Showing 18001 words to 21000 words out of 226733 words
boye ba, ta yadda idan ta yi wasu abubuwanta a bayane ake iya gannin yarintarta da komai nata
A nutse ya ce" IBTISAM yaushema kika fita a ciwon abinda wancen ya maki? Kin ga bana son aikin gagawar nan fa, shi yake sakawa mu aikata aikin dana sani, gagawa fa aikin shedan ce IBTISAM"
SHUWWAR ta karkata kanta tana fadin" Aba walahi ba maganar gagawa a cikin lamarin nan, tunda safe muka hadu da shi a wajen kallon taron da aka yi yau, a kadan mun yi awa uku da shi muna zantawa, ya fada min ko shi dan gidan waye, ya fada min sana'arsa, ya fada min cewar mamansa ta rasu, aman matar babansa bata da matsala ba zata tsane ni ba zata so ni tamkar y'ar cikinta da ta haifa, ya fada min zan daina kukan maraici haka kuma yayata zata yi alfahari da aurenmu, ya fada min komai Aba yana da nutsuwa sosai kuma yana sona"
"Ya salam, ya salam, IBTISAM dan kawai ya farfada maki duka wadinnan shikenan ya gama zama mutumen kirki sai aure? Wani irin neman aure ne haka da gagawa haka?"
SHUWWAR ta shagwabe fuskarta ta sanyayar da muryarta ta ce" Aman ai kai kake cewa jan maganar aure bata da dadi, yawan tsayawa zance bashi da kyau, idan aure za'a fito a yi a fito a yi kar a tsaya tsaye tsaye ko?"
Dan murmushi ya yi yana fadin" Du na sani, to aman IBTISAM idan ke ya fada maki wanene shi, ke me kika fada masa a kanki? Ina nufin yadda ya fada maki komai a kan rayuwarsa kema haka kika fada masa?"
Tsai ta yi da hirarta tana mai maimaitawa kanta tambayar Liman, kanta ta dago tana kallon fuskar Liman mai dauke da ni'ima irin ta ma'abocin riko da adinin musulunci
A hankali ta ringa tunano hirarakinsu da SUDAIS, gaba daya a hirarakin nasu basu yi maganar da ta shafi usulinta ba, sannan bata fada masa ainahin wacece ita din ba, da aure auren da ta yi da dukan dalilin da yake sakawa ana sakinta ba
Gaba daya sai ta samu kanta da mutuwar jiki da dukan gaban jikinta muryarta a sanyaye ta ce" Aba, idan na ce masa zaune muke daga ni sai aunty sai Fauziya a gidanmu, sannan na ce masa su aunty ke ciyar da ni sannan basa aikin komai, sana'arsu lalataciyar sana'a ce anya zai so hada zuriya da ni? Anya zai so aurena kuwa?"
Dacin da yake ji a zuciyarsa ya cije yana fadin" IBTISAM, idan har domin Allah yake sonki ina mai tabatar maki cewa koda kece a cikin irin halayan nan, zai dauko ki, ya tsamo ki a ciki da adu'a da fada da komai, zai saka ki tsaftace dukan lamuranki kafin ya aure ki ya kilace ki, idan har yana da ilimi sannan yana aiki da iliminsa, IBTISAM idan har yana neman matar aure ne ba dan fadar mutane ba sai domin Allah da kuma zuciya daya, zai aure ki ya kilace ki ne ya kula da ke domin babu Ayar da Allah ya haramta auren koda karuwa ne bale ke"
Ajiyar zuciya take saukewa wani bakon hawayen ya bi ta saman wanda ya riga ya bushe a saman kuncinta tana gyada kanta ta ce" Toh Aba, zan je na kwatanta fada masa abinda ya samu daga cikin LABARINA, idan ya ce ya ji ya gani sai na fada masa ya turo maka magabatansa"
"Na'am ya yi hakan" ya fada a sanyaye, ya sake yi mata nasiha mai ratsa jiki da zuciya sannan ya salameta bayan ya sake nusar da ita ta rike adu'a a dukan halin da zata tsinci kanta a ciki
Da wannan ta baro wajensa ya rakata da kallo yana yi mata adu'ar dace a rayuwa sannan ya ci gaba da lazuminsa yana kore damuwar yayarta da bai ga anfanin yinta da yake yi a cikin zuciyarsa ba
Jiki a sanyaye ta dawo gidansu daidai NAHIDT ta fito a wanka daure da tawul a jikinta, farar fatar nan tata ta sake yin haske, haskenta da kyanta ya bayana sosai, ga dogon gashinta wanda sukai gado wajen wama su da kansu basu sani ba yana digar ruwa wanda ya saka SHUWWAR bin kan nata da kallo kafin ta cire kanta bata amsa mata tambayar da take yi mata cewa daga ina take ba, ta wuce ta nufi dakinta ta rufe tana fadawa saman gadonta a hankali ta furta" Daga yawon banzar take yanzuma ko?, ba zata gane hakan na rusa ni, yana rusata ba? Ba zata gane hakan na sakata a halaka ba? Ba zata gane kyan fatarta da yarintarta na disashewa kowani minti ta karra a duniya ba? Ba zata daina ta yi aure ba? Ba zata kama wata sana'ar ba? Shin anya zan samu miji bayan uwar rikona ta riki sana'ar yawon tazubar a bayane a doron kasa kuwa? Waye wanda zai yarda cewa nima bana aikatawa ne? Ni da kaina na fara tsorata da tarbiyata ta yadda na cire rigata a gaban Elhaj mai shinkafa ba kunya ba komai, anya idan waje ya kure min ba zan saki hanya na zamto mai yawon ta zubar ba kuwa?"................( *Ya Allah,, ka saka tawada irin taka ta salama a cikin alkalamin zannen kadarmu, ka rabamu da halin kaka naka yi na rayuwa mai zafin da zai kaimu aikata haka wa kanmu*😭👏👏👏👏 )
_______________________________
A kalla sun dauki minti kusan ashirin a zaune a falon su uku ba wanda ya furta koda A ne
Hasalima su iyayen shi suke kallo inda shi kuma yake dan kalle kalle kamar wanda yake son gannin wani abin, aman kuma ba hakan bane hasalima a takure yake so yake a yi a gama zaman ya tafi wajen aiki, aman abin ya gagara domin sun yi shiru da bai san ma'anar shirun nasu ba
Dan gyaran murya ya yi a karro na biyu yana dan kallon mahaifiyarsa ta kasan ido kadan a hankali, a tunaninsa da karamin amo muryarsa zata foto domin ya budi bakinsa ya fitar da muryarsa kasa sosai ta yadda amonta ba zai yi karfi ba, sai dai ina, na SHUWWAR din ne da ta ce ta yiwu matsalar a makogwaronsa take bawan Allah, amo mai karfi karfi ya bayana da babar murya ya ce" Mama ina kwana"
Kallon SHIEF OF ARMY ta yi , shima ya kalleta yana murmushi da girmama soyayar da d'an nata ke yi mata a zuciyarsa, domin bai taba gannin wanda MUHYIDEEN ke sadawa kai haka ba yana jira a hukunta shi da ladabi da biyaya har haka ba
Bakinta ta tabe tana fadin" Lafia nake MUHAY"
SHIEF OF ARMY ya dan saci kallonta ya sake sada kansa a ransa yana ayana' Ba zai yi mata magana ba bayan ya san ranta a bace kuma shi kadai ke tankwasata ta tankwasu koda bata so ba'
A bayane kuwa sai ya sake sauke ajiyar Zuciya ya ce" Dama ina so na fada maku ina son komawa kasar da na fito aiki , da zama na shekara biyar, na yarda , ina nufin na amince da proposition dinka na aikin nan da ka taba min magana na kiya Father"
Da murmushi a kan fuskar SHIEF of army ya ce" Masha Allah, masha Allah son ka ce hankalina zai kwonta a kan yannayin tsaron garin nan, ka san abinda ya fi jagula min lisafi da mutanen garin nan? Irin yadda nake da kokonta a kan manyansu da muka zuba suke jansu, na tabata sama ce rubabiya shi yasa kasan ke sake rikicewa"
Da yake an shiga bangare na aiki ne sai gashi harda su karkatowa kadan yana fadin" Abinda na karanta kennan, a tsarin ikon kasar babu baba babu karami, kowa na tafiyar da tafiyarsa ne son ransa, Father kowa na tafiyar da lamuransa bisa tsari na son kai, basa tsoron taka dokarsu su da kansu.... Dan Allah a haka ta yaya civil zasu rayu da kiyaye dokoki dan zaman lafiyar kasarsu? Dole ne za'a ringa haduwa da abubuwan da basu da kyau a cikin tafiyar tsarin garin"
"Abinda na so kwatanta maka kennan tun shekarar da ta wuce da na kawo maka maganar ko zaka iya zuwa cen na shekara daya ne baka fahimta ba, watau MUHAY idan ka ga cin hanci da rashawa da raini ya shiga tsakanin mai laifi da iko abin ya baci, domin an kawo gabar da mutun zai aikata laifinsa kai tsaye da tunanin yan kudadensa zasu fitar da shi, idan fa ba'a daidaita abin ba kuma garin nan sai dai a barshi kawai a maida shi gefe su je su kashe kansu, abinda bana fata a kasata ya faru kennan". SHIEF OF ARMY ya fada yana mai cike da dokin jin yaron nasu zai je garin, abinda ya sani ne cewar sai inda karfinsa ya kare zai tsaya tsayin daka ne ya gabatar da aikinsa kamar yadda ya saba, ba tsoro ba ha'inci mudin rai
Kallonsu kawai take a lokacin da suka gama shigewa cikin hira ta aikinsu hankali kwonce, ga dukan alamu sun gama yanke hukuncinsu
Zamanta ta gyara tana fadin" Abinda nake son ganewa a nan shine, zai koma garin da ya fito wanda yake dauke da tsayin kilometer dubu da dari hudu da hamsin da uku da aikin shekara biyar?"
Abinda yake tunanin zai faru ne ya fara nuna alamu hakan ya saka shi dan sada kansa a hankali ya ce" Eh Mama, aman hakan ba yana nufin na tafi kennan ba , du week-end za'ina yinsa a nan tare da ke ne in sha Allah ko Father?"
Tsatsareshi ta kuma yi da ido , sannan ta kalli mijinta, ta sake kallonsa, ta kuma kalli mijinta,
Sosai abin ya zo mata a ba zata kuma ta ringa danne kanta danma kar mijinta ya ga rashin hakurinta da son nuna masa iyakarsa a kan yaron nata, sai dai ina, mai karatu ba zai iya kwatanta halin da zuciyarta take ciki ba, MUHAY kadai ne a gabanta, ahine kadai nata malakinta, ta ina zata fara kwatanta wannan rikitaciyar rayuwar yaronta a garin nan mai rikicin tsiya ?
Jurewa ta yi ta budi baki kai tsaye ta ce"
🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 WANNAN LABARI NA KUDI NE, GARZAYO KI SAMU NAKI YAR UWA😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 8️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.
*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
Fuskarta ta hade sosai tana kallonsa ta ce" Ban amince ba "
Daga shi har SHIEF OF ARMY fuskar tata suke kallo a lokacin da ta mike gaba daya tana sake fadin" Ba zai yiwu ba, ban amince da haka ba" ta fice a dakin gaba daya ta nufi bangarenta kanta tsaye hakan ya sa suka bita da kallo kafin MUHYIDEEN ya maido dubansa kan Father dinsa ya ce" Father sai ka barta ta tafi kuma?"
Murmushi SHIEF OF ARMY ya yi yana fadin" Ban san abin ba zai birgeta ba, da ba ta haka muka hayota da shi ba son, aman zamu bita da laluma ka san mata da sarauta gashi dama mamanka da tata sarautar ta tagwaitaka dake mintsininta ana zaman kalauma sai ta ji tana sha'awar rigima da mutane"
Shima murmushin ya yi yana sake maida kansa gefe da barin da Father dinsa yake yana dan dana yatsarsa manuniya tana dan bada kara kadan kadan
SHIEF OF ARMY ya karra gyaran murya ya ce" Ka binciketa waye ya sakata zuba maka abin nan a tea?"
Kansa ya dago yana kallon wajen da yake yana girgiza kansa ya ce" A kasan zuciyata nake jin idan na ji wanda ya sakata hankalina zai tashi"
Da mamaki ya ce" Aman wannan dalilin ne kawai zai hannaka matse mata waje har sai ta sanar maka wanda ya sakata aikata maka haka? Ko kana zargin wani ne baka fada min ba? Muhyideen me yasa ka cika son yin wasa da lafiyarka har da ranka, me yasa ba zaka iya fitowa ka fada min me yake cikin zuciyarka ba?"
Kansa ya dago ya sake kafe fuskar aminin mahaifin nasa da kallo kafin ya furzar da iskar bakinsa yana maida kansa kasa ya furta" Ka yi hakuri Father"
Ya jima yana kallonsa bai iya furta ko A ba , sai da ya gama tunani a kansa kafin ya ce" ka san menene ? Nakan afka wani tunani daban a kanka da irin yadda kake mu'amalantata, na san akoy hali zanen rai, aman kuma nakan ji tunani kala daban daban na shigowa cikin zuciyata a kan mu'amalar dake tsakanina da kai, SON anya ka daukeni a matsayin uba a gareka kuwa?"
Muhyideen ya dago da sauri jin furucin Aban nasa
Yana kallonsa ido cikin ido ya lumshe manyan idannuwansa ya ce" Kai ubana ne, kana da dukan damar da uba yake da a kan y'ayansa, idan ka umarceni na maida wata a cikin matan da na saka ko wacece zan Maida, haka idan ka auren wata ko wacece zan zauna da ita har zuwa lokacin da Allah zai katse zamanmu, na san lamurana a duhu suke, bani da wanda nake zargi a abinda nake gani , asalima ina gudun tsananta bincike a kan hakan, zuciyata ke raya min abinda zan ji na iya daga min hankali, shine kawai Aba"
Ajiyar zuciya SHIED of army ya sauke yana jin kaunar MUHYIDEEN har cen kasan zuciyarsa kafin a nutse ya ce" Na gode yarona, in sha Allah watarana zaka zauna da mace zama mai tsayi, ni na san da haka, kuma ina rokar haka a wajen Allah a kanka, domin auri sakin bashi da anfani haka kuma cikar halitar D'A namiji ya kasance da mace a gefensa........ka je ka fara rarashin mahaifiyarka, a kulun ina sake tunasar da kai ko me kake yi, ka guji daga mata hankali, domin hakan na iya taba komai naka duniya da kiyama, sannan ka daina yi mata shiru idan tana magana ka ringa kokarin amsata ka ji? Ta tsani shirunka ko yayane yana daga mata hankali ainun"
Murmushin da shi ya san ya yi abinsa ya yi kafin ya mike a nutse ya juya cikin tsaftar jiki da ta tafia, cikin kamshi mai nutsuwa da naci, cikin tafiya ta kasaita tamkar wani dan sarki ya bar bangaren ya fito yana sauke ajiyar zuciya hadi da kallon sararin samaniya yana gannin gajimare da ya lulube rana hakan ya haifar da dan lumshi lumshi kadan a garin
"Barka da safia yaya" daya daga cikin y'ayan CHIEF OF ARMY ta fada da kashe murya sosai da kuma sake sada kai bayan dukawar da ta yi again
Kansa ya maido kanta ya yi mata kallo na dan sekwani ya ce" ar u seek?" Domin shi sai ya kamar wata mai ciwo dan gaba dayanta a hade ta Duka din
Dagowa ta yi da sauri tana kallonsa , haka kuma lokaci daya ta ce" Lafiata kalau yaya"
Bakinsa ya tabe ya shiga takawa yana kallon sojojin dake bada tsaro a cikin gidan wa'inda du idan ya karaso sai sun sara masa sannan sun yi jira ya basu damar sauke hannayensu sannan su ci gaba da shawagi a cikin gidan har ya bacewa ganninta
Idannuwanta ta lumshe a bayane ta furta" Ya Allah ka malaka min bawanka , koda yana auri sakin ina so , koda dukana zayana yi ina so"
Yayarta dake hangenta tun dukawar da ta yi ta gaishe da yayan nasu ta gama cika da haushi da mamakin yarinyar, uwa uba da ta ga kamar ya bata amsa yau sai hankalinta ya tashi ta fito ta karaso a lokacin da ya bar wajen tana fadin" Ashe shirmen