Showing 141001 words to 144000 words out of 226733 words

Chapter 48 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

7951

na!, Useina kin zubar da dukan wata kima da nake iya daga maki kafa dominta, ina kauce maki irin ranar nan da zan maki irin wannan kashedin!, Ki kiyaye! Useina ki kiyaye ! Kar ki kuma kiran number wayata, kar ki kuma hadani da mahaifiyata cewar bana zumunci da ke, idan kika kuma zan hadaki da yan barikin daa zasu fitar maki da bariki a ranki, Useina idan kika kuma gigin neman haramci da ni zan goge fuskarki a samab kwalta kafin na dauke kanki da bindiga!, Ki karata da kwaratanki sun isheki , da izinin Allah ba zan yi lalacewar nan da kike burin ki ga na yi ba, ba dai da ke UWATA ba!" da karfi ya karashe maganar yana mai doka hannunsa a jikin garun wanda ita da ya doka a kusa da ita, ita ta tsorata da haka harma ta yi gagawar rintse idannuwanta jikinta na rawa a tsorace ta sake kallonsa da idannuwanta da suka cika da hawaye, bakinta na bari ta ce" Muhay, yaya zan yi? Kadarata ce soyayarka"

Da wani bacin ran a amon muryarsa ya ce" Ki saurara haka, da nake daga maki kafa ban titsiyeki ba ba dan komai bane sai dan jin kunyar zumunta, kadara? Ke taki salon kadarar lalle ina jinjinna mata, kadarar taki ce son kowani gara? Ke Useina yara kannana kike mu'amala da su, mu'amala lalataciya, kin dauka ban sani bane? Ki ce MUHAY kai din son zuciyata ne na yarda wanda kike so ki baje a saman bed dinki zan yarda aman ba kice min ni kadararki bane, ni son zuciyarki ne Useina wanda aikata aikin banza ya saka kike jin sha'awata, ilar aikata aikin banzan da kike yi kennan Allah ya saka maki kwadayin abinda yake guba a gareki, Babar matsalar kuma bayan shirme kin fara hauka a kan lamarinki, USEINA ba zan taba kasancewa mai yi maki biyaya ba ko ki fahimta ta laluma ko duniya ta ganar da ke!"

Daga haka ya matsa ya juya ya barta a wajen, wanda barin nata da ya yi ya sakata dukewa a wajen tana cire dan kwalinta hadi da sakin kuka tana mai rukunkume hannun nata a jikinta

Da dan karfi ta ce" Sai dai ka kashe ni, kana tunanin tunda na tunkari kowa da maganarka zan ji tsoron birgarka ne?, Kennan har dauka kake soyayarka da bukatar da nake biyawa kaina da wasu mazan daya ne?, Zaka gani, yadda ka kawo har yanzu baka mu'amalanci mace ba, ba zaka taba mu'amulantar wata ba, ko yar gidan uban waye!"

Sai da ta ci kukanta sannan ta mike da dan kwalin ta nufi ciki ta nemi wajen ruwa ta kunna ta wanke fuskarta sosai ta gyara daurin dan kwalinta sannan ta juya da niyar fara isar da sakonta a yau yau ba sai gobe ba!

A lokacin da ta shigo Mama ta gama sallar la'asar kennan Shuwwa na tsakar yi ta karaso da sauri ta zauna a kusa da yar uwarta ta riko hanneyenta ta fashe da kuka

Kukan da ya saka Mama zabura a tsorace tana kallonta

A gigice Mama ta shiga fadin" USEINA menene? Tun dazu na fita na nemeku sama ko kasa ban ganku ba menene? Kukan me kike? Ina yake ne?"


Useina ta sake waigawa wajen da SHUWWA ta kai sujadarta ta karshe ta ce" Yanzu Hasana dama SON zai yi auren matar da saboda ita zai nuna min komai na iya faruwa idan har ban fita a harkarta ba?, Dama zan ga irin ranar nan?"

Mama ta kalleta a hankalce ta ce" Useina kin ga, ki nutsu dan Allah ki fada min me yake faruwa yau kuma?"

Useina ta sake yin yadda ta saba dan ta hauda Maman da sirikanta, ba kunya ba jin tsoron Allah bale na Muhay da ya gama ja mata kashedi ta ce" Tunda na shigo dakin nan yarinyar nan ke kin wani irin kallo, tunda ta ji kin yi maganar rigar jikina ta dameni tana gannin kin fita ta ce da ni kamar yar bariki?, Ta dora da fadin bama kama bane yar bariki ce ni, raina ya bace na budi baki da niyar yi mata magana shikenan Son ya tare ya hanna, hakan ya bani mamaki na tsatsareshi da ido uwa uba a gabana ya rukunkumeta ya shiga kissing dinta, Hasana da kika shigo ya saketa ya jani ya gindaya min kashedin a kan matarsa yana iya yanke zumunci da ni kwata kwata, cewar a kanta babu abinda ba zai iya yiwa kowa ba ciki kuwa harda ke da kika haife shi, ya ce yana iya zabarta ya bar kowa, in ina gardama na tambaya ina tsohuwar matarsa?, Hasana kina kallo ya sake auro mana masifa?"

Irin kallon da Mama ke yi mata dole ya saka mutun a cikin tunanin fasarar kallon

Mama ta tsareta da duban nan ne tamkar tana son gane ita din wata irin halita ce?

Tsoro, tashin hankali kala kala suka ziyarceta,
Tabas abinda Shuwwa ta fada bata yarda da shi ba domin maganar da ta fada sam karyar bata tsaru ba, ta dai hakura ta bar maganar a haka ne dan ta cire wasi wasi da shakun dake cikin zuciyarta

Sai dai a yanzu wanda kanwarta ta fada ya sakata a cikin tashin hankali
Gaba daya maganar da ta fada tana iya zamtowa gaskiya duba da a saman Shuwwa din ta shigo ta same shi, sannan a gaban idannuwanta ya damki hannun yar uwarta ya fita da ita, bayanma wannan a kan wani dalili zata yi masu karya ne? Shin da gaske ne abinda ta fada cewar MUHAY ya fada a kan Yarinyar nan?

Hankalinta idan ya yi dubu ya tashi har kunnayenta suka jiyo mata salamewar sallar Shuwwa ta juyo da sauri baki da hanci a bude tamkar zata hadiye su da su tana kallonsu da mahaukacin mamakin da ya ki buya

Ta san bata da bakin da zata taro maganar nan, da farkoma ita ta saka kanta a cikin ramin nan, anya kuwa tana iya fitar da kanta?

Mama dake kallonsu jin zuciyarta zata buga ya saka ta mike da sauri ta nufi hanyar fita ba tare da ta yiwa kowa magana ba, wanda hakan ya daka Shuwwa mikewa da sauri da niyar bin bayanta, sai dai riko mata mayafi da akai aka dawo da ita ya sakata juyowa da sauri tana kallon matar nan da fuskarta ta zame mata tamkar ta kumurci

Yar dariya ta yi tana kallonta ta ce" Dama kin yi hakuri kin anfani kyanki ta hanyar da ta dace da ke, da kin guji zakin da ba mahadin Barewa ba to da ina iya yi maki hanyar da zaki mori kyan naki......kina neman yiwa al'amarin da baki da ci a cikinsa shishigi? Meye mahadin hanyar mai cin ciyawa da mai cin nama? Uban dawa yake sai zakanya zata iya da shi ba ke ba!"

Tana gama fada ta zo da niyar wuceta ta tafi, sai dai abinda ya dakatar da ita jin muryar Shuwwa wace ta cika da mamaki da bugawar zuciya tana kallonta ta ce" Ji mana?"

Dan dakatawa ta yi ta juyo tana kallonta da cikaken rashin tsoro irin na rikakiyar yar bariki tana kallon Shuwwa din da jin wata magana ta rainin wayau tana neman yi mata wai ji mana?

Shuwwa ta dan sake dubanta tana kiyasta shekarunta a zuciyarta a nutse ta ce" Mama?, Sorry wacece zakanyar? Wacece barewar?"

USEINA ta yi wani yannayi na ta dan shaka kadan kafin ta dan girgiza kanta a kausashe ta ce" Kece Barewar, da kike nama a gaban zakanya, watau ni!, Da zaki yi biyaya zaki iya tsira da mutuncinki?"


Tabas bata yi hasashen jin cewa Useina ce zakanyar ba, ta zata ko y'arta take YIWA yaki, sai dai da ta fadi hakan kamar ta gaura mata mari ne, domin sai da ta ji kamar zata kifa kafin take iya rike kanta tana kallonta ta ce" Mama, wai ke Zakanya a matsayin uwar zaki kike nufi bakya so danki zaki ya rabi Barewa ko yaya fahimtar da ni?"

Haushi ya saka Useina nunata da yatsa ta ce" Ke saurara min, ba shirme ya tsayar da ni a nan ba, idan baki fahimta ba zaki gane !"

Da sauri Shuwwa ta bi bayanta gannin ta sake juyawa zata tafi da sauri ta saka hannunta ta janyota baya ta yada ta juyo a haukace da mamaki tana kallonta

Tun daga kasa har sama Shuwwa ta daukota da kallo kafin ta sauke a saman fuskarta
Yar yatsarta manuniya ta nuna mata zaryan tana kallonta a kausashe ta ce" Ki cewa haukan dake kullawa ko kuncewa a cikin kwakwaluwarki cewar na amshi tayin, ki fadawa rayuwarki cewa da aure ko babu tabas sai na zama Barewar Zakin nan, domin sai ya farauceni ba dare ba rana dan ya ci abinda yake lafiya a gareshi watau ni da nake namana wajenshi!, Ki karra sakawa cikin zuciyarki cewa zaki baya cin zaki bale tsohon nama ai ba na Uban dawa bane!, Ki fadawa kadararki, ko nace gangancinki cewa na siya da farashi mai tsada ba gudu ba ja da baya sai na deba kuma sai na amshi kaya a duk lokacin da hakan ta kama!, Kina iya sakawa a sakeni, aman walahi ki sani sai na haukata duniyar mafarkinki ta yadda zai dawo ya zamto mumunan farkawarki!, Domin ni zahiri ce , kuma na sha iskar duniya sosai ta yadda YAR BARIKI irinki ba zata gigitani ba!, Dama kin kadaice kanki kin sha shinkafar bera an turbune ki da wannan abin kunyar, a gaba ki gani a aikace cewar ya zabeni a kanki!".........


Da mugun mamaki Nahidht ke kallonsu , tunda ta tunkaro take jin maganar Shuwwa a kausashe ya saka ta shigo da sauri

Abinda ta gani ya sakata zubawa Shuwwa ido tanai mata kallon ko ta haukace ne?

Da sauri ta kalli matar da itama mamaki ya nemi halakata ta sake bin yarinyar da ta rainawa ajawali kallo kafin ta fita da sauri tana kai hannunta wajen zuciyarta dake dokawa da gudun balakin tsoron da ya fi na kashedin da MUHAY Ya yi mata karfi

A zabure Nahidt ta juyota tana kallonta kafin ta saketa ta shiga fadin" Shikenan, shikenan, hankalinki ya kwonta, ke wannan fa itace abokiyar tagwaitakar mamansa, me ta maki da zafi da kika nuna mata kalar naki haukan ? Kin san da an sake ki an gama? Mun shiga uku yanzu Shuwwa sai da kika tsinke auren? Tabas Idan mama ta farka sai ta ci uwar ubanmu"

Shuwwa ta kai zaune dabar tana jin wani irin ciwo a zuciyarta wanda bata san dalili ba rai bace ta ce" Walahi, walahi ko ya sake ni sai na bishi irin yadda karya zata bi shi, sai na zamto tamkar bindi a jikinsa, sai ya fuskanceni na gigita rayuwarsa, yadda wannan tsohuwar guzumar take sonsa ba zata taba samunsa ba, ke Nahidt Son Muhay take yi , so irin na soyaya!"

Nahidht ta yi wani irin zabura tana sakin hijab dinta kasa
Jikinta na dan rawa ta dauko Hijab din tana kallon Shuwwa ta girgiza kanta ta ce" Ke kin ji me kika ce?"

Shuwwa ta yi wani murmushi mai ciwo tana gyada kanta

Nahidht ta yi gagawar zuwa wajen salaya ta gyara shi da kyau tana fadin" walahi talahi duniya ta zo karshe, bara na yi sallah kar a tasheta da sallah a kaina, Innalilahi Allah ka sa na auri malan kafin a busa kaho, mun shiga uku Shuwwa na shiga uku wannan matar da tsinaniya ce? Ke gaske na kasa gaisheta ashe uwata ce a bariki Innalilahi wa inna ilaihi raj'une.....Shuwwa mun shiga uku...." Haka ta yi ta sambatu, ita kuma Shuwwa din gaba daya jikinta tamkar wace aka zarewa lakkah
Ya kasance ne ta kurawa waje daya ido ta kasa fahimtar komai
Bata taba jin tsana da kyamatar a rabi abinda take jin a yanzu kamar nata ne irin kar matar nan ta rabe shi domin ai d'an y'ar uwarta ne irin na yau ba

Da wani takaici ta tashi ta fice ta nufi dakin da mahaifiyarta take ta zauna ta zuba mata ido tana kallonta

A yanzu tsafta ingataciya na tare da iyayensu, sai ramar da dan ciwon da ake magani ba dare ba rana
A haka ta tare har yar uwarta ta tardota suka zauna tare ba tare da sun yi tunanin makomarsu a kusa ba, ganni suke koda iyayensu na hali na rashin lafiya a yanzu da suke raye babu mai cin masu, ganni suke dukan wanda zai ki su shikenan ya ki su ai ga mamansu a kwonce ota zata so su! ( Uwa kennan, iyaye kennan, Allah ka gafartawa iyayenmu, ka sa su gama da duniya lafiya,, wa'inda suka rasu Allah ka jikansu, ka basu aljannah ya Allah)

__________________________________________

Bayan sallar magariba


"Ka ga, ai yaren sai ai masu uzuri ko? , Yaren sun cencenci uzuri sosai........, Abinda yake damunahhhhh, abinda na kasa hadiyewa shine zancen gaba dayansa, Meme shin dukkan abinda matanka ke yi mata kafin ka rabu da su gaskiya ne ko kuma ba gaskiya bane?, MUHAY da gaske kaine zaka ce wai saboda matarka nima sai ka bata min?, Ka ga ni fa na haifeka.....gaba daya sai nake kin yarda da maganar ban san ba tsananin sonka ke ya sa haka ko menene?, To aman idan ban yarda da maganar ba da me zan yarda? Kai ka ki zama ka yi maganar da ni..... Sam baka yarda da ni ba, kana boye min damuwarka sosai Muhay....., Shin me yake faruwa tsakaninka da mamanka???? Innalilahi wa inna ilaihi raj'une MUHYIDEEN zuciyata ciwo take yi, shin ka kai shekarun da dole zan yi hakuri da halayanka na rayu da kai a haka ne ko menene ?, Shin ya kai wajen da zan maka biyaya ne ba ka yi min ba?......"

A sanyaye CHIEF OF ARMY dake kallonta cike da tausayawa , sannan ya kalli MUHYIDEEN dake duke kansa a kasa a gabanta yana sauraronta tana kuka , gaba daya ta rikice ta shiga a duhu, so take sai an fahimtar da ita ko menene, bayan bata san rashin sanninta ya fi sanninta kwonciyar hankali ba

A sanyaye ya ce" Wife....."

Kanta take girgizawa ta ki koda kallonsa

A sanyayen ta ce" Dan Allah Abansa kar ka ce komai ka ji?, Na san so kake ka ce min na bar maganar ko? Kar na takura masa ko? Shi ga wanda ya isa ko?, Shikenan ya tashi ya tafi.....ba zan ji haushin matarsa ba domin yarinyar nan tunda na ganta na ji ina kaunarta a raina, na ji ta kwonta min a matsayin matar d'ana, harma na ji tarihinta na karra jin tausayinta da muradin talaf mata, gashinnan har yanzu bata dawo ba, ta yiwu ta tsorata da yannayina ne, bata san a cikin halin kaka naka yi nake ba, abubuwa sun shige min duhu kuma an ki a fitar da ni..........., Ai ni zan yi farin ciki ka so iyalinka fiye da kowa, sannan ka sawakewa yar mutane da baka kulawa ka barta ta tafiyarta ta samu daidai ita, aman ba zan takura maka ba idan ka ga dama ne Muhay......" Ta karashe tana cicibawa da niyar bara masu wajen, stlll kuma tana kukan

Hankalinsa ya karra tashi, sosai hankalinsa ya tashi

A rikice ya rike kafafuwanta yana sada kansa a jikin gwuiwoyinta muryarsa na fita da kyar dan furucin da zai yi bai san me zai haifar ba , ya dago idannuwansa da sukai jajajir daidai hawayenta sun sauka suka sauka a saman fuskarsa , da gagawa ya ringa girgiza Kansa ya ce"




๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ Oh rainarhhhhhhhh๐Ÿ˜Œ๐Ÿ˜Œ๐Ÿ˜Œ๐Ÿ˜Œ๐Ÿฅบ๐Ÿฅบ๐Ÿฅบ๐Ÿฅบ๐Ÿฅบ๐Ÿฅบ๐Ÿฅบ๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜ALK'ALAMIN KADARATAH





Na

*Sajida*


Page


5๏ธโƒฃ0๏ธโƒฃ



Da gagawa ya ringa girgiza kansa ya ce" Mahmahnah......."

Mama ta sake jin wani takaici na sake tukota dan hakaa ta janye kafarta fahimtar da ta yi baa fada mata ba zai yi ta zagaye shi da sauri ta nemi barin dakin

Chief of army ne ya yi gagawar dakatar da ita ta hanyar ambatar sunnanta kai tsaye sanann ya mike shima jikinsa a mace yana kallon bayanta

Muryarsa a sanyaye ya ce" Na so ki kasance mai hakuri da kawar da kai har Allah ya nuna maki alkhairin abin, domin tsananta bincike bashi da wani alkhairi , bashi da kyau, sai dai kashhh, kin kasance mai yawan son bin didigin abubuwa, gashi yau har kuka kike masa dan yana kare ki da bacin rai?, Hasana yaya zaki yi da gabar dake tsakanin Yaronki da yar uwarki?, Ya nisanta kansa da ita , kin matsa kin kisanto shi da ita, subahannalah, Hasana"

A dan tsorace ta juyo tana kallon Chief of army, sannan ta kalli Muhay da ya kifa kansa a jikin kujerar da ta tashi gaba daya jikinsa na jijiga kamarma wanda yake yin kuka ko menene? Tashin hankali mai girma ta ji na karra ziyartarta, sai dai a yanzu babu gudu ba ja da baya ta riga ta kawo wannan gabar bata da halin yin koma baya

Tana kallonsu Mijinta ya dan sake matsota kadan, a sanyaye ya ce" Zan iya kiran hakan da muguwar Kadara, wace ke sake samun waje a wajen wanda ya yi wasa da fadawa Allah, tabas zuciya ce bata da kashi, aman kuma Allah ya bamu hanyar da zamu iya samun kadararmu da sauki idan har muka kai masa kukanmu, kin ga da ace tun da farko da ta faraa jin irin haka ta yi kokari ta nemi shawara sannan ta sake kusanta kanta da ubangijinta , to da tabas ta samu sasaucin koma menene, sai dai kash, kadara, sakaci, muguwar taraya, son zuciya ne suka hadasa haka, kuma sakaci da adu'a ya sa abun ya sake yin tasiri a kanta....."

Sake kure fuskarsa take da kallo tana ji tamkar ta saka haannunta tta bude masa bakinsa ya yi magana ta yadda zata ji takamaiman abinda yake faruwa, domin a yanzu kwata kwata ya durmiyata a cikin wani duhun fiye da farko

Aa sanyaye ya ce" Tana son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login