Showing 132001 words to 135000 words out of 226733 words
ta karaso wajensu ta kai kasa kamar yadda suke kasa ta zubawa fuskokinsu ido tana kallo
A hankali ta daga hannunta ta kai daidai fuskar Shuwwa dake kuka tamkar zata side ta shafa gefen fuskar tata a hankali , sai kuma ta saki wani irin lalausan murmushin da ya bayanar da farin ciko, nutsuwar da ta jima bata yishi ba a saman lebunnanta duda a busshe yake kamar yadda hannunta yake bushe kafin hannun nataa ya sakai ya tafi ya fadi kasa , alamu suka nuna kansu na ta suma ne
Ihu suka saka kusan a tare, wanda ya saka Mama zabura daga hawayen da take ta nufo su da sauri tana ambaton sunnan Allah gannin yadda NAHIDHT ke girgizata tana sake girgizata tana ihun fadin" ANNNA,, kar ki mana haka, baki mutu ba tun baya kar ki mutu yanzu, Anna ki tashi ki ji irin rashin jin da muka tafka ki zane mu, Anna kin san da ni yawon banza na ringa yi Ibteen Papy kuma ta ringa aure auren maza? Anna Annannnnnnnnnmmmmmmmmmmm"
Idannuwansa ya rintse a kansu a lokacin da IBTISAM ta mike tana nufo shi da wani irin wawan karfi ta juyo wajen da ya juya ta rukunkume shi a jikinta gaba daya ta fashe da wani karayan kukaa tama sake shigewa jikinsa, hakan ya sa sukai tangal tangal sannan ya sake tsayawa da kafafuwansa yana sake rintse idannuwansa
Muryarta na rawa ta ce" Kana kallo bata motsi Yalabai, dan Allah ka rufa mana asiri ta tashi, koda bata da hankali koda me ta zama muna sonta a haka......ka ga a rashinta babu irin abinda bamu gani ba,, ashe dai da gaske da nake cewa bata mutu ba haka ne? A ina ka sameta? Ina papyna ?"
Hannunsa ya sa a hankali ya baambareta daga jikinsa yana kallonta yadda du ta rikice take son komawa jikin nasa
Kansa ya maida wajen Mama a dan hankalce ya ce" Ku shigo wata motar mu kaisu asibitin kudi,, na so na kilace shi a bashi kulawa irin abubuwan karya sihiri, aman mu je asibitin kawai"
Mama ta amsa shi da kai, shi kuma ya karasa ya saka hannunsa ya dage Nahidt daga zubun matan da ya yi ta mayar da ita gefe sannan ya sake dan rage tsayinsa ya makawa Nahidt din wani kakausan kallo gannin zata sake zubun mata ya saka hannayensa ya dauketa ya nufi motar da ita, inda su kuma suka kasance kamar idan kana son kaza ta biyoka idan ka dauki y'ayantan nan
Sosai ya kwontar da kujerar gaban ya dorata ya saka belt ya daureta kafin ya juyo wajen da suke jira ya basu waje su shiga
Fuskarsa ya hade sosai yana kallonsu kafin ya masu nuni da Mama da ta fito da ky da kanta , masu tsaronta na biye da ita ta dakatar da su ta karaso tana dubaa number dake jikin abin ky din har ta gane ko ta wace mota ce ta dauko dan haka ta zagaya da kanta ta yi Bismillah ta bude ta shiga da tunanin yaushe rabonta da yin tuki
A nutse ta fitar da motar daga layin ajiyeta ta dawo kan hanya, hakan ya sa ya masu nuni da cen zasu shiga
SHUWWA da muryarta ta disashe tana kallon fuskarsa kanta a dage a sanyaye ta ce" Aman me zai hanna ni na shigo nan din yalabai?"
Sai da ya dan rintse idannuwansa kafin ya bude a kan lebenta shima ya furta" Haka na yi ra'ayi !"
Da sauri NAHIDT ta ja hannunta suka koma motar da Mama take suka shiga kowace na dan dagowa tana hangen tasa, har ya gama waya da baban datijon Malamin da yake masa taimako kafin ya koma gaba ya shiga ya tayar yana sauke ajiyar zuciya ya dauki hanya
Sunna isa babar asibitin aka amshe su
Likitocin da ya samu mutane ne da suka sanshi suka kuma bashi daraja ba ta karfi da tsoronsa ba, sai ta cencentarsa a matsayinsa na nagartacen mutun mai boyenyen kyakyawan halaya, sun saba amsar marar lafiya daga hannunsa, sun kuma saba bashi kulawa
Sau dukansu sun zauna ne sun yi jigum jigum, uwa uba irin kukan da suka rikice da shi su biyun du sun rikita masa uwa baiwar Allah sai janyo su take yi a jikinta tana faman rarashi da faman bada baki a lokacin da suka ga ashe harda mahaifinsu a cikin motar nan, kuma mahaifinsu dogon mutun mai cikar halita da kwarjini ne ya dawo haka sai gaba daya suka sake rikicewa da wani koke koken wanda yake hahauda ciwon kansa
Gwuiwoyinta a kasa suke, kanta a saman cinyoyin Mama, hannayenta a zagaye da kaffafuwan Maman tana kukanta ba ji ba gani, hakan ya sa jikinta ke rawa, kuma hijabin ya sake dame mata jikin sosai, dama irin mai bin jikin nan ne
Doctern ne ya zo ya dan tsaya a gefensa yana mai yi masa bayani a kan dukkan abubuwan da suka dora su a kai, ya sake yi masa bayani a kan ciwukansu zasu samu sauki idan har sun samu kulawar da ta dace, ya dora da fadin cewa baban abinda ya fi yi masu ila itace yinwa, ya karashe da dora tambayar mamaki yana kallon MUHYIDEEN dake sauraronsa yana kuma amsar dukan takardun da yake miko masa kamar haka" Sir ama da mamaki, bayin Allahn nan a wani daji kuka samo su haka? Kuma na ga yar budurwar nan na kuka kamar ta hada jinni da su, sorry yar kyakyawa zasu samu sauki ai cuta ba mutuwa bace, dama cutar ke samuwa da gagawa lafiya kuma yar a hankali ce in sha Allah.................."
Yar budurwar da ya fada ya nuna ya karashe maganarsa a kanta ya juya ya kai dubansa kanta, hakama Mama dake ta rarashin su ta dago tana kallon Likitan da MUHAY dake tsaye yana sauraron bayaninsa
A hankali ta rage muryarta sosai tana ta ce" Ku yi hakuri da kukan nan haka, kun ji fa likita ya ce zasu samu lafiya kau? Ku mu yi masu adu'a shine zai sa su samu lafiya ba kuka ba............."
Takardar ta karshe ya amsa a hannun likitan ya juya ya fita bai ce komai ba
Likitan ya yi dan murmushi shima ya sake komawa dakin hutun da aka ajiye mutanen kowane da dakinsa, dakunna ne masu tsadar gaske , asibiti ce tamkar a turai, komai abin kallo ne abin ba'a cewa komai, ya sake duduba komai ya gamsu da komai da irin karrin ruwan da aka jona masu mai dauke da vitamine din da zai saka su cin abinci da sauransu sannam ya juyo ya dawo ya wuce office dinsa dan ci gaba da duba mararsa lafiya
An dan dauki lokaci ya dawo da waya a hannunsa ya mikawa Nahidht ita sannan ya kalli Mama ya ce" Ta koma Gida"
Mama ta kalle shi tana ayanna' Zama ka kawo kanka ne' ta dan gimshe tana fadin" Ban fahimta ba"
MUhay ya ce" Ta koma gida ta yi kukan a cen"
Mama ta dan tabe baki tana fadin" Ba zai yiwu ba ai Ka ga ba zata iya nutsuwa a gida ba bayan iyayenta a nan a kwonce"
Dan juyawa ya yi yana kallon yadda yayar tata ke kuka tana ta gyada kai ga dukan alamu rarashinta ne Aban na Shuwwa ke yi domin ya ce yana ta kiranta baya samu hankalinsa a tashe, shine ya bashi ita, kuma ta bude baki sai zayane masa komai take yi hankali kwonce kuma gashi sai ajiyar zuciya take yi ga dukkan alamu rarashinta yake yi, ya cire kansa ya dawo wajen Mama ya budi bakinsa da kyar ya ce" Za, zamu, zamu koma ta cenza kayanta mu dawo Mahmanah........."
Irin yadda ya karashe Mamanah din ya saka Mama dan murmusawa a hankali ta dan ringa shafa kan Shuwwa ta ce" Daughter, tashi ku je gida ki yi wanka ki dauko mana abinci da abin bukata, idan kuka dawo sai Nahidtma ta je ta kimtsa ta dawo kin ji?"
Kanta ta dago hakan ya sa ya zubawa fuskarta da ta yi jajajir ido da lebenta da har suka dan tasa dan tsabar kukan da ta ci da ranta
Yar ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya koma bakin hanya yana kallon wucewar mutane har suka gama magana da Mama da kuma Nahidt da ta bata Abanta sukai magana wanda a sanyaye ya ce" Kina ji yar gidan Aba, ba kuka ya dace ku yi ba mana, farin ciki ya dace ku yi, sannan ku godewa Allah, in sha Allah jirgin gobe da ni zai taso zamu zo mu yi ta fadawa Allah, in sha Allah ko menene zai zo da sauki kin ji?"
Kanta take gyadawa tana dan hawayen ta ce " Abahnahhhhh, ba ka ga yadda Abunah ya dawo ba"
Irin muryar nan mai hade da kuka da shagwaba ce ta yi anfani da ita hakan ya sa ya dan sake juyowa yana kallon wayar dake hannunta da kuma kunnenta
Juyar da kansa ya yi har suka gama ta taho tana tafe tana rangaji ga ciwon kai, ga tashin hankali gaba daya sai take wani rangaji tamkar zata kifa haka take ji da kyar ta iya fitowa har ta samu ta bi bayansa dan Mama ta ce shi zai mayar da ita gidan ta cenza kayanta, gaba daya tamkar ba Shuwwa yar rigima da fitina da kaudin tsiya ba, wannan lamari ya sa gaba daya jikinta ya mutu bata da wani karfin aiwatar da komai sai ido
Tunda ya fara tukin bai tsaya ya kalleta ba har suka karaso gida ta bude ta fice ta nufi bangaren Mama
Motar ya rufe Shima ya fito ya nufi bangaren na Mama
Yana shiga masu aikin suka ringa gaishe shi
Sai da ya gama kare masu kallo kafin ya salamesu ya nufi dakinta
Bai tsaya neman izini ba ya tura kofar ya shiga, a lokacin tana daure da tawul a kirjinta
Sosai gabanta ya fadi, harma ta so zabura ta rufe suturar jikinta , sai dai irin yadda sukai ido cikin ido ga rashin karfin jiki ga dacin zuciya sai ta kasa kwakwaran motsi bale har ta aiwatar da abinda ta yi niyya
A nutse yake takowa yana sake saka idannuwansa cikin nata har ya matse mata wahe sosai yana kallon fuskar tata ya ce" Shi din danginku ne?"
Kasancewar bata gane ko wa yake nufi ba sai ta samu kanta da kurawa bakinsa ido tana ta son gane wane?
Huci ya furzar yana kallonta a dan kausashe ya ce" Shi din ta ina ya zama Abanki?!"
Da dan sauri ta kalli fuskarsa, sai kuma ta sada kanta , ta sake dagowa zata yi magana ya daka mata tsawar da ta saka kanta mugun sarawa harma ta saki Tawul din da take rike da shi da hannayenta dan kar ya fadi, sai dai sarawar da kanta ya yi ita kanta bata san a lokacin da ta sake shi ba ta kai hannunta dan ta rufe idannuwanta da shi, hakanma ta ga kamar rufeta zai yi da duka, hakan ya sa ta karaso da sauri a haka din da take ta sake rukunkume shi da karfi ta saka kuka tana goga fuskarta a jikin rigarsa tana mai karra shigewa jikinsa
Watau abu ne da zai sameka da baya yi maka shawara, hakan ya sa gaba daya du irin karfi da irin yadda bawan Allahn nan ya iya rike jikinsa dan kare kansa fadawa ko menene sai gashi ya yi tangal tangal ya hade bayansa da jikin garu da karfin da ya saka shi sauke ajiyar zuciya yana sake zarro idannuwansa da zuba mata ido yana kallonta
Kukan da take yi shine abinda ya fi hargitsa dukkan wani kuzarinsa, da dukkan wani tunani nasa
A jikinta ko pant babu bale a kai ga maganar bra, ta gama tube dukan wani abinda zai iya tarewa ne zata shiga wanka ya shigo, kuma a halin da take ciki burinta a rarasheta ba a karra firgitata ba, sai gashi ya mata ihun nan da ta ji zata haukace gaba Daya
A hankali ya kai hannunsa bayanta dan ya cireta a jikinsa jama'a rasululahi sallalahu alaihi wa salam yarinyar nan da bata da hankali?, Ya salam, ya salam yaya zata halaka shi bayan babu laifin da ya yi mata? Meye haka? Menene wannan take yi bayan shi tambaya kawai ya mata dan ya ga ai dai idan iyayen nata ne gasu sun bayana menene kuma ya hadata yiwa wancen katon magana da shagwaba me dinta ne? Shine zata auka masa??????
Jama'a ku raba😂😂😂💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 4️⃣6️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
*Aunty ni so nake na yi kiba, nima na ringa juyi ina yada hannu😂, Uhum kanwata kennan ba zaki kasheni da dariya ba, a gaskiya ni dan radin kaina ba zan yi sha'awar na yi kiba ba, kin ga motsawa nake yi sosai dan na zube, domin ita kiba bata da wani dadi, idanma ta yi yawa shikenan ke da kanki kin kashe kanki ne, idan dan mai gidan ne zaki zame masa kaya ne, komai sai ya yi......., Idan dan kawayenki ne zaki dawo abar tausayi domin ko kaya ba zaki saka ki ji dadi yadda kike so ba, sai idan kibar nan ta zame maki dole watau kin yi kin yi aman ina kin yita, to irin wannan zan iya cewa dole ce, ki yi kokari kar ki zaune ki koyi motsawa da dukan karfinki ta yadda kibarki ba zata hanna ki komai ba,aman kin ga? Yin kibar nan ko ga lafiyarki bata da wani kyai, domin shekaru na dan karuwa kin bani kennan, Allah ya daidaita mana yannayin jikinmu....., Aman kuma idan muguwar ramar nan ce ki dan gwada wannan, in sha Allah zaki ga cenji a kwana bakwai ........ Madara ta ruwa ki zuba kopi daya, ki fasa kwai ki yi anfani da yelow din dake cikinsa ki saka cikin madarar ki dan juya sai sun hade jikinsu sai ki zuba cokali daya na zuma ki motsa, ki sha kofi daya kafin ki kwonta barci, daga kin farka ki sha kofi daya, sati daya ki gani idan baki yi jiki ba to gaskiya ki yi hakuri😂*
Hannunsa ya kai kusa da kafadarta da niyar cirota daga jikinsa, a hankali ya dora hannun nasa ya dan nemi janyeta daga jikin nasa, sai dai kamar cingan maimakun ta bambaru daga jikin nasa sai ta kara shigewa tana girgiza kanta da muryar kuka sannan shakakiyar murya ta ce" Abanah ne, ka ga tunda muka zo anguwarsu yake tsaye a kan rayuwarmu, yana mana nasiha sannan shine madaurin aurena, wani abin ne ya same shi shima??????"
Fahimtar da ya yi cewar ta fa shiga hali na kidima ne ya saka shi dan sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Ur nude"
Da rarume rarumen ta dan dakata, a hankali ta sake maimaita abinda ya fada a cen kasan zuciyarta
Da sauri ta rintse idannuwanta, gabanta ya fadi, tsoro da kunya da mamaki suka cikata, mene? Yana nufin ba komai a jikinta?
Sai a yanzu ta tuna tawul din da ta rike a hannayenta bata rigai ta daura shi a kirjin nata ba, kennan faduwa ya yi? Aman yaya aka yi bata ji sanyi na dukan jikinta ba? Shin ya salam, ya salam, sai kuma ta yi gagawar dago kanta daga jikinsa sukai ido hudu da idannuwansa da ta kasa tantance jan bacin ran da ta saba ganninsa da su ne ko na menene?
Da karfi ta dan saka ihu kadan ta cika gaban rigarsa da gudu ta yi bayi a haka din domin bata tunanin zata iya kuma daukan tawul din da ya fadi, kafin ta dauka gani take yi dukkan wani asirin jikinta ya idasa bayana kennan, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, yau itace tube zigidir a gaban namiji harma a jikinsa? Ai wayewarta bata kai cen ba, babu namijin da ya taba gannin jikinta haka a bude a bayane, babu shi
Da ido ya raka ukunta dake sama sunna kasa har ta bacewa ganninsa kafin ya maido dubansa a hankali a kan bed din Mama
A hankali ya iya daga kafarsa ya cirata ya koma bakin bed din ya zauna yana hadiye wani abu a wuyansa ya kawo hannunsa ya dafe gaban goshinsa a hankali ya furta" Mahaukaciya ce, ya salam bata da hankali yarinyar nan ko daya"
Gaba daya gannin al'amarinsa na sake hauhawa ya saka shi mikewa da dan hanzari ya fito yana rufo mata dakin sanan ya shiga bin falon da kallo dan sake tabatar da abinda ya gani a shigowarsa shin ana nan ko an fita? Dan idan ana nan ba zai barta da su ba, babu abinda ba zai iya faruwa ba duba da su sun dage a kan son gannin bayansa, ita