Showing 66001 words to 69000 words out of 226733 words
ina zubewa a kanka kai kuma kana amsa kana kuma tarairayata da zuciya daya, Aba ban ce bana sonsa dan na saka ka kuka ba, iya gaskiyata ce na fada, aman ka yi hakuri walahi zan je, zan tafi bana so ka yi kukan". Gaba daya rikicewar da ta yi ya sake saka masa farin ciki da godiya ga ubangijinsa
Walahi ba dan ya sakata ta amince da auren nan ya saka shi kuka ba, har zuciyarsa ya ji ba dadi da take son bijire masa a yau da ya yi bugun kirji ba tare da ya nemi shawararta ba ya daura mata auren nan, aman a yanzu da ta nuna cewar eh shima uba ne sai ya ji farin ciki da sanyi a cikin zuciyarsa
Yana godewa Allah har wani takama yake idan ta ce da shi ABAHNA din nan, shi dai ya san yana iya haihuwarta da cikinsa idan ya yi auren shekara ashirin da uku, dan ya amsa idan ta kireshi da Aba ai ba laifi ya aikata ba ba kuma abin kunya bane, SHUWWA y'arsa ce , yana farin ciki da haka, ba sai ya nakuda ya haifa ba zai ce ga d'ansa tunda Allah ya bashi mai yi masa biyaya ya rasa mikin dake damunsa na rashin d'a a duniya
A sanyaye yana murmushi ya furta" Allah ya yi miki albarka SHUWWA, Allah ya faranta maki yadda kika faranta min, Allah ya sa alkalamin kadararki daga yanzu ya tashi daga rayuwa mai gigitarwa ya mayar da ke rayuwa mai saka shauki da farin ciki da kwonciyar hankalin zuciya, ki gane sai ka zauna fa mutun kake iya gane wanenen shi, ni gani nake shi din zai so iyalinsa sosai , kingama abokiyar zamankima a cen babar kasa take zaune, a nan ke kadai ce kuma in sha Allah ba zaki samu bacin ran zama da su baki daya ba"
'kuturu, harda mata gareshi? Koda yake ai da ganninsa zai yi hali na mai maimaita Ubaiiii yana barbara da zarar ya ga mace, hm, zama da shi? Abah zan dai je na dawo ka sama min miji , zan tafi ne dan na ga ka fara kuka, aman zan dawo maka ne da shokiiiina na mika maka takardar sakina ka sama min miji, kai auren kansa sai na hakura da shi dan na kula gigitani yake yi, rayuwa ai yar sanyi ce sosai' wannan abubuwa shine Shuwwa ke ayanawa a cen kasan zuciyarta
"Shuwwa?" Ya fada a sanyaye yana kallonta dan ta afka tunanin da har bata ji salamar gwogonsu dake fada masa cewa yan daukan amarya ne suka karaso ba
A nutse ya ce" Ki ji tsoron Allah a zamanki da shi, ki yi masa biyaya da dukan karfin iyawarki, ki sani aljanarki ce zaki je nema Shuwwa sannan ki dauka zabinki ne shi din ba hadaki akai da makiyinki ba, zaki kwatanta haka?" Malan ya fada yana sake kallonta hakan ya sa ta sake jin zuciyarta ta karye sosai, ta kalle shi, ta juya ta kalli gogonsu ta kasa furta koda A ne
Gogonsu ta yi murmushi tana zama a kusa da ita sosai ta kamo hannunta na dama tana kallonta ta ce" IBTISAM, gashi na sanki a kuraran lokaci, duda ba mutuwa mukai ni ko ke ba aman zaman aure zama ne na tafia aa rayu da miji ba shirme ba, ki sani ni mamanki ce, Allah ya jikan mahaifiyarki ba zaki kuma yin kukan maraicin rashin uwa ba, kar cenjin da kika samu ya rude ki SHUWWA jinnin dake gudu a cikin jikinki ba na ja da baya a gaban gwagwarmaya bane ko wace iri ce, uwa uba babar kokowar duniya itace ta mace da mijinta, da yardar Allah furucinsa zai dawo bege a gareki, maza yiwa Abanki salama mu tafi ba'ai masu dare a wajensu duda matar uban gidansu za'a kawo ta yiwu mu ko karfe nawa muke son shiga ko fita muna iya yi kanmu tsaye" ta karashe da dan barkwonci bata kula da kallon kun shiga uku da Shuwwar din ke binta da shi ba
Wannan jawabi da gogonsu ya saka bata daukarwa Abanta alkawarin zama lafiya da abokin gaba ba, da wannan aka luluba mata abin rufa abinda ba'a taba yi mata ba, a yau kuma uwa uba rakiyarta harda NAHIDT wace sai da aka zo shiga dankareriyar ferarin da za'a kaita a ciki Malan ya sake jadada maganar cewa daga cen a sada NAHIDT da gidan Hamza bisa umarnin manyansu
Ita dai a yau bata da ja in ja da KOWA, kai bama zasu gane bane aminiyarta da kanwarta ta aurar fa? Ai yau ita shagali takeda a gabanta mai zafin gaske, a dai kai rigimatu kurjin gwuiwar nan a dawo a ga bidi'a ta arziki, yau Malan zai gane itace Nahidht (🥺 Hum)
Lafaya ce aka nada mata a saman wando da rigarta masu santsi farare kal , hakama lafayar fara ce kall
Sun tanaji kayan nan ne saboda irin wannan lokacin da sukai tunanin zasu sadata da dakin Hamza ne
A tanadin nasu harda makup suka so cencada mata sai dai a yanzu ta tsaya a kan kafafuwanta ta nuna cewar bata cikin yaren makup, su je kawai su sadata da dakinta kowa ya kama gabansa, a cikin zuciyarta kuwa kudirinta shine abinda sunna zuwa zata biyo bayansu? Shirme suke yi da batawa kansu lokaci
Matar tsohon ganaral, watau maman Hamza da gogonsu ne rike da ita a tsakiyarsu
A hankali bayan sojojin dake tsaitsaye sun bada damar ana iya fitowa da ita Matar tsohon ganaral kasa kasa sosai ta furta" Ki karra sada kanki My daughter ta yadda yarensa ba zasu ga fuskarki cikin sauki ba, domin matar uban gidansu kike, zasu ganki ne bayan ya ganki"
Jajayen lebunnanta ta dan dantse a hankali, domin tunda aka ringa ambatar masha Allah tap wannan tsaro haka? Gabanta ya farra faduwa, saima da aka ringa fadar to wai dama haka gidan baban yake kamar a turai? Ta ji zuciyarta na yi mata mugun bugu na zartacen ka'ida
Bindigogin dake hannayensu wa'inda suka ririke su biyar a laye a bakin hanyar shiga bayan sun gama yin jawabai na oyoyo da maraba da zuwa wa madame din oga ne suka daga sama suka harba wanda hakan ya saki gigitacen karan da ya firgita dukkan wani bakon al'amarin, ya saka shauki ga wa'inda suka san ana haka kuma sai mai matsayi ake yiwa hakan watau sai matan manyan ake tarba da hakan
Cikin wa'inda karar bindigar ya zowa a ba zata harda SHUWWA , hakan ya sa ta damki hannun gogonsu muryarta cen ciki ta furta" GoGo bindiga"
Tsinkayo muryar NAHIDT cikin murna tana fadin" Kai soja duniya ne, tarbar oyoyo da kukan abin kisa ake yi, mtssss tsakani da Allah soja zan tafi" ya sakata sauke nanauyar ajiyar zuciya tana sasautawa Gogonsu rikon kasa kasa ta sake fadin" Mahaukata, komai nasu a haukace ba irin na mutane ba, komai basu kya yinsa a nutse ba sai a gigice, cen ku da bindigarku!"
Ita dai goginsu yar daria abin ya bata domin rabin jikin Shuwwa din a jikinta yake dan ta dan rankwasa jikinta sakamakon jin da ta yi santsin wajen na son dagata da dogon takalminta ya maka kasa bayan bata ra'ayin hakan, bata gannin gabanta ga jaraba sun tanaji acokal dan su cocoka gaban Hamza, asge Hamza yayansu ne? Kai jamai
Dukan yan rakiyar amaryar da suka zo sanadiyar Tsohon ganaral da mutanen Matar Malan uwar gida da matar Malan din kanta a bayansu suke, a lokacin da suka ja suka tsaya sunna shirin shiga Nahidt a sanyaye kamar ba ita ba dan Shuwwa din ta ji maganarta ta ce" Gogonmu, dan Allah ku dan tsaya Shuwwana ta yi adu'a kafin ku sadata da cikin gidanta"
Dan matsawa ta yi kusa da Shuwwar din a nutse ta shiga furta" Shuwwan Mamah, shuwwan Abanta, Shuwwan yayarta? Dan Allah ki yi adu'ar neman alkhairin auren nan kin ji? Kin ga kamar da ran iyayenmu, kina gannin wata daraja da ta lulubeki kuwa ? Gaba daya sai na yarda mai daraja kika aura, dan Allah Ibtina ki yi adu'ar shiga cikin gidan nan da fatan zaman lafia da mijinki kin ji? Ba dan ni ba"
A hankali IBTISAM ta lumshe idannuwanta sannan ta bude ta shiga dan kokarin bude gaban furkarta dan ta kalli yar uwarta da muryarta kadai take ji
Tana budewa sukai ido hudu da junna ashema a gabanta take kadan sannan ta hade hannayenta waje daya tana kallonta
Tunda aka fara lamarin daurin auren nan sai yanzu murmushi ya subuce mata a saman fuskarta da ta ga irin abinda yayarta ke yi mata idan tana so tai mata biyaya
A hankali ta saki hannyensu ta damko na yayarta sannan ta dan matsa jikinta ta rungume ta a jikinta sosai
Muryarta cen ciki tana dan rawa rawa ta ce" Ban taba tunanin zaki iya barina a nan ba mamanah, Nahidt ke ce Mamanah kin va Abama haka ya miko ni"
Ajiyar zuciya Nahidt ta yi tana share mata fuskarta ta ce" Alkhairi muke fata mu dukanmu my baby, kin ga Abanki yana son ki, Allah ya saka masa sonki kamar y'ar da ya haifa, na tabata ba zai miko ki ya manta da lamuranki ba, nima kuma za'ina zuwa kulun kulun wajenki, now ki tayani mu yi adu'ar neman tsari da shedan, da dukan abin ki, adu'ar neman alkhairi a zamanki, koda na kwana daya ne ai kin san alkhairin kwana daya ya fi rashin alkhairin kwana daya kau?"
Kai ta gyada da kanta suka yi adu'arsu suka fara shiga sannan sauran suka bi bayansu
Iyakancesu matar Tsohon ganaral ta yi a fallo su su hudu kadai suka haura sama domin Fauziya tana gidab Malan itama a gau za'a mikata dakinta da sun koma
Ita da kanta Shuwwar sai da ta bude lulubin tana kallon dakin barcinta a lokacin da suma su matar ganaral ita din suke kallo sunna ayana eh lalle wannan kwarya ta samu abokin burminta, sai fatan wannan karron abin ya dore fiye da sauran da yake aura, domin sauranma fa ba baya bane wajen tsaruwa aman wannan din ta ce kau ku bani waje, Shuwwa tana da tsarin kyau da na halita
Kayanta suka ringa sanyo mata na jiki da na harkar turarukanta da su kayan gyaran jikinta akwatunnanta na wajen sauran mazan da suka rabu kaf NAHIDT ta kwaso mata hakan ya sa akwatunnan suke da yawa kuma kaf dinsu aka sanyo su aka yi masu waje ta yadda ba zasu cike komai a tankamemen wajen ba
NAHIDT ta ce" ki ga gida kamar a saudiya Shuwwa?"
Shuwwar ta yi dan murmushi tana fadin" ni bed dinma ne nake kallo ji shi fa kamar ba gadon yin barci ba "
Iyayen dai karra yi mata nasiha sukai suka sauka sunna fadawa Nahidt karfa ta jima kar su wuce ka'ida magariba na son sanyo kanta
Sunna fita Nahidt ta ringa taku tana zagayen wajen ta ce" Masha Allah, ina adu'ar ki samu farin ciki a wajen nan har karshen rayuwarki"
Shuwwar ta jingida da wata doguwar kujera tana kallonta ta ce" Ki yi min alkawari mana?"
NAHIDT ta juyi tana murmushi ta ce" Just fadi koma menene, in dai zaki yarda ki zauna a gidan nan kadara na maki na gama"
Murmushi Shuwwar ta yi tana kallonta ta ce" Ina so, ina matukar so, a kan haka zan iya zama koda a cikin rami kika mikani, domin yadda kike kokowa da samun farin cikina haka nake so a gobe kiyama ya zamto ga ni ga ki a kofar shiga aljannah, Nahi so nake ki yi min alkawarin kin ajiye zina gefe guda, dama ai kin ce dan ki samu kudi ki ciyar da ni da Fauziya kike yi ko? To a yanzu ga yayanmu na tabata sai dai ya kwana bai ci ba da ya barki da yunwa, dan Allah ki zauna a gidansa da aminiyarki kawarki, ki daina yawo "
Nahidt ta dan kureta da ido kafin ta cire tana dan kallon gefe, Shuwwa bata sani bane, ita da kanta zaman sati shidan nan da ta yi a gida ta ringa farin cikin yannayin jikonta dama nutsuwar zuciyarta, abu daya take gwagwarmaya da shi shine sabawa da ta yi da harkar maza wani lokacin sai ta ji kamar zata yi hauka tana bukatar namiji kota halin yaya, azumin da ta ringa yi da zarar ta sha ruwa sai kuma lafiya ta nemi lafiya ne, ita da kanta burinta shine a yanzu ta kilace kanta, ko itama zata yi dace da samun mijin ko wanene, takan kamu da Tsoron anya zata samu mijin da zai mutuntata bayan ita da kanta bata mutunta kanta ba? Ko a haka zata tsufa ne ko a haka zata koma ga ubangijinta ne? Aman idan ta kalli Fauziya sai ta samu jin sanyi a zuciyarta harma da tunanin kila itama watarana zata samu malamuncinta ko wani iri ne,
Dan murmushi ta yi da turaren da take sakawa bed din na ruwa mai farin haske irin wanda baya lalata zannin gado ta dage mata gira daya ta ce" Nd ni me zaki yi min alkawari bayan zama da zaki yi aa gidan nan?"
Shuwwa ta dan kankance idannuwanta tana kallonta da son karrin bayani
Nahidt ta ci gaba da zuba turaran tana fadin" Ke ce malamata a wannan fannin, gigitar son ki yi aure ya saka kika watsar, Shuwwa kin san waye wannan mutumen? Wannan mutumen da kike ganni shine mutumen da ya ba aikinsa mahinmanci ta yadda yake iya mance cikinsa saboda aiki, aure aurene da shi domin inaga kece ta tara a gidansa, ya kasance sakin mace abu ne mai sauki a wajensa , Shuwwa zan bar neman duniya ta hanyar haram idan kika dauki mutumen nan kika ajiye shi a gabanki kika mayar da shi DEFI dinki!, Shuwwa takamarsa kudi, mulki, kyau, ke kuma takamarki ramin da kike da shi a jikinki da sansanyar murya kasa da tashi, kowace mace nada su aman ba kowace ta gane cewar bindiga ce a tare da ita ba, kowani namiji ko waye shi yana da takama aman yana sada kansa ya kwasa dan samun nutsuwarsa banda mata maza, Shuwwa shin zaki yi gwagwarmaya ta yadda ba zai sakeki da wuri ba koda kuwa yana cikin layin wa'inda zasu sake ki? Ki duba ki gani a bayane ya san wa ya aura, iyayensa ne sukA gani suka aura masa, a yanzu kina gaban rigimarki ne kiri kiri, shin zaki yi yadda ya dace da shi?
Shuwwar dake kallonta, a kasan zuciyarta tana daukan na dauka tana fasara na yarwa
Dan murmushi ta yi tana kallonta ta ce" Ban zo da niyar zama da shi ba, aman sai na ji ina ra'ayin gannin shin soja yana da zuciyar iya son mutun? Nima bana sonsa aman sai na ji so na ga idan shi ya kamu da son mace yaya yake?, Nahi zan kwatanta iya abinda na iya a zamantakewa da ta shi, Idan ya so sai ya bani takardata, domin ko ana ha maza ha mata ni ban ga gidan zama ba, kyansa bai rudeni ba, kudinsa bai makantani ba, mulkin da yake da shi a hannunsa kuwa na fi gane na dan kasuwa wanda yake sarkin kansa ba na mai zamani ba, watarana ba shi bane!"
Hamdallah Nahidht ta yi tana ajiyewa ta karaso ta rungumeta irin rungumar da larabawa ke yiwa junna sannan sukai salama bayan ta bara mata wayarta da kati lode a ciki ta sauko da dan gudu gudu ta tarda su domin tuni sunna cikin mota ta bar Shuwwar a tsaye a sama tana hangen fitarsu har suka fice gaba dayansu a falon kasan
A hankali ta fara jin tsoron girman wajen na shiga jikinta harma ta fara jin kamar tsigar jikinta na tashi
Daga inda take tsaye ta fara jin tsoron daga kafarta dan zuwa ko nan da nan ne
Agogon hannunta ta kalla a hankali tana gannin lokacin kiran sallar magariba ya yi hakan ya sa a kasan zuciyarta ta shiga zikiri tanaa hailala dan ta korar da tsoron dake taso mata
A firgice ta juya jin an bude kofar dakin da duk a tunaninta nata ne domin ita da za'a shiga bata lura da wata kofar ba batama san dakunna nawa bane a saman bale har ta iya tantance wani abin, haka kuma duba da a jikin junna suke kunnenta dakin bayanta ya bata aka bude shi ya sa ta juyo a firgice dan gannin abinda zai fito daga ciki
Ido hudu sukai da shi da jalabiya fara kal a jikinsa yana dan sharce ruwan dake nunin alwalah ya yi hannunsa na dama kuwa rike da carbi mai ruwan zeba sai walwali yake mai shegen kyau
Shi, bai cire idannuwansa a kanta ba, domin a shigarsa ciki barci ya samu ya yi wanda sai zuwa dazu ne ya farka, harbawar bindigarsu ta sanar masa abinda yake faruwa ya koma ya ci gaba da barcinsa dan ba huruminsa bane, sai yanzu da ya fito ya ga mutun a tsaye da gangan ya janyo kofar da dan karfi dan ya shaida mata da mutun dan ya ga ko waye hakan ya sa ta juyo da sauri tana kallonsa
Daga sada kan nan nata ta samu ta dago ta juya ta mayar da hannayenta jikin karfen harda dan dora kafa daya ta ci gaba da kallon falon tana jin gaba dayama Tsoron ya fice mata a zuciyarta a kasam zuciyar tata kuwa tana ayana' Au ashe kaine har na furgita? Nama zata wani abin tsoro ne'
Da dan mamaki ya bi bayanta da kallo
Mamakin da ya saka shi binta da kallo ba komai bane sai na shareshi da ta yi da nuni kamar bata gane waye shi ba a rayuwarta
Ku gane, ba wai son ta damu da shi ko ta kula shi yake yi ba, ko daya, abinda ya tsinta bamban da matayensa ne ya dan saka shi hali na mamaki, domin shi dai zai iya cewa kama daga mahaifiyarsa, Abansa, yayan gidansu, matan da yake aure, yarensa na wajen aiki ko a cikin gari da zarar ya zo waje akan bashi daraja ne wata kala daban, kowane da irin rawar jikin da yake dan yi masa sannu idan ya zo waje, zai iya cewa bai taba wanzuwa a waje aka juya masa baya aka wancakalar da wanzuwar