Showing 6001 words to 9000 words out of 226733 words

Chapter 3 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

7977

shiri

Da hannunsa ya matsa gaba kadan ta yadda kowa zai iya ganninsa da kyau ya ja ya tsaya tare da doka kafarsa daya a kasa lokaci daya kuma ya daga hannunsa gaban goshinsa kadan ya sara masu da karfi yana mai fara wak'ar sojoji wace kowani soja du girmansa, du takamarsa zaka ga yana da wakokinsu a kansa kuma yana iya yin wakar a kowani yannayi

Ai kam muryoyi maza sai zuka bude , tun karfinsu sunna amshi sunna karra jin kwonjinsu na budewa ya sake budar bakinsa da karfi ya furta" Repos!" ya sauke hannun nasa ya juya ya bar wajen ba tare da ya kuma yiwa wani magana ko wani alamu ba ya karasa wajen tafkeken apash din da aka ajiye masa ya hau yana murda ky din ya warce shi da gudu ya nausa cikin garin dan yin patrui, watau kama tsagerun shima da kansa

Ajiyar zuciya suka sauke a tatare sunna karasawa gaban yarensu dan su karra daidaita yannayin aikinsu domin tafiyar nan dai da LIEUTENANT GANARAL aka yita ba da wani wanda zasu yi sakensu son ransu ba, dan haka idan sunna son zaman lafia kawai su aiwatar da aikinsu yadda ya kamata

___________________________________

SHUWAR ki saurara abinda nake fada maki, a gidan redio, A gidan TV a komai da kika sani na sada labarai sun fada sun sake fada cewar LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN ne ya sauka a garin nan, ke me yasa bakya son zaman lafia ne? Ki dawo ki zauna ya fada ya sake fada kar wanda ya fita, idan kika fita wani abun ya ritsa da ke yaya kike so na yi ne?"

Gilas din dake saman fuskarta ta sasautawa gani ta kaleta kasa kasa kafin ta ce" Aunty, tsakaninki da Allah abinda ya sa kike min kugin kiran nan tun daga cen cikin falo kina gudu har na tsaya na zatama wani mugun abu ne ya faru? , Kin ga da mai a motar nan kuwa?"

Bata bata amsar da mai a mota ba sai kokarin karra nusar da ita kar ta fita da ta kwatanta yi aman ina, kai tsaye SHUWAR ta saka hannunta ta janyo kofar ta rufo tana daga birkin da ta dane da kafarta wanda ya dan dakatar da motar ta ja motar a hankali a hankali kafin ta idasa janta ta wuce gaba dayanta

Tuki take tana mamakin garin gannin du irin tarin al'uma irin na garin nan yau sai daidaiku ke yawo a cikin gari

Ita dai take motarta ta yi da gagawa ta yi kwana ta idasa gidan Elhaj Mai shinkafa

A kafarta ta sauka ta idasa shiga bayan sun gaisa da mai gadin du a tunaninsa wajen y'ar Elhajin ta zo hakan ya sa ya barta ta shige hankali kwonce

A kanta ta gama hardace yaya gidan nan yake tunda a kulun idan sunna tare shine yake yi mata bayanin yadda gidansa yake da bangarensa da na matayensa

Kai tsaye ta durfafa cikin falon da idan bata haukace ba kamar yadda yake ce mata bangaren dama shine nasa na hagu kuwa na matansa wannan shine bangaren daman

Kofar falon da take hangen makekiyar TV ta madubin shigar ta saka hannunta ta tura ba tare da ta yi salama ba ta shiga tana kale kalen falon har idannuwanta suka sauka a kansa shi da matarsa sunna zaune wace itama ba zata wuce da shekarunta ba domin haihuwarta daya a gidan har ya ga ta tsufa yake son sako SHUWAR din

Da yar gagawar maganarsa ya ce" Ke ke, SHSSSSSSHUWAR me kike nema a nan kuma?"

Sama da kasa ta sake binsa da kallo kama daga yannayin jikinsa har zuwa tumbinsa masha Allah
Gaban goshinta ta dafe tana fadin" Kai Allah, kai jama'a kai yanzu in banda hauka irin naka ko nice karuwar ai ka yi hakuri da ni ta yiwu ka samu iri a gidanka, koda yake na ga wannanma ba laifi dake zaunen, Watau ELHAJ kai sana'arka ce haka idan na kula?"

Fuskarsa ya hade sosai yana kallon matarsa ya ce" Ke Umi tashi tashi maza maza ki tafi bangarenki, kuma idan na ji maganar nan a bakin daya daga cikinku walahi sai na sake ki na rantse maki"

Da sauri Umin ta mike tana sake kallon SHUWAR tun daga sama har kasa ta wuce ta gefenta ta tafi

Mikewa ya yi yana fadin" Har gidana zaki shigo ki nunan akuyanci? Ashe baki da wayo? To na rantse maki na fiki iya iskanci idan tunaninki ke yar iska ce, zan yagalgala ki nai maki dala dala, abinda kika hannani kamawa zan kama yanzu na fatataka shi har sai ranki ya bace, kuma ko ina aka je kece marar gaskiya domin ke kika tardo ni har cikin gidana"

Rigar dake saman rigarta ta kama ta cire ta yar a nan kasa
Lulubin dake saman kanta na farin mayafi ta ja ta cire ta yar a kasa hakan ya sa lalausan baki sidik din gashin kanta bayana a kunce ba ko gyale a jiki
Gashin ta shiga barbazawa ta kama rigar tata daga baya da sauri ta yaga tana zarro idannuwanta ta ce" Fine, abinda na so yi kennan sai gashi ka taimaka min, ka ga da zan ratso ta nan yaya hudu na hadu da su yan mata a zaune sunna hira, haka kuma na hadu da wasu mazan, babu abinda zai fitar da kai a maganar da zan fada cewar ka zo zakai min fyade ne, Elhaj kana tunanin ko y'ayanka zasu yarda da kai ne bale matanka? Bismillah ,, ga babar shedar da zata nuna cewar na juya dan na gudu ka yagan rigata, na rantse da Allah kaine zaka kwana ciki, ashe baka san kaidin mace ba? Barama ka gani!"

Da sauri ta bude muryarta tana ihun"kai Wayo jama'a ku taimakeni zai ketan hadi, Wayo a taimakeni Elhaji zai fada min, haba Aban husna ka rufan asiri ka barni da mutuncina kar ka manta kaima ka haifa fa, kana da yan matan gasunnan birjik idan akai masu haka yaya zaka ji?"

Ido ya zarro hadi da yin baya yana zarro idannuwansa hadi da dora hannayensa saman bakinsa har yana taune harshe wajen fadin" Ke ashe baki da hankali?, kin ga dan girman Allah ki rufa min asiri, ni ba abinda zan maki, ki wuce ki bar min gidana kar ki tonan asiri a cikin anguwa!"

SHUWAR ta ce" na rufa maka asiri? Ni da ka yankan tikitin zawarci rana tsaka dan an zo an fada maka zance ka so rufan asirin ne? Ka fitar da ni kawai, bilahilazi sai ka bani million goma ko zan bar gidan nan cikin salama idan ba haka ba kuwa ga message dinka na jiya na barazanar da ka min bayan daurin aurenmu cewar maza maza a matse kake idan ba Haka ba kana iya yanka min tikitin zawarci, duda na zo din ka yankan ko? To du na goge rarashin da na maka har magariba ta sanyo kai kafin mu hadu da kai a yanzu Elhaji a shirye nake ko ni ko kai domin idan baka bani kudin nan ba zan maka ka kotu da shedar fada min da y'ayanka da matanka zasu bada da ta wayata inaga dole a leka gidan maza a amshi tarbiya!, ka bani ko na tona maka asiri duniya ta jimu!"

Yadda ka san mai kamun aljannu, yadda ka san mahaukaciya tartibiyarta haka SHUWAR ta zamewa ELHAJ mai shinkafa, tabas idan ya taba yin dana sanin rayuwar bariki to a yau ne, da ta san dalilin da ya sa ya saketa dan ya gane yayarta itace macen da yake mugun son aura ko ta yayane dan su yi zaman aure da junna domin tun ranar da ya ganta a shagonsa ya haukace sai bai kuma ganninta ba, bai kuma san ita ko wacece ba da cewar tana rayuwar bariki ba sai a jiya wanda Hakan ya daga masa hankali ya rikita shi harma ya kaishi ga aikata aiki irin na shirme ya makawa SHUWAR din saki uku wanda dalilin sakin nan sai da ya yi kuka domin ya tashi a ba wan ba kannin duda burinsa daga baya ya samu yayar su yi aure domin ai ba abinda ya shiga tsakaninsu da SHUWWAR din , sai ga kuma wannan wawan dirowar daga sama

A haukace ya ce" Yaya kike tunanin zan ajiye million goma a dakina bayan ga banki ga komai gari cike da barayi?"

Da karfi ta ce" Kar ka raina min hankali, ka manta ka fada min akoy asirin da akai maka na harkar kasuwancinka da aka haneka saurin kai ajiyar kudi banki? Cewar ka'ida ne kudi baka kaisu banki sai ka tara na kwana biyu ko ba kai ka fada min ba? Kudin kasuwarka na jiya yana dakin nan, bari ka ji Elhaji bilahilazi ka fitar min da kudin nan kai Wayo zai tuben rigata......" Ta fada tana daga rigar tata gaba daya ta cire a jikinta wanda hakan ya yi daidai da buga bangarensa inda suka kai dubansu a tare a haukace sannan suka kalli junnansu

Zata kuma kurma wani ihun ya kai gwuiwoyinsa kasa yana hade hannayensa duka biyu jikinsa har yana rawa ya ce" Ki yiwa girman Allah zan dauko zan dauko shuwar kar ki tonan asiri a anguwar nan sunna gannin mutuncina sosai...." Yana fada yana mikewa da yin ciki da gudu gudu haka tuwon duwawu da tumbinsa ke rawa babar babar har ya shige ciki

Da sauri ta wawuri rigarta tana sakawa tana sake waiwayen kofar da ake bugawa daidai ya fito da wata bakkar jaka ta saka hannunta ta warta ta juya da sauri bata ko tsaya ta sake bi ta kansa ba tana fadin" Ban gama da kai ba, yadda ka ciran wahala sai na wahalar da kai !"
Kofar ta bude pagam sukai ido hudu da baban dansa da ya zo gaishe shi yake jin yar hatsaniya aman kuma ba zai iya shiga ciki mahaifinsa bai bashi damar hakan ba

Da ido suka raka junna ita da shi kafin ta cire kanta da sauri ta wuce ta nufi get, inda shi kuma ya raka bayanta da kallon mamakin wacece ita a dakin mahaifinsa da irin shigar nan ta riga da wando pakistan damamu kanta ba dan kwali, ga wani wawan kanshi da take bari du idan ta gita?

Kansa ya saka dakin da salama a bakinsa yana kallon mahaifinsa da ya amsa yana juyawa ya nufo tsakiyar falon yana fadin" Zauna zauna Abdul Mutalab ina zuwa"

Maimakun ya zauna din sai ya samu kansa da karasawa wajen da dan kwalinta ke yade ya duka ya dauko yana kallo
A hankali ya kai dan kwalin wajen hancinsa yana lumshe idannuwansa ya shinshina , dadadan kanshin da dan kwalin ke fitarwa wanda ta manta tsabar kidima ta tafi ta bari a nan

Dago kan da zai yi ya ga mahaifinsa ya fito sai zarro ido yake da waya a hannunsa ya sauke dubansa a kansa hakan ya sa da sauri ya jimke dan kwalin Yana sake gaisar da mahaifin nasa

Har yana inda inda ya ce" Abdul Mutalab ka ga yarinyar nan da ta fita, ita nake so ka kai kararta domin sata ne ta min, sunnanta SHUWAR, zan fada maka har anguwarsu da komai da komai nata, kudinane a jakar nan million goma sha uku, Abdoul Mutalab ta tafi da su kai dai sheda ne ka ga fitarta da jakata"

Samun kansa ya yi da kure fuskar mahaifin nasa da kallo, SHUWAR?, Sunnan nan kamar shine sunnan da yaron shagon Aban nasa ke fada masa sunnan budurwar da aka daurawa mahaifinsa aure da ita jiya ne? Ama idan haka ne ai ya shiga uku ya lalace......
hasbunnalahu wani'imal wakim ina zai saka kansa ne? Dan kwalin nata ya sake jimkewa yana amsar wayar da mahaifinsa ya bashi mai dauke da numberta yana sake jadada masa cewar ya fa maida hankali tunda likita ne shi yana iya fita idan wani bashi da damar fita ya yi maza ya je ya shigar da karar nan tun yau tun yanzu!

Shi dai samun kansa ya yi da fitowa ya fice a gidan ya shiga motarsa ya zauna yana dora kansa a jikin sitiyarin motar a hankali ya furta " SHUWAR, Allah ya sa ba ke aka daurawa abana ba dan Allah, ke ko barauniya ce ke ba komai zan ajiyeki a gidana na kilaceki ta yadda ba zaki fita bama bale har ki yi satar kin ji?, SHUWAR ke wace yare ne ce?"akinsa da karfi ya ce" cije a kasan zuciyarta tana aya💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥


*The Hero writer*


*SAJIDA*


_Bismillahir rahamanir rahim_


PAGE:. 4️⃣


*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*






*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*


*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*



*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*



*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*





Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.


*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618


Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰



A daidai lokacin da Abdul Mutalab ke begen SHUWAR da tunanin maimakun ya kai kararta saboda million goma sha ukun mahaifinsa gwara ya nufi kampanin sadarwa a bi layinta a sanar masa ina take wacece ita hankalinsa tashe ya dauki hanyar da ta dauka ba tare da ya san asalin nan din ta nufa ba
ita kuma a daidai lokacin Jar danja ce ta tsayar da ita a cikin motar hakan ya sa ta dauki lokaci mai ban mamaki bata saki ba
Gannin kamar Danjar ta ki ta saki sai ta saki karinta ta shiga neman ribom a cikin motar ko zata ci sa'a ta samu dan ta daure kanta da shi, a irin lokacin ta taki rashin sa'a domin wayarta dake cikin motar ce ta dauki kuka tana dubawa ta ga bakuwar number, har zata share sai kawai ta daga tana ajiyewa a gefenta tana ci gaba da neme nementa hankali kwonce duda irin yadda yanzu take gannin garin shallllll sai daidaikun mutanen dake tafiyarsu a gefe da gefen kwalta aman a tsakiyar titi duma wanda ya san ciwon kansa ya nemi waje ya ajiye brakarsa dan samun kwonciyar hankalinsa

"SHUWWAR a ina kike ne?" Ta ji muryar namiji na tambayarta da kama sunnanta kai tsaye hakan ya sa ta sake duba wayar dan gannin number daidai da ana kwonkwasa mata gilas din motarta

Dagowar da zata yi ta ci karro da abinda ake fadin kana samun faduwar gaba dake hadasa maka cikinka ya juya daga inda yake ya dawo kasa , a da bata san ana juyawar ciki ba sai yau,
Hannun mutumen ta fi kurawa ido wanda hannun ke jujuye irin a mumurden nan irin hannayen da ake nunowa a film din yan indiya wanda yawancin lokaci mukan yi daria mu ce ku ji wata karya wai hannu ne haka,
Kafin take sauke dubanta a kan fuskarsa da bakin gilas din dake saman fuskar sannan ta waigo da sauri wajen da aka sake buga mata da gagawa da dan karfi tana sauke numfashi da gagawa tamkar mai cutar athsma, domin har ga Allah sai ta ajiye hakan a matsayin ita kadai ta ga halitar nan

Da sauri ta nemi fitowa dan ta kula hakan yan jagaliyar sojojin ke so ta yi a lokacin da ta sake gannin sojoji ne zagaye da ita tamkar yar ta'ada
Lokaci daya magangannun Fauziya suka ringa dawo mata a kwakwaluwarta na irin tsaron da aka saka a kasar da hanni da akai kan fita kwata kwata

Tana budewa tambayar da aka fara yi mata ta sakata shiga inda inda gaba daya ta rasa me zata bada amsa

Babur din ya caka ya ajiye ya sauka yana matsar da sojan xake yi mata tambayoyin dan ya kula kamar ana sako taushi a lamarin, gefe ya maida shi da hannunsa ya karaso daf da ita sosai hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login