Showing 180001 words to 183000 words out of 226733 words
bakya iya bambance maganar da zaki yiwa mahaifiyarki?"
Da sauri ta fahimci abinda bakinta ya fadi, ta kuma nemi nuna ba haka take nufi ba, sai dai mamanta bata bata dama ba ta ce" Ki saurara, ki kula, kar ki saki ki je gaban mijinki kina sakin maganar du da ta zo maki, ki iya tauna harshenki ko a kan kawa ce bale mijinki ko mahaifanki, na zauna a nan ne dan mu yi maganar film ko ta shashanci? Magana nake maku ta gaskiya!"
SHUWWA ta kalleta da kyau idannuwanta na rage girma ta ce" Mama, kina nufin mu din masu gata ne bar haka aman muka kasance a cikin garanrambar rayuwa irin haka?"
Nahidt ta ce" Mama kina nufin dama Abanmu sarki ne muka rayu a cikin garinsa aka rasa mai bamu tuwo har sai da na nema ?"
Shuwwa ta dora da fadin" Mama dama garina na rayu datawan ggarin da samarin suka ringa aurena sunna sakina?"
Kuka ke neman kubce masu, Nahidt da muryar kuka ta ce" Saboda mulki ne akai mana hanyar halaka aka haukata mana mahaifinmu, aka wulakantar mana da mahaifiyarmu? Shuwwa anya zamu iya yafewa mutanen da suka aikata haka kuwa?"
Shuwwar ta ringa girgiza kanta hawayenta na zubowa ta ce" Wani irin yafewa ne zamu iya yi? Ki duba ki ga irin yadda muka rayu a garina? Ashe garin nice mai damar ihun fadin garina ne?, Har muka bar garin akoy masu kiranmu y'ayan agulla, baki shinne sunnayenmu, karuwai y'ayan iska haka sunnanmu yake Umahhhhhhhhh"
Idannuwanta ta lumshe itama hawayenta ya samu danar zubowa, sannan ta basu dana sukai kukansu sosai da magangannun cewar tabas ba zasu taba yafewa wanda ya saka suka shiga a wannan rayuwa ba
A sanyaye ta ce" Ku yi hakuri,......"
Sai kuma ta matso da kanta kusa da su kafin ta janyo su jikinta a hankali tana dan taping din bayansu a sanyaye ta sake furta" ku yi hakuri, kun san kowani bawa da kalar jarabawar dake iya samunsa a rayuwa, sannan tun ran gini tun ran zane........., Kun ga Allah ya halicemu ne da wannan rubutu a tare da rayuwarmu, aman kuma ya sanyaya mana zafin rubutun ta yadda ya bamu ikon gannin yau cikin hayacinmu, tabas an cuta mana, an zalincemu, aman kuma muna tafe da haka ne da sakayar mai sama, da kariyarsa a garemu......"
Ta ja numfashi ta ci gaba da fadin" Mutane ai kowa da irin yannayin rayuwar da yake kwabawa, tabas basu yi maku adalci ba da suka mu'amalanceku a haka koda baki ne ku, komai zafin kadarar kasancewarku tare da junna ya dace su baku daraja komai kankantarta domin yan Adam kuke masu daraja................., Aman duka wannan ba shi zai saka mu kasa godiya ga Allah ba, kafin mu rabu kun rayu ne like a princess domin mahaifinku ya yi nema ya wadatar da ku da zufarsa ya kuma shagwabaki da soyayarsa..........., Bayan mun rabu kuma ku kadara kun fuskanci jarabawar rayuwa ce wace Allah ke yiwa ingantatun bayinsa ita, Nahidt, IBTISAM babu abinda zaku yiwa kowa domin a gabanan ba burina ku ci gaba da rike kowa a rai ba, burina ku rayu cikin farin ciki da shinfida kyakyawar shinfidar soyaya a gidajen aurenku, kun ji y'ayana?"
Da wannan ta rarashe su, ta lalame su sosai, har suka dawo suka saki jikinsu suka ringa hira
Magariba na yi da kanta ta yi tsaye a kan shirin y'arta domin Mamansa na cen wajen mutanen da zasu yi mata rakiya wa'inda suka taru harda taruwar mamaki, domin sun taru sosai kamar rakiyar sabon aure, koda yake ita ta yi gayar mutanenta na arziki cewar za'a yiwa amaryar MUHAY rakiya gidansu da zasu tare, da yawan ciki kuma sun zo ne dan su ga sabuwar amaryar da zai kwalawa saki kwana kusa, dan kowa ya sani ne Muhyideen baya zama da matan aure, shi a nan nasa kalar hau din ya sauka
A wannan karron yan rakiyarta dakinta da Fauzy ce a ciki, kasancewar mijinta ya koma gida dan ya je wajen dangin iyayen nasa ya fara yi masu maganar bisa umarnin Father ya sa aka saka ta kwana da ita kafin safiya ta yi maza ta dawo gida, domin gidan a zagaye yake da sojawa ta ko'ina sannan tana da masu aiki birjik, domin gidan ya wuce misalin a ce ba za'a dauki yar aiki ba
Da katon Hijab din da aka saka mata mai ruwan madara suka rakota suka sakata a cikin mota,
Tabas aure mai gata daban yake, domin a da bata yi kukan rabuwa da gida ba a yau sai gashi motocinsu na dagawa ta fashe da wani irin kuka tana dora kanta a saman cinyar Fauzy tana ji kamar ta rabu da iyayenta kennan ba zasu kuma haduwa ba, watau yau ta san ta tafi a gefenta babu yar uwarta , aminiyarta, mamanta, aure ya raba , rabawar da ya saba, watau rabawar da sai dai ta zo ta ga gida ba dai ta zo ta zauna a gida ba a fatan da suke yi gaba daya
Tabas gida ya ginu, sai fatan samun zaman lafiya a cikinsa, haka kuma yan rakiya sun sadata da dakinta, inda matar Father ta sake yi mata nasihar da ta saka ta yi nazari ta kuma gane cewar Eh lalle haka ne......ko me ya tunkaro rayuwarta idan ta yi hakuri ita zata yi galaba a kansa, ta kasance mai hakuri a kan komai, ta yi hakurin ibadah, ta yi hakurin ibadah........domin ibadah mai daukan dogon zango ce har sai idan numfashinka ne ya katse
A haka suka fice suka barsu su biyu ransu, kuma Fauzy ta shiga waya da mijinta hakan ya sa ta shaka ta yadda bargo a kusa da ita ta kwonta domin ba zata iha shigewa dakin cen makeke ta yi barci ba gaskiya , ana iya sacema ai a dakin gaskiya!
HML Shuwwa
______________________________________
Washe gari sai da Fauzy ta tayata dukkan wani abinda ta san ya dace ta tayata, watau jera kayanta, da sauransu sannan suka yi wanka suka karya kafin ta yi mata salama domin Nahidt ce da kanta ta yi kiransu cewar Su MUHAY fa sun dawo maza su tabatar sun gama abinda ya dace ta dawo gida dan gayacen ana masa nasiha, ga dukan alamu kashedi ake masa
Ita dai ba dan ta so ba ta bar Fauzy ta yi tafiyarta, tana tafiya kuwa sai kewa da girman falon ya nemi ya dameta, dan haka ta kunna TV ta kwonta tana jin motsin masu aikin da ta saka biyu su zauna dan taa ringa jin motsinsu a shashen nata domin sun yi girkinsu sun gama tatare da ita har sunna mamakin dama ta iya girki haka? Kuma ba kiwya sannan amarya? Sun yabawa tsaftar girkinta domin sun yi karantun girkin ne su aman kuma sun yabawa nata girkin, harma suka bada hankalinsu dan kara daukaka iliminsu a fannin girki.
Tana tsaka da kallon Film din da ake nunowa a tashar larabawa ya bude kofar a hankali ya shigo da salama a bakinsa ya ja ya tsaya yana karewa falon kallo da kuma wace ke kwonce saman doguwar kujeraALK'ALAMIN KADARATAH
Na
*Sajida*
Page
6️⃣3️⃣
Tana tsaka da kallon Film din da ake haskowa a tashar larabawa ya bude kofar falon da salama a saman lebensa a hankali, sanann ya sanyo kafafuwansa sosai yana maida kofar ya rufe ya tsaya yana bin falon da kallo har ya sauke duban nasa a samab wace ke kwonce saman doguwar kujera sanye da farar riga irin doguwar nan mai siririn hannu , aman rigar ta tatare ta yi sama kusa da cinyarta wace hakan ya sa cinyoyinta suke waje da farar safar dake kafarta fara fesss tana dan balancing din kaffafuwan nata
A hankali ya hauda duban nasa har saman fuskarta, nan sukai ido hudun da ya saka shi kwacewar ajiyar zuciya yana sake tunanin to ba zata mike ta masa sannu bane dai da sauransu dai haka?
Ita kuma ta cire dara daran idannuwanta ta dan mike a kwoncen da take ta maida dubanta saman TV din tana yi kamar bata gane ko wanene ba, domin tsakani da Allah tafiyarsa ba labari ya mata ciwo a zuciyarta sosai, ba kuma taso a kuma aikata irin haka
Sake kallonta ya yi da kyau, kafin ya tabe baki ya sake bin dakunnan dake jere a falon da kallo yana tino maganar da mamansa ta fada a kanta cewa bata yarda ba koda wasa ya saki yarinyar nan ko ya yi mata abinda zai raunata farin cikinta da gangan, ta cire lamari na zaman tare aman bayan wannan kawai karma ya wani muzgunna mata aka ce
Dan jan hanci ya yi ya idasa shiga yana muzurai ya nufi dakin da yake tunanin nan ne ya dace ace nasa ne, domin idan bai manta yannayin ginnin nan ba dakin na biyu ne ya dace ya zamto dakinsa, tunda dai ai gidansa ne kuma baban dakin ne ya dace na mai gida kau?
Da kallo ta raka shi gannin ya bude mata daki ya shiga, ta sake tabe baki ta kuma gyara zamanta bata bi bayanshi ba bale ta tambayeshi me zai yi a dakinta ne?, Gaba daya tana so ta ga ciwon bakinsa har ina ya kai ne?
Yan mintunna tsakani ya fito daure da tawul ya karaso wajen da take zaune a hade ya ce" ina kayana suke?"
Dagowa ta yi dan ta kalle shi, sai dai da sauri ta cire kanta gefe tana jin kamar zata kurma ihun tsoron yadda tawul din ya masa, gaskiya soja bashi da kunya, shi sam baya iya suturta jikinsa nsa a gaban yara kanana?
A dan daburce ta ce" Wasu kaya kuma?"
Ya sake dubanta da dan haushi haushi ya ce" Na shiga bayina na tarar da bruch da maclean pink, da tawul pink pink a ciki, sannan tawul din nan yaya za'ai ya min ya min kadan!, Ina aka saka min kayana ne ni? An ce an kawo min komai?"
Da mamaki ta kalli daga dakin da ya fito , hakan ya sa ta ce" dama akoy hanyar dake sada wani dakin da wani ne?"
Kin bata amsa ya yi yana yi mata kallon da zata iya fasarashi da harare, hakan ya sa ta mike tana fadin" Mu je dai in gani "
Gaba ta yi ya bi bayanta , haka kawai idannuwansa suka sauka a bayanta dake juyi kamar wace ke yin hakan da gaya, yana biye da itan idannuwansa kyam a saman bayanta har ya zo gam ya hade da garu ba tare da ya san ya karaso wajen ba kuma a daidai garun yake tafia ba
Kasancewar abin ya zo masa a ba zata dole ya yi saurin dora hannunsa a goshinsa yana furta" aushhhhhh"
Turus ta yi ta juyo da sauri dan gannin abinda ya saka shi yin Aushhh, sai dai tana juyowa ya yi gagawar ajiye hannunsa yana matse fuska irin ga jarumin nan, hakan ya sa ta bi kirjinsa da kallo da hannunsa har ta sauke dubanta a kan hannunsa na dama da ya jimke, wanda ke nuna alamun ya daku fa
Bakinta ta dan tabe kadan da dan baya baya ta fara idasa shigewa dakin , sai dai me itama tana shiga ta harde da dogon wandon da ya cire ya yar a nan kan kofar dakinta hakan ya sa sai da ta yi tangal tangal kafin ta diba duwawu a kasa
Dan kara ta saki tana dafe kugu hadi da kallon abinda ya yarda ita
Da wani takaici ta dago dubanta ta sauke a kansa domin sai ta kula kamar wanda yake murmushi a saman lebensa, sai dai sunna yin ido hudun sai ya sauke idannuwansa kasa wajen wandon yana kallon wandon hadi da dan cicije lebensa na kasan
Da takaici ta bi dakin da kallo, ai kam ta ga gajeran a yashe a nan kusa da gadonta, gadon da ta yiwa gyara na kasa da kasa, tunda ta gyara shi fa tana son shiga ta kwonta aman idan ta tuna shinfidar da ta malala masa sai ta ji cewar gaskiya tsaftar jikinta ba zata hau gadon ba, watau gadon ya sakata maka masa shinfidar yan gayu irin ta sarakai , shinfidar da ta rantse da ubangijin talikai ta dauki kusan minti ashirin tana yinta, shine ya tako ya cire mata dan kampai ya yar mata a gaban gadonta sannan ya cire safar kafafuwansa da ya tako datin kasar da ya fito da na anguwanni ya dora mata a saman shinfidarta ita?, Uwa uba abinda ya fi kona mata zuciya ashe takalmin dake kafarsa da shi ya shigo mata daki? Oh no wannan daya, ba zata dauki wannan ba gaskiya
Hakan ya sa ta dago yar yatsarta ta yi kalar balbalin balaki sannan ta shiga fadin" Saurara malan saurara, ba zai yiwu ba gaskiya, a gidan nan za'a zo ne a dauki byro da takarda a ware abinda ake iya yi na yi hakuri da wanda idan aka yi lalle lalle za'a iya tono abin bacin raina, ka ga yarda gajeran wando a ko'ina ba tsafta bane, kazanta ce tukuru mai lasisin tsiya, idan ka cire yabadaibadai dinka kaimin bayi ajiye min idan na shiga zan wanke na shanya, bale ka ga ba zan dauki a cikin gidana a ringa shigo min da takalmi ba, lallalalalalaalalalalala, sannan a dakina a zo min a ari tawul dina kuma a karashe da ajiye min safa a saman bed? Shinfidar nan ai kana gani ka san na wahala wajen yinta, to shi musulmin kirki ba an ce ya sowa dan uwansa abinda yake sowa kansa ba?, Wannan lamari sam ban ji dadinsa ba, kar a kuma ina dalili ina dan mafari ne........?"
Ta karashe tana sake kallo fuskarsa, domin tunda ta fara magangannun nununawa ne take yi tana jujuyawa ta yadda zata masa gwari gwari ya gane da kyau ya kuma kiyaye, sai da ta ajiye maganar tata ne sukai ido hudu, ido hudun da ya so tuna mata cewar a maganar da ta yi fa kamar shine mai gidan, yama taba fada mata cewar ta daina cewa gidansa gidanta dan ba gidanta bane, sai gashi yau ta ce gidan nan nata ne,
Ido ta kikifta tana shagwabe fuska irin na jariri dan shagwaba, hakan ya saka shi saurin nunota da yatsa ya ce" Kar ki saki, kar ki saki ki min kallon nan dan ko kin yi sai na fada maki!"
Bakin ta idasa shagwabewa hakan ya saka shi zubawa fuskar tata ido yana kallonta har na tsayin minti daya da sekwani kafin ya sake gimshe fuskarsa yana fadin" Ba zai yiwu da gidana ace za'a bani karamin daki maimakun wannan, sannan da kike cewa wandona ni dan kampai ba dan kampai bane ba!, Kuma yanzu na fara cire wando na yar a inda na ga dama ai ban ce ki dauken abina ba! Ke ke tsayama ki ji......."
Sai kuma ya yi tsittt kamar redio ce ke yi kuma aka kashe, da sauri ya sake kallonta sannan ya kalli kansa, wani iri ya ji na kunya na son lulubeshi da takaicin kansa, yanzu wannan yar kucik din yarinyar ce ya tsaya yake kirtawa kashedi? Wannan har jaririyar ce ya yiwa kashedi?
Juyawa ya yi yana tafiyar nan ta gagawa sanann wace ake jefa kafa hakan ya sa ta bi bayansa da kallo har ya bacewa ganninta kafin ta sauke nanauyan ajiyar zuciya ta janye wandin daga kafafuwanta ta mike ta karasa ta duka ta dauke gajeran ta nufi bayinta a bayane tana fadin" Gidana ne ba naki ba....yenyenyenyen, gidana ne ba naka ba malan, sai ka daukeni daga nan din na gani mana!"
Ko da dare ya yi bayan ya dawo daga sallar isha'i ya gama salama da masu gadi ya shigo falon ya samu falon ba kowa , hakan ya sa ya nufi dakinsa yana cire doguwar rigarsa hadi da shafa cikinsa yana jinsa a cike har yanzun domin dazu ya shaki girkin da ya tarar sosai, ya ci girkin nan sosai da sosai har sai da ya ji zai yi amai, a gaskiya ya san yarinyar koda ba hankali akoy iya girki
Yana bude dakin ya ji wani sabon kanshin turaran wutar mai dadi
A hankali ya samu kansa da sakin lalausan murmushi yana kunna fitilar dakin, domin kanshin ya masa dadi a hancinsa
Idannuwansa yake warawa sosai a saman kanta
A kwonce take saman gadonsa ta dukunkunne ga dukan alamu barci ta fara
Idannuwansa ya kankance ya nufi gadon ya saka hannunsa yana jan bargon hadi da fadin" Ke ke sauko min a gado meye haka?"
A zabure ta farka tana kallonsa, sai kuma ta rintse ido tana sakin dan karamin kukan tabara ta ce" Walahi na gwada kwana a dakina ba zan iya ba, tsoratani ake yi har ce kin ake yi wai ke fita, ka ga ban saba kwana ni kadai ba domin tsoratani ake yi ......."
Ido ya sake zuba mata yana tunanin shin me ya aikata na laifi da horonsa ya kasance da wannan yarinyar ne? Hasbunnalahu wani'imal wakim shi kam yaya zai yi da yarinyar nan ne? Ya san ai tana da aljannu aman kuma har su hannata kwana ita kadai yanzun a dakinsa zata kwanan masa ne? A yana kwana davan dabanma yaya suka karata balle a sunna barci daki daya?
Bargon ya idasa janyewa ya sauke shi kasa ya shinfida da kansa sannan ya dauki matashin kai ya jefa sama da idannuwansa ya mata nunin ta sauka kasan
Shinfidar ta hanga , ta kuma kalle shi, wai tsakaninsa da Allah kasa zai sauketa ne?
Gannin yadda ya tsaya mata kerere ya sakata ziro kafafuwanta tana jan dogon wandonta mai santsi ta sauke kafafuwan nata kasa tana sake binsa da maraitacen kallo irin na a ji tausayin mutun din nan, har ta