Showing 99001 words to 102000 words out of 226733 words
dan ba kyau bana so ana kallona kai tsaye hakan na dagan hankali"
Da mamaki ya ce" Daga jikinki kika cire? "
Hannunta ta yarfe a dan birkice ta ce" Ai ka ga tsiryar, ka ga tsiyar fa, na so ka ganar da ni dala dala ta yadda zan bada amsar da itace daidai, ka ga na rantse maka da wa bilahilazi a lokacin da zan cire ban yi tsirara ba, da rigata har kasa a jikina na cire na rufe abbu wanda ya ganni a zirr"
'subahannalah, subahannalah, subahannalah?' yake ta maimaitawa yana kallonta itama tana kallonsa
A kausashe ya ce" Kin saba fitowa ba kaya dakin nan ne?"
Kai ta girgiza da sauri tana dago yar yatsarta ta ce" a dakin nan idan ka ga na fito to fa da tawul ne a jikina, ai na ki jinnin bayanar da tsiraici a duniya sani ne baka yi ba walahi"
Rai bace ya ce" Saurara, kina ji?"
Ya dan yi shiru yana sake murzar yatsunsa biyu, a kausashe ya sake fadin" A ilimance, a gayance bayanar da tsiraici bashi da wani anfani a rayuwa, a kan wani dalili zaki cire wando a gaban camerar da baki san wa ya sakata ba ki lauya a jiki?, Me yasa ba zaki kasance kamilaliya koda ta da gangan ce ne? Me yasa ba zaki kwakwayi halayar boye sirinki koda da karya kike na dan lokaci ne? Ke kin kuwa san ko budurwa haramun ne ta bayana tsiraicinta bale ke? .........." Dakatawa ya yi yana sake kallon yadda ya sada kanta kamar da gaske sauraronsa take, kamar da gaske biyaya take yi masa, hakan ya sa a kausashe ya ja tsaki mai zafi ya mike yana tunanin ba shine zai fada mata ba, zai kaita wajen wanda ya jajibo masa ya fada mata, ya hannata saka shi magama, ya koya mata hankali tunda ya kula bata da shi, zai je ya sama mata hanyar samun hankalin nan
Kasancewar ya mike wandon nata ya fado gabanta ya take ya wuce yana fadin " Nonsense !"
Da sauri ta mike har tana cin tuntube ta ce" yalabai dan Allah muna son zuwa mu gaisar da Aba dan Allah dan annabi👏"
Juyowa ya yi yana kallonta haka kuma idannuwansa suka sauka a setin akwatunnan kayan da gaba daya suka dauki hankalinsa, haka kawai ya ji kayan basu yi masa ba kai harma yana son sannin ita kuma haka rayuwarta take soyan setinnan akwatunna haka kamar na aure? Samun kansa ya yi da sake maimaita kamar na auren, ya sake kallonta yana son tambayarta shin rainin da ta yi masa harda na dauko akwatunnan kartin mazan da ta ringa aura ta kawo masa gidansa? Har sai ya ringa jin yana son tambayarta kayansu ne take anfani da su? Sai kuma wani abin ya ce da shi ka dakata tukunnan, ba ita ya dace ka tambaya ba, dan ga dukan alamu ta dafa karya ta shanye ta sha romonta tsaf abinta, a zuciyarsa ya ci gaba da ayana' Sam bata da lafiya, ta yiwu iskokan ne ke hargitsata kau?'
Kansa ya girgiza ya fice ya nufi dakinsa da gagawa ya shiga shiryawa ya gama ya fice a gidan gaba daya
Ajiyar zuciya ta sauke a tsaye a jikin tagar dakin ta raka motocin da ya shige suka tafi da kallo
A hankali ta taka ta dawo wajen da wandon ke yade ta duka ta dauka tana zama saman kujera ta jimke wandon a hannunta
Da yannayi na ranta a soshe ta ce" Wanene warar imanin da har yake yakin son gannin tsiraicin matan aure? Da ace jai tsaye nake fitowa ba sutura a jikina ta yiwu da wadda ya laka camerar nan yana da kilishen sasan jikina tsirara?, Da me da me zai yi da shi da zarar na ki yi masa biyayar son hada kai da yake son yi da ni dan ya cutar da wannan mutumen? Shin me mutumen nan ya yi da ake neman rayuwarsa ido rufe haka ne? Ya zama wajibi na mike na je wajen wanda ya saba bani shawara mai kyau, gyaran dakin zan yi idan na dawo!"
Dagudu gudu ta dauko abayarta lumbukekiya ta lumbuka sannan ta warto nikaf dinta da safarta ta kafa ta cire wancen ta saka bak'a ta dauki mayafin abayarta ta nanada a kanta sannan ta daura nikaf din ta dauko wayarta da jakarta wace take kyautata zaton da kudi a ciki ta juyo da dan gudu gudu tana fatan Allah ya sa Nahidht ta farka su je su samu dan sahu ya kaisu masalaci
Masu aikinta ta samu sunna ta aiki ba ji ba gani gefe daya kuma Nahidt ce zaune cikin shiga ta bayar itama nikaf dinta a gefe a ajiye tana ta aikin Voice. What's up hankali kwonce
Murmushi ta sakar mata tana fadin" Tashi mu tafi "
Nahidt ta mike tana daukan Nikaf dinta ta ce" Um su Shuwwa an zama hajia a kadan na kusa awa a nan ina jiranki sai yanzu ta nan mijinki ya wuce sai da ya tsuguna har kasa ya gaishe ni, kai Allah dai ya masa albarka"
SHUWWAR da ta farra barawa masu aikinta salahun gyaran da take so su yi mata ta juyo tana kallon Nahidht
Kai ta girgiza ta juya tana kare masu kallo
Haka kawai ta ji bata yarda da ta barsu a gidan nan su kadai ba, dan ta tabata da dan gida akan ci gida
A hankali ta shiga fadin" Ku tafi kawai, idan muka dawo zamu yi aikinma ai ba yawa"
Su dukansu da mamaki suke kallonta, zasu yi? Gyaran wannan makeken falon? Sai dai basu da damar yi mata musu, kuma sun ga direba da escort din dake jiranta sun san fita zata yi, a dole sukai mata salama suka fice gaba dayansu hakan ya saka Nahidt yin yar dariya tana fadin" Wollah wani lokacin kamar mai hankali idan kikai wani abin"
Sake kyaleta ta yi tana kakarsge dukan wani abin wuta tana cire igiyoyin sannan ta dauki abin rufewa suka fice ta garkame babar kofar kafin ta tsaya tana kallon sojan da ya matso ya sarra mata a ladafce ya ce" Hajia Sir ya ce idan kin fito ga motar da za'a kaiki anguwar cen da eacort"
Daga ita har Nahidt ido sula zarro da mahaukacin mamaki sula juya wajen tsaleliyar farar motar dake ajiye kal tana shinning
Dan ihu NAHIDT ta yi ta nemi yaye Nikaf dinta da kokarin kwaso shoki, da sauri SHUWWAR ta tareta tana girgiza mata kai ta ce"💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 3️⃣3️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
Dan ihu NAHIDT ta yi ta nemi yaye Nikaf dinta da kokarin kwaso shoki, da sauri SHUWWAR ta tareta tana girgiza mata kai da yaren larabci ta ce" Kar ki yi irin haka a gaban yarensa mana kar su raina mana wayau"
Nahidt ta yi murmushi tana mayar da Nikaf dinta ta hade irin kar a ga damartan nan ta bi bayan SHUWWA da tuni ta sauka ta nufi wajen shiga mota
Budewa suka yi suka shige Direban ya ja su
Sai da ya hau bakin titi ya tambayi wajen da suka nufa
Nahidt ta ce" Wajen Masalacin Malan zamu tafi?"
Shuwwar ta kalleta tana girgiza kanta ta yi murmushi ta ce" Kennanma ba karuwan muke ba ko?, "
Ta fuskanci Direban a nutse ta fada masa kwatancen gidan malan da hausa sannan ta sake hade fuska tana tunanin wannan amarya ta malan mai kananun iskanci!
Tunda suka nufo gidan ake raka motocin biyu dake dauke da su da kallo har suka karaso kofar gidan malan
Makotan gidan Malan du sunna lekowa dan kallon farar motar da kuma motar dake dauke da sojoji a bayan farar motar wadda sunna tsayawa sojojin suka didiro daga bayan motar suka shiga gabatar da aiyukansu na tsaro
Sai da suka bada damar cewa tana iya fitowa daga motar sannan direban da soja daya dake gaba suka basu damar fita
Murmushi Shuwwa ta yi tana girgiza kanta a ranta kuwa ayanawa take yi' Rayuwa mai abin mamaki'
A nutse suka nufi karamin get din sukaiwa mai gadi salama
Sarai ya gane su domin ba zai iya kasa gane y'ar Malan da yayunta ba hakan ya sa da fara'a yakr masu barka da zuwa cike da murnar gannin a motar alfarmar da aka kawota harma ya ce" Aaa su y'ar gidan Alama ce?, To ku shigo da motar mana?"
SHUWWA ta yi murmushi tana girgiza kanta ta ce" gani na yi da maza , ba'a shedawa matan gidan da baki ba shi yasa baba"
Shima murmushin ya yi yana bude masu da kyau yana fadin masha Allah ai ga kayama ana saukewa
Gaba dayansu suka juya sunnan kallon ikon Allah ana sauke kayan abincin, ai yanzun ba yadda Shuwwa ta iya da Nahidt sai da ta saka buda tana fadin" Duniya labari, ga Shuwwa ta zo gaishe da ubanta an zo da kayan cima, kai Allah mai iko wuce mu je an fara leke"
Itama shuwwar din sai ta ringa jin wani farin ciki daban a zuciyarta ta yi gaba tana salama a bayane ta nufi direct baban falon matan gidan
Uwar gidan Malan ce ta fara fitowa da hijab dinta da carbinta tana amsa salamar
Gannin fuskokin su Shuwwa a lokacin da suka cire Nikaf din sai ta ringa sakar masu murmushi tana fadin" Marhababiku"
Shuwwa ta zauna dangalgal saman kujera tana fadin" Barka da safia Hajia "
Da murmushi wadace a saman fuskarta ta amsa gaisuwarta ta juya wajen da NAHIDT ke tsaye bata idasa shigowa da kyau ba ta ce" Yau kuma kece a tsayes a bakin kofa?"
Nahidt ta yi dan murmushi tana fadin" Ai dama rakiya na yi Hajia, shi yasa na tsaya daga nan"
Yar dariya ta yi ta nufi kofar ta kamo hannunta tana fadin" Ki shigo, ko kar ki shigo, ki sani zan je ne da kaina na rarasheki, na duka na baki hakuri sannan na fada maki cewar dakinki ya fara dati, dakinki dake gidan nan yana son fara tara yana, shin yaushe zaki gane ki tataro ki dawo tun kafin Aban Shuwwar ya fara fada ne?"
Da dan mamaki tana kallonta ta budi baki zata yi magana suka ji shewa da tafa hannu sannan ta ce" Ikon Allah, wannan shi ake kira munafurci, ke yanzu Malama kece da budar baki da yiwa wannan matar sannu a cikin gidanki harda tsohon munafurci kike budar baki kika ce ta yi ta zo dakinta na jiranta?, Wani dakin kike bayani a cikin gidan nan? Inace a bangaren nan dakunnan biyar ne daya naki, daya nawa, daya na bakinmu, daya na masu aikinmu, dayan kuma na wada Malan ke kira y'arsa ce, a ciki ba'a ginna dakin kilaki ba ko kin manta?"
Malama ta girgiza kanta tana kallonta bayan ta zaunar da Nahidht dake tsaye da farko ta ce" Ke dai Furera ina so ki koyi iya bakinki, ki kiyaye rayuwa, Furera shin ba'a aurowa ke aka auro min ke kike zaune? Da kike zannen dakin waye, da waye da waye ba shi zai hanna Malan aurar biyu ya cikashe da mu ya jera hudu reras abinsa ya zamo sarki cikaken mutun mu kuwa mu share masa fadarsa ya yada zango, ki kiyayi yowa lamarin ubangiji shishigi na kula Furera idan kina magana kikan yi kokarin nuna kin isa da yannayin rayuwarki!"
Furera ta idasa shigowa tana cire hijabinta taa ajiye saman kujerar tana kallonta ta ce" Ganewa ne baki yi ba, ko da aka auroni aka kawoni gidan nan dama dan kin gaza na zo, a yanzu kuma da ke kike hada mijina da wannan da babu wanda bai bude ya dana ba ina so ki fahimci cewar ni ban gajiya ba, ba kuma zan yarda mijina ya auri sauran gayu ba salon in da wani boyayen lamari a maka mana kau? Ba zai yiwu ba"
Idannuwanta take karra rintsewa da karfi tana cije lebenta sannan ta bude ta kalli Furera ta maida dubanta kan Malama
Malama kam mamakin furera ya kasa barinta, ita takamarta da an yi magana ta ringa hoboro ita ga matar so matar da aka auro mai ganihar kuruciya menene menene, a rayuwarta wannan din shine abinda ta fi kwarewa a shi, domin ko matsalar mijin nata ta kasa fahimta bale har ta yi yaki da son kanta da zuciyarta ta taya shi neman abinda ke kayar masa da gaba, ta kasa fahimtar nacin Malan a kan Nahidt, ta kasa gane cewar Nahidt na iya zamewa rayuwar mijinsu mugun jarabawa ko kyakyawar jarabawa, ta kasa yin irin nata ta koyi hakuri ta koyi kaunar kasancewar Nahidt a tare da su, harma ta fuskanci cewar jihadi ne idan har ya aikata hakan, su kuma idan suka talafa masa zasu samu nasu sakamakon mai kyau, ita abinda ta fi kwarewa a shi shine wannan daga kan da jiji da kai ita ga matar malan, ta bi ta rikita lisafin masu karamar kwakwaluwa na cikin anguwa ta koya masu gori da kadarar mutun, dan rashin hankali ta koya masu abubuwa mararsa ma'ana har sai yanzu da daidaiku ke gane wacece ita suke barin makarantar izgilinta sunna fuskantar rayuwa ,
A tausashe ta budi baki zata yi magana a tsawace Furera ta dakatar da ita da hannunta tana fadin" Dila Malama kar ki ce min komai a nan, da bana nan da kin ci min amana kin lalumi karuwa an lakawa mijina an ci amanat..............................................."
Tassssssssssssssssstssssssssssss tsadadan marin da ya sauka a kusa da bakinta ya sakata daukewar magana da firgici harma ta juyo a haukace tana kallon wanda ta auna mata tikiten tashin hankalin nan na kakausan mari mai balakin zafin tsiya
Ido ta kwalalona lokacin da ta ga ikon Allah, ba ita ba, harta da Hajia Matar Malan, da Nahidht idannuwan suka zarro a lokacin da Shuwwa ta cire Hijab dinta ta je da gudu ta janyo cazar waya idannuwanta sun kade a haukace ta ce" Baki gane ba Furera, an jima da daina zagi , bara na ci ubanki a cikin gidan naki ki kai karata ke har yar tasha ce a nan? Da nake raga maki kin dauka dan kin isa ne? Tunda baki da hankali bara na gwada maki shegantakama iyawa ce sai ki samu dalilin tsanarmu da zaginmu, banza jahila da kike anfani da laifin wani kina zaginsa da shi bayan ke dinma halita ce da Allah ya halita baki da tabacin yaya gobenki take!"
A haukace ta zuga mata zugawa guda ta daga ta sake zabga mata , hakan ya sa da dukan karfinta take kokowar son kwace bulalar sai dai kamar yadda SHUWWA ta fada mata cewa shegantaka iyawa ce, haka abin yake, bata san cewa idan ka tashi neman fitina jinjinar kanka kake yi ta yadda zaka yarda da kanka cewar zaka iya, ta dauko da zafi tana wasa da shi a hannunta ne bata san cewar akoy masu dibansa daga cikin tukunya su kaishi baki ba, ta yi wasa da damarta tun ana bata girma sanadiyar mai girma har ta kai wajen da aka ajiye gefe aka fuskanceta a matsayinta na mutun
Da karfi ta hankadeta hakan ya sa ta maku da jikin garu tana haki ta nunota da yatsarta ta ce" Kin jima kina zaginmu da sunna karuwai, kin jima kina dukan kirjin ke kin isa ba'a isa a auro maki karuwa cikin gidanki ba? Furera an fada maki ban san cewa kece matar da ta bini gidan sarakuwata ta ce ni karuwa ce har mamansa ta saka ya sakeni ba?, Ko baki san cewar na san da kafin na tare kika je kika yi bayanin wacece ni wa Elhaj mai shinkafa ba har ya bani tikitina a cikin mota?, Ko ji kike ban san cewa ke din nan kece wace ta yiwa matar uban mijina bayanin wacece ni ba har aka hanna shi tarewa a dakina har zuwa ranar mutuwar aurena ba?, Ke takamarki musulma ce ke anya kina jin tsoron Allahn da ya haliceki kuwa?, Kin san zaki mutu kuma zaki je gaban ubangiji me zaki ce masa a kan tsangwamarmu da tsanarmu da kika yi dan mun kasance masu aikata laifi wa shi da halicemu maimakun ki yi mana nasiha ne?, A anguwa kin tare gaba kin tare baya kin kula mana shari kala daban daban ya zamto makotanmu bamu da kyakyawar alaka da su dan kin nuna har mata bi muke yi? Ke meye shedar fa zaki bayar a gobe kiyama a kanmu ne?, Furera walahi sai kin mike mun kashe junna yau a falon nan ko ni ko ke!"
A haukace ta sake yin kukan kura ta nufeta tana ihun fadin" Ki tashi na ce ki tashi!"
Dan gyarn murya ya yi yana idasa shigowa ya yi salama a sanyayensa yadda ya saba ya sake