Showing 90001 words to 93000 words out of 226733 words

Chapter 31 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

7947

zama saman kujera hakan ya sa Nahidht ta damko hannunta tana fadin" ke dadina da ke wawuya ce ke, miji zaki ce zaki ki zuwa bayan ya yi kiranki? Ai zuwa ake komai ta fanjama fanjam,"

Shuwwar ta ce" Nahidt ki dakata, ki fa ankare da lamarin mutumen nan fa, ki fa kiyaye fa Nahidt du inda kike tunani ya zarce nan fa"

Nahidt ta dan juyo tana kallonta ta ce" To ko dai tsoronsa kike ji ne?"

Da sauri ta girgiza kanta tana fadin" Allah kiyaye na ji tsoronsa kawai bana son wulakanci irin na sojoji ne!"

Nahidt ta ki ta tsaya ta jata suka fice gaba dayansu suka nufo falon tana ayana' Shuwwa baki da mutunci, tunda aka kamo mu aka watsomu nan kika tsani soja, bayan ba sojaa bane ya kamo mu kin hade dukan mai iko kin masa fenti, dan an kamo ki baki ga kabarin su Mama ba? Sun rasu Shuwwa ya dace ki yi hakuri'

Kasancewar a zaune yake ya ba bangaren dakin na Nahidt baya hakan ya sa bai ga fitowarsu ba, domin keyarsa ke kallonsu sai bakon dake zaune ne sukai ido hudu da junna

Ido SHUWWAR ta zarro kasa kasa ta ce" Hamza?"

Nahidt ta ce" Kai, to me ya zo yi? Yaya aka yi aka barshi shigowa warhaka?"

Shuwwa ta ce" Na fada maki tarko ne zai ci ubanmu ne a gaban yayanmu"

Nahidt ta dan sakarwa hamza murmushin yake itama kasa kasa sosai ta ce"Na ce me kikai masa kin ce ke ba komai ba, to mu je mu gani yadda Allah ya yi da mu"

Hamza ya yi dan murmushi yana kallonsu a sanyaye ya ce" Ku karaso mana"

Sake kallon junna suka yi sannan suka shiga karasowar kowace na saka abinda take sakawa a cen kasan zuciyarta

Zama sukai suka saka shi a tsakiya har ya zamto kafafuwansa na gogar nasu domin a saman kujera daya ne suka zauna gaba dayansu

Gaishe da MUHYIDEEN Nahidt ta fara yi sannan ta juya itama wajen Hamza tana gaishe shi kamar yadda Shuwwa ke gaishe shi bataiwa MUHAY magana ba

Dan murmushi ya yi a sanyaye bai amsa gaisuwar tasu ba sai ya shiga tambayarsu da damuwar dake saman fuskarsa ya ce" Shin baku yi farin cikin samuna a matsayin yayanku da muka fito ciki daya bane ko ba zaku yi zumunci da shege bane?"

Da dan karfi Nahidt ta ce" Muhamadu rasululahi sallalahu alaihi wa salam mun shiga uku"


SHUWWAR ta kalle shi a sanyaye ta ce" AA Hamza me yasa zaka ce haka dan Allah, wata irin magana ce zaka ke fadi kai tsaye a gaban kowama dan Allah, me yasa kake son neman wulakantar da mu baki daya ne Hamza ?"

Hamsa ya yi dan murmushi yana kallonta ya ce" Na fa kula da ku fa Shuwwa, asalima irin farin cikin da na yi jin nima ashe ina da kanai ashe soyayar da na ji farat daya inai maku dan ku din jinina ne ku du ban ganta a saman fuskokinku ba, Sannan tunda muka tafi gida da NAHIDT gatanan bata da sakewa da ni irin na da, a da takan zauna mu yi ta hira muna ta shan ihunmu da dariyarmu aman a yanzu ban san me yasa du ta cenza ta fi kaunar zama a daki, karshema ta yi tafiyarta ta bar mana gidan wanda hakan ba iya ni ba, Fauziya kanta sai kuka take yi na hakan ta damu ta kuma shiga cikin tsoron dalilin da ya sa kuka aikata haka?, Dan Allah bakwa jin dadi da farin cikin samun dan uwa a kusa da ku kin ga fa ko sunnana gatsal kuke kamawa dan Allah bakwa sona ne ku?"

MUHYIDEEN Bakinsa ya tabe yana zaunen dai yana sauraronsu aman kuma ba kallonsu yake yi ba

Wayar da Dad dinsa ya kiresa a kanta ya shaida masa yayan matarsa na waje dan Allah a sanyo shi hankalinsa ne ya tashi bai ga Nahidt ba yana son ganninta a kan dole ya sauko ya bada dama aka sanyo shi ce ta dauki tsuwa hakan ya sa suka kai dubansu gaba dayansu kan wayar ciki harda shi,

Hannunsa ya saka ya dauka ya daga kiran yana karawa a kunnensa hakan ya ba SHUWWA damar rage sautin muryarta sosai tana ruruko idannuwanta domin so take su dauki maganarta da mahinmanci kasa kasa sosai ta ce" Yayanmu, kar ka yi maganar ahalinmu a gaban bako mana, gaba daya fa ba abinda kake tunani bane ba, ita dama tana son zuwa wajena shine ta zo"

Hamzan shima ya rage muryarsa sosai ya ce" Mijin naki ne bakon?, Kuma tana son zuwa ba zata bari mu shirya mu zo tare ba shine zata zo gidanki da kayanta na sakawa? Ni fa aikin me nake yi ne da ba zan rike kanwata daya kwal ta gabana ba?"

NAHIDT ta ce" Du fa ba inda ka nufa ba na nufa big brother, kai ka san muna cikin farin cikin gannin ashe muna da kai a duniya bayan mun fitar da ran cewa muna da wasu a duniya harma muka ga danginmu, abin ne ya zo mana a baibai shi yasa muke ta shawarar yadda zamu dauke shi idan ka yi la'akari da mun taso ne mu mu biyu,, daga baya muka hadu da Fauziya sai baban Shuwwa shikenan ne, ka ga dole komai zai zo mana a baibai"

SHUWWA ta dan dago daga kallon Hamza da take ta sauke a kan fuskar MUHYIDEEN a kasan zuciyarta tana cike da mamakinsu da zasu saki baki sunna son tona asirinsu a gaban wannan mutumen mai yannayi irin na wulakanci salon gobe ya wulakantasu a banza a wofi
Idannuwansu da suka sarke da junna ne ya sakata sake kallon fuskarsa sakamakon abu biyu
Na farko fahimtar da ta yi magana ne yake yi a wayar ashe? Sai na biyu ankara da ta yi kamar ya harareta

Idannuwansa ya cire a cikin nata ya maida gefe yana sauraron maganarsu da Father dinsa ya sake maidowa ba wai dan wani abu ba sai dan ya fahimci yarinyar nan da irin nata salon haukan

Idan ba idannuwansa ne ke masa gizo ba kamar ita dayama harare take yi, sai ya samu kansa da ayana' ta yiwu aljannun nata ke sakata abubuwa, may be na dazuma da ta yi aljannun nata suka sakata, ga aljannu gaa hali sun hadu? Gaskiya ne Dad ya iya hadi'

"Kana jina kuwa?" CHIEF OF ARMY ya fada bayan ya dire maganarsa a kan korafin da Mahaifiyarsa ta kawo kan bata san me yake faruwa da zumuncinsa da yar uwarta ta jinni ba

Dan muzgutawa ya yi ya mike ya nufi hanyar ficewa kafin ya tsaya a nutse ya ce" Father, bana so ne abinda yake bayanane a gareni ya bayana a wajen Mamanah, ina ta kaucewa bacin ran Mamanah a kan haka, dan Allah ta yi hakuri ta daina min maganar nan"

Gaban CHIEF OF ARMY ne ya ringa faduwa har ya so ya nuna a gaban matarsa dake jira ya gama ta ji yaya suka yi da yaron nata

Dan kauda kansa ya yi yana mikewa ya nufi ciki, lokaci daya kuma ya juyo yana kallonta da hannunsa ya nuna mata ta dakata sannan ya shige ciki
A nutse ya ce" Ka gane, ba wai yaren da ka bani a rufe bane damuwata a yanzun, zan iya ce maka gaba daya tunanina ne ya daukeni ya maka ni wani wajen daban, wanda idan har haka to fa lalle duniya zata bani tsoron da bata taba bani ba, domin ba zan yi uzuri ko na dubi dalili komai girmansa ba, dan kuwa abinda ake neman nuna bashi da mahinmanci harma ake son nuna saboda wani dalili na nan gidan duniya ne aka aikata haka na iyaa hanna kaina dauka, Son kunnayena na son jin ka ce min lallaalalalla ba abinda nake tunani bane ke damun matsalar da Mahaifiyarka ke fama da ita ka ji?" ...................bayannuear shirun MUHYIDEEN ya saka CHIEF OF ARMY bakinsa na rawa ya ce" Talk to me plz, tall me tunani ne da shedan ke sakawa mutun a rai"

Idannuwansa ya sake lumshewa kansa na sara masa,

CHIEF OF ARMY ya kai zaune yana fifita da hannunsa lokaci daya kansa ya fara cazuwa da ciwo wanda ke sukarsa har cikin idannuwansa
A birkice ya ce" Menene gaskiyar MUHAY ?"

Kirjinsa ne ya shiga bugawa d karfin gaske wanda hakan ya saka shi rintse idannuwansa muryarsa a cen ciki ya ce" I'm sorry Father "

Yannayin muryarsa ya sake saka zuciyar CHIEF OF ARMY a cikin zulumin da Tsoron jin abinda zai iya fitowa
Watau abin ya yi masa munin da bai san ta inda zai kama ba
Shin a cikin aikin shedan din wanene ya yiwa zuciyarsa galaba da mugun karfin da baki ba zai iya furta halin da zuciya ke ciki ba

A sanyaye ya ce" Ina so ka zo karshen watan nan, ba zan karbi uzurin komai ba, ina so ka zo ka fada min dukan abinda yake faruwa dan na san ta hanyar da zan bi na sanar da mamanka, domin a duniya bana son abinda zai cenza farin cikinta da walwalarta da sukuninta wa zuwa bacin rai, kai ka san wacece ita, idan kana neman sanyi, farin ciki, annuri ka zo kan mahaifiyarka ka ja ka tsaya, ina so na san shin abinda nake tunanin nan menene dalilinsa? Kudi ne ko kishin mu'amala ne na yau da gobe wanda yake samuwa ta hanyar rufewar ido ruf?, Ya Allah"

Shima ajiyar zuciyar yake saukewa a sanyaye ya ce" In sha Allah Dad"

Da kyar ya iya cicibawa ya nufi falon
Yana fitowa sukai kicibus tana tsaye sai kallon kofar take

Dan murmushi ya sakar mata cike da tausayinta, duka duka zamantakewarsu da ita da shi bata dauki lokaci mai tsayi ba domin rasuwar aminin nasa kanta bataa fi shekaru goma sha biyu ba, bayan rasuwarsa kuwa ta shekara uku kafin ta yarda ya aureta, aman halayanta da sanyinta da biyayarta ya saka zai iya rantsewa bai taba zama da mace ya masa dadin da yake ji da ita ba a dukan rayuwar da ya yi da mata a rayuwarsa, sai dai kuma abu daya da ya sani bayanane shine a kan yaronta takan rikice wani lokacin, har sai ya goronta mata sai kuma kunya ta sakata fara biyayoniya da shi


Kai ta sada tana murza hannayenta , har kunnenta suka ji mata yana fadin " Ga mamanka nan Son"

Duda ta kula kamar jikinsa ya yi sanyi a kan kafin ya shige ciki da eayar, sai bata saka komai a ranta ba ta ajiye hakan a matsayin yannayi na dan Adam ta amshi wayar ta dan koma falon a nutse ta shiga amsa gaisuwarsa kafin ta dan saurara tana jin muryoyin su NAHIDT ta ce" Baki ba kuka yi?"

Sai a lokacin ya sake juyawa ya ga gardama cw ta kacame Hamza ya ce sai dai Nahidht ta bi shi ita kuma tana kokarin son nuna masa ita bata jin dadin yannayin shirunsu

Dann ajiyar zuciya ta sauke a rarabe ya ce" Eh inaga wai ko yayanta ne yake neman yayarta"

Gaba daya mama bata fahimci inda yarensa ya nufa ba, amayb ta san ita din da ya fada yana nufin matarsa hakan ya sa ta ce" Bani ita mana mu gaisa?"

Dan tsai ya sake yi yana dubansu gaba dayansu ya ce" Ku gaisa kuma?"

Mama ta dake tana amsawa da eh

Dan shiru ne ya sake biyo baya kamar wanda yake karantar sunnayensu a jikinsu gaba dayansu daidai lokacin da NAHIDT ta ce ita sai dai idan gidanta zai kaita, SHUWWA ta dubeta a tsanake tana fadin" Walahi ba zaki koma gidan nan ke kadai ki rayu ba, da muna tare da kema yaya muka kare da mutanen anguwar nan bale ke kadai? Wai ba zaki saurara bayanina na dazu ba? Yaya ka ga kawai ka barmin ita a nan ni na riketa idan ya salameni sai mu koma gidanka tare ka ga ita fa ba zata iya zaman gidan naka ba wai bakwa surutu , ka san dama Fauziya fa ba cika surutu ta yi ba, ta fi gane murmushi , dama idan ina nan ne muke wuni muna yi , plz ka fahimta"

Mama dake sauraro ta yi tsitttt tana jin muryar yarinyar da yannayi na sanyi aman kamar a dan harzuke take, sannan tana kalkaltu a furucinta duda hausa take yi aman hakan zai saka ka gane cewar akoy wani yare mai kakaltu a harshenta ta ce" Muhay, balabiya ce?"

MUHAY ya sake yin zuru yana sauraron mamansa da wata tambaya kuma har sai da ta sake maimaitawa kamar wace ke nuna sannin wannan gyadi gyadin nada mahinmanci a rayuwarta

A hankali ya ce" Ban sani ba nima"

Mama ta waigo Wajen CHIEF OF ARMY da ya afka a damuwa ta tunani tana fadin" Abansa wai ka ji wani bakon rashin kirki a wajen yaron nan? Fisabililahi wai bai san wani yare bace matarsa?"

Muhay ya sauke ajiyar zuciya yana so ya ce da ita zai sake kira idan ya hau sama ya ji Abansa na bada takaitacen tarihin yarinyar cen, hakan ya saka shi dan yin gyaran murya da niyar yi masu salama ya sake ji ta maimaita kalmar ya ba Shuwwa waya hakan ya saka shi yin tsai kasa kasa sosai ya ce" Mama na fa fada maki bata da lafia fa"

Mama ta ce" Subahannalah, Son zazabi ke damunta ne ko mene"

A kasan zuciyarsa ya shiga maiamaita' Kai zazabi kuma? Mama me na maki ne da daren nan?'

A bayane kuwa sai ya daka fuska ya karasa wajen da suke zaune wanda yana dawowa sukai tsittt kamar wasu munafukai da zancen da suke yi su dukansu bayan ya ji a kan fadan da suka afka dan sun kwatanta su basa so ta koma cen ita daya ne dan kar ta samu kanta wa aikata tuban muzuru

Wayar kawai ya mika mata , ita kuma ta amsa tana kallonsa ta ce" Na kai maka daki ne?"

Da mamaki ya juyo yana kallonta, ta kai masa me daki? Kamar wani wanda suke da wani mu'amala da junna?

"Ke SHUWWA kira ne fa" Hamza ya fada yana nuna mataa alamun dake nuni da kira ne hakan ya sa ta duba da sauri bayan ta danna

*FATHER* Din da ta gani ya sakata zaro ido da sauri ta dora wayar a kan cinyar Nahidht tana fadin" Babansa ne"

NAHIDTma ta zarro ido tana dagawa ta karra mata a kunnenta tana mata nuni da ta yi magana tana taa zarro mata idannuwa dan ta yi maganar aman ta kasa gaba dayama sai ta gaza motsin kirki ga waya a kunnenta

A nutse mama ta furta maganarta kamar Haka" ASALAMU ALAIKUM WARAHAMATULAH WA BARAKATUHU"

Ido SHUWWA taa lumshe sanadiyar jin wataa lalausar murya na nema mata amincin ubangijinta

A sanyaye ta budi bakinta ta ce"💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥


*The Hero writer*


*SAJIDA*


_Bismillahir rahamanir rahim_


PAGE:. 3️⃣0️⃣



*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*






*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*


*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*



*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*



*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*


*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618


Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰



A sanyaye ta budi bakinta ta ce" Amen wa alaikumus salaam warahamatulah wa barakatuhu........"

Sai kuma ta samu kanta da sake sada kanta a hankali taa furta" Barka da safiya "

Kasa kasa Nahidt ta ce" Ke wuni ne"

Muryarta ta shiga dan rawa ta samu kanta da fadin" Wuni, wuni ne, Barka da wuni"

Mama ta ringa sakin murmushi a nutse ta ce" Barka da warhaka y'ata, fatan kina cikin koshin lafia, yaya bakunta?"

SHUWWA ta samu kanta da jin nauyin matar da kuma son ta yi mata biyaya, ji take kamar muryar matar ne ke sakata yin biyaya koda bata shiryawa hakan ba

A sanyaye tamkar ba ita ba ta budi bakinta muryarta kasa kasa sosai bayan zakinta ta karra mata biyaya wanda koda mutun ya ki fadin ne ba zai ce muryar nan bata saja masa jin wani iri har cikin zuciyarsa ba, da dan inda inda ta furta" Alhamdulilah"

Daga tsayen da yake a kansu yana kallon gefe ya samu kansa da juyowa yana kallonta, ba dan wani abu ba sai dan ya gaskata kunnayensa da tunanin ko yayar tata ce ta amshi wayar ne ta yi magana a hankali irin na masu hankali? Domin shi dai tunfa ya santa da biyaya ya santa, kanwar ce bata da hankali

Da fara'a Mama ta ce" Masha Allah, Allah ya miki albarka, in sha Allah sai kin zo kin ji? Ina nan ina jiranki da izinin Ubangiji"

SHUWWA ta dan kalli fuskar Nahidt dake rike mata da wayar a hankali ta ce" To Mama, a gaida Aba da mutanen gidan in sha Allah"

Mama kam da farin cikinta ta ce" Amen zasu ji yarinyata, na gode sai an jima"

Kai ta gyada ta kasa fadin wata maganar har wayar ta bada hasken dake nuna ta mutu

Tana kula da kiran ya mutu ta dora mata wayar a saman cinyarta

Hamza da ya mike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login