Showing 48001 words to 51000 words out of 226733 words
masu bat, dayar kuma, wannan din kuma bata yi maki kama da hoton sarkin garin nan marigayi ba? Har farin fatarta? Hoton dake kafe a falon Aba wanda bayan ya rasu aka dora kanninsa da suke uba guda domin d'ansa na cikinsa an wayi gari ba shi ba labarinsa? Hajia duba ki gani ko dai yau na tashi a haukace ne? Ko kuma gajiya ra saka nake hade haden nan?
Hajiyar ta juya wajen da NAHIDT ta ja su Fauziya jikinta na rawa tana fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une kin ga Shuwwa abinda na so na fahimtar da ku cewar anya zuwan nan namu nan alkhairi ne kuwa zai tabata, kin ga matar cen ta malan ce take son kwatanta kamar zaman kanmu muke yi kin ga matar cen da suka kawo kayan ta kafemu da ido har ana son zaunar da ita ta ki zama mun shiga uku"
Hankalin Shuwwar ne ya yi kololuwar tashi ta juya zata kalli matar daidai matar ta fice da mugun sauri, hakan ya sa ta dora hannayenta bibiyu a saman kanta tana fadin" Idan aka fasa auren nan shikenan, shikenan aunty , idan aka fasa walahi ina iya rasa raina, wayo Allahna na tafi wajen Aban na fada masa ya rufa min asiri ya daura kin ina son Hamza, walahi ina sonsa idan ba'a aura min Hamza ba ina iya mutuwa"
Da mugun sauri ta juya itama har bata gannin gabanta hakan ya sa suka mara mata baya sunna son tsayar da ita aman ta kasa sauraronsu ta nufi falon da ta san a cen Aban yake
Tunda matar nan ta shigo kanta je kasa jikinta na dab rawa ta sake maimaitawaa yayansu wanda yake shine baba a dakinsu gaba daya ta ce" Allah ya karra maka lafia walahi, walahi kamanin sun bace, yarinyar tamkar an zaga karra da *TINANA* , sai dai kuma kamanin yar uwar tata ne suka sakani a rudu, me hadin kamanin marigayi sarkin garin nan da nata? Har farin bayan kar duniya mun san d'a daya ya malaka har ya koma ga ubangijinsa, yarinyarma ta yi kankanta ace y'arsa ce gaskiya idan aka auna mutuwarsa da yanzu"
A guje ta sake warce hannunta ta fado dakin tana neman fuskan Abanta dake zaune shika hankalinsa a tashen yana son jin karshen maganar nan
Da sauri ta idasa gabansa ta duka tana hade hannayenta ta fashe da wani kukan da ya saka kowa juyowa kallonsu ciki harda CHIEF of Army da iyayen Hamza , daidai NAHIDT ta karaso ita dinma tana kukan ta tsuguna a gabansa itama ta hade hannayen nata hakama Fauziya ta shigo itama nata hankalin a tashe
A gigice take son yin magana aman ta kasa hakan ya sa Nahidht farin" Sun ce sun fasa auren su dinma ko MUHAMAD ? zasu daina aurenta ne ko? Shikenan haka zamu kare rayuwarmu dan bamu da iyaye?, Menene laifinmu?, Dan Allah ku rufa mana asiri kar a fasa domin ko ni idan aka fasa auren nan da Hamza na shiga uku, dan Allah ku dubi maraicinmu ku bari a yi aurennan, idan har dan maganar amaryar malan ce kar ku dora hakan a kan Shushu, mu mune bama jin magana aman shushu babu abinda ta sani , burinta ta yi aure, burinta ta je ta bautawa aure, burinta ta samu kanta a dakin mijinta, ku yi hakuri a yau a daura auren nan, ko a nan ne a daura kawai ba sai sauran sun zo ba....." Ta idasa da fashewa da kuka daidai Aban Hamza ta mike yana karra kallonsu muryarsa har rawa take wajen furta" *TINANA?*"
DIF Nahidht ta yi da ihun kukanta jin an ambaci sunnan mahaifiyarta wada ba zataa taba manta wani lokaci ta taba gannin takardar mahaifiyarsu da sunnanta na usil banda Buzuwa da ake kiranta da shi
A rikice ta juyo tana kallonsa, shima kuma ita din yake kallo hannunsa still na rawa ya sake fadin" *TINANA?*"
Zabura ta yi ta........
*GARABASA GARABASA, DUKAN WADDA TA BIYA KUDIN ALKALAMIN KADARRATA ZATA SAMU GARABASAR WATA KOKOWAR KYAUTA IN SHA ALLAH, WANNAN GARABASA CE🥰*
Domin samun ci gabansa in sha Allah ki garzayo ki biya kudinki yar uwa, a kan farashi mai sauki ..........domin a gaba ne zamu gane kaifi irin na ALKALAMIN KADARAR bayin Allahn nan
Me yake shirin faruwa da su
Ina zasu dosa?
Yaya maganar gagarumin daurin auren nan da ake shirin daurawa?
Su SHUWWAR da NAHIDHT su wanene su?
Me dangin Hamza suke nufi da maganar ambaton Nahidt da sunnan yar uwarsu?
Meye gaskiyar maganar kamanin SHUWWAR?
Dukan wannan zai zo a bayane a tsare ta yadda mai karatu zai karanta cikin shauki in sha Allah
Daga alkalamin SAJIDA😍🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
+22793811618💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 1️⃣6️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.
*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
Zabura ta yi ta mike daga tsugunen da take a gaban Malan har sai da daurin dake saman kanta na dan kwalinta ya fadi kasa warwas tana kallon Aba
Muryarta ce ita dinma ta dauki rawa rawa ta ce" Ba, Ba , mamanmu ce *TINANA*"
A bayane Aban ya karaso da sauri yana rike hannunta yana fadin" Hasbunnalahu wani'imal wakim, mamanku? Ke da wa? Inna take? Inna TINANA take Hawau itace, kin ga itace wannan din jinninmu ce, yarinya ina TINANA? Ke din ke da waye kika ce mamanku ce TINANA?"
Sai kuma ya yi shiru da gagawa ya juya wajen baban Hamza da suma gaba daya hankalinsu ke kan su SHUWWAR din balema Chief of army da yake kallon yarinyar da tausaya
Yana zuwa ya ce" Elhaj, ka ga wannan ai jinnin Hamza ce, yar mamansa ce, ko ba haka kike nufi bane yarinya? Dan Allah ki fahimtar da mu kamanin nan naki da kanwarmu"
Gannin du a rikice suke ya saka Ganaral fadin" Bismillah, Elhaj ka zauna ka ga yarinyar du ta rikice kana gannin kanwarta itama du ta shiga a halin rudu, ku zauna mu yi magana a tsanake dan Allah".......daidai nan kira ya shigo a wayar Ganaral hakan ya saka shi dagawa yana mai amsawa
A nutse ya furta" Masha Allah, ka sa abokinka ya kula da baki ka shigo a nuna maka falon da Malan ya sauki baki muna ciki, ai da dan saura lokacin daurin auren bai cika ba, ba za'a tsayar da mutane ba, ka shigo "
Daga haka ya katse yana fuskantar mutanen dakin shima ya kasa yin magana
Malan da Shuwwar ta yi karkadab da hannunsa ne ya samu a hankali ya janye yana sauke ajiyar zuciya a nutse ya furta" alhmdulilah, in sha Allah dukan abinda Allah ya yi a yau alkhairi ne, domin zabinsa muka nema, shi muka fadawa, koda na tsayin sati takwas ne kadai muka dauka muna fada masa zamu iya cewa Alhamdulilah sannan mu yi hasashen cewar ya ji mu ya kuma amsa rokonmu, NAHIDHT da SHUWWAR, shin zaku iya saka nutsuwa a firgicin dake tare da ku ku bamu labarin abinda ya faru da iyayenku har kuka samu kanku a kasar nan?"
NAHIDT ta hade hannayenta a wajen kirjinta tana girgiza kanta ta ce" Wace irin Nutsuwa ?, Walahi bani da halin samun nutsuwa , kawai a bar maganar idan aka daura auren sai a yita mana....."
Salamar Hamza ya katse furucinta su dukansu suka bishi da kallo
Fauziya ta maida kanta ta sada tana hanna kanta fashewa da kukan itama
Shuwwar ta bishi da kallo har ya karasa wajen iyayen sa bayan ya nuna rudanin gannin dakin a haka ya duka kasa yana gaishe su sannan ya juyo wajen yan matan har kan SHUWWAR da ta kura masa ido kafin ta idasa zama gaba dayanta tana sauke ajiyar zuciya hadi da fadin" Ga kama nan, Nahidt ga kamarku nan?"
Da karfi Nahidt ta ce" A gidan uban wa, ba kamar da muke yi da kowa, ke tashi mu tafi"
Shuwwar ta girgiza kanta a sanyaye ta ce" Babu inda zamu je, ko mun je ma dawo ne, NAHIDT ko mun gujewa abinda nake hasashe ma dawo da kafafuwanmu ne"
Ta juya tana fuskantar Hamza da ya zauna a kasa yana kallonta , irin yadda take magana a nutse sai ya ji gabansa na faduwa
Shi sangartaciyar nan mai ihu idan abu ya daga mara hankali yake son ganni
Ganninta ta yi sanyi yanzun sai ya tsinci fargaba a tatare da motsinsa
A hankali ta ce" Sunnana IBTISAM KABIR A KABIR MAHADI, sunnan auntyna NAHIDT KABIR A KABIR MAHADI, an haifemu a kasar Riyad ne ni a watan January 2 a shekara ta 1998, auntyna kuwa a watan Décembre 18 a shekara ta 1989, mutanen da muka sanni a rayuwarmu wa'inda suke rayuwa da mu kwonciya da tashi sunne mahaifiyarmu wace ake kiranta da Buzuwa, sai mahaifinmu KABIR wanda suke masa inkaya da ABDALLAH, munna nema ba dare ba rana kamar yadda du wanda ya je kasar da niyar nema yake yi, iyayenmu a tsaye suke a kanmu bama zama bamu ci ba, basa barinmu zuwa wajen da zamu tarda hatsari, haka kuma sunna taka tsantsan da tarbiyarmu shi yasa muke da tarbiya a kan sauran sosai, mun yi sauka tunda kannanun shekarunmu sannan mun yi harda a kawunnanmu ta alkur'ani tun bamu kai ko'ina ba domin mun tashi da yaren a bakinmu hakan ya sa karantawa da fasarawa baya bamu wahala, ya zamana abu mafi sauki a rayuwarmu, Mamanmu tana da hira sosai da fara'a, a kanmu zata iya batawa da kowa, idan mutunci kake so da mahaifiyarmu ka kiyayi wulakantamu, idan ka wulakantamu zaku iya sabawa da ita, mahaifinmu kuwa sam bashi da hayaniya, ya kasance mai yawan shiru shiru, gashi basa so a masu maganar kasar da suka fito su dukansu, bamu san dalili ba, ko mu mukai masu tambayar wai muma ba asalin yan Saudiya bane? Sai suce basu sani ba kuma kar mu kuma yi masu tambayar, sunna da baban mukami a wajen da suke sana'arsu, sunna da karfi sosai domin ana shayinsu ana kuma girmama su, Ba zamu taba manta shekarar da muka wayi gari ba su ba labarinsu ba, ko salama bamu yi da su ba domin sun saba yin irin tafia sallar nan tare, makociyarmu ke fada mana cewar......."
Shiru ne ya ratsa ta sada kanta tana shashekar kuka hakan ya sa Nahidht rike hannunta da yake rawa ta budi bakinta ta ce" Makociyarmu ce ke fada mana cewar sun rasu a wajen arf, daga wannan ranar makociyar tamu ta bayana mana wa'inda ke binsu bashi, du irin tarin dukiyar da suka tarra sai da ya zamto an biyo su bashi hakan ya sa dole muka fada aiki dan idasa biyan bashin da ake bin iyayenmu domin mun san cewa ko sisin kwabo na hanna kwonciyar kabari, sannan dole mu nema ko dan mu saka a bakinmu......."
Bakinsa na rawa ya ce" Shin kun ga gawarwakinsu ne?"
A hankali SHUWWAR ta girgiza kanta tana fadin" Mun je, mun sake zuwa, mun fadawa mutane sun tayamu nema bamu ga gawarwakinsu ba har aka yi suturar mamata ranar juma'a , a lokacin kuma aka hanna mu shiga dan karancin shekarunmu aka koremu, daga baya mun je kaburbura mun yi ta bin sunnaye aman kun san yawan wajen da girmansa har aka kamo mu aka dawo da mu kasar nan bamu samu muka gama zagayen makwontan ba, sai dangana muka yi kamar yadda makociyarmu ke fada mana cewar mu yi hakuri mu bisu da adu'a, sun rigaya sun rasu babu yadda muka iya hakan muka yi hakuri har aka gama aikin haji aka koma daga nan aka dawo da kame, muka taki rashin sa'a wata fita da mukai zamu je gidan da muke goge goge aka kama mu aka kawo mu kasar nan"
Innalilahi wa inna ilaihi raj'une..... shine abinda aban Hamza ke maimaitawa kansa a kasa yana girgiza kan nasa
Gogon Hamza ta yi gagawar fadin" Dan Allah bayan Buzuwar bata da wani sunnan ne? Yar budurwa kamar na ji kin ambaci wani sunnan bayan wancen?"
Du irin yadda ta cika da tsoron maimaita sunnan da ta taba gani a takardar mahaifiyarta haka ta budi bakinta ta ce" *TINNANA* "
"Muhamadu rasululahi sallalahu alaihi wa salam, dan girman Allah yaya wadinnan yayan Tinanarmu ne, walahi y'ayanta ne Innalilahi wa inna ilaihi raj'une TINANA ta rasu? Ta rasu bamu nemi gafarayar junna ba? Ta rasu bamu nemi afuwar juya mata baya da nuka yi dan ta samu ciki ba? Ta koma ga mahalincinta da mikinmu a zuciyarta? Wayo Allahna"
Hamza da cikinsa ya juya daga zaunen da yake ya yi raf da hannun babansa yana zarro ido ya juya yana kallon baban nasa bakinsa na rawa ya ce" Babana mu je a daura auren mana, daga baya sai a dawo a tatauna inaga kamar sun san su Shuwwana ne ko?"
Da tausayi mahaifinsa ya kalle shi yana jimke hannunsa da kyau ya maida dubansa kan CHIEF OF ARMY da ya yi dan gyaran murya ya kalli NAHIDT, ya kuma kallon Hamza, ya kalli Shuwwa ya maida dubansa kan iyayen nasu, a tausashe ya furta" Subahannalah Astagfrullah, subahannalah "
Gogon Hamza ta girgiza kanta tana fadin" Wani daurin aure Hamza, wadinnan kannenka ne uwarku daya da su Hamza, mamanku daya fa da su, ai ka san ba maganar aure tsakanin jini daya ko Hamza"
Ido ya zarro yana son mikewa tsaye jikinsa na rawa haka Shuwwa itama ta mike tsaye lokaci daya idannuwanta na firfitowa waje ta juya da sauri tana kallon Hamza sannan ta juyo tana kallon NAHIDT da ta yi mutuwar zaune hannayenta bibiyu saman kanta
Maimakun ta ji salati ya fito daga bakinta sai wani ihu da ya fito da karfi ta kurma shi tana dora hannayen nata itama su biyu a saman kanta
Idannuwan nan nata masu rukowa waje ta karra rukowa a birkice ta furta" Auntyyyyyyyyy" sai kuma luuuuuuuu ta tafi sakamakon juwar da ta kwasheta ta nemi makata da kasa
A tatare suka nemi tareta ana ta di kira da salamewa daidai wayar Chief of army ta kuma daukan tsuwa hakan ya sa cike da tausayi ya mike yana amsawa
A birkice NAHIDT ta kalli Malan tana fadin" Muhammad, ba za'a daura auren ba kennan?"
Malan gannin sun rikice yana kallonta ido cikin ido ya ce" Na zata farin cikin kun hadu da ahalinku ya fi komai a yanzu NAHIDT ?"
Hamza dake rike sa Shuwwar wace ta dora kanta a damtsen hannunsa idannuwanta rufe ruf ya ce" Haba Aban shuwwa, wani irin farin ciki kake so mu tsinci kanmu a ciki? Tabas ni na ji farin cikin gannin kannenaina, aman hakan na nufin ta haramta a gareni? Aure na uku kennan fa zai lalace min kamar masu bakin uwa ? Ita kuwa na biyar fa kennan idan ban mantaa irgen ba fa?"
Malan zai kuma yin magana Ganaral ya ce" Son, dube ni, ka kwontar da hankalinka mana, na san kana kulace da yan uwan mahaifiyarka aman inaga wannan abin farin ciki ne ga kowa koda hakan na nufin an fasa daurin aurenka ai Allah zai baka wata, itama hakuri zata yi haka Allah ya nufa da rayuwarku ku dukanku"
NAHIDT ta karkata kanta ta ce" Ba zaka gane bane Baba, ba zaka gane ba walahi, wayo Allahna Shuwwa tashi mu tafi kin ji? Tashi"
"Ina zaku je? Kuma kun yi mana fushin ne? Kuma ba zaku sauraremu bane? Daga nan babu inda zaku nufa da ya fi garin Tanus" gogonsu ta fada da dan alamu na iya gaskiyarta ta fada kennan hakan ya saka Shuwwar kureta da ido tana kankance idannuwanta dake ruruwa da ruwan balaki tana niyar yin wata maganar dan ba wannan mata