Showing 45001 words to 48000 words out of 226733 words

Chapter 16 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

8058

zaku rayu da farin ciki ko bakin cikinka tare, wace zata haihun maka ta dauki dukan nauyi naka, itace zata zamto abar da za'ana harin rayuwarta har a ringa furucin kar ka sakkar mata fuska zata rainaka ne? Wani raini ne ya yi saura kai da kake kasancewa zigidir a gabanta bayan ka fita shekaru ko yayane? Wani raini kake magana a kansa matar da ta ga ka rikice ka nemi nutsuwa ka kuma samu a tare da ita? Idan a duka bayan wannan bata rainaka ba ai bai dace ka yi tunanin zata rainaka ba a rayuwa, maganar raini ai ta kare da ace kana da hankali, kin ga Hamza yana da mutunci, abinda kike ta jaje kansa kan shaye shayensa kin ce ya halata ka zauna da mashayi bayan ka san mashayi ne? Wannanma gaskiya ne aman yaya kike so mu yi? Mu shine mutun a wajenmu, shansa kuma bai hanna shi ibadarsa ba, ido rufe ya hanna ki sha sannan a bayane ya nuna burinsa ya dauna sha, shaye shaye na saka bawa aikata munanan laifukan da ba zai iya gogewa ba a duniya, a haka zamu amsa mu kuma taimaka masa muma har ya daina, in sha Allah zai daina sha Shushu kuma zaki ji dadin zaman aure da shi"
Nahidt na murmushi ta ce" ki kunce min kunshin nan na wanke na yi wanka na je kasuwa, na ga kurkum dinmu da madarar sun yi kasa sosai bara na je na siyo kayan gyara da kuma kayan hada turaran wuta da na ruwa da su humura mu zo mu jika na jikawa mu soya na soyawa mu shiga shiri, Shushuna kin san sai na maki garra a wannan auren..........sai na fitar da bokici bokici na kayan aurenki, yanzu ne zan aurar da y'ata ! Ta karashe da yannayin tsokana dan ta san yanzu shushun zata ce ke ni yayata ce ke mamana ta rasu
Sai ta ga Shushu bata ce komai ba tana daria kawai kasa kasa itama ta kama kunshin ta shiga cire mata a nutse

Tabas yanzu ne suka dauki auren nan da mahinmanci
Sau uku kawai Malan ya lamuncewa Hamza zuwa wajensu dan shirye shiryen da suke yi, a wannan zuwan nasa uku da ya yi a falonsu ake yin zaman gaba dayansu a ringa hira anna barkwonci
Watau Hamza kamar wani jigo mai saka su farin ciki ya zame masu, a ranar kuwa da ya zube kudin gyaran amaryarsa sai da suka kusan haukacewa gaba dayansu domin a bayane suka rikice da tarin kudin nan
A lokacin Nahidt ta riki kudin ta ce" kai dai kawai Allah nuna mana Hamzanmu"
Shuwwar kuwa kai ta sada tana daria kasa kasa dan ta san fitarsa ake jira su kwaso shoki a gidan nan, domin jiya jiyan nan take maganar kudi ya fara kasa sun shiga uku

Kafin ya tafi yake fada masu maganar kawo lefe ya ce in sha Allah ranar daurin aure karfe bakwai mata zasu kawo lefe, domin a ranar ne danginsa na cen gidansu Tanus zasu zo sun ce sai sun zo zasu kawo lefen da mamana, kin san babana da son ya kankaro min daraja, to dai inaga fen zasu hade su kawo su, mu dai da angwaye zamu zo mu rakashe a kada manaa ganga oh...su Hamza za'a angwance................

Ire iren barkwoncin da ya saka Shuwwar din kanta yi masa waje mai mahinmanci ta ajiye shi a cikin zuciyarta
Zata iya cewa sonsa take yi, ta kamu da sonsa ne, yo ai ya isa a so shin, meye aibunsa? Bashi da wani aibu da zai zamo aibu a wajensu gaskiya, ko daya bashi da shi

Daga wannan lokacin bayan gyaran jikin amarya da suke yi sai suka koma gyaran baban falon
Watau dafe dafen kaza irin nasu na saudiya da suka koya a wajen mahaifiyarsu babu kalar wanda basu dafa mata ba kuma suka tisa keyarta ta cinye
Idan aka zo fannin maganin sanyi, maganin basir , tsumi kuwa cikinta har ya saba du irin yadda take nuna ta gaji cikinta ya cika a haka yayarta zata ajiye mata ta ce da ita ke dai dan karra sha ke dai kin jiya yar kanwata?

Da wannan suka ringa tunkarro lokacin har ya yi saura sati daya daurin auren, a nan ne Shuwwar ta fitar da akwatunnantaa dake jejere a dakin da suma rufe suka baje komai

A nutse suka fitar da kayan dinki masu mugun yawa wa'inda Shuwwar ta murje ido cewar in dai sunna so ta dauka sai sun dauka summa
Ai kam suka daukan kayan fitar biki masu yawa suka bari magariba na yi suka shige motarsu suka nufi wajen telensu wanda dama su yake jira

Kaya suka zube masa suka zube masa kudi da kwanakin da suke son kayansu
Ya kuma amsa ya amshi kalolin dinkunnan da suke so ya rabawa yarensa suka shiga aiki

Ana sauran kwana biyu daurin auren Shuwwar , hakan ya sa yayunta suka shige cikin hali na busy
Ba tarro suke yi nasu na kansu ba, abinda ya shigar da su a busy hade haden garra ne, idasa rurufe tarin uban turarukan da suka hadda mata na wutan ne da na ruwan, ga kuma na saudiya da suka siya a garin mai tarin yawan gaske irin na cikin yan kannanun kwalaben nan mai masifar dadi, Shima sun masa wajensa daban sun daure..............kai gata dai shuwwa ta same shi sai fatan alkhairi da zaman lafia da mijinta

Daga wanka ta fito tana tafia a hankali ta zauna saman kujera gaban sif dinta tana lumshe idannuwanta sanadiyar kanshin da jikinta ke fitarwa mai mugun dadi da irin laushin da jikinta ke karra dauka balema idan ta taba ruwa
Manta da ta hada mai karra fitar da darajar fatarta ta janyo a nutse ta shiga shafawa tana sake lumshe idannuwanta dan santsin da yake karrawa jikinta gaba data ga kuma irin nasa kanshin mai sakawa bawa nutsuwa a zuciya

Wayarta mai kirar apple watau iphone wace angwonta ya gwongwajeta da ita ta shiga dan haskawa alamun kira na shigowa

A nutse ta janyo wayar ta daga kiran tana karawa a kunnenta ta yi salama da sansanyar muryarta

A sanyayen shima ya ce" I'm sorry wifey yau du ban yi kira ba, kin san menene? Yadda kika san tashin duniya haka babana ya dauki daurin auren nan, har tunani nake anya anguwar nan ta dauki bakinsa kuwa? Yanzuma daga masaukin da zai sauke uban gidansa nake kin san bayan ya yi ritayama akoy kyakyawar alaka tsakaninsa da Chief of army, so ya tabatar masa shi zai mika sadakina wa Malan shine fa du babana ya rikitamu kan zuwan bawan Allahn nan, ina fata ba'ai min fushi ba?"

Dan murmushi ta yi tana lumshe idannuwanta ta ce" Ban yi ba"

Watau jan aji, ko yace girma irin na Shuwwar na bashi mamaki, tamkar wadda ta shafi jinnin sarauta wani sa'in, shi tunda ya santa idan ka ga ta budi baki ta maka doguwar magana ta danganci abubuwan da ta gani na rayuwa ne irin sake saken da maza sukai mata na aure, bayanshi ko da su Nahidt sai dai ya ga kasa kasa ta yi tsokana ta kuma koma ta hade abinta kamar ba ita ta yi ba, sai Nahidt din ce zata ringa bambami ana riketa, wani lokacin har tunani yake shi mai maganar nan sai ya hadasa mata ciwon kai ai, domin shi dai tsakani da Allah, Allah ya yanka masa abin magana yi zai yi ta yi abinsa

Yar dariya ya yi a hankali ya ce" Kina irga awani kuwa?"

A kasan zuciyarta ta ayana' fiye da tunaninka, domin na fika zumudin son gannin ranar nan, abinda na koya shine rike zumudin hakan a cikin zuciyata domin a aure hudun da na yi na bayana ban ga alkhairin hakan ba'
A bayane kuwa sai ta ce" Awani? Na me kuma my Hamza?"
Ido ya dan zarro ya ce" To wai me na maki da zaki rama ne my kanwa? Yanzun sai kice bakya duba agogo du wucewar minti kina ayana saura yan awani? Kin ga yama ta yi fa, daga safi ta waye saura kwana daya tak, daga an yi wani wunin sai a fara irga yan awanin da zasu rage Hamza ya zamo mujin Shuwwa"
Murmushi ne ya subuce mata hakan ya sa ta kashe kiran da sauri tana sauke murmushinta a bayane
Mikewa ta yi tsaye ta shiga dan takawa hakan ya sa duwawunta dake cikin tawul jujuyawa a bayane ta ce" Nd shuwwa ta zamo amaryar Hamza.....wayo Allahna ashe za'ai min auren gata nima kuma har a tarra al'uma irin haka? Wayo farin ciki kasheni?"
Tana sambatun farin cikinta wani kiran ya kuma shigo mata wayar
Du a tunaninta shi din ne, domin kira a wajensa har ajiye wayar take yi ta ki dauka sai ya kirayi ta Nahidt yana fadin Allahn da ya sa in bakya son jin muryata ai ga Nahidt ga Fauziya sai mu kwana muna labari sai dai haushi malama!
Number da ta gani ta sakata dan kura lu'u lu'un idannuwanta tana kallo domin bata san number ba, kuma ta sha dawowa ta tarda misss call da number an yi kiranta bata kusa
A hankali ta daga kiran tana karawa a kunnenta ta yi shiru
A sanyaye ainun ya ce" Aure bai haramta tsakanina da ke ba Shuwwar, bai haramta ba, na zo yau na samu Malan dan na fada masa cewar na je na yi bincike ina iya aurenki yake fada min ya maki miji?, Shuwwar ni ban san me na yi nake fuskantar jarabawar sonki haka ba, mahaifina ne ya ja min ko?, Shine ya ringa fade fadensa har Allah ya kama shi ta kaina ko?, Shuwwar wani zaki sake aura ya sake ki kina ji kina ganni bayan kin san ni ba zan taba sakinki ba?, Shuwwar tunda na gila karyar ni mijinki ne a gaban mutumen da na san a lokacin da ya yi niya da yanzu sai dai tarihina kina tunanin zan bari wani ya raba mu ne?, Haba my Shu dan Allah ki cewa Malan bakya son wancen ni kike kin ga in ba haka ba zaki karra yin wani auren a sako ki ne"
Da dan karfi ta ce" ba Amin ba , kai Abdul tsaya ka ji na fada maka gaskiya, ka ga da kai, da babanka, da sojan nan da kake alakanta kanka da jarumi dan ka yi magana a gabansa na tsane ku!, Ku shafa min lafia ka ji? Mijina da zan aura kuma yana sona, Alhmdulilah ya san wacece ni kuma a haka yake son abinsa, kai barama ka ji ka kuma kirana walahi sai na wahalar da rayuwarka, da ace ban yi rantsuwar ni da soja ko police sai a lahira bane da kai kararka zan yi su rufeka na huta!, But yanzu ina mai gargadinka kan ka shafa min lafiya ka ji bayanina?"

Tana gama fadan ta kashe tana zabga uban tsaki a bayane ta mike ta shiga fitar da nikaf dinta da rigar da take sakawa dan karra dumama dumin jikinta domin a yau zasu fara kunshi da kuma alawa dan cire gashin jikinta da ya kwonkwonta lumbuk, tana yi tana mita da fada a bayane tana fadin jarabar banza da wofi sai ka zo ka sa a sakeni, yo in aurena ya zauna sai na tarda mai shinkafa na ce da shi to azalumi na auru yaya ranka?😂

Babar ranar
Kwaramniya ke tashi ta manyan almajiran malan dake sake kimtsa kofar gidan da aka saka manya manyan runfunna har kwaya hudu , irin dankara dankaran nan
Mutanen anguwa tuni suka ringa cika gidan malan tunda garin Allah ya waye dan karra ba idannuwansu kalaci da mamakin lamarin Malan din, domin a cikinsu kalilan ne suka dauki hakan da fuskar fahimta harma suke adu'ar Allah ya sa wannan din idan aka yi shine na dindindin

Dankara dankaran sojojin dake zagaye da anguwar kuwa idan ka gani sai hankalinka ya tashi, tamkar zasu je dan jijibin yaki ne domin tuni Tsohon ganaral da amininsa Chief of army, da aban Hamza suka samu karasowa a yanzu da yake karfe takwas sunna baban falon Malan na alfarma sunna karra tataunawa dan idasa shirya lamarin daurin auren, sannan sunna jiran matan da suka zo da sha tara ta arziki na akwatunnan amaryar su shigo su shaoda masu cewar sun bada kuma an amsa

Wayar dake hannun Chief of army ce ya sake bugawa a karro na bakwai, zuwa yanzun an daga sannan da muryar da ya amsa ya saka shi yin dan Murmushi yana fadin" Kai fa ka ce da kai za'a daura auren nan, kuma ka ga mu tuni muna tare ka da san aminina ne Ganaral, me zai hanna na jiyo jiniyar sojojinka kun karaso anguwar ne? Ka zo son zan ji dadi idan ka zo"

Goshinsa ya tatare yana mamakin lamarin Father dinsa, yanzun har sun je wajen daurin auren da aka saka karfe tara za'a daura shi? Eh lalle yaron nan dan gata ne, watau sun je su yi jiran bakinsa ne ko?

Dan nishi ya dan fitar kasa kasa ya ce" Zan zo "

Chief of army ya yi yar dariya yana fadin" Ina duban hanya "

Daga nan ya kashe yana fuskantar baban Hamza ya ce" ka ce min tun zuwan nan da ya yi sau daya da na ce ya je bai kuma komawa ba?"

Daria ya yi yana fadin" Haba aminina kaima ka san zuwanma da ya yi dan maganarka ce ai, ka ga ranar farin cikin da na yi kuwa? Allah dai ya kara girma aman garin nan ana tsoton Lieutenant ganaral walahi, baka ga yadda ake kwasa tsakaninsa da mararsa jin magana ba"

Shima yar dariyar ya yi ya ce" Ai ana cen ana kwasa da mamansama, aure fa aka daura masa sau biyu kadai ya je , kuma a zuwan nasa biyun sau daya tak suka hadu da matar, cewa ya yi mahaukaciya ce sai tana kafeshi da ido kamar mai farfadiya, kai dai ana nan ana fama da rigimarsa "

Ire iren hirar da suke ta yi kennan sunna shan dariya ga zazafan kunnun fulawa da ya sha uban madara da kayan kanshi yana turiri yana ta tashi a gabansu an zuzuba masu a manyan kofofi na kwalabe , ga sanyin AC da falon ya dauka kai abin dai sai hamdallah kawai

A cen cikin gida kuwa a falon matan Malan bayan an karbi kayan amaryar matar Malan uwar gida itace a tsaye a gaban lamarin, domin a lokacin da malan ya yi tsaye ya dubi idannuwanta ya nuna mata yin hakan shine farin cikinsa ya saka ita kuma mikewa da dukan kokarinta da zuciya daya ta amshi su Shuwwar harma take hidima da su
Ko a yanzun matan da suka zo da akwatunnan sun samu tarba ta mutunci har sun cika da mamakin gannin hakan duba da yadda dan uwansu ya fada masu cewar ko me suka tarar kar su saki su nemi wulakntar da yarinyar, idan har suka ga wani abin batanci a tare da ita kar su manta d'an yar uwarsuma yana da kashi a cikinsa a haka suka amshe shi suka nuna masa so har zasu bashi y'a
Su abinda suka tarar kwata kwata basu ga abin tsatsamta ko na wulakanci ba
Sai da aka gama zube akwatunnan da suka girgiza matan daje falon Nahidt ta fito da waya a kange a kunnenta tana amsa Hamza dake shaida mata suma sun taso da jama'ar daurin aure sun nufo gidan Malan din , hakan ya sa ta shigo falon tana murmushin da ya sake fitar da kamaninta sak sak sak da mahaifiyarta, domin idan baku manta ba Nahidt ce ke kama da mamansu, Shuwwar kuwa ta dauko kamani da mahaifinta wanda shi har suka rabu da shi ya ki jinnin ya ji an ambaci sunnan kasar nan, mutane da yawa kan cewa ai kurciya akai masa wada ta fitar da shi daga kasar kwata kwata harma ya ki jinnin maganar kasar bale mararin dawowarsa cikinta

Idannuwanta ne suka shiga cikin na matar da ta mike tsaye a tsorace ta kafeta da ido
Bakin matar na rawa tana nuna Nahidt ta ce" wannan wannan wannan wacece?"

Amaryar Malan da ta san dama a rina, harma zuciyarta ta gama dumewa da farin cikin gannin haka ya fara bayana, a zuciyarta ta ayana'an zo wajen, dama na san wani sai ya gane da wannan karuwar ce zamu aurawa danmu kanwarta?' hakan ya sa da gagawa ta ce" Wannan? Ai yayar amaryar ce, sunnanta NAHIDT, gidansu a nan baya yake shi Malan din ai taimaka masu ne yayi duba da ba tare da iyayensu suke zaune ba" (Dan adam kennan, domin ba zan ce malan bahaushe kennan ba dan kuwa kaf duniya akoy masu irin halayen nan a kowani yare, hanyar da zata bi ta hanna farin cikin wani take nema dan kawai tana jin tsoron rabarta da farin cikin ke iya yi ya saka ta zama tamkar mahaukaciya)

Dukan mutanen falon da mamaki ita suke kallo da wannan dogon jawabi haka
Da sauri matar ta sake kallon NAHIDT da ta yi mutuwar tsaye cikin shagarta ta watsetsiyar farar shada ta sha zubi blue mai haske da fari hakan ya sa shadar kara fitowa sosai take kyalkyali

Matar ta kai dubanta da sauri kan hannun da ya riketa wace ke zaune a kasa muryarta kasa kasa ta ce" Gimbiya ki zauna, nima tunda na ga wucewarta tun dazun sai da na mata irin kallon nan, aman kema kin san ba zai taba yiwuwa ba, ki zauna kin ji?"

Ina hannunta ta janye tana karra kallon NAHIDT da gaba daya duniyar take neman yi mata zafi da mugun tsoro da fargabar kar a kuma fasa auren kanwarta
Daidai Fauziya ta fito da Shuwwar tana rike da hannunta ita kuma tana sanye da doguwar farar riga mai laushi sai hijab dinta fari dogo sosai har kasa wanda ta sha wankan ruwan turare da na wuta ya kasance shigowarsu ya sake harmutse kanshin falon sai dadadan kanshinta ya sake dauke dakin gaba daya , a lokacin ne kuma matar ta sake zuba mata ido itama tana kallonta

Kanta ne ta ji ya fara juyawa, harma ta fara tunanin ko ta haukace ne da yan matan nan biyu daya ke kama da yar uwarsu da ta bace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login