Showing 165001 words to 168000 words out of 226733 words
ya dace ta bashi amsa ne?
A hankali ya dora kansa a saman kirjinta ya lumshe idannuwansa yana shakar kamshin dake wajen
Wani irin abu ya sake tuko shi mai rawa da bari ya dake yin sama sama da shi ya nemi maka shi a kasa a zaunen nan da yake
Ba zaku gane bane, daba ce a kule a jikinsa mai neman hanyar da zata bale ta yi yawo tun karfinta, tareta yake yi tunda ya n tana iya mikewa harma ta nemi abinci a jikin jinsin da ba irin nasa ba, kakau yake yi mata yana sake daureta tam da dukan karfinsa, sai gata tunda ya hadu da wannan yarinyar karama, yar ficiciya, mai halaya irin na mahaukata, mai aljannu, take sake hauda farashin lafiyar jikinsa, ya sani halalinsa ne sai dai gaba daya idan ya tuna mazan da ta aura daya na bin daya kowane yana zuwa wajen nan dole ya ji zuciyarsa na kuna da tunanin a kan me? Me yasa ta ringa gagawa a rayuwarta ne? Me yasa bata kasance mai hakuri bane? Ya salam abin nan ma ci masa tuwo a kwarya, yana hargitsa tunaninsa da zaman lafiyarsa sosai , shi yasa ya gwamace nesa da ita fiye da kasancewa haka da ita, aman a irin ranar nan da zuciyarsa ta babale ta rikice ta haukace da irin umarnin da mahaifiyarsa ta bashi na ya amshi dukiyarsa ya ba wanda yake so ya kula da abinsa ya bar mijinta ya huta hakannan, sannan ta bashi umarnin ya kama aikin da ak damka masa da hannu bibiyu ta yafe masa duniya da kiyama, sanadiyar haka kishiyarta ta yanke jiki ta fadi sumamamiya shi kuma ya fice a dakin ido rufe ya nufo bangaren mamansa yana nemanta, gannin bai sameta ba da sasarfa ya nufo bangarensa ya bude dan nemanta, sai gatan kuwa a gabansa tana turara muhalinsa baban bukatarsa ya samu dan moment da ita, ta rike shi a jikinta ko yayane, ta bashi abincin nan da yake so sannan ta shayar da shi da ruwan nan a bakinsa, ya zuka ya masa shan da sai ya kusan karar da shi kaf din ya jima da kishirwar nan a makoshinsa
A hankali ya talabo kumatunta ya rike sosai a hannunsa kafin ya sake matse kisancin da ya raba fuskarsa da tata sannan ya rike da kyau ya shiga shakar numfashin da take furzowa daga hancinta da bakinta har ya hade lebenta da nasa
Da mugun saurin balaki ta cire bakinta tana zazaro ido da sake kura masa ido da son gane shi din ne kuwa? Me yake damunsa ne yau?, harma ta saka hannunta da dan sauri ta dauke nasa dake saman rigarta ta gaba dardar abinsa hankali kwonce tana ture hannun nasa a hankali ta ce" Dan Allah ka bari....." Sai kuma ta juya da niyar sauka a samansa dan gaba daya yau wani iri ya zame mata
Yawun dake makogwaronsa ya hadiye da kyar sannan ya wartota jikinsa ta yadda ta fado, bai bata damar gane komai ba ya sake hade bakinsa da nata
Cikin barin jiki ya ringa tsotsar leben nata wanda hakan ya sa daga ita har shi jikinsu ke rawa kamar zasu hade su zamto abu daya a zaune a saman kujerar
Numfashinta ke neman barin gangar jikinta, hankalinta ke ta kololuwar tashi yana neman rikitar da ita gaba daya,
Laushi, kanshi, zafi zafin bakinsa da harshensa da irin kissing din da yake yi mata wanda ke nuni kamar rayuwarsa na depnded da lebunnanta ne ya saka kwakwaluwarta neman tsayawa da aiki kwata kwata
A birkice ya idasa saukowa kasa da ita yana sake kanainayeta a jikinsa hakan ya sa dukan wani abu dake jikinsa mai aiki ya motsa, haka kuma wayarsa ce, ky din motarsa ce du suka zubo kasa a saman cafet din da suke
A birkice ya ja dofuwar rigar dake jikinta mai laushi ya cire mata ita ta hanyar sakin bakinta yana cirewar kuma ya zubawa mutanen ido yana kallonsu, haka kuma dukan jikinsa na rawa
Farin shiga ne da farin shiga, sai dai kowa na tunanin dan uwansa tsohon hannu ne a cikin lamarin sai dai kashhh, babu wanda ya san cewa ainahin dan uwan nasa bai san lamarin nan ba
A hankali , sannan a daburce ya durfafe su ya dora hannunsa na dama a sama sannan ya masu matsar nan mai zafi wace ke bambanta sabon shiga da tsohon hannu
Zafin ya kai mata har kwakwaluwarta da matsananciyar jin kunyar abinda ya kai hannunsa har jikin wannan wajen, gaba daya ta rukunkume shi tana rintse idonta muryarta na rawa da abin kuka kuka ta ce" zafi , ka bari zafi"
Sake cirota ya yi yana ta kallon abin da tunanin ya saka a bakinsa ne ko aa?, Dama abin ba dadi bane yake yi masu idan aka taba ko menene?, Bai san cewa ba eh lalle dadin ne, aman farin shiga koda da dadin ba dai farkon tabasu ba gaskiya, dole zata ji zafi zafi komai dadinsu
Numfashinsa ke sauka a tsere a tsere, gaba daya ya idasa bale boturan rigar tasa daga gaba sannan ya sasauta rikon da ya mata ya kuma nemi sabule dogon wandonsa
Du tana langwabe ne a jikinsa jikinta a mace tana tunanin babu kasa me ya kawo zancen kokowa?, Wai me yasa ya nemi haka nema ita kam?
Sai dai a lokacin da ya idasa cire dogon wandon nasa harma ya sake mayar da ita jikinsa a hankali ya dauki hannunta ya kai wajen da daga ita har shi sai da suka dan zabura , ita na tsoron abin, shi kuma na jin hannunn mace koma yace wata halita bayan shi ya taba wajen nan na farko a rayuwa
Ji ya yi zai mutu so yakr kawai ya yi ko hankalinsa zai kwonta, nauyi da zafin da mararsa ta dauka ne ke son halaka shi, a birkice ya kara kusantota da shi ta yadda zai iya yin adu'ar saduwa da iyali kamar yadda adini ya koyar ya yi matukar sanyayar da muryarsa ya fara fadin " *"Allahumma jannibna shaid'an...wa jannibi shaid'ani ma razak'tana (Ya Allah ka nisantamu daga shaid'an, ka kuma nisanta shaid'an daga abinda za'a azurtamu da shi)* "
Sai dai kashhh, muryarsa ba muryar sirri bace, muryarsa sam bata da sirri, adu'ar nan tunda ya fara furtata ta dawo cikin hayacinta, birkice ta gane nufinsa a lokacin da ta ga ya karra jan pant din dake jikinta, a hakan Idan ta fahimta ya gama shiryawa yi ne zai yi, za'a mayar da ita cikakiyar mace a gida daya da iyayenta da sirikanta, za'a mayar da ita cikakiyar mace a saman cafet a irin wannan lokacin, namijin da bata san menene asalin niya a zuciyarsa a kanta bane zai auka mata a irin wannan lokacin ya mayar da ita cikakiyar mace?, Idan fa yana gamawa da kwalon mangwaro zai yada ne ya huta da guda? Idanfa zata kasance ne abinda zai dana ya zubar ya dauki wace ta dace da shi? Shikenan sai ta zamto ba dan abin kurin da take tanada dan birge mai ita? Shikenan zata tashi a babu abinda zata ba MALAKKINTA? , hakan ba zai yiwu ba sam, ba zata iya ba
Ganewar da ta yi ya sasauta mata riko yana neman cire nasa Abinda ya masa katanga da ita ya saka ta janye da mugun saurin balaki har tana dakuwa da kujerar dake kusa ta zagaya ta afka kicin din falonsa taa janyo da karfi ta rufe ta datse da ky sannan ta silale a nan daga ita sai pant ta hade bayanta da jikin kofar ta rintse idannuwanta jikinta na ci gaba da yin gab gab gab tamkar zata summa dan tsoro
Tunda ta arta a gujen ya raka sittin saba'in din da kallo ya yi mutuwar zaune da sake zuba mata ido har ta mako kofar da ya ji tamkar ta soka masa wani mashi ne a kahon zuciya, ya sake zubawa kofar ido yana jiran ta sake budewa taa kuma fitowa aman abin ya gagara rufma kake gani ta rufe kicin din da ya zamto masa tamkar bakon abu a wajen
Tsai ya yi da tunaninsa ya sake zubawa kofar ido, dukkan wani abu dake iya saka shi a duniyar farin ciki ne ya fara saukar da farashin farin cikin kafin mararsa ya sake dauka ya daure sosai da sosai ta yadda ya rintse ido da karfin balaki ya sake budewa a hautsine ya sake zubawa kofar ido
Bakinsa ya so budewa dan ya yi kiran sunnanta da kowani irin yare Allah ya sa ya samu hakan, sai dai sunnan nata ya ki fitowa saima ya samu kansa da nauyin baki kamar yadda mararsa tai masa nauyi
Hannayensa ya saka bibiyu ya dafe gaban goshinsa sanann yaa dauke wuta
Ya jima a haka kafin ya sake dago jajayen idannuwansa ya zubawa kofar ido a cen kasan zuciyarsa yana mai tambayar kansa tambayoyi kamar haka' Me hakan yake nufi? Ko fitsari take ji? Aman da fitsarin take ji ai da ta fito zuwa yanzu ko? Kuma fitsarin a kicin..........'
Ya sake tsatsare kofar da kallo ya sake ayanna' Shin guduna ne ta yi? Aman a kan wani dalili ? Ban kai matsayin yi da ita take nufi ba ko me?, .....' gaba daya bayan yannayin da yake ciki sai ya ji kansa na neman tarwatse masa, hakan ya sa ya shiga dadafawa da kyar ya iya mikewa da duku duku ya nufi dakinsa wajen da maganinsa yake ya duba ya ciro har kwaya hudu ya aha maimakun biyun da yake sha ya kora da ruwa mai sanyi sannan ya baje saman kafet din dakin barcinsa yana damke da mararsa yana ta zufar wahala har ya samu ya tafi a duniyar barci mai matukar wahala
Da kyar ta iya lalabawa ta fito ta dauki rigarta da hijab dinta ta zurmuka sannan ta fice a bangaren nasa ta nufi wajen adarta
Tana zuwa ta tarda ita kwonce tana waya da Malan dinta hankali kwonce
Fadawa ta yi jikinta ta rukunkumeta still jikinta na rawa sosai tana ta son saka kanta a kirjinta ta labe
A tsorace ta ringa kallonta tana neman zama da son ajiye wayar gefe tana fadin" Shuwwa? Shuwwa ke Lafiya ?"
SHUWWA ta sake komawa jikinta ta labe tana ta sauke ajiyar zuciya hadi da kallon bayanta dan du a tsorace take
Hankalin Nahidht ne ya fara tashi da gasken gaske, dama iyayen du basa nan matar Dad an yi asibiti da ita da yarenta dake koke koke sai sune a gidan, sai ta fara jin tsoron ko wani ne ya biyota haka? Ko kuma wani abu ne ya samu mijinta
A rikice ta sake riketa tana fadin" Shuwwa wai menene? Wani ne ya biyo ki? Ko wani abun ne ya samu mijinki?"
Shuwwar ta girgiza kai a birkice tana fadin" Ba zan kara ba, na zata zan iya abinda kuke fadi ashe ba zan iya ba, wayo Allahna ni tsoronsama nake ji, kennan ya wulakantani shikenan ya sakeni? Ai gwarama sautan da suke sakina basu yi komai da ni ba!"
Fahimtar inda maganar ta dosa ya saka Nahidt rungumeta a jikinta a sanyaye ta ce" Hey babyn auntynta, wanu irin kar ya taba ki?, Haba autan mama mijinki ne fa , kece fa mai kokari mai jajircewa"
Tana girgiza kanta ta zauna tana kallonta ta ce" Wani irin jajircewa gareni a gabansa?, Burina na faranta masa, ban sani ba ko bani da sa'ar a soni domin Allah ne?, Tubeni fa ya yi yake neman amsar abinda na dade ina rikewa nawa da nufin ya kwace m......"
Rufe mata baki da ta yi tana girgiza mata kai ya sakata yin shiru tana jin yadda zuciyarta ke dokawa da karfi sannan ta sake kwontar da kanta a saman cinyar Nahidht dake dan shafa bayanta
Sai da NAHIDHT ta kula ta dan fara dawowa cikin hayacinta kafin a sanyaye ta ce" Sirrinki ne fa, ibtin Aba sirrinki ne wannan, duk matar dake bayana sirrinta da mijinta lalle ta yi asara koda kuwa Allah ba zai hukuntata ba, balatana haramun ne, sannan yaya kike so ne?, Me kike so ne?, Ai yama yi kokari da yake kallonki kina dauke da abinda yake malakinsa , aman bai taba nuna maki yana so ba sai yau, shine kika guje shi, haba yar albarka kin san da ba'a gudun namiji ko? Duk soyayar da yake maki idan dai ke din nan kin zamto wace bata yi masa adalci walahi zai iya hakura da ke ne domin a kan wannan lamari maza basu da hakuri fa, Na san cewa a cikin duhu kike aminiyatah, na san cewa a cikin wasi wasin so ko kiyaya kike daga wannan bawan Allahn, aman zan fada maki wani abu, wasu mazan Allah ya sa kin fi zinari kyali, kin fi gol daraja ba zaki taba ji daga bakinsu sun bude sun furta maki kalmar so ba ko wani abun, su haka Allah ya halice su, ba zaka iya cenza su ba fa, ko me zaka yi ba zaka iya cenza su ba SHUWWA, koyon zama ake yi da su da halinsu sai a ci ribar zama da su, su a aikace suke nuna kalar tasu soyayar, kece baki yarda cewa wannan bawan Allahn na sonki ba, aman mu dake tare da ke mun riga mun yarda, Shuwwa ba zaki iya tantancewa ba, aman idan kina waje idannuwansa a kanki, haka kuma idan ya fuskanci wani na iya kallonki koda yayanmu ne baya iya boyewa, da idannuwansa da kuma motsinsa yake yakin dukkan wani abun da zai rabe ki, aman sai na ga ke sam bakya duba da haka........... Wani irin cutarwa kuma kike magana a kai? Ni fa ina gannin girmansa da kimarsa koda duk duniya zata ki shi, domin shine silar samun farin cikinmu da muka rasa.....shin ke bakya gannin hakan ne kanwatah?"
Shuwwa da idannuwanta ke lumshe tana biye da dukkan bayananyar uwarta ta dan dago ta ce" Nahidht so kike ki ce min shi a haka zan rayu da shi tamkar dutse? Bayan ni burina na rayu da namiji mai min kukan yana sona? Ya ringa min ihun yana so na?,ya zamana tamkar jelata sai abinda na ce ya yi zai yi? Ya nunan so a gaban kowama ya kareni da dukan karfinsa ya shagwabani? Yaya zan iya rayuwa da mutun mai halayarsa?"
Nahidht ta dan zarro ido da mamaki ta ce" Ki ce kawai rayuwar mafarki kike so ko kuma nace rayuwar karya?"
Shuwwa ta ce" Kina nufin babu soyaya a gidan aure? Ko bashi da zuciya ne shi a jikinsa?"
Nahidt ta yi Murmushi tana girgiza kanta ta ce" Babu soyaya ake zaune? In babu soyaya an saka maku wuka a kawunanku ne?, Dukan gidan dake dauke da mace da mijinta da y'ayansu koda tana zaune da shine domin y'ayanta to fa idan aka bincika akoy soyayarma, halaya ne na yau da gobe ke disasheta, da ace zasu kamanta dawo da kyautatawa da zata dawo , Shuwwa da kin fada ya yi uwarsa ce ke?, Ko kuma da kike so ya zamto tamkar jelarki kece mijin ba?, Kin ga ibada ne aure, zama ne na ibada, dukan ibada kuma sai da juriya da hakuri koda za'a kai ga ci, ki sani rayuwa baban nasarar da kika yi a yanzun amsa sunnan matar aure, zaki idasa ga ci ne idan kika yi hakuri kika ci gaba da zama da shi, Allah na tuba rayuwa ai zo mi zauna zo mu saba ne Shuwwa, zaman da yake kulun cikin dariya da farin ciki ina tsoronsa, ai zama dole akoy sabani wani sa'in, aman kuma ana ganewa ana hakuri da junna shine daidai, kin ga ina so ki fahimci wanene mijinki sannan ki masa adalci a zamantakewarku, kar ki yi wasa da damarki, kar ki yi sakaci da aljarki Shuwwa, ba zan so ki kasance mai yiwa mijinki rikon sakainar kashi ba, idan kuwa yana zuwa kina kauce masa babu abinda ba zai faru ba ciki harda daina gannin girmanki da karo wasunki da zasu tarbe shi da zarar ya buda hannayensa., Ba'a barin namiji da yinwa Shuwwa, ba'a yi........"
Fuskarta ta shagwabe sosai tana langwabe kanta ta ce" Ni tsoro nake ji ne Nahidt, walahi tsoronsa nake, kuma yanzunma cewa ya yi yana jin yinwa da ishirwa kin ga baima ci abincin ba inaga ya kwonta barci"
Nahidt ta sake kureta da kallo kafin ta yi murmushi tana girgiza kanta ta ce" Mace bata kadan, komai girman namiji kuwa baya fin karfinta Shuwwa, rijiya ce mai daukan guga, haka kuma babu wanda ya girma da dadi koda girman bariki ne, sannan ki kokarta ki koma ki gani ko zai yarda ya ci abincin yanzu kin ji? In bandama abinki mutumen da kece shedar yawun yan bariki a kansa ne kike son yin wasa a lamarinsa?, Koda yake baki san menene kalmar nan ba, bana so ki santa ta tsiya kanwata, bana so ki san sharin yar bariki, domin wata yar barikin komai taurin kan namiji sai ki ga ta shawo kansa cikin sauki bale naki mijin da yake da bukatar hakan? Wai har kin manta niyarki a kan kudurin mamansa a kansa?"
Ido ta lumshe tana sauke ajiyar zuciya tana ta auna magangannun Nahidt din, har aka fara kiraye kirayen sallar magariba Nahidht ta mike tana fadin" Abanki fa gobe zai juya dan ya sanar masu wai da wata magana, ban san ta mecece ba da ba zasu iya bara min shi ya karra kwana biyu a nan ba ni kam"
Ita dai da ido ta rakata har ta shige bayi kafin ta sake gyara zamanta tanaa jiranta
Tana fitowa a bayin itama ta shiga ta kwabe suturarta ta shiga tsaftace jikinta kafin ta dauro alwallah
Sai da ta cenza kayanta ta yi sallah sannan ta mike ta koma bangaren nasa da wani hijab din ba wanda ta cire aa jikinta ba
Tana shigowa ya yi daidai da dawowarsa kennan daga masalaci da carbinsa a hannunsa na hagu yana ja a hankali, a hannun damar kuwa waya ce yake ta gwada kiran Dad dan ya ga basu dawo ba, ya yi ta gwada kiran wayar mamansa bata shiga, gashi harda sultan a yan rakiyar bayan yanzu yaronsa ke fada masa tarkonsu fa yana daf da kama kurciya domin wanda