yana mai sanar da dukan wani farar hula cewa ya ja ya koma , yana godiya da halartar daurin auren da aka yi yana fatan alkhairi"

Ana fadin haka sojojin suka shiga bada kokari ta wajen janye mutanen da suka tabata babu su a cikin hurumin maganar cikin mutuntatawa ba cikin wulakantarwa ba har suka idasa janye su gaba daya sannan suka sake zagaye wajen da iya wa'inda abin ya shafa

Ajiyar zuciya Muhammad ya yi yana sake sadda kansa, haka dukkan yawancin wasu manya manyan wajen kawunnansu a kasa suke a sade ciko harda shi din da kansa sarki Khamissss

Sosai ya iya controling din kansa a sanyaye sosai ya furta"Zaka iya hakuri da goyar dake son kaika wuta ka adana tsufanka ka rufawa kanka asiri ka yi aiki na ilimi ka mika kayan aron dake hannunka kuwa Papah ba tare da an wulakantar da junna da tashin tashina ba? Domin shi rufin asiri dadi gareshi koda a wajen mai laifi ne, ina fata alfarmar rufa maka nima Allah ya rufa min"

Kamar yadda ya dauki maganar haka shima ya dago da dogon kallo jikinsa na bari
Zufar dake tsago a jikinsa mai tarin yawa ce, hankalinsa a tashe ya furta" Ta yaya? Ta yaya ka rayu bayan irin ukubar da ka gani? Ta yaya ka warke daga cutar haukan da kake ciki?"

Idannuwansa ya saka cikin nasa tarrrrr a kausashe ya ce" Ta hanyar wanda ya busa maka numfashi, Khamiss Mutalab ta yaya ka kwaci hakin da ba naka ba, ka tura wajen da baka da masaniyar fadawar kafafuwa, ka bi da bita da kulli kuma ka ki kyautatawa kasarka? Ka yi kokarin yin komai da murmushi domin kasarka na kallonka, ana haskaka ne!"

A firgice ya juyo wajen da masu dauka suke, bayanan da suke ne ya sake saka zuciyarsa neman tsayawa
Juyowa ya sake yi a birkice ya ce" Kana nufin na baka kujerar da a kanta na aikata shirka? Kujerar da na fitar da kai sannan na haukata dan uwana? Kujerar da nake mulka da dukkan karfina? Kana so ka ce ni zan baka kujerar nan? Mema zai sa na baka ne?"

Ajiyar zuciya ya sake saukewa yana fadin" Bama so ka tona mu sai ka tona mu?, Khamiss a yanzu ace a barka a saman kujerar nan da shekara goma zai zamto ne idan ranka bai fita daga gangar jikinka ba to fa tsufa irin sosai din nan zai kama ka wanda zaka dawo baka fahimtar komai dake gabanka, haka ka zaba ne? Kuma ka san ko da karfin Allah zan iya amsa, bale talakawana suka ce ka sauka ka bani abinda yake nawa!"

Zai kuma yin wata maganar a gigice Muhyideen ya karkato kadan shima ya make murya sosai, sai dai ina, muryar tasa ba zata fita a hankali sosai din ba ya dan dube su ya dan yi murmushi ya ce" Allah ya karra lafiya a gaskiya idan aka amshi kujerar nan ta laluma ni aka cuta, inaga fa har rantsuwa na yi kan sai na yi wasan kura da azalumin da ya aikata haka dan na zubar da sheda ta kasance izina ga mai son aikata irin haka, ka ga fa......"
Sai kuwa ya mike ya kwabe babar rigar dake sama hadi da hular dake saman kansa ya zubar, cikin lamari na ikon Allah sai ya kwabe dayar rigarma wace daga ita sai farar ciki kadai ta rage ta cen ciki mai siraran hannaye irin rigar nan dai ta maza sai ko wandon shadar da yake sanye da shi, hakan ya bayanar da bindigar dake jikinsa da manyan damatsunnansa
Hankali kwonce ya juya wajen su Aban Shuwwa da ya yu mutuwar zaune ya wangale baki da hanci yana kallonsa ya karasa a nutse ya dan yi murmushi ya ce" Siriki dan bani Alkur'anin mana"

Ido ya kyafta da sauri, sai kuma ya dan zabura ya bashi alkur'anin da aka zo da shi dan hakan
Ya amsa da hannu bibiyu ya koma gaban sarakan da dukkan wasu masu kallo
Wajen camerar ya juyo ya ce" Ku kashe daukan zaku dauki wajen nadi"
A yadda ya yi maganar a dole suka kashe sunna kyamewa da takaicin rashin daukarwa al'uma wannan rahoto mai dumi dumi

Da kyau ya ajiye alkur'anin saman kujerar ya tsaya a gabansu sosai ya bude muryarsa ya ce" Allah taimaki Baba KHAMIS, inaga ya dace mu yi mu gama dan walahi kade kade nake ji a cikin gidan cen da busa kar aje harda kartin makadan nan aka shiga kuma ita kuma tana wajen, da wahala ta kasa yabawa, Gaskiya ka san kun san abinda ka aikata shi yasa aka sameka a nan, to ba yadda ban yi da su ba kan a yaku masarautar taka a tube maka rawanin ta balbalin balaki suka ce aa, ai kawai a barka da halinka, an cuce ni sosai , sai dai bani da yadda zan yi gaskiya, aman inaga an fara gabatar min da bidi'a, tunda dai sai kwana kwana kuke yi gashi shi kuma d'anka ne ko yayane zai sasauta, ni kuma HUKUMA ne, akoy hakkin ma bima al'uma hakkinta, gashi kuma aban namuma al'umar ne, kawai ka dan fahimta a gama tunda ga takardar saka hannun shugaban kasa ya tuge ka, kun yarda sarauta ta shiga siyasa har ya gama aiki fa, kawai zoben nan ne zaka ciro ka bamu a saukake jirginka na jiranka ka koma ka hada dukkan abinda ka ga zai gyaraka dan bama ja baya da balaki ko na waye da izinin Allah, idan ba haka ba kuwa gaskiya zan Shure komai na fara dankara maka Alkur'ani mai tsarki watau ka rantse ta yadda zaka kuturce, sannan na gabatar da hukunci a kanka a kan laifinka, dan shara'a tana hawa kan tsohon da baya iya motsawama bale kai da karfin kaunar mulki ya sa har yanzu ka iya irgen kudi!"
Da karfi ya idasa maganar wadda da yawa sai da suka rintse idannuwansu ciki harda sarki Khamisss sannan ya sake fadin" Alkalan na wajen, sun auna sun kuma ce kai nawa ne, Baba ka fa aikata kidan sake tashi yake!"

Aban Shuwwa ya lumshe idannuwansa yana godiya da Allah da har yanzu MUHAY bai shaki Khamisss ba, a yadda MUHAY ke tsaye shi da kansa sai da ya sha jinnin jikinsa, yaron ya gama ginna jikinsa ne daidai da zamaninsa sai fatan Allah ya kiyaye ya karre, gashi sam bashi da tsoro, idan kuwa abu ya gamo shi da mai laifi kawai sai fatan Allah ya sanyaya, bale mai laifi irin na Khamiss? Gaba daya ya mayar da kasar tamkar ta yan daba, a cikin kasar baki daya har kwatance ake da rashin mutuncin yan garin, a bayane ake fadin shaye shaye ai sai garin, lalata sai garin uwa uba ya ba karuwai dama sunna yin lamarinsu harma ya hanna a yi kamu, shi din nan da tsufansa da komai yana sana'a ta miyagun kwayoyi ne a cikin kasarsa, y'ayansa kuwa harda wanda ya yi kisa bai jima a gidan yari ba aka fitar da shi ya fitar da shi waje, matayen kuwa sun bude waje waje na holewa a bayane ba a boye ba, kuma yana zaune shine magabacin wajen ya yi mirsisi yana wulakanci, ga hakkin d'an zumu da ya so salwantarwa, ga ta d'an uwansa da ya salwantar ya hada da hauka...............sosai MUhay ya so a hau kotu a bayana komai, sai manyan suka ci karfinsa , a yanzu kuma ana salamar kowa aka shiga wannan dan tataunawa kunnayensa suka fara jiyo masa busa da kida irin na bare bari a cikin gidansu, an kuma tabatar masa ai iyaye na taka rawar murna da yan mata, gidan ya dauki harami, baban tashin hankalinsa a yanzun kam ba zasu gane ba gaskiya, ya dace a ba kowa hakinsa kawai a watse ina dalili wai?!

"Menene hujarku ta cewa wannan din jinnin ABDULAHI ne? Me me yasa za.....mmmm mmnnmnmnmn!"
Da karfi Muhay ya kaiwa kujerar dake gefe duka hakan ya saka sojojin nan gaba dayansu kwasar ihu irin na sarawa suka sarra masa sannan du suka sake maido hankalinsu wajen, ciki harda Dad da bai san lokacin da ya mike tsaye jikinsa na tsuma ba

Da karfi ya ce" So kake mu raba naman jikinka a Wajen nan ne ko so kake mu nuna maka namu salon kwayar ba tare da mun sha komai bane!"

Da sauri Aba ya mike yana kokarin sanyayar da ahin ya ce" MUHYIDEEN ka ga yarona, ka san taurin kai ne da Papah, kawai ka barshi ya tafi ai aikin gama ya gama bai san yana barin wajen aka shiga gyaran wajen ba, ko ya koma yanzu ba mutanen da ya bari zai tarda ba bale ya samu shiga fadar da take tasa, ba sai an kai ga haka ba kar ka manta uwa daya uba daya suke da mahaifina, ko ba komai akoy zumunci"

D'an IBRAHIM ne ya karaso yana hawaye da muryar kuka ya shiga fadin" Zumunci YAH UMAR? YA UMAR idan akoy wanda ya wulakantar da zumunci ai bayan Papah Khamiss ne, nima dan aikin gidan nan nake ba kowa ba, da bakinsa ya fada min cewa na yiwa matarsa biyaya ko na koma tsince tsince irin na ubana, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une idanma aka tausayawa wannan mutumen ai an tafka kuskure mai girman gaske wanda sai Allah ya kama mu, cikin da Gimbiya ta haifar ka san ko na wanene?.........."
Ya juya wajen sarki khamisss da zuwa yanzu burinsa daya ne ya bace battt ya samu kansa koda a dokar jeji ne da wannan balakin dake gabansa, shi fa tsoronsa daya kar su sake shi daga shi sai wannan mutumen, idan hakan ya tabata bai san me zai faru ba, dan yana gudun ya karya masa wuya a nan
Yana hawayen ya ce" Papah na fadi ko cikin waye y"arka ta cikinka ta raina ta kuma haifa?"

Wajen ne ya sake daukan tsitttt, yar jaridar da har jikinta rawa yake ne ta samu bakinta da fadin" Kar dai ace nasa ne?"
Sai kuma ta saka hannayenta tana rufe bakin nata tana zarro idannuwanta domin kamar wace ta saka aka juyo kanta du anna kallonta

Jikinsa na rawa ya saka hannunsa yana jan zoben dake hannun nasa ya sake dagowa da wani irin tukukin bakin ciki yana kallonsu ya ce"💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥


*The Hero writer*


*SAJIDA*


_Bismillahir rahamanir rahim_


PAGE:. 7️⃣0️⃣



*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*






*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*


*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*



*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*



*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*


*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618


Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰







A rikice jikinsa na rawa ya ringa kallon Sarki Umar, sai kuma ya kalli MUHAY , haka kuma ya kalli jama'ar da ya zo da ita, wace yawanci karara ya fahimci a yanzu da suka ji ainahin abinda ya rufe su da shi shekara da shekaru karara kamar masu jira a miko masu shi su yi yaga yaga da namansa, mutun biyu ne kawai suke cikin hali kwatankwacin wanda yake ciki, watau halin rudani da tashin hankali ya ce" Wa ya ciro shi daga dakin da na rufe shi? Da hannuna na shake shi yana barci aman bai mutu ba? Dogari salau ya ce da hannunsa ya aikashi kiyama ashe bai kashe shi ba? Shi rai nawa ne da shi da zan ringa hada shi da hatsari kala daban daban aman yana mikewa yana Rayuwa?........... Shi shi wani irin................ "

Tsittttt kake ji wajen ya dauka , harta da muryar Zarki khamiss din lokaci daya ta yi shiru , haka kuma du aka zazaro ido sanadiyar bindigar da MUHAY ya ciro a kugunsa ya damko gaban rigar Khamiss ya dorata a saman kansa
Idannuwansa sun karra rinewa a kausashe ya ce" Sai da na ce Kar a bi ta haka, irinku basu hau kan decision dinsu ba sai da suka yarda da taurin kansu, da biahewar zuciyarsu, suka nuna min ba sai an kai haka ba, domin irinku yadda suke son abin duniya haka suke son duniyar kanta, domin sun riga sun daukaa cewa matabata ce koda sun mutu babu tsatuwa a gaban Allah bayan mutuwar, sai dai ni gaskiya a yanzu ba zan iya ci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login