Showing 171001 words to 174000 words out of 226733 words
ya buda hannayensa., Ba'a barin namiji da yinwa Shuwwa, ba'a yi........"
Fuskarta ta shagwabe sosai tana langwabe kanta ta ce" Ni tsoro nake ji ne Nahidt, walahi tsoronsa nake, kuma yanzunma cewa ya yi yana jin yinwa da ishirwa kin ga baima ci abincin ba inaga ya kwonta barci"
Nahidt ta sake kureta da kallo kafin ta yi murmushi tana girgiza kanta ta ce" Mace bata kadan, komai girman namiji kuwa baya fin karfinta Shuwwa, rijiya ce mai daukan guga, haka kuma babu wanda ya girma da dadi koda girman bariki ne, sannan ki kokarta ki koma ki gani ko zai yarda ya ci abincin yanzu kin ji? In bandama abinki mutumen da kece shedar yawun yan bariki a kansa ne kike son yin wasa a lamarinsa?, Koda yake baki san menene kalmar nan ba, bana so ki santa ta tsiya kanwata, bana so ki san sharin yar bariki, domin wata yar barikin komai taurin kan namiji sai ki ga ta shawo kansa cikin sauki bale naki mijin da yake da bukatar hakan? Wai har kin manta niyarki a kan kudurin mamansa a kansa?"
Ido ta lumshe tana sauke ajiyar zuciya tana ta auna magangannun Nahidt din, har aka fara kiraye kirayen sallar magariba Nahidht ta mike tana fadin" Abanki fa gobe zai juya dan ya sanar masu wai da wata magana, ban san ta mecece ba da ba zasu iya bara min shi ya karra kwana biyu a nan ba ni kam"
Ita dai da ido ta rakata har ta shige bayi kafin ta sake gyara zamanta tanaa jiranta
Tana fitowa a bayin itama ta shiga ta kwabe suturarta ta shiga tsaftace jikinta kafin ta dauro alwallah
Sai da ta cenza kayanta ta yi sallah sannan ta mike ta koma bangaren nasa da wani hijab din ba wanda ta cire aa jikinta ba
Tana shigowa ya yi daidai da dawowarsa kennan daga masalaci da carbinsa a hannunsa na hagu yana ja a hankali, a hannun damar kuwa waya ce yake ta gwada kiran Dad dan ya ga basu dawo ba, ya yi ta gwada kiran wayar mamansa bata shiga, gashi harda sultan a yan rakiyar bayan yanzu yaronsa ke fada masa tarkonsu fa yana daf da kama kurciya domin wanda aka danama ya. Haukace a kan neman su a cikin garin dan anma buga hotunnan an yadda da sunnan ana nemansu za'a fara kilace mahaukata ana basu kula.....to dai ya yi saken da aka gano sunnansa ne a jikin jaridar dake yada labarun
A lokacin da Dad ya daga wayar muryarsa a matukar sanyaye ya yi sakama kafin ya dan saurara yana jin amsar Dad din sannan ya ce💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 6️⃣0️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
A lokacin da Dad ya daga kiran muryarsa a matukar sanyaye ya yi magana sannan ya saurara yana jin abinda Dad din ke fada kafin ya ce" Ina fata jikin da sauki Aba?"
Dad ya sauke wata irin ajiyar zuciya yana fadin" Ban san yaya zan kwatanta maka abinda yake faruwa ba, an yi faduwa daidai da rashin lafiyarta, wai tana fama da zazafar zazabin nan mai saka surutu, ka ga dai yanzu likita ya jona mata magani jikinta ne ya dauki wani irin zafi sosai Son, na rasa gane menene rashin lafiyar nan kuma......."
Zai yi magana ya ringa jiyo salalamin mutanen dake zagaye da matar Father, sannan ya ringa jin hatsaniya irin sosai din nan, kai harma da furuci kamar haka"Hajia me kike yi haka kar ki cire suturarki mana hajia Innalilahi wa inna ilaihi raj'une menene wannan?"
Da sauri ya kalli wayar domin ba'a yanke kiran ba saima muryar Fathern da ya ji yana fadin" Menene wannan kamar kamun aljannu?, Ke? Ke? Hajia meye wannan kuma?"
Hakan ya sa da dan sauri ya sake kafe fuskarta da kallo yana datse kiran da tunanin abinda ya dace ya yi , ga barcinsa ba wai barinsa ya yi domin maganin yana saka barci sosai, ko yanzu da kyar ya iya mikewa sallar nan
Juyawa ya yi da nufin tafia, sai dai muryarta ta dakatar da shi a lokacin da ta hadasa masa da bugawar zuciya da ta furta" Ina zaka je kuma? Ya ja yaa tsaya yana rike da labulen kofar fitar sannan ya juyo yana kallonta hakan ya sa ta dan daburce kadan tana sosa gaban goshinta ta ce" Gani na yi dare ya yi fa, kuma baka cikin shirin fita aikin dare ko?"
Har ta dire maganar lebenta yake kallo da tuna moment dinsa na dazu da ita
A hankali ya saki kofar ya nufota, hakan ya saka gabanta faduwa, sai dai bata gudu ba ta dake tana kuma kallon fuskarsa
Yana zuwa ya tsaya yana kallon fuskarta ya ce" Kar na fita ne?"
Dan tsuru ta yi tana tambayar kanta tambayar tasa kamar wace take son gane yaren, sai kuma ta dan gumtse bakinta ta bude ta ce" Gani na yi baka ci abincin da kuma ruwan ba gayacen a rufe yadda na barshi"
Wajen abincin ya kai dubansa wanda sai yanzuma shi ya kula da shi har ga Allah, to in ba ita ba ai wata yinwar ta kori wata gaskiya
Bakinsa ya tabr ya juya yana fadin" Cinye abinki na koshi!"
Da ido ta raka shi har ya bacewa ganninta kafin ta sake sauke ajiyar zuciya tana shafa dogon karan hancinta hadi da lumshe idannuwanta ta nufi dakin barcinsa dan gyara masa bed dinsa da tatare gajeran wandonsa dan ta tabata ba zai taba shiryuwa da yarda gajeran wando ba a inda ya cire shi!
______________________________________
Da Mugun sauri ya idasa shiga wajen da likitar sojan ta kawo shi ta nuna masa cewar matar Dad na ciki da likitoci a tare da ita da su Dad din
Hankalinsa tashe ya shiga yana kallon yadda likitan nan ke magana su Dad gaba daya hankalinsu a kansa ga kuma gefe daya likitoci mata biyu da su Mama na ririke da ita tana ta fuzga tana dumumuwa mararsa dadin sauraro masu kamanceceniya da tonon silili da bugun kirji da fitsarar harshe da komai , sannan sai ihun a barta mutuwa zata yi ta yi gunduwa gunduwa take yi, abu shi ba na mai iska ba, shi ba na mai fitar rai ba, shi ba na mahaukaci ba, abu dai abun mamaki da tsoro , abun rikita zuciya tashi daya abun haukata bawa
Likitan ya sake fadin" CHIEF, abinda ke hadasa irin wannan crise din ba komai bane sai rashin lafiya fa muke kira da NERO PALU, shi Nero palu zan iya kwatanta maka shi a matsayin muguwar masasara, watau zazabin dake kama jiki ya cinye karfin jiki har ya haye ya nemi taba kwakwaluwa, tabas wannan zazabi yana da hadari sosai domin bama fatan rashin lafiya ta yiwa mutun yawa har ta kaishi da haka, wannam zazabin idan ya rike mutun mukan hada dukan kokarinmu bayan mun fara rike Allah, domin yana saka mutun ya yi har fiye da haka, ciki harda dabi'u irin na mahaukaci, tube suturar jiki, zage zage, kokowa, neman fita da gudu, sakin kashi a jiki, yakushi ne, dukka ne, magangannu ne masu muni sosai, domin akan shafe dukan wani hankaki na bawa ne a zuba masa rashin hankalin, daidaiku ke yin irin rashin lafiyar nan a cikin hali na summa, dayawansu kuwa idan suka tafi duniyar summan basa dawowa shikenan, wannan zazabi yana da hadarin gaske domin wasun idan suka dawo hayacinsu kwakwaluwarsu na tabuwa, wasu zasu jima sunna yin jinya, wasun kuma sai ka ga Allah ya taimaka sun tashi garas abinsu............ Ba maganar aljannu bane wannan kar ku ce zaku tafi da ita , ku yi hakuri mu daureta haka dan kar ta lahanta jikinta sannan ta lahanta na kusa da ita, in sha Allah zamu bi crise din nan sau da kafa har ta dakatar sai mu saka mata magungunnan fa zasu karra talafa mata wajen sake dawowa hayacinta da samun lafiyar zazabin"
Gaba daya abin wani iri ya zo masu duba da su basu karanta ba, bayan hakan take, Nero palu gaskiya ne, ba cutar iskokai bane cuta ce da zafin zazabi ke hadasa shi har ya haye ya taba kwakwaluwa, daga nan sai abinda Allah ya yi, wasun daga nan ake kwasarsu a kaisu gidan mai rukiya, kana ja da karfi kana kokowa da zazabin da kake fama da shi, malamin na daneka yana tofa maka abubuwan alkhairi yana so ya kwontar da iskokan, wani sa'in akan yi dace Allah ya yiwa abin tsawa, wani sa'in kuma dacen kan hadewa da ALK'ALAMIN kadararka wanda ya riga ya zanna tun kafin a haliceka cewa ta wannan dalili zaka dawo mahaukaci ko ka rasa rayuwarka, ko kuma ka ga baban tashin hankalin da baka taba tunanin akoyshi a cikin duniya ba......kadan daga aikin zafin zazabin nan, baban matsalarsa shine yawanci idan hankalinka ya dauke din nan dukkan wani abu na sirrin ratuwarka ke dagowa ya bayana da bakinka, alkhairi ne ko shari ne, ko menene da bakinka ne zaka fadi cewa ni da nake yin kaza da kaza? ......... Ku tambayi likitoci zasu baku bayani dala dala cewar tabas haka ne kuma hakan ke faruwa
Da wannan lamari aka taki rashin sa'a ya fado a kanta, a daidai wannan gaba, a irin wannan babar rana da mijinta ya wayi gari ya sauke dukkan wani nauyi da yake ji ya masa girma a saman kansa, sai ga matsala ta rashin lafiya ta fado, ta kuma zo da karfi, cikin kudurar ubangiji irin wannan,
Da karfi suka kakamata bayan an gyara mata hijabinta Allah ya taimaketa da masu rufe mata suturarta a kusa, suka samu suka daureta a jikin gadon da take kwonce, irin daurin da ba zata iya jima kanta rauni ko ta daki wanda ke gefenta ba, karfi ne tamkar na aljannu ke jan mutun, domin kana iya watsar da mutanen dake gefenka idan abin ya motsa, yana yi ne kuma yana kwociya
"Walahi walahi sai na kashe MUHYIDEEN da hannuna, sai na kashe shi , yadda yaron nan da uwarsa suka shigo min rayuwar gidana da mijina ina mulkina son raina aman suka zo suka fi karfina ya zamto mijina ya samu yaron nan a matsayin dan da yake fatan samu namiji aman bai samu ba, shine komai nawa da na y'ayana ya dawo hannunsa harta da shawarar abinda ya shafemu sai ya nema a wajensa uwarsa ta ciri ta kullu tabi bokaye ta shanye mini mijina sai yarda ta yi da shi ita karuwar algunguma mai........"
Da sauri ta karasa wajen ya dora hannunsa na hagu a saman bakinta ya damke da mugun karfin da ya sa ta hade da fatar tafin hannun nasa ta gala wani wawan cizon da ya ratsa dukan gaban jikinsa dan azabar zafi harma ya fara ji zufa na neman karyo masa, aman ya danne ya sake dora dayan ya danne bakin nata sosai yana rintse idannuwansa wani irin tsoron Allah na shiga dukkan sasan jikinsa da tsoron haduwa da shi a gobe kiyama da wani laifin, sannan ya sake yarda cewa ko me bawa yake yi a duniya dama Allah ke ara masa , kalilan ke samun dama irin wannan wace zasu bayana kafin su koma ga mahalicinsu, in ka yafe masu to, in baka yafe bama to, dama damarsu basu je a makance ba, watau sunna aikata aikinsu a boye da mugun nufinsu a zukatansu ba
Kallon da Dad ke yi masa, da Mahaifiyarsa ke yi masa, da kuma matar mahaifinsa ke yi masa, a gangaro kan sarakuwarsa dake tare da su, da sirikinsa dake gefe yana tofa mata adu'a a bayan an sake suturtata da hijabinta ya shigo shima yana tofa mata adu'a da nema mata sauki a wajen Allah, gaba daya suka zuba masa ido kowane da yannayi na firgicin furucin bakinta da kuma irin yadda ya damke bakin ya rike kam ya kuma hannata karasa furucinta, aman kuma a yadda take kokowar sai ua saketa zaka tabata da zarar ya saki bakin nan komai na iya faruwa ya saka shi sake gyara tsayuwarsa yana sake damkar bakin nata da hannunsa yana rintse idannuwansa ya ce" Kun san zafin ciwon nan babu abinda baya hadasawa, ciki harda dumumuwa kamar yadda likita ya sheda mana yanzu, dan haka nake so dan Allah ku fita ku dukanku waje har ta samu lafiya"
Dad kallonsa yake yi jikinsa na neman fara bari
Muryarsa na rawa ya ce" Mu fita waje ko ka saki bakinta?, MUHYIDEEN MUHAY, sake min bakinta now!"
MUHYIDEEN ya sada kansa yana girgiza kansa a sanyaye ya ce" Ka yi hakuri Dad, ba zan iya sakin bakinta ba"
Mahaifiyarsa da ta yi baya baya a hankali ta rike garun dakin ta sake zuba masa ido, sannan ta zubawa matar nan dake kwonce ido, kafin ta lumshe idannuwanta hawayen da take ta sharewa na tausayinta tun dazun wasu suka sake zubo mata masu daci sosai sai kuma ta rike hannun Tinana da ta sake rike hannunta a hankali ta shiga bin bayanta suka fice a dakin kwata kwata suka fice a wajen har suka hade da y'ayanta mata da suka yi zuru zuru an hanna su shiga wajen , Suka wuce su ba tare da sun iya kula tambayoyinsu a kan jikin mahaifiyarsu ba, ya rage sauran mace daya da kuma su Dad, wace itama ta sauke ajiyar zuciya ta girgiza kanta ta juya ta wuce a dakin tana tunanin tabas son zuciya da rashin godiyar Allah sun kai matar nan sun barota , hakan ya rage daga Dad sai Sultan, sai Muhyideen da ya ki sakin bakin nata
Da karfi Dad ya shamace shi ya warce hannunsa a saman bakinta, kamar jira take ta dora da fadin" Ke kuma Salma yadda na haife ki da cikina aman kike juya min baya a kan kudirina da shirina na son kashe dan iskan yaron nan ba damuwa, ai gari da yawa maye ba zai ci kansa ba, da kudina a jakata na tabata zan janyo da yawa da zasu kama min, sai na ga an fita da gawarsa a makara a wulakance zan samu nutsuwar zuciyata, mijina na ni kadai ne sai ko y'ayana, du wanda ya ratso duniyata da mijina sai ya shiga uku wannan alkawarina ne!, Sannan da mijinki ke maganar karra aure ki sani ba zan taba bari a maki kishiya ba, yar iska mai zuciyar mahaukata da baki san ciwon kanki ba bale na uwarki! Ana wulakantani kina nanuke da su ke ga ta kirki ko? In dai mutun ne mugun ice ne,, su ji suke tamkar ki mutu su karra yawon kudin gadon ubanki a kanki............., Ita kuma uwar Uma itama sai na................"
Bakin ya sake damkewa bayan ya bi Father da kallon tausayi yana girgiza kansa ya waiga gannin Aban Shuwwa na kokarin barin dakin a birkice ya ce" Sultan "
Wani irin birki mahaifin Shuwwa ya ja ya juyo da sauri yana kallon bayan MUHYIDEEN
MUHYIDEEN ya sake tausasa kalamansa ya furta" Aikinka ne hanna yaduwar fitina ko wace iri ce Abah, ka taimaka ka shiga a matsayin da Allah ya nadaka a kai ba wani dan adam ba, kana da ruwa da tsaki a ciki a matsayinka da Allah ne ya baka, ka dube mu ka kama Abahna, ka kwatanta masa cewar wannan din ba komai bane ba, karma ya daga hankalinsa a irin wannan, Allah ne ya kadara masa haka , wannan al'amari a rubuce yake tun kafin a halicemu, Dan Allah kar ya rikita lafiyarsa ko ya saka a ransa ta yadda zan rasa wani uban a karro na biyu, ya sani wannan din sirrinmu ne na cikin gidanmu, dama ba lale kowa ya zama yadda ake so ba, fatana wannan din shine na karshe a wajenta, Abah ka fada masa bani da karfin fuskantar wani hargitsin bayan wanda na bari a dakina da kuma wanda na tarar din nan a irin wannan lokacin, Aba bani da karfin iya jure haka a irin wannan lokacin Abah....... ba zan iya ba Abah....................." Ya karashe a matukar raunane yana sake kallon yadda take dago kirjinta da karfi tana mayarwa a jigace haka kuma so take ya sakar mata bakin ta idasa tonawa kanta dukan asirin dake ajiye saman zuciyarta wanda ya hadasa mata nauyin zuciya sosai ya hanna mata sukuni take kwana take tashi da shi ( Astgfrullah wa atubu ilaiki )
A hankali ya karra sada kansa yana ta tofa mata adu'a, tun tana yi karfi da yaji har muryarta ta disashe ta dawo yi a hankali , kafin ta yi shiru idannuwanta rintse, watau barci ya yi awon gaba da ita
Sai da ta yi barcin nan ne sannan likitocin suka shigo aka shiga jona mata magungunnan du da