Showing 222001 words to 225000 words out of 226733 words
kantama da ta yi sallar la'asar, to shinefa tana zuwa ta ga gidan kamar ana wata sallah kowa bishasha yake ga dukkan alamu yankama aka yi aka shiga aikin naman sadaka sai ta daga kafa da sauri ta karasa bangaren mijinta dan ta tabata a cen zata iske abinda ya dace ta gani
Ido ido sukai da mutanen falon har ta sauke a kan lalausar fuskar mijinta wace a yau annurinta ba boyaye bane ga kuma wani abin kafar karuru ce a saman cinyarsa yana massaging a hankali a hankali
Myrmushinsa ne ya daukaka ya bi kafar tata da kallo da ta janye sakamakon shigowar Furerar domin ko a gaban Hajia bata yarda haka ya faru ba dan zucoya ita bata da kashi, ita kuma ta yiwa kanta alkawari ne yarinyar nan ba zata yi abinda za'a ce eh lalle Nahidht baki kyauta ba a kanta, ta fi so ta yi gigin sake shiga huruminta da kangin kanta ta yadda zata zartar da abinda ta yi niya a kanta da dalili aman ba haka ba kai tsaye
Murmushin dake kan fuskarsa bai gushe ba, haka kuma bai damu da rashin gaishe da mutanen da bata yi ba domin ta yi salama sai dai ta kasa gaida kowa tana dai bin mutane da kallo bayan ta cire nikaf dinta ga karnin ranar da take na wuni a gari tunda bata riga ta yi wanka ba ya ce" sannu da dawowa Furerah........"
Dan murmushin yake ta yi sai kuma ta ce" Barka da yamaci Yah Ustaz....., Shin me yake faruwa a nan ne?"
Carab ya shaida mata abinda yake faruwar, dan shi ai ya dauka Furera da Hajia daya suke kuma zasu iya nuna soyayarsu wa soyayarsa, sai dai kashhhhhhh, hannunta na rawa ta ce" Yah ustaz, kana nufin yarinyar da ka auro jiya, wannan dandin itace ke dauke da cikinka? To wayema ya fada makaa cewar tana da ciki? Me kuma ya tabatar maka naka ne????"
To fa, tunda ta shigo har ga Allah MUHAY kallo daya ya mata ya juyar da kansa wajen wayar dake hannunsa ya danna ya shiga domin shi baya son rashin kunya, fetsarare kuwa kallo daya yake masa ya gane shi, sai yanzu da ta dire maganarta ya sake dagowa ya shiga dumbin yan mamakin jim furucinta
A hankali Malan da maganar ta dake shi yana sake kallonta ya ce" Fure? ......."
Shuwwa ta dantse hakorinta bayan ta ce" Hurera take!"
Malan ya sake fadin" Ki je bangarenki"
Furera duda ta ga yannayinsa haka ta kasa hakura da wutar da ta fara ruruwa a kirjinta a wani haukacen ta bude baki ta kurma ihu tana dora hannayenta duka biyu saman kanta tana fadin" Malan, dama rike cikin ka yi sai a fara zaka ba ba ni ba? Malan dama kana iya yiwa mace cikin ni ka ko bani malan me na tsare maka da ka ba karuwa ciki ni ka hannnnnnnnnnnnjnjj........." Sai kuma luuuuuuuuuu ta tafi ta daku a kasa gaba dayanta alamu na summa suka bayana a tatare da ita
Malan ya lumahe idannuwansa yana girgiza kansa yana kuma jimke hannayensa yana ta ambaton sunnayen Allah da son daidaita fushinsa kafin ya kai gareta
Muhyideen ya sauke murmushi ya dauki ruwan kankarar dake gefensa ya karasa ya maka mata shi yana tsaye a kanta ta farka a gigice da wani ihun ta kuma dora da haukan magangannun mararsa dadin ji har sai da abin ya kai masa makura ya tafka mata wani uban ihun fa ya saka ta zarro ido ta ja baya da sauri tana hade hannayenta a kirjinta tana kallonsa jikinta na bari
A kausashe ya ce" Baki ji Muhamad ya ce ki je bamgarenki ba ko sai an kaiki ne?"
Ido ta ringa kikiftawa tana kallonsa tana kuma kallon Malan da jiran ya yi magana mana waye wannan ya bari ya shiga fadansu na cikin giida? Gannin bai yi niyar yin magana ba ta juya ta fice a dakin da sauri tana mai ci gana da hanna kanta tube komai na jikinta ta fice a gidan tana kurma ihun da kukan nata
MUHAY ya juyo yana fadin" Kaima ba kowa ba ake fadawa irin maganar nan mana, wani fa makiyinka ne baka sani ba"
Malan ya dago kansa yana fadin" MUHYIDEEN Furera ce fa, Furera iyalina? Yau Furera ce ta min min wannan abin? Ashe rashin hankalin nata ya kai haka? Ni walahi ji nake kamar na saketa na huta da shirme irin nata, ina dalili mace ba hankali ko daya? Ka ga har kiranta ta yi da mugun sunnan nan bayan na yi alkawarin du wanda ya kuma kiranta da shi sai na zane shi in dai na fi karfinsa?"
MUHAY ya sake tabe baki yana cewa" Gaskiya gwara kawai ka saketa, kai ni walahi na yi mamaki ko dai auren dole aka yi maka da ita ne? Ina dalili wannan fa ba zaka iya dukanta ba gaskiya tana iya nanaka da kasa baka ganninta ne wai? Yayama kake iya juya abar nan ne? Kai sbahanalahi gwara na auri kamar gajiyarka sau dari da wannan matar, kana gani fa gaba daya ba laushi ba lausasawa, ai da gangan na daga muryata dan na bambance da ihuna da nata wanne ya fi karfi? Wannan ta kwarara maku shi tsakiyar dare ai sai ku zata farmaki aka kawo ko yan fashi ne, inaga ka saketa ka auro wata ya fi alkhairi kawai"
NAHIDt ta yi saurin fadin" Haba yaya MUHAY, Haba abana kai kuwa ya saketa ya kawo wata fa kake cewa, ai ya yi hakuri ya sanyayar da zuciyarsa ya yi adu'ar Allah ya dora shi a kan daidai in sakin nata ne daidai to Allah da kansa zai karrar da zaman ba tare da ya kawo wata ba , idan kuwa ba shi bane Allah ya shiryeta, aman ba ruwansa da fadanmu gaskiya, kai ni nama yafe mata kawai a bar maganar ai dama ba kowa zata birge ba, aman ba sai an kai da su duka bama, duda na yarda da sadaukina ba ita ba ko gaba da ita yana iya horarwa ta kuwa yi la'asar ta yi sanyi walahi, aman bana so ni ma yafe na kuma yafe a bar maganar dan Allah"
Ido da hanci suka zuba mata daga Shuwwa dake jira ace a je a zaneta har mijinta
MUHAY ya juya wajen da nikaf din Shuwwa yake ya dauko yana miko mata da safar hannayenta yana fadin" Dan maimaida kayan nan mu tafi gida kin ji? Inaga Nahidt ta zama munafuka, wai mu zata nunawa zagaye? Ke din? Idan kin tashi yin kokowar dai da ita ki kula fa cikin nan dan idan ta nausa maki hannunta ya bare zan rufe ku ne a matsayin kun yi kisa, yan wulakanci kawai"
Shuwwa din kanta sakawa ta yi cike da mamakin kisar antyn tata, haka dai suka yi tafiyarsu da fada suka barta ta sake rike abinta tana rarashi da nuna masa dole zai ga irin haka, kawai ya kyale maganar cikin a yi fatan Allah raya itama Allah ya bata nata
Shi kam a gaskiya ya zama wajibi ya kaurace mata, ba dan komai ba sai dan kankin kanta, idan ta mike a haka zata fara halaka kanta ne a banza da wofi, gwara ta gane ta yi hankali
..............................................................
*A gurguje*ALKALAMIN KADDARATA
PAGE 7️⃣9️⃣
NA
SAJEEDA
END🤧
Cikin gata da kulawa suke
rainon cikinsu abun gwanin sha'awa, duka mazan lallab'a mtan suke dan wani abun idan suka nemi kirtashi dole suke nuna musu sunyi saranda ba dan komai ba sai dan cikunan jikinsu, kowace da na ta kalar laulayin, Shuwwa dai ba mai tsamari bane sai dai kawai canzawae yanayi na kana tare da d'an mutum a jikinka, inda Nahidt kuma har yau baccinta take sha hankali kwance, wanda hakan ba k'aramin shiga hakk'in malam yake ba indai kwananta ne, sai dai ya ya iya? Da ta fara fad'a masa baccin ma ba za'a barta tayi ba dole yake komawa daddab'ata har ta koma baccin, ya d'auki son duniya ya d'orawa cikin nan, fatanshi a yanzu d'aya ne ya ga me za ta haifa, mace ko namiji? Ya ji kukan jariri shima a kunnensa a hannunsa sannan ya ga yan halbe halben hannaye a hannunsa, yana matukar so ya ga budewar ido da Kuma kallon da za'ai masa a hannunsa, yakan ji tsigar jikinsa na tashi idan ya ga tana tube rigarta a gabansa, ba dan komai ba sai dan gannin da gaske jikinta ya fara tasawa ta yadda dole a gane shafafen cikin nan na dauke da dan mutun, domin tun yanzu cikin nata turawa yake yi sosai wanda hakan ya sa yake kan yi mata adu'a ba dare ba rana da fatan Allah ya bata ikon jure dawainiyar cikin da ita da kanwarta wace suke haduwar sati sati ko a gidan Malan din ko kuma a gidan Shuwwa din, ko a je gidan Mama wace ta ja masu kashedon su rage zuwar mata gida kar su jaza mata maganar mutane ace ta aurar da yaren aman kulun sunna gindinta ita kam su yi zamansu a inda suke
Shuwwa kam takan zuba tabararta idan ta rayo mata, tun dan zazabin farko farko da ta yin nan shikenan ya bi lafiyar jikinta sai dan karan kwadayi na cin salak wanda ya saka MUHAY koyar wanke salak, domin kadan daga aikinta a talatainin dare ta dan lalubeshi tace cikin nan du ya sakani aiki irin na yan giya, ka ga wai salak........., Sai ya koyi ajiye kayan wankesu a kusa idan ta bukata sai ya fitar da shi a frij domin idan aka saka salak a frij wajen da baya kankara sai ya shafe sati biyu bai yi komai ba, yana wankewa tana darwayewa tana yankawa a gefe ta more sannan ya mori lamari domin bata rowar kam ita, Nahidt ce ta harbu da harbi irin na rowa , mamansa kuwa ta mayar da zuwa abinda ya fi komai sauki a wajenta, dan ta nuna a yanzun a bar Shuwwa da maganar balaguro ita kam bata so, a barta ta reni cikin nan cikin nutsuwar da zata haife shi lafiya ba tare da an shiga wata damuwar ba, duda sun san basu isa su hanna komai ba, aman sunna kamanta kiyayewa
A bangaren Sultanma yana gabatar da mulkinsa daidai gwargwadon iyawarsa, ya saka an fitar da Uncle dinsa Ibrahim an dawo da shi fadar an kebanceshi a waje mai kyau ana ta yi masa dukkan taimaakon da ya dace na sihiri, cikin amincin mai duka kuwa a yanzun ya daina doke doke da neman fita da gudun da yake yi a da, sosai har ya fara kawo hankali a kan kiran sallah yana kamanta son zuwa ya gabatar da ibadarsa, hakan ya sa hankalin Sultan ya karra kwonci ya ci gaba da yin iya kokarinsa dan gannin garinsa ya dan samu daidaituwa, domin gari ne an riga an rushe sai a hankali koda za'a samu kansa, ba laifi samari na jin nasiha sunna kuma kokarin neman aiki hakan ya sa kashe kashe da fadace fadace a kan yan mata du ya ragu, summa yan matan yawanci da suka dakatar da makaranta sun koma bisa nasiha da shirye shiyen da aje gabatar masu a gidan redio na jan hankali da nasiha da nuni cewa kansu suke halakawa ba kowa ba, shi yasa du yawanci wa'inda suke iya jin kira suka sauko suka shiga kimtsa kawunnansu cikin salama sunna dawo da darajarsu koda kadan ne a cikin da yawan
Furera kuwa ta ga rayuwa gannin idonta, domin abu da ya yi abu da kansa ya sakata a mota ua mikata gidansu ya samu datijon mahaifinta ya sanar masa abinda yake faruwa, ya kuma taushi tsohon da ya rikice da tsoron kar aje ya saketa ne? Ya nuna masa ko daya bao saketa ba, zai so ta gyara halinta idan har zata iya zama da shi ta daeo su zauna, idan kuwa ta ga gaba zata karra dan ta samu haihuwar da na kasa bata a gannin shikenan sai a gabatar da komai cikin salama ta yadda zumunci zai dore
A nanne mamaki ya cika tsohon yake maganar wace haihuwa? Shin furerar ta manta accident din da ta yi tun tana budurwa wanda ta shiga mawuyacin hali domin cikinta ne ya fi dakuwa da mashin din da ta hau daga makaranta zuwa gida, wanda likita ke fada masu mahaifarta ta tabu ko kuwa bakin kishinta ne ya rufe mata ido? Shi kam malan rasa ta cewa ya yi domin a nan tsohon ya kirayeta ya tunasar da ita maganar da ya ringa mamakin yadda take rusa kuka tana fadin ai likita ba Allah bane bai isa ya yanke hukunci a kan haihuwarta ba
Rai bace datijon ya salami malan sannan ya lalubi butarsa ta alwallah ya jefeta da ita rai bace yana fadin" Ki kula, bakinki ya iya magana yanzu dai sai ki shige gidan ki ci abinda muke ci, dama ke kike taimaka mana sai ki tsiro da sana'a sannan ki kasa zaman ki ga idan da riba, ke ba'a guje ki dan halayanki ba kece mai abin fada a bakinki? Hurera ba zan ce maki duniya ba domin idan kuka karra lalacewa a kan haka ni zaki dawo ki kashe, Allah ya ganar da ke da kalar ganiyarsa wace zaki fahimta"
Tun daga ranar take rayuwa a gidansu, rayuwar da ta zo mata a cenji, ba yan aiki ba kudin cefanen Malan bale sansanyar muryarsa da lakausan gadonsa uwa uba abinda takewa kishin babu shi, haka ba cimar da ta saba sannan ba sanyin AC domin gidansu rufin asirin Allah ne Alhmdulilah aman iyayenta ba masu kudi bane, itacema ta gyara gida har suka samu rufin asirin domin ko a anguwar a haka sun fi kowa rufin asiri, shine take baza rashin da'arta son ranta har ta gunduri abokin zaman nata, da kyar da jibin goshi bayan ta cike wata biyu a gidansu aka dawo da ita ta dawo ta ci gaba da zama ba ruwanta da kowa sai mijinta tana kuma gannin yadda cikin mattar da ta tsangwama din ke karra girma da kuma irin yadda kamar da wasa yanzun a anguwar ake mutuntata bayan a da ta dora kowa kan hudubar tsiya ana wulakanta bayin Allahn
______________________________________
*Watani tara da kwana bakwai*
Nishin dake sake tashi a kusa da ita ta sake waigawa tana kallo, a sanyaye sosai ta ce" IBTISAM ko mu koma gida ne? Shin na tabo Mijinki ya maida mu gida ne? Kin ga halin da kike ciki kuma gashi Allah bai sauketa ba har yanzun , bana so ki jigata y'ata"
Mahaifiyar MUHYIDEEN da ta dawo gidansu kusan wata daya da sati daya kennan bayan alfarmar da ta nema ta gudo dan zama da Shuwwa din wace ta zama abin tausayi sanadiyar kumburin da cikinta ke sakata, ta sinkime gaba dayanta cikin ya mata girma sosai, tunda suka yi scanning aka sheda masu fa biyu ne a cikin ta kasa hakura sai da ta lalaba mijinta ya bata dama ta dawo kusa da su da zama domin ita dai ko hauka take ba zata taba turo abokiyar tagwaitakarta ba, duda yanzun Useinar ta fara daidaituwa da lamuran da take fama da su dan kuwa da kanta ta nemi da mijinta ya sawaka mata ta kuma nuna cewa aurensu haramtace ne zata je ta kadaice kanta, wannan dalilin ya sa ta daga ta yi tafiyarta kasa mai tsarki ta yanke hulda da kowa kan tana bukatar kusanta kanta da
Ubangijinta ko zata samu rabauta ko zata ji zuciyar a sake irin na mai kyakyawar tuba, shi yasa itama ta dawo ta sake rungumar lamarin yaronta da matarsa sai wajen Mama da take zuwa su yi zumunci ta dawo tana kula da Shuwwa sosai
A yanzu lokacin haihuwar tata har ya zarce aman kuma shiru, sai Nahidht da itama ta gama ficewa a hayacinta ce nakudarta ta tashi tun da daren jiya har zuwa yanzu karfe goma sha daya na safiya shiru bata haihu ba, gashi likitocin sun nuna cewa nakuda ce take ta zama bata idasa nuna ba sannan sunna kyautata zaton a cikin nan ba daya bane dan irin motsin da abin cikin ke yi bayan girmansa, domin Malan kiyawa ya yi a masa scan ya nuna ya fi so idan lokacin ya yi zai ganni da idannuwansa
Kai ta sake juyawa tana maida hawayen da suka cika idannuwanta ta sake kallon dakin yan haihuwar da Nahidt ke kwonce muryarta a raunane ta ce" Mama, dama kowama haka yake haihuwar ne?"
Hajia da ta dawo da abincin ranar da ta koma ta dauko domin ita Furera bata zo ba tana dai cen tana kula da abincin gidan dan Malan kam ba kanta yana masalacin asibitin koda wani abin cen ake tarda shi ya kasa katabus ta dafata bayan ta nanade mata dardumar da aka shinfida mata a kasa a sanyaye ta ce" Kanwata , kowa da irin yadda take zuwar masa, duda