Showing 78001 words to 81000 words out of 226733 words

Chapter 27 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

7948

saka shi sake kallonta da mamaki ya ce" Subahannalah, me haka yake nuni kennan furera?, Ya salam wannan furuci naki zaki yi gatsal a kunnen yarinyar dake mutuntani take min kallon yaya a gareta?, Me hakan yake nufi da furucinki?"

Hawayen da take rikewa ne suka shiga zubo mata tana kallonsa ta ce" Mun kasa fada maka dan muna shayinka, ko nace dan muna Tsoron bata maka rai kuma abu sai hauhawa yake yi?, Wani girmamawa ga macen dake kama sunnanka kai tsaye? Fitsarariya ce, watsatsiya ce Malan, me kake ji a hira da ita? Me zuciyarka ke son kaika ta baro da girmanka da darajarka, da karatunka, duniya na mutuntaka kana waya a tsakiyar dare da wannan matar? Ka manta kanwarta ce ke kiranka da Aba aman ita tana kama sunnanka ne gatsau Akaramalahu ? Yanzu da nake cikin bukatarka na fito na sameka a waya da ita tana kashe maka murya duba ka ga ka amsa gayatarta ta waya ya Ustaz baka gannin tunkudaka take yi bakin rami ne A'UZUBILAH?, Yaya zaka yi da hakina ko kuma kyautata mana da kake na tsayin lokaci ne zaka zubar a tashi daya ka riki sharin yar bariki?"

Hannunsa ya jimke yana kallonta yana girgiza kansa a tausashe yace" Subahannalah, yanzu da tsarkakeken harshenki kike munana zato wa yar uwarki musulma dan ta kasance a cikin kadarar rayuwa sannan ki dora a kaina dan kin ji jikina a amshe da yannayi sanyi sanyin dake hurawa ko kin manta irin lokacin nan koda baki tabani ba a tabe nake ne ya subahannalah shine zaki yi kalaman nan dan zuciyarta a tabe take ta nemi da jin daga gareni a kan kaurarta gidan kanwarta sai hakan ya zama laifi har ki ce yaya hakinki da nake ci?, Ki yi hakuri idan har ina take hakinki kin ji? Ki tashi mu je daga daka dan mu waye damuwar in sha Allah" (😌 kai jama'a😌)

Nahidt kam wani abu ya ringa tukar zuciyarta ta kafe wayar da ido
Gaba daya kanta ne ya kama ciwo da wani madaukakin bacin rai dake shigarta na musaman
A duk fadin duniya idanma ana tunnanin basu da kara da kawaici kowa ya zo ya ji sunna da shi domin sun yiwa malan a kan matarsa
Dukan abinda matarsa ke yi sun san ita ke yi sun kuma san rura wutar kiyayarsu da yan unguwa ke sake yi harda huduba ta matar malan da suke samu ba ji ba gani idan ta dauki magana da nufin zatai wa'azi sai ta ringa kamanta shedancin kansa da sunnansu tana kwatanta ko makotaka ta hadaka da su to fa ka yi kokarin kiyaye imaninka, watau ita tana rayuwarta ne da neman fitina da hayewa musuluncin kansa bayan ba haka musulunci ya zo mana da shi ba

Tamkar mai fama da cutar hawan jinni haka kanta ya kwashi ciwo sannan jikinta ya ringa daukan mijirya yana sakawa , barci kuwa ya ce mun yi da ke yau zan ziyarceki ne? Kama kanki malama, hakan ya sa ta ringa hawaye tana sharewa a hankali ta fashe da kuka tana fadin" Bariki kennan, mai barin bashi kala daban daban, ita bariki ko baka shige ba ka kwatanta bale ka shige har ka mutu sai ka samu wanda zai bika da bita da kulli, Bariki mai zubar da mutunci warwasss a kasa, da ba dan Bariki ba anya kuwa da matar malan zata iya wulakantani? SHUWWA, Shuwwa kin gani ko?, walahi gidanki zan kaura ni dai, gidanki zan kaura, kin ga da kina nan na fada maki abanki ya mikawa matarsa waya ta zageni da kin ci min uwata har cikin gidanta, ni kuma da na samu Abanki na fada masa me yake tunani? Hala abinda ta fada haka shima yake tunani?, wai Shuwwa dan kawai na kireshi zan gaishe shi shine ya kashen waya? Allah kaimu safiya tun karfe shida zan tafiyata gidanki ba wanda zai sani dan na kula nema suke su rabani da kanwata bayan ita kadai ta rage min !" (🤔, Nahidt kin fara zuwa da bidi'a gidan Shuwwa kuma?☹️ Soja mata saman kanka☹️)

A cikinsu kowace ta kwana ne da abu bako a cikin zuciyarta
SHUWWA haka kawai take jin wannan abin da ya yi a bayane ba banza ba, koma meye ba karami bane ba zai saka shi zuba mata tea ta sha kafin ya tafi da shi, shin haka yake yi da kowama ko tsabar bai yarda da ita bane ya saka shi aikata haka?
Nahidt kuwa ta kwana da kudirin zakara ya bata sa'a ta sauka a kusa da kanwarta, sosai zuciyarta ke ciwo da abinda take kira wulakancin Malan, ta gama yarda cewa a kusa da Shuwwa ne kadai zata yi rayuwa cikin farin ciki, a gidan yayanta babu abinda ta rasa na rayuwa, Fauziya na gefenta koda yaushe, sai dai bata san me yasa ba yanzu Fauziya ta cika sada kai idan sunna hira, bata sakewa irin na da a yi ta ihu da kakaba daria, takan zauna du a takure ne bata san dalili ba sam, duda takan yi tunanin ko matsalar barikin da suka taba tare ne yake saka Fauziyar rashin sakewa a kusa da ita? Ko a tunaninta zata riketa ne ko meye? Koma dai menene ta kawo ido ta zuba zata koma kusa da wada ba zata taba wulakantata ba duk rintsi, wace idan ta budi baki ta ambaci sunnan bariki dan ta yi kuka ta wawureta ne ta kuma tambayeta yaushe zata daina, ba dai dan tai mata gori ba

__________________________________

Shi mutun idan ya san ciwon kansa ya kasance mai yin sauko dan aiwatar da aiyukakan dake gabansa, bama mace wace ya dace ace ta yi safiyar mamaki ta gyara gidanta dan gudun mutanen daka iya yi mata safiya ko mijinta kansa dan kar kazantarta ta zauna a idannuwansa, babu abinda ke kawo wulakanci irin kazanta, kazanta batai ba a rayuwa,
Wadinnan dalili da Shuwwa ta rike ya sakata karfe biyar na yi ta diro daga saman bed ta nufi kasa ta kunna fitilu ta shiga kunna kayan wuta ta zuba turaran wuta sannan ta dauko kayan share share tana dan yatsina fuska ta gyara zaman audugar matarta da ta saka domin yau ta farka da jinni

Saman ta haura tana dan nishi dan ta jido kaya ta ajiye a kofar dakin nasa ta kwonce zanin da ta daura a saman yar yololuwar rigar barcinta wace da kadan ta dara cibiyarta ta dan zazage zannin da kyau ta dan wara kafarta dan ta gyara daurin zannin kanta a kasa , kan nata sanye da hular barci mai laushi mai kyalkyali fara kal ruwan rugar dake jikinta itama mai santsi mai lafewa a jikin mutun sannan mai siririn hannu

Kofar dakin ya bude yana dan yin hamma idannuwansa suka sauka a kanta da zannin a hannunta tana sake kabewa zata daura

A zabure ta dago sukai ido hudu, ta maida dubanta kan cinyoyinta dake waje har zuwa kan jan pant dinta mai raga raga
A haukace ta juya da zannin ta gyara tana daurawa hakan ya sa ta bashi bayan kafin take rufa zannin a cumurmure ta daura shi sama sama sosai tamkar bagwariya hakan ya sa gaba daya idannuwansa a kan duwawun nata har ta juyo du ta rikice kirjinta na hawa sama da kasa kar zai bale ya fito daga ciki ta raba gefensa bakinta na rawa ta ce" Zan , Zan shige ciki"

Daga haka ta yi kasan hannunsa dake dafe da jikin garun ta shige dakinsa wanda ya yi mutuwar tsaye a wajen da yake ba tare da ya gane halin da yake ciki ba

Da balaki ya juya ya bi bayanta a lokacin itama ta rasa ina zata nufa, gaba daya ta rikice ganninta da kato ya yi a haka, waima uban me ya fitar da ita da asubar nan ne? Ta bari idan ya yi tafiyarsa sai ta yi aikinta mana, yanzun a banza katon wofi ya kaleta?

"Ke ke zo nan!" Ya fada a kausashe yana nuna mata gabansa

Gaban nasa ta kalla ta karra karewa tsayuwarsa kallo, adu'a ta shiga yi a cen kasan zuciyarta na neman tsari da shi, sannan ta shiga takowa jikinta ba karfi sosai ta nufo inda ya nuna matan

Hannunsa ya saka yana fadin" Ki gyara wannan abin dake jikinki kafin ki karaso min nan!, Kin ga tsayama a cen na fada maki ki fita a harkata a cikin gidana kin ji abinda na fada maki!"

Dukan jarumta, da tsaurin ido irin nata da rashin Tsoro ta yafo tana kallon hannayensa da bemab maboya a dakin nasa kasa kasa ta ce" wai gidansa, gidana dai"

Dif dakin ya dauka domin tsittt ya yi da fadan dan ya ji abinda ta ce
Kai, wayo, anya ba gamo ya yi ba? Anya ba aljanna bace ta shiga lamuransa aka daura masu aure? To aman idan aljanar ce shi me ya mata? Yanzu ace yyarinyar nan ta rasa wanda zata raina sai shi? Cewa fa ta yi gidanta ne fa?

A kausashe ya ce" kika kuma cewa gidana naki ne sai na baki mamaki a cikin gidan nan, kin ga ni fa ba shashasha bane da kike son mayar da ni abin wasanki, sannan da kika fito kike sakin zani a gabana a tunaninki da irinku na kai min da tuni ban zama bunsuru a kasar nan ba? Ki kiyaye haye min har na samu mafitar rabuwa lafiya da ke domin idan kikai wasa sai dai ki sake jewa wani katon a kakarye!, Shirmen banza da wofi, ke mema kika zo yi dakina ne?!"

SHUWWA ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa ta ce" To aman ai gyaran dakin zan yi ko?, kumama ka ga soja nifa ba abinda kake tunani na zo yi ba walahi ko daya, gani na yi a dan zaman da zamu yi da kai wanda nake fatan ko yau ne ya katse nima a yabeni ya fi da ai min Allah wadai kau?, kuma da nake cema gidanka gidana ne ba fa dan ina nufin hakan har cikin raina bane dan dai na dan farkar da yarenka ne kar sunna neman kawo min raini, bayan wannan gidanma ai na gwamnati ne gaba daya......". Ba da tsayaya bane take bashi amsa, irin amsar nan ce kana magana kana marairaicewa kana karya kai da nuni da hannayenka wanda ke nuni ala dole kai a tsoracema kake da mutun sannan a ladafce kake bashi amsa fa ba wai a hargitse ba, idan dai mutun mai rauni ne dole zai birkice a kallonta, idan ba mai rauni bane kuwa bakinsa zai iya yi maka gum ko ka ga mutun ya rikice yana zaginka da magulmaci ka bar masa waje, ba wani gulma ya rikice ne bawan Allah

Shi kam lamarin kukar da shi ya yi ta yadda ya kasa furta mata A ya zuba mata idl yana tunanin idan ya warceta ya dokata da garun nan ta summa yana da zunubi ne ko lada? (😌)

Alamun za'a tada sallah da ya fara ji ya saka shi juyawa da sauri ya fice a dakin ya barta a nan tsaye

Bakinta ta tabe tana kallon madubi ta shiga kunce zanninta a nutse ta gyara a fili ta ce" Ta yiwuma haka aikinsa daga ganni ina daura zanina ka wani kalla kuma ka so nuna nice fitsarariya?, Wollah ka ci kanka tuf tuf ka shafa min lafiya wollah!"

Kayyan ta koma ta kwaso ta dawo ta shiga aikinta da jiki, aiki ne da ta riga ta saba, aiki ne da take yinsa da farin ciki ba da jeka na yika dan ka zamto min dole ba, aiki ne na kwonciyar hankali da sannin hannunta, hakan ya sa a nutse ta gama gyara ko'ina ta kunna turaran wuta sannan ta shiga ninke kayan da ta wanke jiya ciki harda gajerun wandunnansa da ta zubawa turaran ruwa ta dan ajiye saman kujera dan su bushe kafin ta ninke hakan ya sa ta shiga kiciniyar ninke zannin gadon hankalinta kwonce abinta

Budewarsa da shigowarsa da tafiyarsa mai dan gagawa ya sakata dan waigawa ta kalle shi, shima ya tsaya ya zubawa wandunnansa na ciki ido da mamaki ya kalleta da sauri ya sake kallon wajen wandunnan

Itama wandunnan ta kalla, sai ta samu kanta da tsurawa wandunnan ido cike da tunanin abubuwan da a da bata yi tunaninsu ba
Tsintar kanta ta yi da tambayar kanta a kasan zuciyarta' SHUWWA anya kuwa lafiyarki kalau?, Wandonsa fa kika wanke kika kuma fitar zaki ninke, kin ga kallon wandunnan yake idan ya sake kwatanta ki kamar kwartuwa fa? Ke kam kin zama wace bata san ciwon kanta ba, wada ta lalace ko? Yaya kike so ya ce bayan dama ya gama fasaraki a yar duniyar karshen zamani?'

A hankali ta dago dubanta da dan satar kallo ta sauke a kan fuskarsa
Kai sojan nan ba dai kyau ba wollah, saima idan ya hade fuska kyansa ya fi fitowa
Idannuwanta cikin nasa suka sauka tsamo tsamo
A hankali ta dan kikifta ido tana kallonsa ta bude baki ta ce"








😘😘😘😘😘 Morning all, na ce ba yau juma'a ko?😒raba gidanta da karti na mata girki ya matukar kayatata ta ce"😌💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥


*The Hero writer*


*SAJIDA*


_Bismillahir rahamanir rahim_


PAGE:. 2️⃣6️⃣



*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*






*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*


*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*



*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*



*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*


*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618


Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰









A hankali ta dan kikifta ido tana kallonsa ta bude baki ta ce" Na ga sun yi datti ne sai na wanke su, baka ga darzar da nai masu ba."

Idannuwansa ya rintse yana jin ikon Allahn dake faruwa da shi, ya sake budewa yana kallonta ya ga a tsayen take abinta, d'an kifta ido ya yi yana sake kallonta yana karantarta, gaba daya yarintarta da k'ananun shekarunta ne suka bayyana a idannuwansa.
Sai ya samu kansa da tunanin anya ta zarce 17 kuwa?, Haka kuma ya shiga tunanin shin me ya saka ta zab'i rayuwar bariki da aure auren maza a rayuwarta duda ya san da wahala abinda aka ce ta ratso ta zo kasar nan ta zamto nutsatsiya, aman sai ya samu kansa da tunanin koma meye bai dace ace yarinya karama irinta ce ta saka kanta a muguwar rayuwa har haka ba.

Abinda yake bashi mamakin na gaba shine, irin yadda take tsayawa a gabansa kamar tana jiran ya yi magana ne kanta tsaye tana kallonsa bai san me take kallo a jikinsa ba kallon nata kuma ba irin na matarsa ta cen bane, ita wancen daga nesa ne take kura masa ido da zarar ya kalleta kamar munafuka sai ta sinne kai.

Ita wannan bata kallon nasa sai idan tana jira ya bata amsa, irin yadda take kuma bashi amsa kai tsaye na matukar bashi mamaki, wai shin ita bata jin tsoronsa ne?

Iskar dake bakinsa ya furzar yana nuna mata hanyar fita ya ce" Kin yi bakuwa ki je."

Ido ta karra kura masa ta kalle shi ta kalli hanyar da ya nuna mata, ta ce" Ni kuma? Bakuwa a nan?"

"Ya salam" ya fada yana dafe gaban goshinsa ya tattara hannayensa ya dago duka biyu ya ce" ke, mu nawa ne a dakin nan? Ko aikena kikai na je na gano maki ke din ko ba ke ba?"

Da sauri ta zagaye shi tana fadin" Sorry " ta nufi hanyar fitan

Har ta kama kofar zata bude muryarsa a ciki ciki ya ce" SHUWWA."

Turus ta yi tana jin gabanta na faduwa haka kuma ta juyo a hankali tana kallonsa.

Hannunsa ya dago a hankali ya nuna mata hannunta sannan a saman lebensa ya ce" Give me."

Hannun nata ta kalla, ido ta zarro domin gajeran wandonsa ne a hannun nata baki irin mai hade da pant din nan mai raga raga
Da sauri ta karasa ta kama hannun nasa da hannunta na dama ta saka masa wandon ta rufe tana karra zarro Idannuwanta ta juya da gudun da ya saka shi bin kafafuwanta da kallo da hannayenta da take yarfewa ta fice a dakin kwata kwata.

Kofar da ta rufo masa ya kurawa ido na dan lokaci yana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya nufi wajen da wandunnan nasa suke ya ajiye dayan ya nufi wajen bed dinsa ya zauna yana kai hannunsa kusan hancinsa dan ya dan goge hancin nasa.

Sansanyan kanshin turaran ruwan da ta zubawa wandunnan ya daki hannayensa hakan ya saka shi lumshe idannuwansa a hankali sanan ya sake budewa ya zubawa hanyar da ta fita ido yana sauke ajiyar zuciya kafin ya tabe bakinsa ya dan karra kwontawa dan yau sai karfe tara zai bar gidan.


______________


"NAHIDT" ta fada da dan karfi tana zarro ido sannan ta shiga saukowa da gudu gudu ta nufo NAHIDTH da ta mike tsaye itama tana kallonta.

Hannaye suka budewa junna tamkar wa'inda suka shekara basu ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login