Showing 225001 words to 226733 words out of 226733 words

Chapter 76 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

7978

ban taba haihuwa ba aman an haihu sosai a hannuna in sha Allah zata sauka lafiya mu yi ta mata adu'a ta yi kokari sosai domin har yanzun tana ta karra rike kanta sosai "

Mama zata karra mata wata maganar sai ga MUHAY din ya karaso
A sanyaye ya sake yi masu wata salamar yana dukawa da ledar dake hannunsa ya shiga budewa yana kallonta ya ce " kin ga na kawo maki yalon nan yau du baki nema ba"

Fuskarsa ta karewa kallo mai cike da haiba , sajensa luflufluf a kwonce, lebunnansa sunna kyalin jansu haka kuma yannayinsa dake tafe da sanyin fa jikinsa yake da shi tun jiyan shima na nakudar Nahidht din da ya tsorata shi har yake tunanin idan ma Shuwwa din ya tashi yaya zai yi da ransa ne? Malan yana masalaci sauka yake yi ba ji ba gani ya kasa cin komai sai karatu yake yi bawan Allah, shi idan tasu ta zo ko yaya zasu kwashe? Likita ya ce lokaci ne bai yi ba da zarar lokaci ya yo zata haihu ba wata matsala a tare da cikinta, wai bata wuce ka'ida ba, aman ai yanzu a satin na wucewar ka'idan take ko? Wanke yake nufin idan bara haihu ba za'a iya yi mata fashi

A sanyaye ta lumshe idannuwanta sakamakon ciwon da ta saba ji mai dantsa mata har bargonta da ya sake tashin mata
A hankali take dan numfashi da bakinta idannuwan nata a rintse rufffffffffff har sai da ta ji abin ya lafa mata sannan ta sakar masa murmushi a hankali ta ce" Ka ci abinci ne?"

Ajiyar zuciya ya sake saukewa yana tunanin wai abinci, ita dai a yi sha'ani kawai, shi ba abinci ba yai idonsa idon yan sholisho suka wani kwasa a guje dan sun gansa a lifan dinsa ya yi gaba ko kallo basu ishe shi ba, to ina hankalin kallonsu ne yana ta kansa?

Mama ta sake sauke ajiyar zuciya ta dauki wayarta ta sake kiran Mahaifiyarsu

A sanyaye ta ce" Haba gimbiya wannan wace irin karra ce haka? Ya dace ki zo ki ga Nahidt, yarinyarnan tun jiya take kan gwuiwa, har yanzu shiru, ki zo ki dubata sannan ki karawa yar uwarta kwarin gwuiwa, tunda ta zauna din nan ta kasa koda motsi sai dai ki ga tana rintse ido tana kuma budewa"

Maman ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Aa Umaansu, bayan gaku kuma ni din idan na zo me zan masu? Nakudar wata da har take sati tana ja? Allah ya raba lafiya, sai dai......."
Sai kuma ta yi dan shiru

Mama ta ce" Sai dai me?"

Maman Shuwwa ta ce" Ita IBTISAM din, ki dan matsanta mata kan ta mike daga inda take ko ta kwonta ki gani? Idan ta yi to, idan kuma hakan ya gagara fa ina tsoron irin nakudata ce take yi wace sai dai na yi ta surutu a zaune idan kuwa aka yi wasa daga zaune idan har na karkata to dan bada kan d'a ne"

A zabure Maman ta juyo wajen su Shuwwa din tana kallon yadda Muhay ke mika mata hannu yana fadin" Kalleni, bara na kamaki ki mike mu tataka zaman nan bashi da kyau fa kin sanni, tun safe a haka kike fa yau ko ciwon bayan bakya ji?"

Idannuwanta ta kuma rintsewa sanadiya ras ras ras ras din da take ji har kwakwaluwarta ta dan janye hannunta tana dan damkar hijab dinta kadan har sai da ta lafa mata sannan ta ringa sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" ka ga, kafafuwan nawa gaba daya yau basa anfanuwa, haka kuma kamar an girkan duwawun na kasa wani motsin kirki da na ce zan ringesa nan hakarkarina yake rikewa dole dai zan dawo na zauna a haka............ka bari idan Nahidt din ta haihu sai mu shiga "

Mama ta farra zarro ido zata mike likita ta fito da sauri tana fadawa wata nurse kan maza ta kirawo likita kai ya fara badowa

A haukace ta yi baya dan kiran likitar tasu, hakan ya sa Mama mikewa zurbat ta karasa wajen Hajia da ta mike tana fadin" Ya Allah ka rana lafiya alfarmar annabi, ya Allah ka rana lafiya"
A dan rikice ta ce" Anya Ibtisamma ba nakudar take yi ba?"

Hajia ta juyo tana kallonta ta ce" Nakuda kuma Hajia? A hakan?"

Mama ta ce" Kinga fa yannayinta fa? Yarinyar nan bata da lafiya zo ki gani"

Sunna karasowa likita na shigewa aka rufu a kan NAHIDt wace karfinta ya gama karewa jikinta a mace ta galabaita ta gama ficewa a hayacinta ta riga ta san tata ta kare wai wani ta nisa? Ta yi me idan ta nisa? Tun dazu ai take nisawar babu abinda ke fita a jikinta gaba daya an gwaleta gaban kowa ana mata nisa, bata san cewa da ake cewa idan lokacin fitowar dan ta yi fitowa yake ba sai yanzu da ta ji wata irin azababiyar nishi ta taso mata daga kirjinta ta fetso aabinda ya tafi da dukan kuzarinta ya yagata tana ju likitar ta idasa janyoshi ta fitar daga jikinta tana kuma neman maida numfashi wata nakudar ta kuma kankama wace ta idasa sadakarwa tana ji ana daidaitata da sauransu da kyar kamar ba zata iya ba sai ga wani dan ya fado duniya mai calarar kuka domin da ihunsa ya diro duniyar yana kukansa tun karfinsa kafin ta nemi tafiya duniyar summa inda suka hannata ta hanyar du da ake hanna mace tafia duniyar summa a irin wannan lokacin domin jinni ke dauka idan ka tafin ta yiwu ka tafin kennan

Ana bidiri ne a ciki a waje kuwa wani bidirin ya barke
Da gudu Hajida da ta gama kiran malan a waya cewar ta sauka ta sake duban dayan jaririn da aka kuma fitowa da shi aka nufo wajen da ake auna su a gogoge su kafin a ba masu su su tana zarro ido ta cewa likitar" Likita biyu ne?"

Likitar ta yi murmushi tana gyada kanta lokacin malan ya karaso idannuwansa na zubar da hawaye ta sake maida hankalinta kan Shuwwa da ake kokowar sai ta motsa aman fadi take da bakinta a rikice kamar haka" wani irin juyawa cikina yake yi, abin jinsa nake daf da fita ima tsoron juyawar nan na yi kashi a zaune, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une wayo Allahna cikina bayana, kafafuwana tamkar basa jikina, wayo Mama"

Tashin hankali, a nan fa katonta ya aniyar neman kinkimarta a rikice yana fadin " Ke kin ga ki fa bi tashin hankalina a hankali, mu je gida kawai na shiga uku Mama kin ga ta ki ta motsa"

Da gagawa likitar ta karaso da wanda ke tura gadon nan tana fadin" Ina takardarta ne? A wata na nawa take ne?"

A rikice duka yake dan haka yake fadin" Mu fa haihuwar yayarta muka zo bamu shirya tata ba, kin ga ita ai da tun satin da ya wuce aka ce zata haihu aman bata haihun ba, mu yanzun da haihuwar yayarta muka zo me zai saka mu yi yawo da takardarta?..........." Hannayensa ya dora saman kansa jin abinda likitar ke fadi da karfi cewar" Nakudarta fa ta nuna haihuwa ce fa"

Ai kam rikicewa iya rikicewa sun rikice, ba mai ba dan uwansa hakuri harda su Malan din
A kofar dakin haihuwar suke daf da daf gaba dayansu, abun ne ya hade masu goma da gomiyatara, du irin zumudin da Malan yake ciki sai da ya sare da tsoron haihuwar a ransa
Sai dai cikin hukuncin ubangiji ita nata haihuwar bai dauki lokacin na Nahidt ba, domin dama ta jima tana nakudarta a yanzun ta zo kan gaba ne kuma ita jiran ciwon da ya girmi wannan take koda zata ce bata da lafiya dan mamansu fada masu take su iya rike bakinsu a dan kwayam kwayam din nakuda kar su tarawa kansu mutane bayan nakudar bata wani nuna ba a ringa cika asibiti ana yamadidi da su, su a wahalce wanda yake tare da su a wahalce, shi yasa ta dauka cewar nakudar idan ta taso sai ta suma kamar sau bakwai dan azaba, gannin du irin azabar da take ci bata suma ko daya ba sai ta ajiye hakan a matsayin mai zuwan na zuwa a gaba, ashe ita hanya nata budewa bata sani ba, sai a kan gadon haihuwar ne ta ringa salallami da kiran sallah tana fadin kaico rayuea ashe haka ne abin? Toh Allah mun gode maka (πŸ˜ŒπŸ˜‚πŸ˜Œ kashhhhh )

A wannan rana daukacin familyn nan uku sun tsincin kawunnansu a matsanancin farin ciki da kukan jarirai hudu ya garwaye kunnayensu yayaryayar yaayayayayayar sunna tsala shi ba ji ba gani sojojin Shuwwa sun bayana yan mata guda biyu tsala tsala hakama na Nahidt jaruman ustazanta guda biyu yan samari tsala tsala, a dole suka rikice da kukan farin ciki kafin duniya ta dauka..................




*sunnah*

An gabatar da taron radin sunnan yaren a baban masalacin fada, inda taro yake gudana a cikin fadar na amaren jegon guda biyu, domin gannin za'a rikice aka hade waje daya ake gabatar da taron
A wannan ranar MUhay da Malan baka har hanci, farin ciki suke ciki mai girman gaske sunna kuma godewa Allah da suka wayi gari MUHAY da baby girls dinsa masu sunnan iyayen matarsa da na mahaifiyarsa akai masu inkiya da Ummi da Mami, sai Malan dake da zaratan samarinsa wa'inda shima ya saka sunnan mahaifin Nahidt da nasa mahaifin ake masu inkiya da alhusain da alhasan

Da yama likis akai hawa na dawakai da matasan fada sukaiwa jikokin sarki dan taya murna, a nan zaratan sirikansa suka sako sho tsakiya a saman ingarman dokinansu wa'inda MUHAY ya warci nasa ya neki tafkawa da gudu Malan na murmushi ya ce" Ka ga MUHYIDEEN ka fa kiyaye fa doki ne"

MUHAY ya yi yar dariya kasa kasa a tunaninsa ya ce" Sai kace ba katon Shuwwa ba? Kai dai Allah sa mu cika da imani kawai ................"

Sarki ya yi murmushi yana kawar da kansa a ransa yana godiya da Allah da ya a zanen *ALKALAMIN KADARARSU* ake cakude da farin ciki mai girman gaske, hakan ya sa komai rudanin duhun zanen ALKALAMIN suke fuskantar farin rubutunsa sannan su furta hamdalah a fili da badini wa buwayi gagara misali.....











*Alhmdulilah*





πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° ALK'ALAMIN SAJIDA NEπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° Na gode sosai da gannin wannan rana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login