Showing 138001 words to 141000 words out of 226733 words

Chapter 47 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

8004

sihiri ne ina mai tabatar maki in dai ba a zannen kadararsa ba Allah ya rubuta a cikin yannayin nan zai rayuwa har mutuwa, to fa nan da yan kwanaki zamu ga haske a lamarin, ki daina kukan haka kin ji?"

Kanta ta ringaa gyadawa tana sauke ajiyar zuciya

Shima ya sauke ajiyar zuciyar ya ce" Kin ga, da Malama da furerama suka ce a gaisheki"

Dan tsatsareshi da ido ta yi ta ce" Malan ina amsawa harda na fureran"

Dan kallonta ya yi kadan , sai kuma ya dauke idannuwansa a kanta ya nemi da ta sadashi da mutanen dake ciki, dan ya kula so ake a kure shi sosai, shi kuma in sha Allahu ba za'a kureshi ba yau din nan, kuma azuminsa da yardar Allah sai ya kai abinsa a cike cif
___________________________________

A lokacin da MUHAY ya fito da nashi kalar neman fitinar idannuwansa suka sauka a kan matar dake nufowa inda yake

Har ga Allah sai da gabansa ya fadi sakamakon ganninta a wajen nan, sannan zuciyarsa ta yi bakin kirin da ganninta

A hankali ya juya da niyar barin wajen dan ya cenza hanya, sai dai bai kai ga aiwatar da hakan ba ta yi murmushi tana kawar da makeken gilas din dake saman fuskarta wanda ya cinye rabin girman fuskar mai kalar duhu tana kallonsa da kyau ta ce" Ina zaka je?"

Dakatawa ya yi ya sauke numfashi dan ya daidaita kunar da zuciyarsa ke yi ya juya a saukake ya kalleta sau daya duba irin na ido cikin ido kafin ya ce" Hajia momy ce ke tafe?"

A hankali ta ringa ji ranta na baci da kiranta da sunnan momyn nan da yake yi, sai dai ba komai ta tabata jinkirinta zai zo karshe wata rana, dan haka itama sai dan murmusa masa tana sake binsa da kallon da ya fi tsana a duniya kafin ta ce" Nice kw tafe sweet men"

Baki ya tabe ya juya ya koma ba tare da ya ce da ita ta biyo shi ba, sai itace ta daga kafarta da dan sauri tana biye da shi tare da kallon askin kansa wanda sama sama ne aka aske masa , bakin gashinsa ya samu gyara na musaman sai walwali yake, har zuwa kunnensa da wuyansa

Dakin da Mama take ya tura a hankali ya shiga da salama a bakinsa

A yanzu SHUWWA na kwonce a saman bed din dake dakin, Mama kuwa tana zaunenta ne da carbinta a hannunta tana ja

Murmushi ya sakarwa Maman kafin ya wuce direct wajen da Shuwwa ke kwonce ya zauna a gefenta hakan ya sa ta dan janye kaffafuwanta sannan ta so juwaba barin da garun yake, sai dai dannewar da ya yiwa rigarta ya sa ta kasa aiwatar da hakan sai a haka ta tsaya

Shigowar ouseinarta ta sakata sakin murmushin da ya fito tun daga kasan zuciyarta mai cike da so da kauna harma ta mike daga zaunen da take fuskarta na idasa wadatuwa da farin ciki ta ce" Marhababuki yar uwatah......"

Ouseinarma wani sansanyan farin cikin ganninta ne ya mamaye zuciyarta, tsakani da Allah tama son yar uwarta so daya tak da babu hadi, baban matsalar da yake sakawa take karra yin nesa da ita shine soyayar da take yiwa yaronta mabambanciyar soyayar da ta dace ace tanai masa

Ita da kanta ta sani, ta san cewa abinda take ciki ba alkhairi bane, ta kuma san cewa lalle yaronai mutunci ne da ya kyaleta har yanzu bai tonata ba, aman kuma baban abin Tsoron bata jin Tsoron ya tona tan, ta gaji, ta gaji iya gajiya

Doguwar riga irin yar dubai din nan mai watsetaen stone tun daga sama har kasa wadda a kalla zata ci dubu casa'in ce a jikinta, sai dai dametan da ta yi ne ya saka yar uwarta bin rigar da kallo harma ta kasa hakura ta ce" Kanwa, wannan damamiyar shigar fa?"

Shigar tata ta bi da kallo , sannan ta juya wajen wanda ta yiwa din, abin takaici ko kallo bata ishe shi ba, uwa uba abinda ta gani a bayan wajen da ya zauna ya saka gabanta faduwa da sake zubawa wada ke koncen ido har sai da Mamma ta sake fadin" Haba Ouseina wannan ai ya dame da yawa, da ki hakura da ita ko kuma ki bada a bude maki, idan kuwa in tela ya taba lalacewa zata yi ki ringa saka mata baban hijab a sama, wanann ko a zaman gida bata dace da ke ba Kanwata"

"Zaki fara ko?, Ko zama fa ban yi ba ni yau kin fara kuma, wai wacece ke kwonce haka a bayan Baban yarona?" Ta fada tana mai son nufar Wajen da Shuwwa ke son mikewa dan ta gaisheta aman kuma ya wani danne mata rigarta ta kasa aiwatar da motsin kirki, shi kuma yana sane da dane rigar tata da ya yi, haka kawai yake ji a kasan ransa baya so ta yi mata irin abinda ta saba yiwa sauran matan da ya aura kafin ita

Muryarta cen ciki ta ce" Yalabai ka danen riga ka dagani na tashi......."

Kasancewar Mama ta juya tana fadin" Ina zuwa bara na ga ina Nahidt ta makale ne haka su zo su ci abinci, hakan na nufin ta fita a dakin da gano Nahidt ya saka shi juyowa da kyau ta yadda ya sauke idannuwansa a saman santaleliyar cinyar SHUWWA da take son ya dan daga ta janye rigarta

Ba zato ba tsamani ta ji hannunsa a saman cinyarta daga dan sama kadan ya dora
Dorawar da ya yi da niyar ya dan taba wajen ne dan ya isar da sakonsa wa yar uwar mamansa, sai dai a hankali ya samu kansa da dan matsa wajen kadan kafin ya dago idannuwansa ya sauke a saman fuskarta da ta yi tsuru tsuru ta zarro ido cike da mamakin sabon salo wai kiran sallah da usur

A tsorace ta so waigawa dan ta kalli Matar da idan ta fahimta da kyau ana nufin abokiyar tagwaitakar mamansa ce ko menene?, Sai dai baban tashin hankalin da bata taba zato ba, wanda shi kansa bai tana zato ba, wanda ya kusan buga zuciyar ouseinar mahaifiyarsa a lokacin da bataa shiryawa gannin diramar yaron nata har nan ba, domin du ta dauka da gangan yake yi kamar yadda ya saba ja mata kashedi kala daban daban a kan haka, sai dai lokaci daya idannuwanta suka sauka a tashin hankalim a lokacin da ya manta a ina suke? Ya manta me suke yi? , Harma da wa yake? Ya sasauta ya ringyesa ta yadda ya rankwafo mata, gashi ya sake danne mata tifafi ba zata iya ja ba koda ta yi yinkurin hakan, gaba daya yaa halaka mataa tunani a lokacin da ya yi mata rumfa sosai idannuwan nan nata da take zarrowa ya tsayar da su kau kamar ta summa domin ido cikin ido ya saka a nata kafin yake sauke lalausan lebensa a saman nata leben mai dumin tashin hankali , ya ciro da harshensa kadan ya dan lashi leben nata harma ya karra neman sake lasar leben nata sai dai bata bashi dama ba domin jikinta ne ya dauki rawa ta yi gagawar kawar da fuskarta bata san ta yiwa kanta rami bane, domin leben nasa da ya tashi bai sauka a ko'ina ba sai a domin wuyanta hadi da sajensa, shi kuma lokaci daya kanshin turaren kashin kanta da na wuyan nata suka saka shi lumshe idannuwansa yana jin wani takuraren tashin hankali na ziyartarsa harma ya saka hannunsa a hankali ya talafi..................






Mun higa uku😌😌😌😌ALK'ALAMIN KADARATAH





Na

*Sajida*


Page


4️⃣8️⃣


Maganin tumbi.......................

Ki samo KANANFARI, LEMUN TSAMI, SHINKAFA,
Ki irga kananfari kwaya goma sha biyar, sai debi shinkafa cikin hannunki, sai ki yayaka lemun tsami biyu manya har bayansa a cikin tukunya ki saka kofi biyu na rufa ki dafa su
Sai sun dafe sosai sai ki kawo ki markade ki shanye
Kina yi da sasafe, sanann idan zaki kwonta har ya maki daidai yadda kike so😍😍😍😍









A hankali ya saka hannunsa da gashin dake lulube da shi du suka mike sakamakon aikata abinda bai tana aikatawa ba da ya yi , ya tura ta kasan bayanta ya talabeta a jikinsa ta yadda jikinta dake rawa gab gab gab ya hade da kirjinsa a hankali, sannan kanshin da suke bazawa na jikinsu gaba daya ya garwaye waje daya , ya sake lumshe idannuwansa a wuyansa ya shiga dan goga mata sajen dake fuskarsa ba da nufin ya hadasa mata jin kowani irin felling ba, asalima yana yin haka ne dan ya samu ya dan sake nutsar da hankali abokiyar tagwaitakar mamansa da ta yi mutuwar tsaye, kanta ya sara, hankalinta ya tashi, ta zuba masa ido tana son lalle lalle sai ta fadawa kanta cewar ya yi haka ne dan ya bata mata ba dan da wani abu a tsakaninsa da yarinyar da har yanzu bata kalli idannuwanta ziryan ba

Idannuwanta ta rintse, nan take wasu irin hawaye masu dumi suka shiga gangarowa
Ba wani abu ya hadasa mata haka ba sai irin bugun da zuciyarta ke yi na bakon lamarin da bata taba fuskanta a rayuwarta ba ko da wasa, namiji bai taba samun kusanci irin yadda bawan Allahn nan ya samu a tare da ita ba kama daga jiya zuwa yau

A hankali ta saki bakinta da niyar fashewa da kuka, sai dai maganar da Mama ta yi ya sakata ta jikin kirjinsa da dumin kirjin nasa ke ratsata ta dan waiwayo dan kallon abinda ya saka Maman fadin haka

Da mamaki take kallon irin tsayuwar da irin kallon da matar nan ke yiwa bayan MUHAY wanda ya hadasa mata matsanancin mamaki har Mama ta saje furucin cewa" Useina? Useina? "

Sai kuma firgigit ta zabura wanda hakan ya nuna cewar batama san da ana kiran sunnanta bane kwata kwata

Mama ta maida dubanta kan MUHAY da ya rintse idannuwansa abu biyu na ziyartarsa wa'inda suke da girma sosai da sosai a zuciyarsa

Da kula ta ce" Muhyideen lafiya?"" Domin bayansa ne ake gani ya rufeta sai jikinta dake dan bude kadan haka

Mama gannin bai amsa ba sai ta karasa tana dan jan rigar Shuwwa din tana fadin" Abanta ke son shigowa Nahidt ta karasa ta amso mana abinci a wajen nurse da na saka a dumama mana shi, dago mana me yake faruwa ne?"

Dab tsaki Useina ta yi ta juya da sauri da nufin tafiya, hakan ya saka Mama juyawar itama tana kallonta da mamaki ta kuma fadin" Kai wai meye haka ina magana daga kai din har useinar kun ki bani amsa? Meye haka me yake damun yarinyar? Bayan fitana wani abu ya faru ne?"

Cak Useinar ta ja ta tsaya kafin ta juyo da yannayi na bacin rai har tana dardarwar baki ta ce" Me zai faru a ciki,? Me kike so ya faru ne Hasana? Kina kallo? A gaban idannuwanki?!!!"


Da karfi ya dago yana mayar da Shuwwar kwonce wace ta yi firgigit ta mike daga kwonciyar da ya maida ita wannan karronma tana janye rigarta taa gyara da kyau, sai dai daga ita har Maman a saman hannunsa da ya dora ya damki hannun Useina ya jata ya fita da ita idannuwansu suka sauka kafin su kalli junna sunna masu zarro ido ,

A firgice Mama ke kallon Shuwwa ta ce" Y'ata me yake faruwa ne ? Wani abu ya faru tsakaninki da maman naki ne?"

A hankali Shuwwa ta girgiza kai tana fadin" Mama ko gaisawa bamu yi ba da ita"

Kan mama ya daure sosai, Nahidht na shigowaa da Malan ta ce tana zuwa ta fice da sauri, sai dai du irin neman da ta yi bata gansu ba haka ta dawo tana ta leke leke daidai Malan na basu adu'o'in dake karya sihiri, ayoyi ne kwaya shida na cikin Alkur'ani kamar haka
*SURORIN QUR'ANI, GUDA SHIDA DAKE KARYA SIHIR KO ASIRI.*

*1.Suratul Tauba:ayata 14.*

*2. Suratul Yunus ayata 57.*

*3.Suratul Nahli:ayata 69.*

*4.Suratul Isra,i:ayata 82.*

*5.Suratul Shu,ara:ayata 78~82.*

*6.Suratul Fuslilat:ayata 44*

A sanyaye ta zauna samana kujera taba fuskantarsu, gaba daya jikinta tamkar bata da lakkah,

Duda sun gaisa dama, haka Malan ya sake gaisheta a mutunce yana mai sada kansa a gabanta,

Mama ta amsa shi tana sauke gwauron numfashi ta sake dagowa ta kali wajen yan matan, sai ta ga ai ita suke kallo da yannayi na damuwa shinfide a saman fuskokinsu

Malan ya sake sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce" Alhmdulilah, Mama Aban ne Allah ya sa na gani, domin ita Maman an shiga ainahin gyarata, in sha Allah zamu sake dukufa da kanmu mu ringa yin adu'o'in nan, sannan zan koma gida dole dab na tatara almajirai a yi ta saukar alkur'ani da dukan abubuwan da Allah ya sa aka sani na karya sihiri, domin dukkan abinda aka fada na faruwa da bawan Allahn nan, koda da firgici to fa akoy abinda ke kada shi gaba......"

Mama ta gyada tana kallonsa ta ce" Allah ya saka da alkhairi Malan, Allah ya biya, mun gode sosai Malan, Allah ya da mu ga hasken lamarin"

Malan ya amsa a nutse kafin ya mike yana yi mata salama dan bashi da sakewar da zai karra jimawa a dakin, duba da yannayinta wanda ga dukkan alamu wannan abu da ya faru yanzu ne da yaronta da matar nan mai kama da ita sosai, ya kula hankalinta du ba a kwonce ba, tana yawan daga kanta ta kalli hanyar fita sai kuma ta dawo da dubanta kansu

Malan na tafiya Nahidht ta raka shi, Shuwwa ta samu damar sake fuskantar Mama

A hankali ta rarafo ta dan dakata tana kallon yannayin maman tana kuma tunanin shin shakuwarsu ta kai idan ta ga tana cikin bacin rai ta yi tambayar abinda yake damunta ko kuma ta koma ta zauna kar ta janyowa kanta fitina?

Sai dai gaba daya sai ta kasa, Shuwwa ce fa, ba zata iya ba gaskiya , hakan ya sa a nutse ta fuskanci Mama ta ce" Mama?"

Mama ta kalleta da sauri tana sauke ajiyar zuciyar dake nuni cewar tana yawan tunani ne

Itama ajiyar zuciyar ta sauke a sanyaye ta ce" Mama me yake faruwa?"

Mama ta yi rau rau da idannuwanta tana shanye abinda ya taru a cikinsu, ta watsa hannayenta ta ce" Nima ban sani ba Shuwwa, ban san abinda yake faruwa ba, na tarar da ita tamkar ta suma ko ta ga bakuwar Halita tana fuskantarku, na ga kuma shi ya rufe ki a kwoncen da kike, gashi da hawaye a saman fuskarki dake nuni da kuka kike, Sannan ya damki hannun Useinata da irin wannan rikon ya fita da ita da karfin da ban san me hakan yake nufi ba......gaba daya kun sakani a duhu gaba dayanku......"...... Ta karashe tana kallon SHUWWA din da ta sada idannuwanta kasa tana tunanin amsar da ta dace ta ba Mama

Mama ta riko hannayenta tana kallonta ta ce" Menene tsakaninsu ne?, Ya dace ace du duniya babu masu ganewa junna irinsu, a lokacin da na haife shi na tafi saudiya da mahaifinsa hutu mun jima a wajenta yake, yar uwar haihuwata ce, tare muka zo duniya da ita, kulun kukana a kansa shine ya yi zumunci da ita, aman kulun bashi da amsar bani, ban taba jin na tsani shiru shirunsa a rayuwata ba irin na a kan yar uwata, gaba daya na fara tsorata da lamarin, wai me yake faruwa ne?....."

A hankali Shuwwa ke girgizawa Mama kai tana kallonta ta ringa harhada abinda zata fada mata duda ta san da wahala ta yarda da furucinta, ita kanta wannan abin ya bata mamaki har yanzu kallon jan da ya mata take yi a idannuwanta, da kuma irin kallon da matar ke masu, abin na son ya dan tsaya mata a rai, aman kuma bata ga dalili ba shi yasa ta fuskanci Mama ta ce" Mama ni cikina ne ya murda min har na fara kuka, shine ya rikeni dan na daina kukan, shine maman itama take min sannu"

Mama ta kure fuskarta da ido, kwarai ta san maganar ba haka bace, aman sai ta samu kanta da son yarda da maganar fiye da sake saken banzan da take yi a zuciyarta, dan haka sai ta ringa sauke ajiyar zuciya itama ta sauko kasan saman tabarmar suka zauna suka zubawa hanyar shigowa ido kowace abinda ke zuciyarta ya fi karfin ya barta ta yi hira a bayane koda kuwa da gangan ne
______________________________________









😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍ALK'ALAMIN KADARATAH





Na

*Sajida*


Page


4️⃣9️⃣




Jan hannunta yake , tana biye da shi tamkar zata kifa domin saurin ba daya ba, haka kuma karfin ba daya, a haka a wulakance har ya samu ya samu dogon corridor din da yakan zama idan ya kawo marar kafiya ya buya a nan ya turata har sai da ta daku da jikin garu kafin ya tsatsareta da idannuwansa da sukai jajajir yana kallonta

Da bacin rai yaa shiga magana yana dago hannunsa da ya wara ya jimke yana fadin" Ki kula idan zaki fuskanci mai daraja ki yi mata magana, ki kiyaye harshen ki wajen yi mata furuci domin kalma daya na iya laladan sauran farin cikin da kike tunanin kina da shi a rayuwa!, Useina ki kiyaye tsawarawa mahaifiyata, domin idannuwanta dake akoy a doron kasa ya saka ban daga ki na murzaki a kas

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login