Showing 60001 words to 63000 words out of 226733 words
1️⃣9️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.
*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
CHIEF OF ARMY ya sauke ajiyar zuciya yana duba agogon hannunsa yana lalubar wayarsa a dan yana son yin call ya ce" Hakkun, hakan ba shi zai sa muma mu yi watsi da su ba, in sha Allah Allah zai daidaita lamuransa da kansa, ka ga barama na ji wajen da dan rigimar ya shige, domin so nake a yau a mika masa iyalinsa, su je cen su karata, idan har aka dauki wani lokacin ina tsoron rigimarsu su dukansu"
Malan kam farin ciki ne ya kama zuciyarsa, kamar sun san abinda yake cikin zuciyarsa kennan
A daidai lokacin da CHIEF OF ARMY ya shiga tura kira a lokacin Matar malan uwar gidan ta yi salama ta tsaya a kofa tana neman izinin shigowa domin an amsa mata aman ba'a ce da ita ta shigo ba, ita kumaa ba zata shiga kai tsaye ba
Malan ne ya mike yana sake gyara hular saman kansa mai shegen tsada wace ta amshe shi ta fito da kyansa sai sheki yake uwa shine angon ya karasa ya dagaa labulen yana amsata
Kayan abincin da ya ga ta zo da su ya saka shi sakin murmushi yana kallonta kasa kasa sosai yaa furta" Barakalahu fihk Ya Maryama"
Murmushi ta yi masa kasa kasan itama ta ce" Ya Imam, ya dace a kula da cikin bakinmu, uwa uba na amarenmu, ga abincin nan na baka ka mika?"
Kansa ya dan girgiza yana bata hanya aman ya umarci masu aikin da suka rakota kan su ajiye a nan su juya
A nutse ta ringa kaiwa tana ajiyewa a tsakiyar falon bayan ta yi salama ta gaishe da mutane
Ba tare da ta tsaya kale kale ko tsegumin komai ba ta gama ajiyewa ta juya ta fita abinta da zuciya daya bayan Malan ya sake rakata yana mai shi mata albarka da kyakyawan murmushi a saman fuskarsa wanda hakan ya sauka a fuskar Nahidt dake kallon matar tunda ta shigo har ta gama ta juya
Bakinta ta tabe tana ayana 'Kinibabiya kawai, shi kuma katon banza!'
Matar malan kam wajen baki ta koma hankali kwonce biki ya ci gaba da tafia tana mai basu dukan kulawar da ta dace tamkar yar uwarta ta jinni ake aurarwa, ita itace uwar gidan malan, ita sukai aure na budurwa da saurayi da malan, ita din yar gidan wani hamshakin mai kudi ne, sun hada kansu da kansu da Malan da soyaya hakan ya sa rashin haihuwarsa baya daga mata hankalin zama da shi sam, abinda ke damunta matarsa ce sai ko wadinnan mutanem dake kayar mata da gaba da irin tsoron da ake yawan bata a kansu ana fada mata cewar idan ta yi sake wani abu ya faru tsakanin yan matan nan da malan ta shiga uku ta lalace tana ji tana gani mijinta zai gagareta
Sai dai a yau, a irin abinda ya faru a yau
ta idasa zubar da dukan wani makamin neman fitina da yaki da take yi da yan matan nan
Ko a da ta san babu abinda sukai mata, matsalarsu daya ce na mijinta na matukar girmama al'amarinsu, sannan amaryarsa na karra rura wutar kiyayar hakan
Aman idan ta yiwa abin nan duban tsanaki wai ita meye ribarta a ciki? Ita din dake tirata tana sakata tsanarsu ita dinma ba barinta ta yi ba, sannan au dukansu sun rigaya sun sani ne idan har Malan ya yi niyar auren NAHIDT basu isa su hanna shi ba domin Malan ba sakaran namijin da zai tsaya mace ta haramta masa abinda Allah ne ya halata masa ba, ba zai wulakanta su ba, aman kuma ba zai yi faduwar tasan da har zasu hanna masa aure ba matsawar ba haramun bane, to fa zai aikata ne
A yau ta fara shayin lamarin yarinyar nan SHUWWAR
Da ake cewa hadasa ga mai rabo taki ce , to fa tabas yana kasancewa a lamuran yarinyar
A aure auren da take yi bata taba auren marar mutunci ba, sake saken da ake yi mata bata taba haduwa da wawan da ya yi tsaye kan sai ta maida masa dukiyar aurensa ba, kai idanma ba rufewar ido ta mutanen dake hadasa mata masifa ba sunna gani da zarar an saketan take samun wani na gani na fada ya aureta da daraja duda zagin da ake yi mata cewar karuwa ce kanwar karuwai ce , bazawara ce ,meye meye, sannan dukan mutanen anguwar nan sunna mamakin mazan dake sakinta kuma su dawo sunna nacinta gar sai Malan ya yi da gaske koda za'a shafa mata lafia domin akoy wanda sai da Malan ya hada shi da yan hizba aka yi masu tsakani kafin ya shafa mata lafia dan kuwa a ya sake tan ya kuma nace da kai kawo wajenta har sai da ran Malan ya kiya ya nuna me kuma yake so? Ai ba aure tsakaninsu tunda mahaifiyarsa saki uku cir ya saka ya yi mata, ya yi hakuri ya shafa mata lafia
Ga wannan auren irin yadda aka shirya shi, kiri kiri matar Malan amarya ta yi haka ne dan a fasa a cikin dumbin al'uma, sai gashi an yi daurin auren da gaba daya kasar ta dauka ba iya garin ba , an aura mata mutun mai daraja da ganninsa in dai ba a jarida bane to fa kai tsaye dan kana gadarare baka isa ba sai dai idan mugun laifi ka yi wannan fa zaku jone ne ku yi zumunci na dogon lokacin da sai ka yi daka sannin aikata laifi a duniya!
Wadinnan abubuwan da ta hada waje daya ya saka ta yo watsi da komai ta shiga neman kyautatawa mijinta ta yadda koda auren watan ya yi to fa darajarta ba zata yi kasa ba, sai daima ta yi sama
Malan kam yana gama yiwa Hamza bayanin a tashi a ci abinci sukai ido hudu da NAHIDT dake kada kafafuwanta
Idan ba gezau idannuwansa ke masa ba harararsa ne NAHIDT ta yi bayan bai san laifin da ya yi mata ba, abin haushin dayan kuma kanta a bude yake tana ta kade kaden kafa jar yanzun bara rufe gashin kanta ba
Kai ya girgiza ya ka wajen su Aba da suka mike su uku
Abincin ya nuna masu , nan Aba ya yi yar daria yana fadin" Allah ya karra maka lafia ai gida yana cen cike da jama'a, ana ta girke girke abin ba'a cewa komai, ga baki sunna ta cigiyata da Hamza, yanzun zamu tafi da Abansu da Sire, Shima Sire zai je ne wajen MUHYIDEEN din dan a daidaita komai da wajen da za'a saka amaryar kafin yama ta yi, sai dai ina mai son fada maku a kaita da wuri gudun shigar duhu ka san cen anguwar basa bari a sshiga ko a fita da zarar duhu ya shigo sai yasu yasu"
Malan ya fahimta ya kuma gode, a nan ya taka masu bayan sun gama yin magana da Gogonninsu da kuma Hamza a kan maganar NAHIDT da zarar an sada SHUWWA da Fauziya dakunnansu su san yadda zasu yi da ita ta yarda ta koma gidan Aban Hamzan ko kuma ta tare gidan Fauziya kafin Allah ya fitar mata da mijin aurenta itama ta yi aurenta ta yi tafiyarta gidanta, domin ba zasu barta ta sake yin rayuwar zaman kanta ita kadai a gida ba
_________________________________
"Ka bari ka sauka ka huta haka mana son?, A kadan ma kusa minti ashirin ina irga gudun da kake a saman keken nan , ni da kaina na gaji sai haki nake yi bale kai" CHIEF OF ARMY dake dan zagayen keken da MUHYIDEEN ke sama a dakin Gym dinsa yana ta tukawa ba ji ba gani zufa ta gama wanke masa jikinsa gashi bashi da riga sai wandon da tsayinsa bai fi gwuiwarsa ba na gine dake jikinsa ya takarkare sai kikitu yake da keken motsa jiki irin katuwar nan har ya kai ta fara kikau kikau dan kamar wanda yake son gigibeta daga wajen da aka ginata ana sakata
Bakinsa ya dan tabe gannin ko ya nuna irin ya san yana wajen nan bayan du idan ya zo wucewa ta gabansa sai ya kalle shi domin ba'a rufe ido idan ana irin haka juwa ke kwasar mutun ta maka da kas
Dan murmushi ya yi ya ce" Da ka ji kunya idan aka ji yau da ni kake fushi MUHAY"
yanzunma bai ce da shi A ba hakan ya saka shi tsayawa a gabansa yana kallonsa ya ce" Meye laifin a ciki?, MUHAY tausaya mata na yi yarinyar abin tausayi ce, kai baka taimako ne?, Ka ga kar ka ilata kanka domin an sanar mon tunda ka zo nan ka shige baka kuma fito ba, karka zarta abinda zuciyarka ke iya dauka ka ilata kanka dan an maka aure, idan tsoronta kake ji ka saketa na yafe maka, ka saketa kawai"
Ido ya zarro yana kallon Father dinsa
Tukin da yake yi ya dakatar yana dantse lebensa na kasa da karfi da kuma mamakin Father
Wai me babansa yake so da shi ne kuma? Ba ya daura masa ba? So yake yi Kuma sai ya kashe shi ko me? Ya sani sarai baya son hayaniyar nan dan girman Allah yake yi masa?
Father ya dan duba agogonsa ya sake kallonsa duba da ya tsaya da tukin keken ya ce" Yanzun ni damuwatama ka ga yadda zaka fuskanci matarka ta gida ka fada mata ka yi wani auren a nan tun yanzu ka mata kishiya, ka san mata fa da tsanar kishiya, akoysu kishi sosai, to dai ka fada min zaka yi hakuri ka zauna da ita ko sakinta zaka yi? Sai na koma da sannin abinda zan fadawa iyayenta , rayuwa ce na tabata Allah zai bata wani mai jin kai, mai tausayi, mai son talafawa maraya, mai iya rike maraya da zuciya daya , mai .............."
"Dad please " ya fada a kausashe yana kallon Father da kallon dake nuni da na fahimci inda ka nufa
Sauka ya yi daga saman keken yana daukan tawul dinsa ya karasa wajen kujerar da yake zama ya zauna tawul din a rataye a wuyansa ya jimke hannunsa guda ya rike da dayan hannun a tafinsa yana kallon Father da ya karaso ya zauna shima a saman kujerar yana kallonsa
Furucinsa na nuni da ransa a cinkushe ya ce" Why zaka nuna idan ka isa da ni , irin a tsorace kake da abinda ka yin nan bayan kai ubana ne?, A kan auren mahaukaciya zaka nemi yin kuka dan zan sauta? Father idan ka wankan mari a lokacin ka ce in na yarda na furta mata kalmar saki zaka tsaba min kana tunanin zan kauce maganarka ne? Kennan dai ni maraya ne kuma dan iska ne ta yadda wanda nake kallo a matsayin ubana zai ce min in har bai kai matsayin da yake tunani da ni ba shikenan na aikata????????"
Ya karashe yana mai sake dantse lebensa yana saka idannuwansa cikin na Father wanda jikinsa ya yi mugun sanyi da tarin kaunar MUHYIDEEN a cikin zuciyarsa
Shi ya san yaron yana da tauri aman kuma yanada mugun laushi a wajensu
A hankali ya rike hannunsa yana kallonsa ya ce" I'm sorry Son"
"I'm sorry Muhay, u see idanma akoy taimako to akoy wani ikon Allah a cikin hadin nan, MUHAY lokaci daya na ji yarinyar ta yi min, na ji ina so ta kasance a cikin ahalina, ...... MUHAY kai yarona ne, ina sonka tamkar d'an da na haifa da cikina, mahaifinka aminina ne da bani da na biyunsa, mahaifiyarka yar uwata ce sannan iyalina, "
Dan saurarawa ya yi stll hannayensu a cikin na junna ya ce" Kai ka san da ba haka na yi maka ba da ka aikata abinda zai sake shiga cikin tarihin rayuwarka, ka san da mahaifiyarka ta fara tunanin ko namiji ne abokin dake birgeka a mu'amalar intim?"
Ido ya zarro yana dan ja baya kadan hadi da rintse idannuwansa
CHIEF OF ARMY ya sake riko hannunsa ya ce" Kar ka ga laifinta, babu abinda ba zata sakawa ranta ba, ni da kaina na fara tunanin fara nema maka na aljannu domin abin nan na damunmu, MUHAY a yanzu ya dace ace muryoyi na kiranka Aba, sannan muryoyi na kiranka mai gida, why zaka fi ba aiki mahinmanci fiye da zama da mace? Ka kuwa san irin dadin zama da mace ? MUHAY ko baka da lafia ne?"
"Ya Rab" ya fada da dan karfi yana mikewa hadi da ba Dad baya yana mai dafe gaban goshinsa da hannunsa na dama dayan hannun kuwa ya rike kugunsa da shi yana dan cicije lebensa na kasa wata matsananciyar kunya da girma da furucin Dad din nasa sukai masa a kwakwaluwarsa ba na wasa bane
Dan murmushi Father ya yi a boye zai sake yin magana MUHAY ya juyo da dan sauri ya ce" Dad plz na koshi hakanan, na dauka iya dauka plz ka idasa aikin Ladan Allah ya biya my father"
Father me zai yi banda dariya domin karfi da yaji a bayane MUHAY ke ture maganar baya so a yita
A nutse ya ce" Allah ya yi maka albarka, plz ka kwatanta zaman da ita ko yayane"
Shi dai tawul dinsa ya sake dauka da ya fadi ya juya da niyar barin wajen gaba daya a ransa yana ayana 'Waye zai zauna da wa? Mahaukaciyar? Macen da maza suka ringa gani sunna mikawa yan uwansu? Gaskiya ba matar aurena bace ku da kuka daura kwa dawo ku kunce abinku da kanku'
Father ya daga murya yana fadin" A dakin dake kusa da naka za'a sakata wancen baban cen duba da yana da komai ciki, Son ni mamakin da nake yi girman gidan nan walahi, kuma ima jinjinawa masu gyaransa sosai da sosai ace waje komai fari? Ai sai hypo ya ji jiki kulun"
Shi dai tafiyarsa ya yi yana sake ture haushin a kusa da dakinsan da aka ce za'a ajiye wancen abar, su dai suka sani koma a ina ne kansu ake ji daga su har itan, yana nan walahi abinda ya sani shine zai daura igiya ne ya daura kafafuwanta a sama kanta a kas as punishment koda kallonsa ta yi balantana shiga harkarsa!
Ajiyar Zuciya Father ya sauke a hankali ya furta" Ya Allah, ka sa yarinyar nan ta zamto cikon farin cikin yarona, Allah ka sa kar na ji kunyar hadin nan, ka sa ya jure ya iya zama da ita ya Allah"
*A GIDAN MALAN*
Kyan alkawari🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰☺️
Garabasa: Dukkan wanda ya biya kuddin ALKALAMIN KADARRATA yana da kyautar novels dina baki daya ciki harda na kudin in sha Allah🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰, ka yi min magana zan turo maka🥰🥰🥰😘😘😘😘😘💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 2️⃣0️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI