Showing 156001 words to 159000 words out of 226733 words

Chapter 53 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

7996

kuma daidaita, ina so ki fuskanceni da kyau........a jinninki babu wulakanci, tabas jinninki na tafe ne da hau da baki da jarabawa kala daban daban, aman kuma jinninki bashi da wulakanci a ciki, shin zaki karra damkar astagfari sannan ki yi min biyaya ko yayane ?"

Itama da sauri take gyada kan nata tana jin wani irin kaunar mahaifin nata a cikin zuciyarta

Abansu ya yi murmushi ya ce" To ku je ku kwonta "

Da sauri IBTISAM ta ce" Aba ni a nan zan kwana a wajenku"


Mamanta dake mikewa ta dan balla mata harrara tana fadin" A ina? Kin ga rashin ta idon tamu bata kai cen ba, tashi ki tafi inda kike da"

Nahidt ta yi gagawar fadin" Mama yau ai a bangaren Dad maman take, ku barmu mu kwana a nan kun ji?"

Mamansu kanta tana matukar son ta kwana tare da y'ayanta, tana kuma son nuna masu kauna karara, sai dai ta rike komai a zuciyarta ta kuma bari har ta idasa nuna masu laifinsu a ilimance ta yadda gobe zasu kama kansu, ba wai dan ta riki abun a rai bane, ko daya, aman dole ne ta koyawa y'ayan nata bambance fari da baki, kadarar rayuwa kuwa ta same su babu yadda suka iya, ita da ta haifama ta yar ta tafi fa? Tana cike da tsoron haduwarta da yaronta na farko, bata san yaya zasu kaya ba, tana kuma cike da zumudin son gannin ahalinta, wai da gaske sun nemeta?

Sandar da aka ba mijinta ta kawo masa sannan ta taimaka masa ya tashi

Tare suka taimaka masa gefe da gefe suka nufi dakin da Maman Muhay ta ce cenne na barcinsu suka shiga da shi
Mama ta yaba sosai hakama shima ya yi murmushi da karamcin mutanen sannan suka fito bisa umarnin Mama suka dawo falo

Sunna Zama Nahidt ta sauke ajiyar zuciya tanaa kallon IBTISAM ta ce" mutuniyar banza , da kice bakya son sunnan mana dazu?"

IBTISAM ta kalleta tana harararta ta ce" Ke da kice ba zaki yi biyaya ba mana, malama kar fa ki tsokaneni kuma ki janyo mana duka kinga dai Mama bata huce ba fa?"

Dan murmushi ta yi ta gyara ta kwonta a saman cafet din sannan ta mikawa IBTISAM hannunta

Itama karasawa ta yi ta kwonta aa kusa da ita sosai sannan suka rike hannun junna

Daga nan babu wace ta yiwa yar uwarta magana sai barci ne da ya kwashe su

Sai kusan karfe daya Mama ta fito domin sai da ta kula da mijinta yadda ya dace har sai da ya kwonta barci sannan ta fito da abin rufa tana tunanin ko sun yi tafiyarsu ne wajen Mamansu ?

Sai da ta ji hawaye ya cika mata Ido da ta ga irin kwonciyar da suka yi sunna barci

Dan murmushi ta yi a hankali ta rufa masu abin rufar sannan ta dafa kawunnansu ta yi masu adu'a ta mike ta koma ciki
Ita kam ba kwonci ta yi ba, Domin bata jin barcinma sam, zama ta yi saman salaya ta yi ta jan carbinta bayan ta yi nafila tana sake rokar Allah kariyarsa, yafiyarsa, farin ciki daga gareshi wa dukkan ahalinta

Da sasafe tana fitowa ta tarda su sunna aiki, hakan ya sa ta shiga yi tare da su, wanda hakan ya saka su cikin farin ciki

Kusan karfe goma wayar Shuwwa ta yi kuka

Da sauri ta nufi wayar dan a zatonta ko yau ya ga dama ya ga message din da ta saka kanta yi masa ba dare ba rana na gaisuwa da fatan alkhairi harma ya yi kiranta ne?
Sai dai tana zuwa ta ga number yayansu ne Hamza, ta daga suka yi hirarsu yadda suka saba, har sai da ya kusan kashewa yake fadin" Kennan da haka zamu ci gaba da yin magana da ku ba zaku fada min cewa kun gansu ba?"

IBTISAM ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Ka yi hakuri yayanmu, ko Fauzy da muka fada mata a tare muka yanke hukuncin kyaleka ka ganta da kyakyawar kama ba a irin halin da muka sameta ba, muna so ka yi mata gannin da zaka ji farin ciki ba wanda zai kona zuciyarka ba, ka yi hakuri"

Hamza ya yi dan Murmushi yana girgiza kansa ya ce" Kin manta ni banma san yaya kamanin nata suke ba? Kuma ganninta a kowani hali ba zai saka na kasa farin cikin ganninta ba, duda ita watsar da ni ta yi ?"

Mamansu da hankalinta ke kan Shuwwa tunda ta furta yaya Hamza ne tana sauraro, kasancewar dakin shiru ne sosai domin ko panka ba'a kunne ba AC ne ke kunne kuma basa hayaniya dan mahaifinsu yana dawowa daga masalaci ya koma ya kwonta ya sa ana iya jin maganar dake faruwa sama sama , dan haka a samu kanta da amsar wayar ta karra a kunnenta har ya dire maganarsa

A hankali ta sauke ajiyar zuciya , muryarta na rawa kadan ta e" Hamza.....?"

Tsai ya yi da dan cin abincin da yake yi zuciyarsa ta bada wani irin bugu mai karfin gaske

A hankali ya lumshe idannuwansa kafin ya katse kiran yana lumshe idannuwansa tare da jin yadda gummi ke neman karyo masa sakamakon jin muryar mahaifiyarsa a duniya

A dole ya mike daga cin abincin ya nufi hanyar ficewa dan ya tarda babansa ya sanar masa cewar yau har ya yi magana da mahaifiyarsa, ya ji muryar mahaifiyarsa shi Hamza
___________________________________

Washe gari
Dukan yadda maman MuHay ta kai da tunanin lamarin maman su Shuwwa abin nata ya wuce haka

Ko a yanzu aiki suke yi a baban filin girkin gidan, gaba dayansu ne suka hade suke girke girken sakamakon sanar masu da Dad ya yi cewar su Muhay zasu taso tare da Malan, da Hamza
Du irin yadda Maman Muhay ta so ta yi zamanta duba da akoy gajiya a tare da ita a ganninta, sai Maman su Shuwwa din ta nuna mata cewa ai ita ai zama a waje dayan nan ne gajiyarta walahi, dan Allah ta barta ta kama masu aikin

Ai kuwa tana kallon girke girke, girke girken irin na larabawa, kayan sarafawa ne wasun babu su aman da wa'inda ta samu ta yi anfani

Cen kusan karfe biyar na yamma ta kai dubanta wajen Mama a hankali ta ce" Mamansu inace da mijin Ebtisemmmmmmmm ne za'a zo yau din?"

Mama ta waiga itama ta kalli Shuwwa, harga Allah tun dazu take ta son ta ce ta tashi ta je ta shirya tarbansa ko yayane, itafa so take su tare dan har yanzun mamakinsa take yi, sam bata ga alamun ya taba kusantar iyalinsa ba, wannan abin ke daga mata hankali walahi, har yanzu fa tana cikin tunanin abu biyu, to wai ko bashi da lafiya ne? Ko kuma baya ra'ayin mata ne..? Subahannalah sosai abin nan ke damunta bata san yaya zata cire a ranta ba, kuma tana kallo fa yarinyar nan fa na iya bakin kokarinta, gaba daya shi dinne ke saka mutane a wani tunanin daban

A nutse ta gyada kanta tana fadin" Eh maman IBTISAM, da shi za'a zo"

Mama ta sake waigawa wajen shuwwa da mamaki a saman fuskarta ta ce" Ke , me kike yi har yanzu a zaune ne?"

Shuwwa da Nahidt suka dago a tare sunna kallonta

Da wani mamakin ta ce" Ba yau mijinki ke dawowa bane?"

Sake kallon Nahidht ta yi domin abin ya mata banbarakwai, sai dai da sauri ta sake juyowa kan mahaifiyar tata a lokacin da ta ce" Ya ina magana kina waiwayarta ne?"

Da inda inda ta ce" Eh, Eh haka Mama tace yau zai dawo"

Da wani mamakin ta sake kallonta jin wai haka Mama tace, me kennan? Yaya zaman auren y'artata yake ne yanzunma? Ko dai daurawar kawai aka yi sunki yarda su gyara zaman nasu?

Miyar Agushin da take yi ta bude ta daidaita dandanonta sannan ta rufe ta sake juyowa da haushi haushi ta cire ludayin cikin miyar ta nufo Shuwwa dake kikifta ido ita bata san me maman nata ke nufi ba💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥


*The Hero writer*


*SAJIDA*


_Bismillahir rahamanir rahim_


PAGE:. 5️⃣6️⃣



*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*






*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*


*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*



*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*



*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*


*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618


Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰







A guje ta diba ta nufi bangarensu gannin itace za'a bugawa ludayin ko me?

Ai kam mamanta bata yi kasa da gwuiwa ba ta rufa mata baya har suka idasa shiga kafin ta ja ta tsaya gannin ta je da gudu bayan mahaifinta ta tsaya tana kallon Maman

Dan murmushi ya yi da alkur'anin dake hannunsa ya dan rufe yana kallonta ya ce" Malama wani abu muka yi ne?"

Ludayin dake hannunta ta nuna ta ce" Aban IBTISAM ka bani yarinyar nan na maka mata wannan ludayin ko zata nutsu"

Kai ya girgiza da dan sauri yana mai jin wani farin ciki da annashuwa da tuna rayuwarsu ta da ya sake fadin" Me zai hanna a gyara matsalar ta fatar baki ne ba sai an taba lafiyar jikinmu ba?"

Mamanta ta sauke yar ajiyar zuciya tana kallonsa ta ce" Mijinta fa zai dawo yau, shin a shiriricewar da suka yi harda ta rashin sannin ciwon kai?, Rashin sannin ciwon kai ne mana Abansu macen da zata yi zaune kamar jaka mijinta na hanya daga tafia? Allah na tuba ko a cikin gari ne ya yi tafiyar awa hudu wajen aiki ko zaman majalisa ai kya kokarta da abinda Allah ya malaka maki ki dan daidaita ta yadda gobe idan ya tashi yi maki gori ba dai na tsaftar jikinki, ko muhalinki, ko girkinki ba, Malama wuce ki je ki gyara masa bangarensa, ki maida hankali ki zo ki kawo kayan abincinsa daban a zuba ki kai ki kilace, ki kula da turaren wuta da na bayi da na gadonsa, sannan ki tabata kin kula da jikinki yadda ya dace .......ko shima sai na koya maki ne?" Ta karashe da dan daga muryarta kadan tana zazaro mata ido

Da sauri Shuwwa ta girgiza kanta ta fito daga bayan mahaifinta ta zagaya da gudu ta wuce a dakin gaba daya ta tafi wajen Maman Muhay dan tambayarta ky din bangarensa cike da tunani kala daban daban

Tunda take fadan, mahaifin Shuwwa ke kallonta
Zai iya cewa rabonsa da irin wannan tunanin a zuciyarsa har ya manta,
Hijabin dake jikinta kiwa sosai yake boye yar ramar da bata idasa cikewa a jikinta ba, fadan da take yi kuwa sai yar duma dumar budurwar da ta sace zuciyarsa dare daya ta dawo masa a cikin tunaninsa
Tabas zai iya cewa bai taba gannin mace mai tsaftarta ba, watau idanma tana da dati to fa idannuwansa basu gani ba, gata da kamshi, gata da dumi.............
A hankali ya samu kansa da dan hadiye yawu kadan a makoshinsa da ya dan bushe a lokacin da ta juya ta fice a dakin bayan an ja masa nasa kashedin shima ta hanyar turo bakinta kadan ta auno shagwabar dake tata ce wace ake yi masa ne ta dan dira kafarta ta ce" Ka ga dai Abanta walahi karma ka ce zaka hannani shakarta, gaba daya yaren nan na kula sun dauki marar kirkin hali da yawa sun zubar da na kirkin, ka ga NAHIDTma jira take na ce ta je ta gyara jikinta dan bakon da za'a zo da shi, aman ba komai daidai nake da y'ayanka ni kam!" Ta idasa ta juya ta bar masa wajen

Dan murmushi ya yi yana girgiza kansa ya sake bude Alkur'aninsa a kasan zuciyarsa yana ayanna abubuwa kamar haka' Wannan rayuwar ita nake so ta co gaba da wakana a tare da ni, na so na yi ta yinta har zuwa cikin kabarina......, Sai dai gashi ga dukkan alamu kwana kusa zata gagareni, domin nadin dake kaina mai rikicin da ban san ko zan iya kallonta a haka tana min girgiza ba......?' (Mamana, auntyna, dan Allah ku duba, ku bude idannuwanku ku duba, koda kune kushewa a tsufa, koda kune magarya a y'aya ya dace ku gane cewar ibada ne, haihuwar y'aya ba shine zai sa ki watsar da komai ki zubar da komai ba, tabas akoy kunya irin tamu ta hausa fulani wace ke hanna mana aikata wasu abubuwan a gaban y'ayanmu ko bakin fuska, aman na tambayeku su y'ayan har cikin dakinmu suke kwana da mu ne?, Ki iya rigima mama koda baki iya ba, ki dan ringa dan jefo shagwaba lokaci zuwa lokaci koda baba bai san me hakan yake nufi ba, ki gane mama nishadinki ne koda baba a yanzun baya andanuwa ta hanyar bed, ki gane ki dan zuba abu irin na yarintama zai saka baba kallonki da murmushi a fuskarsa ya dan dungure maki kai ya ce yau kuma shagwaba ake ji maman walida?, Yau kuma rigima ake ji uman Fatima?, Yau yan rikicin a kusa suke da alama uwar gidan Malan, ba maganar mijinki bashi da kudi a wajenki sarki ne, ba maganar mijinki babu abinda ya sani sai fushi cen dam baki koya masa walwala ba a yanzu ba zai iya koya ba, walahi ko dutse ne shi dabi'a zata shige shi, domin yau da gobe sai Allah , ke dai ki yi kokari idan kin zubar da komai ki dawo da daurin nan naki ture ka ga tsiy a gabansa, ki dan shafa jan baki ki kanne ido, idan yace to yau kuma? Ko dai a kaiki a maki rukiya ne? Rukunkume baba ki jefa shi a gado zai gane aljanu sun shigeki😌, aman fisabililahi dan kawai kin samu jika kamarni shikenan sai ki wani kashe kanki inadarma ba'a habakata?, Lada ne fa, 😌 gaskiya a daina wasa da lada gaskiya, a gyara Mama babama yana son jin dadi gaskiya, kuma tsufanki a wajenmu y'ayanki kika dan kwana biyu walahi a wajensa in kin so kika tsufa, domin kinga damar da furfurarki da yabarki ki ce sai ya maki Ampa😌, ba nufina da shekarunki ki ringa fama da kannanun kaya ba, ko daya, ko daya walahi, wani sa'in da kannanun shekarunma sai ka ga idan yannayin jikin mutun sai a hankali kannanun kayan basa yi masa kyau, ba dole bane saka su, ke dai kawai ki iya dauri 😂babu abinda bama gani ehe, a dai kula😍😍😍)

Gyaran take yi cike da takaici a kasan zuciyarta
Ba komaine ya sakata a cikin takaicin ba sai tunawa da ta yi ko a safiyar yau ta yi masa mesage kamar haka *Barka da safiya yalabai, fatan ka tashi cikin koshin lafiya? Yaya aiki? Allah ya tsare* aman ko nataciyar mayya bai turo mata da reply ba bale ta yi tunanin ya gani, to wai ko bai gannin bane? Ko kuma da wani tunani na daban ne a cikin kwakwaluwar wannan bawan Allahn ne? Koda yake idan ta ce babu ta yi karya, ta san da décision dinsa na rabuwa da ita kwana kusa, to aman ita tana gannin mutuncinsa da kimarsa a yanzu ne dan ya kwatanta kamar shi din ai dan mutunci ne ta hanyar taimakon iyayenta kau?, Aman a yanzu abinda Mamansa ta ce ya matukar bata mamaki, shin ta yaya suke so ta dauko suturarta ta kawo dakin nan ne? Wai me suke so da ita ne haka kai tsaye?

Maida hankaki ta yi ta gama gyaran sannan ta koma bangaren Mama ta shiga wanka
Kukawa da jikinta da mahaifiyarta ta ce ta kwatanta gwargwadon sanninta ta hanyar cire dukkan datin da ta san yana iya zama a jikinta sannan ta saka turare a dukan wani lungu da ta san tana da shi a jikinta komai kankantarsa
A saman kujera ta zauna ta shiga tsara sasaukar Mak'up a fuskarta, wace haka kawia ta ji tana ra'ayin a saman farin fatarta ta dan karra hoda ko yayane sannan ta gyara girarta harma ta saka kajal, ta dora da jan baki mai hawa da rantsatsan dinkin atamparta da ta ciro cikin dinkunnan da akai masu ita da yar uwarta

Sosai ta bata lokaci tana gyara har akai kiraye kirayen sallar magariba
Nan ta gabatar da sallarta, sannan ta saka kayanta ta kashe dauri irin mai tsokale idon ogan nan

Bata dauki mayafi ba, bale hijab, takalminta ta saka plate sai dai mai gashi a jikinsa sosai bayan ta saka safar da ta zame mata jiki

A tausashe take tafiya a tsakar gidan tana hankalce da yannayin gidan nasu na yau, taron sojoji ya fi na da yawa sosai, sannan du idan aka ji motsi sai an duba dan gannin ko wanene, da zarar an ga itace kuwa sai ta ga ana yi mata gaisuwa irin ta mutuntawar nan sannan a bata hanya ta wuce

Ita dai bata damu ba har ta karasa ta kama kofar ta bude da salama a bakinta ta shiga

Sansanyan kanshin turaren wuta garwaye da turarrukan jikin mutanen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login