Showing 144001 words to 147000 words out of 226733 words

Chapter 49 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

7941

sa ne......"

Bakinsa da ya yi furucin ta tsatsare da ido kafin a sanyyaye ta dan juyar da hannunta ta ce" Abansa har yanxu baka fadi laifin ba, ka ce tana sonsa ne ka yi shiru, to wanene bai san cewa Useinata na son Son ba? Matar da a kansa sai ta batawa kowa rai? Ai tana son yarontah......"

Dan sauke ajiyar zuciya ya sake yi zai kuma yin magana Muhay yaa mike tsaye a hankali ya karaso ya kama hannayenta ya nufi wajen zaman da ta tashi ya zaunar da ita kafin ya zauna ya rike hannayenta yana fuskantarta sosai ya sake kallon CHIEF OF ARMY da ya dawo ya zauna a gefenta yana jin tsoron abinda za'a fada mataa domin bata iya tashin hankali ba sam

A sanyaye ya ce" Mahmanah, tun kafin ki haife ni kin san bawa kowa da irin kadarar da Allah ya hukunta zai faru da shi, sannan ina so ki sani cewar abinda yake faruwa launi ne na zane zanen kalar ALK'ALAMIN kadararmu, a cikin lamarin zan so ki dubi wajen dadin fiye da bakin shine cewa har zuwa yanzu makamancin hakan bai faru ba, kennan Allah ya kadarta sannan ya kare mu da kariyarsa........, Baban abinda zamu iya yi shine ci gaba da adu'a, yi mata uzuri, sannan mu ringa nuna mata dan ta bar halayan nan da take yi kwata kwata ta koma ga ubangijinta domin mutuwa ana barin ciki, jariri ya mutuma bale ita, baa lokaci, idan har lokacin yaa yi shikenan baa tsumi ba dabara sai an tafi, shin idan bawa ya je ga ubangijinsa da wannan kayan a saman kansa ina zai saka ransa a kiyama?, Tabas ya shiga uku ya kuma shiga uku, domin ya tozarta komai bayan shi din mai shahada ne a bakinsa........"

" Haba MUHYIDEEN MUHAY, ba zaka fada min ko menene ba sai zuciyata ta buga?, Ka fada min na gaji dan Allah"

Idannuwansa ya lumshe a sanyaye ya ce" shekaru shida da suka wuce ne, a ranar da kika tafi haji tare da Dad, ya kasance bani da wajen cin abinci dole sai a wajenta, da na je cin abinci gidanta ne ta.........." Idannuwansa ya dago a birkice ya zuba mata su yana kallon fuskarta ya ce" a ranar ne ta , ta ce tana sin aurena......." Ta karashe yana mai dantse harshensa yana kuma sadda kansa sakamakon kunya da ta lulube shi bayan furucin nan da ya yiwa mahaifiyarsa wanda Allah yana ganni ya fi jin kunyarsa fiye da komai

Da farko dan shantakai take kallonsa, kafin ta juya wajen mijinta a zabure tana kallonsa

Yannayin da ya nuna ya saka ta gane lalle fa abinda yaron ya fada ne ta ji a kunnenta sannan iya gaskiyar kennan

Da karfi ta so mikewa, sai dai ya riga ya gaje wajen harma ya danne kafafuwanta yana sake sada kansa sosai

Da karfi ta saka hannunta dan ta hankade shi, aman ta kasa domin ya ririketa sosai kansa a kasa

A haukace ta sake ture shi tana mai daga hannunta ta ratsa masa wani ratsetsen marin da ya bada sautin tasssssss a saman fuskarsa sannan ta sake neman dago fuskar tasa, hakan ya sa ya dago fuskar tasa yana sake rintse idannuwansa ya bata dama ta hanyar bata fili ya sakar mata kyakyawa, lalausar, ni'imtaciyar fuskarsa sannan ya ki bata damar tashin dai

A wani haukacen ta sake wanko fuskarsa da mari ta kuma guda, ta daga zata kifa masa na hudu mijinta ya tare yana kallonta muryarsa a rikice ya ce" Me kike yi haka Hasana?"

Da muryar kuka da ihu ihu ta ce" Kai, ka ji me yace? Giya ya fara sha ne? Kana jinsa kuwa? Mamansa fa? Ko ban fahimta daidai bane? Mamansa fa?"

Da sauri ya dubeta a kausashe ya ce" Eh ita din sai me Kuma?, Aka ce Ita din fa sai aka yi yaya? Ko karya akai mata ne? Kina fa gani irin yadda muke kauce maki haka dan mun san ke din nan zuciyarki ba zata dauka ba, a yanzu da kika takura har kika ji sai ki ringa yi masa tankadeta mareta kina cewa ya sha giya? Wace giya kuma da ta fi bayananiya ne?, Hasana ki fuskanci yaronki mana, ke kin san me kika haifa, idan kin san makaryaci kika haifa kuma fine ki karyata maganarsa sannan ki turashi wajenta sai ki rufe taron da fatiha ki kuma tanadi haduwarki da Allah!"

Yana gama fada rai bace ya mike fuuuuu ya fice a falon
Sai dai yana fitowa idannuwansa suka sauka a kan yarinyar dake dauke da igiyar auren MUHAY a kanta tana yi masu labe
Bata zata wani zai fito a yanzu ba , fitowarsa kuma ya sakata saurin juyawa dan ta basar din nan, sai dai ta makaro domin dama ya shaka ne ya fito kuma sai ta fado a daidai gabar da yake neman abin nema dan ya duba duba na tsanaki
A haukace ya damki hannunta ya nufi falonsa da ita, wanda hakan a kan idannuwan matayensa biyu, wa'inda suma sun kasa tsaye ko zaune kowa ya fuskanci baban d'an da mijinsu ke kauna na cikin bacin rai hakan ya sa suma suke shawagi dan gane abinda yake faruwa

MUHAY a sanyaye yake kallonta bayan ta gama maganarta da ihun fadan da ta zuba, fuskarta ta yi jajajir , hancinta ya karra yin tsayi Idannuwanta kuma sun yi wani iri
Ta zama abin tausayi ta sake fuskantarsa na dan sakwani, sai kuma ta fashe da kuka tana girgiza kanta ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, ya Allah ka sa mu cika da kyau da imani, da ban gaskiya da kalmaru shahada a bakinmu, Allah ka sa karshenmu ya yi kyau ya ubangiji, ko me muke aikatawa ba na alkhairi ba Allah ka sa kafin mu mutu mu tuba, ya Allah ka sa mu din masu dacen kyakyawan karshe ne......."

A hankali ya gyara zamansa yana sake riketa a jikinsa domin ta sauko daga saman kujerar gana dayanta ta zube a kasa hakan ya sa ya riketa a jikinsa sosai yana saurarenta

A sanyaye , muryarta cen ciki ta ce" Tabas tsananta bincike bashi da kyau, ba zan kuma ba Son"

Kansa yake gyadawa a hankali yana karra shafa gadon bayanta

A hankali ta sake fadin" yaya aka yi kana sane ka kyale idan ta ce matar da kake aure ta mata laifi na hau na wulakantar da y'ayan mutane har a je da saki?, Ashe halin kadarar da yar uwata ke ciki kennan?"

A hankali ya ringa shafa gashin kanta daa sanadiyyar take hijabin ya sa ya bayana a birkice take sosai

Wayarsa dake jikinsa ce ke ta vibration tun dazu, da kyar ya iya cirota yana dubawa
Gannin Colonel ne ya saka shi dagawa a hankali ya karra a kunnensa yana sauraro

Da kyar ya iya furta magana kamar haka" idan ta ki biyoku ka dauki Sergent Umaimat ta daukota ko a kai ne, kar ta kwana a asibitin nan"
Daga haka ya datse kiran yana sake buda idannuwansa a saman mamansa a sanyaye ya ce" Mahmanah"

Mama ta sake rintse idannuwanta ta ce" yaya zan iya rintsawa?"

MUHAY ya ce" zaki iya Mamanah, nima yau zan iya yin barcin sosai fa, domin kin ga ai kin sani, zakuma ki min adu'a kamar yadda kika saba, wada na san daga kin yi Allah zai amsa"

Mamah ta sake sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Zamu yi mata uzuri ko Son? Sanann zamu yi mata adu'a, zan sake kusanta kaina da ita dan n 💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥


*The Hero writer*


*SAJIDA*


_Bismillahir rahamanir rahim_


PAGE:. 5️⃣1️⃣



*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*






*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*


*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*



*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*



*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*


*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618


Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰







Zai kuma yin magana suka ji budewar kofar falon da karfi, Shuwwa ce ta auko kamar an hankadota sannan ta ja wani uban birki tana waigawa ta nuna hannunta ta ce" Ke , ke bari shi wanda ya turo ki ki rikonin nan a kansa zan huce, in ba sai ya fadan in ni y'arsa ce ba shegiya nake yau ga wulakanci ki dagoni gaba dayana ki dura a mota? Kan ubancen kayasa!"

Nahidht dake rike da takalman Shuwwa din da wayarta ce ta shigi itama ta dan dakata ta juya tana dan daga hannunta da yar dariya tana fadin" An fa gode yalabiya, walahi ban taba gannin mace kamar kato irinki ba, kin dai ga kin cicibota cimak kin saka a mota, Allah ya biya, idan Kuma ta ki zama zan saka a taboki ki ci min uwata ko zata shiryu kin ji? In ba Haukan Shuwwa bama ita ai da galihunta ko yanzu aka busa kaho soja zai riko hannunta, Allah ka sa su ji kaina su aura min Malan ko zan je da galihuna...."

Turus sukai sunna kallon su Mama da MUHAY da ya dafe gaban goshinsa bayan ya karewa Shuwwa kallo wace tamkar zata yi dambe dan kwalinta dama tuni ya bar kanta

Bakinsa ya dan tabe a lokacin da ya tsinkayi muryoyinsu sunna gaishe da Mama , irin basu san tana wajen nan ba

Nahidht ta yi yar dariya tana fadin" Walahi mama mun zata a cen zamu zauna ne, sai ga soja yace mu zo gida, to dai itace ta yi gardama , har ya koma yan mintunna sai gashi da wata ta dauko Shuwwa cimak kamar baby, Allah mai iko, a yau na ga abubuwa walahi Mama"

Mama ta yi Murmushi tana mika hannunta ta kamo hannayensu, da kyar ta iya budar bakinta tana fadin " ku yi hakuri y'ayana wani abu ne ya fitar da ni na gagaw akun ji?"

A sanyaye Shuwwa take kallonta, a hankali ta dan karra matsawa kusanta tana sake kallon fuskarta

Mama ta yi masu dan Murmushi ta ce" ku je ku yi wanka maza ku kwonta ku huta zamu yi magana gobe in sha Allah "

Amsata sukai suka mike suka nufi cikin dakin

Sunna shiga wata gardamar suka dora da cacar bakin har dai Shuwwa ta fara shiga wanka ta barta da waya a kunne sunna zantawa da babanta bayan ta gama fadin ta mata shiru zata zanta da tsohonta, ita dai ta shigewarta ciki da mutuwar jiki

A nutse ya sake dan bata lokaci a wajen mahaifiyarsa, ba wani dogon magana suke yi ba, aman dukkan maganar da suke yi na tafe da kula da kauna irin ta d'a da mahaifi, tana dan nuna alamu na ta yi dana sannin matsawa har ta ji maganar, shi kuma yana yin iya yinsa dan ya kwatanta mata cewar in sha Allah komai zai wuce, har dare ya tsala ya kamata ya rakata har cikin dakinta

A lokacin da zai fita daga dakin nata ne ta dan yi murmushi tana fadin" MUhay, yaren nan basa birgeka?"

Dan dakatawa ya yi yana dan juyowa dan ya fahimci wasu yara fa?

Mama ta sake yin dan Murmushi tana cewa" Ina sonsu a raina sosai, ina sha'awar yarintarsu, sannan ina son ci gaba da kula da su sosai, ka ga su fa dole sai anai masu uzuri sunma yi kokari fa?"

Sai a lokacin ya gane wa'inda take nufi, dan Murmushi ya yi mata a hankali ya furta" Allah ya tashemu lafiya Mamahnah"

Mama ta amsa shi itama tana kallonsa har ya fita kafin ta mike jiki a mace ta shiga bayi ta yi wanka hadi da dauro alwallah ta dawo falonta ta cenza tufafinta hadi da daukan dardumarta ta fuskanci gabas ta shiga kai kukanta wajen ubangijinta tun yanzu, domin ita gyara da sauki take nema a wajensa, ta san cewa shine kadai ya isa ya sanyaya mata halin da ta tsinci kanta a ciki, ta kuma san cewa idan kana da damuwa ko baka da damuwa ka kasance mai kai kukanka a wajensa sannan mai gode masa a kowani irin lokaci, shine baya gajiya da baka, baya gajiya da rokonka a gareshi, shine mai mayar da baki fari, ta kuma yarda cewa shi zai mata.


______________________________________

Kofar ya kama ya bude ya shiga ba tare da ya yi salama ba, to koda dai ya yin gaskiya kunnayensu basu jiye masu ba sam sam

A hankali Nahidt ta ajiye man dake hannunta a ranta tana ayana' Toh fa, me muka masa kuma ya shigo ya bamu daidai da kugunmu? Ni fa har ga Allah Tsoron mutumen nan nake shi yasa bana haye masa, Allah dai ya raba mu lafiya'

Mikewa ta yi tana ajiye man a nan ta dauki hijab dinta ta kalli wajen da Shuwwa ke zaune saman madubi tana fesa turare a jikinta su bayan kunnenta ne, au hamatarta ne, da dai sauronsu ta ce" Bara na ga ko zan samu netwrk din nan a waje "

Sai da ta zo fita sai kuma ta ja ta tsaya tana dan kallonsa ta ce" Yalabai, dan Allah na ce dama na fitar da miji a taimaka a daura mana auren nan kafin su Mama su ankare da abinda na aikata , ban san yaya zamu kare ba, kar su tsine min albarka kuma a zo a shiga uku"

Idannuwansa ya dago a karro na biyu ya sake kallonta kafin ya girgiza kansa bai bata amsa ba yana kallo ta juya ta fita a dakin, ya riga ne ya gama yin waje ya ajiye yarinyar nan cewa akoy wani abu dake damun kwakwaluwarta, koma menene dai akoyshi abin nan

Dan ribom dinta ta saka ta daure gashin kanta sannan ta mike ta juyo face to face da shi

Idannuwanta ta tsatsara a saman fuskarsa kafin ta dan sauke ajiyar zuciya ta ringa takowa zuwa wajen da yake tsaye

A hankali ya ringa kallonta yana fasara me hakan yake nufi? Har ta zo gab da shi sosai tana niyar take taku dayan da ya rage ta auka jikinsa ya samu kansa da dan matsawa yana sake kallonta da mamaki kafin ya ce" Me kike yi haka ne?"

Dan duduba gefe da gefenta ta yi sannan ta sake kallonsa, da zazakar muryarta ta ce" Ban gane tambayar ba"

Idannuwansa ya yiwa micik micik ya ce" Kin ga , karfa ki dauki abinda ya faru a asibiti a matsayin da niya na aikata, na aikata ne dan wani dalili daban ba abinda kike tunani ba"

Idannuwanta ta dan zaro ta ce" Me na ce to ni?"

Da kallon kar ki rainan wayo ya kalleta ya ce" Dama bana so ki ce din, ki kula ni kar ki fada min!"

Bakinta ta dan tabe tana juyawa a hankali ta shiga dan takawa ta ce" Dadin abin jikinka ai ba laushi ne da shi bale a so fadawa!"

Ido ya dan tsura mata kafin ya saka hannunsa ya damko nata ya juyota gaba dayanta yana kallonta ya ce" Me kike nufi?"

Kasa kasa ta kalla wajen kirjinsa sannan ta dago tana kallon fuskarsa , sai kuma ta shagwabe fuskarta sosai ta ce" Ka ga fa damkar min hannu ta yi da karfi ta ciciboni a gaban mutane har sai da rigar dake jikina ta yi sama har ana gannin cinyoyina , yarenka na kallo ta watsa ni a mota ta rufo, fisabililahi kafin mu rabu ai an wulakanta mutuncinka ko?"

Gaba daya sia ya ji har tsigar jikinsa na neman tashi na bacin rai, da sauri ya kalli wajen kaffafuwan nata sannan ya kalleta da kyau
Wani kunna ya fara ji ransa na yi masa, harma ya shiga tambayar kansa da Colonel bashi da hankali? Shi ya sa akaiwa matarsa tsirara? Lalle zai koya masa hankali kuwa daga shi har ita!

Rai bace ya ce" kina ji, Mama na cikin bacin rai, ki yi kokari ki dubata kafin ki kwonta, shine kawai ya kawo ni!"

Daga haka ya saki hannun nata da ya damko ya juya har yana hada kaffafuwansa wajen sauri ya ciro wayarsa ya danna kiran Colonel

Colonel na dauka da fada fada sama sama ya shiga fadin" Ashe baka da hankali? Da wa da wa kuka je daukan iyalina har za'a dorota a kafada?"

Da mamaki Colonel ya ce" Sir?"

MUHAY ya yi gagawar katse shi da wani fadan yana fadin" Ka saurara malan, kafar katana a waje a gaban karti? Ku hadu gaba dayanku har ita mai karfin a fada kin dalili!" Daga haka kittt ya kashe yana huci ya juya wajen da ya ga an tsura masa ido

Dan murmushin da ya saka gabanta ya kwonci kwonci ya fadi ya sakar mata , wanda ya sa bayan tsoron gannin an shiga da natar MUHAY din dakin cen, ya karra dora mata Tsoron kar dai gaskiya ne da matar tasa tace ya san ko su wa ke bibiyarsa?

Da sauri ta juya tana barin wajen gabanta na ci gaba da faduwa da tarin tsoro a ranta.......................


Sai da Nahidt ta gama kallonsu kafin ta yi murmushin itama ta koma ciki da wayarta a kunnenta sukai salama ta tura kofar dakin Shuwwa tana mai yin salama a bakinta

Gannin shuwwa tsaye ta rungume hannayenta a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login