Showing 117001 words to 120000 words out of 226733 words
fahimci ba da ita ake damben ba, ita kuwa matarsa ba ta daina kallon hanyar da ya bi ba, wato a banzar bazara ya d'auketa? Ko ya ma kalli fuskarta kamar dai babu halittarta a wurin? Me kenan?
Uwar gidan Father ce ta fara k'are mata kallo kamar ta fashe da dariya sannan ta juya ta bar su nan, Umma ma mik'ewa tayi tsaye ta kalleta tana share hawaye, wani murmushin mugunta ta mata tace "Kin gani ko? Ke da banza duk d'aya, gwara ma ni tunda na samu alfarmarsa, kuma baki ga an min auren ba tukunnan, komai na iya faruwa tunda bai cikashe ta hudu ba "
Wata dariya ta bushe da ita ta wuce ta barta nan tsaye, haushi, takaici, bak'in ciki duk sai ya nemi halakata daga tsaye, a gaskiya ba dan ba dan ba sai ta ce Muhyeedeen bashi da mutumci, yanzu ita ya watsar haka? Ka rantse da Allah bai tab'a ganinta ba sai yau, ai ko yau ne had'uwarsu ta farko ya dai kalleta dan ya ga yaya kamanninta suke, sannu a hankali ta fara ji a zuciyarta anya kuwa ba za ta taya gayyatar da ake mata akan farautar rayuwarsa ba? Dan inhar abinda ta gani yanzun zata iya kiransa da kishin amaryarsa yake, to fa kenan ita za ta tashi a tutar babu, da kuma ta rasa shi wallahil azim gwara kowace 'y'a mace a duniya ta rasa, ba za ta jura ba ko kad'an, a sukwane ta nufi na ta b'angaren tana share k'wallar da suka taru a idonta tsabar b'acin rai ga na dakuwa da aka yi jiki duk ya jijjiga
Murmushi babar Ummie ta yi tana girgiza kanta ta juya ta koma dakinta tana neman wayarta dan kiran gidansu, domin ita abinda ya dameta daban sai ta ga ashe su shirme ne a gabansu
Suna shiga d'akin baccinsu ya tura k'ofar ya jefata ciki sannan ya shiga a matuk'ar kausashe yana nunata da yatsa yace "Menene na fita waje a haka? Akan wane dalili ne nan ma sai kin sanar da kowa wacece ke? Hijab d'in ya b'ata ne ko kuma hannayenki ke ciwo da kika gagara sakawa?"
Tsatsareshi tayi da ido tana kallonshi da yanayi na tsoro da mamakin me kuma ta aikata ita? Ta ga dai ai ba da ita ake fad'an ba ko? Katse mata tunani yayi ta hanyar wata tsawa da ya mata yace" Ke! Wallahi idan na k'ara ganinki haka ko..."
Kwafa yayi mai k'arfin gaske tare da d'orawa yace" Ina zaman zamana tashin hankali ke ta kawo min farmaki kuma duk a dalilinki, tunda kika shigo rayuwata d'abi'ata ta shiru ke neman barina, a da na kan iya k'idaya adadin kalaman da nake furtawa a wuni, amma daga sanda kika tunkaroni komai....ya lalace min, ba gaira babu dalili ki dinga sakani ina tafasa, me nai miki, ke ko kece babar maciyar dake sarata kina nokewa ne? Na kula raina kike so karfi da yaji wani ya aiko ki ne? Ke azaluma ce?"
Tafin hannunshi ya saka ya rufe bakinshi har zuwa hancinshi ya dinga sauke numfashi a k'alla sau uku sannan ya d'auke a sanyaye kuma a nutse yace" Na gaji, na gaji da wannan firgici, ba zan iya da wannan tashin hankalin ba, gwara kawai kowa ya kama gabansa daga ni har ke din kin ga na..."
Hankali tashe Mama ta banko kai d'akin cike da tsoron furta kalmar da zata sakata sadda kai a gaban yaran da ta fara gani jiya jiya, cike da muryar k'aguwa tace" Kul! Kul Muhay, kar ka kuma furta wani abun bayan wanda ka fad'a, ya isa haka, yanzu fita anan, fita kawai"
Yanda ya zuba mata ido kamar baya gane yarenta yasa ta d'an d'aure fuskarta ta nuna masa k'ofa tace" Fita na ce, zan sameka yanzu "
Cike da tsoron lamarin da rawar murya Shuwwar ta matsa kusan Mama ta rik'o hannunta gam kamar za ta fashe da kuka tace" Mama, ai kinsan ban yi komai ba ko? Ni ba da ni ake fad'a ba, ban ga abin..."
A tsananin tsawace wanda har Nahidt dake k'ofar d'akin sai da ta razana ya juya tare da d'ora yatsarshi a baki yace" Shiru malama!!!"
K'am ta sake rik'e hannun Mama tana shigewa jikinta dan ba iya dodon kunnenta ya fasa mata ba har da hantarta ya tarwatsa da kad'uwa, Mama kanta saida ta rintse ido tana salallami dan ta san kam zuciyarta ta taso, ita dama tasan tunda ta ganshi garin nan bilhaki fitina yake nema.
Basu bud'a idonsu ba sai da suka ji ya banko k'ofar da mugun k'arfi, a tare suka kalli k'ofar sai kuma Nahidt da ta shigo da mamaki tana sake waigawa tana bin inda ya wuce da kallo.
Murmusawa Mama tayi dan kar su fahimci damuwarta ta d'ago d'aya hannunta ta shafi kuncin Shuwwar tace " Y'ata, karki damu kan ki kin ji, ku je yanzu ku yi wanka ku fito za mu ci abinci, idan mun idar sai mu shiga kasuwar ko?"
A hankali Shuwwar ta jinjina kanta ta saki hannun Mama, cikin dattako ta fara takawa dan barin d'akin, da kallo suka bita har ta fice wanda hakan yasa Shuwwar sakin wata nauyayyar ajiyar zuciya tana fadin" Allah ga marainiyarka nan dai gareka, Allah ka hanna shi karya ni, idan ya karya ni Nahidt aurenta zata yi ba zata yi jinyata ba"
Sai a lokacin Nahidt ta zarro ido da gudu ta nufi wajen wayarta da ta kashe sakamakon mesage din da Malan ya turo mata wanda ya sakata jin matsananciyar kunya da tunanin dama bata da hankali? Ta dauko tana kunnawa da fadin" Allah rufa min asiri kar ya gaji da wulakamcina ya fasa"
(😂😂😂😂😂😂😂😂 Da mun shiga uku mu ahalin gidan ALK'ALAMIN KADARATAH)
________________
Indai ya ce zai zauna a gidan wannan lokacin to tabbas yau sai an yi b'atacciya, dan haka ya karb'i makullin mota a hannun wani soja ya figi motar bak'a k'irar crv Honda ya fita a gidan, saida ya fita ya kad'a kan motar zuwa babban titi dan da fari bai san ina ya nufa ba, tafiya kawai yake kamar ya zumduma ihu ko ya ji dama dama, sai ya ji komai cakule masa yake, wata sabuwar d'abi'ar da ba ta sa ba ke son shigar sa ko kuma yace yake son ara, shin hakan na da alak'a da shigowar yarinyar nan rayuwarsa? Ko kuma dai sanin mai kawo masa farmaki kuma kunya da kawaici yasa yake d'aga masa k'afa ne ke hadasa masa haka?
Gijimmm! Wannan sautin ya shiga kunnuwansa yayin da nisa da yayi a tunani da b'acin rai ya haddasa masa had'ari, da mugun sauri ya taka birki ya bud'e motar ya fito a sukwane hankalinshi kuma a tashe, duk da yasan hankalinsa baya wurin amma kuma komai zai iya faruwa, ba zai ji mamaki ba idan har aka ce masa wannan had'arin zai iya zama tarko na masu bibiyar rayuwarsa da son ganin bayanshi, amma haka ya dake ya sunkuya kan matar da zai iya kiranta dattijuwa tunda ba yarinya ba ce ko a fuska.
Maida hankalinshi yayi ga k'afarta dake fitar da jini amma sai k'ok'arin gyara gyalenta take tana son mik'ewa tsaye, a nutse tare da saka Allah d'aya a gabansa ya kai hannayensa biyu ya dafa kafad'unta cike da kulawa yace "Mahmah, sannu, dakata fa kin ji ciwo."
Kamata yayi ta mik'e tsaye tare da juyawa kan wata tsohuwar robar da ta jik'a saiwar magani a ciki, ruwan da babu a wurinsu yasa ta fito nema da k'yar ta samesu a wani gida nesa da su sosai saboda ba kowa ke da yarda mutum ba yanzu musamman su da ke cikin wani mummunan yanayi.
Ganin robar yashe ruwan sun watse haka ma maganin yasa hankalinta tashi sosai ta dinga nuna robar tana hawaye tana fad'in "Sun zube su ma, sun zube ko? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Yah Allah , Subhannalah Subhannalah" ta katashe furucinta na kalkaltu kadan haka idan ka ji dai maganarta zaka fahimci ba bahaushiya sak bace
Kubcewar da take ta son yi zuwa ga robar yasa shi k'ara dafe kafad'unta yana duban k'afarta dake ta fitar da jini yace "Mama ki kwantar da hankalinki ki nutsu, muje na kai ki asibiti."
A d'an razane ta juyo ta kalleshi tace "Asibiti? Ni zan je asibiti? Ka ga Yana can fa zai mutu, yau abin ya fi na da ban da sukuni idan ban je na same shi ba, mutuwa zai yi, mutuwa zai yi haka yake cewa idan bamu tafi ba mutuwa zai yi "
A hankali ya k'ank'ance idonshi yace "Wa ye zai mutu Mama?"
Nuna masa bayanshi ta yi, a nutse ya juyar da kansa bai ga komai ba sai filin dake wurin da kuma wata bukka da zai iya cewa ya hanga a d'an nesa kad'an, sake juyawa yayi ya kalleta yace "Mama me ye a can d'in? Wa ye zai mutu?"
Fuskarshi ta kalla da idonta da sukayi fari fat tsabar rashin saka kwalli sai d'an sirkin ja da suka fara yanzun na hawayen da take, cikin nu💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 4️⃣0️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
*DA SASAFE KAFIN KI CI KOMAI KI SAKA TAFARNUWA KWAYA UKU A CIKIN COKALI KI LULUBETA DA ZUMA KI CINYE SUMUL SAI KI YI BROSH......KARIN NI'IMA NE*
A tausashe da rikaken yaren buzancinta ta ce" *"Elishe jehadine itamatak, yara atunaso agrawadah, tunane tuta wulih*"............. Da sauri ta dafe gaban goshinta ta kuma dauko harshen larabci dan ta tabata ba gane yarenta zai yi ba, yanzunma a kidime ta ce" Subahannalah , *Innahu zauji, sa ya mutu hunaka, alaina an nazhab, laqag intiqalal yaum*"
Sai kuma ta yi kwalkwal da idannuwanta tana sake rike damatsunnan hannayensa domin ya dafata ne yana kallonta a wani rikicen wannan karron da yaren turancinta gangariya ta ce" *My husband, he is dying,he said we have to go,His condition is critical* "
Sai kuma t samu kanta da yin shiru na dan lokaci tana kallonsa, kamar kurma, ta rasa gane yana gane yarenta ko baya ganewa? Wani yare ne shi? Me yake ji? Kwata kwata ta manta da yana mata maganar zai kaita asibiti, kai tama manta da wani yare ne ya yi mata magana, yanzun ta dauki yaren karshe da fatan Allah ubangiji ya cidata ya ganeta a raunane ta ce " *Mijina ne, gayacen zai mutu, wai sai mun tafi, yau abin ya tashi sosai*"
Ta cika shi ta hade hannayenta ta ce" Ka barni na koma gare shi, ta yiwu idan na bashi maganin ya koma barcin"
Sakinta ya yi yana kallonta a lokacin da ta sake rage tsayinta sosai tana dafe gwuiwarta ta kwashe sauran magungunnan nan ta maida cikin robar irin ta almajiran nan ta sake juyawa ta komaa wajen da ta nunaa masa tana dingisawa haka kuma jinnin na diga a kafarta domin ta bugu sosai, aman abin mamaki ba buguwarta ce a gabanta ba, hasalima fama take ta karasa wajen da tai masa nuni
A hankali ya ringa juyawa yana karewa wajen kallo kafin ua sauke ajiyar zuciya ya nufi wajen da ta bi aa hankali
Sai da ya shige wajen sosai sannan ya saka hannunsa ta bayansa ya ciro bindigarsa a hankali yana sake kusanta kansa da wajen yana hankalce da yannayin wajen
Shi kam bai ga komai na suspect ba, hasalima wajen shirunsu ya yi yawa sosai
Sai da ya karaso ya dan saurara kunnansa ya dan hada kunnen nasa da jikin zanar yana sauraro
"Ki kunceni babu inda zan je , ki kunceni mu gudu kin ji, ki kunceni bakya jin zafin da nake ji ko? Zafi nake ji a jikina kamar zan mutu, gaba daya duniyar nan garin mai zafi ce, so nake na ji na tashi sama na gudu, mu tafi so nake na tafi"........... Muryar wani namiji ke fada a rikice kamarma kokowa suke yi da matar
A hankali ya samu ya dan daga rufar buhun da aka yi a kan kofar, hakan yaa tsorata su gabaa dayansu, saima ya kasance namijin ya fi macen tsorata domin gaba daya ya nemi cumuimuyeta a cikin abin rufar da take lulubi da shi
Jikinta na rawa itama cike da tsoron kar dai asirinsu ne ya tonu haka take kallon MUhay
Shima dan bukar tasu yake bi da kallo, wace da gani baa sai an fada ba wanda ya yi bukar nan ko macen ce ko kuma wani ne da bai iya ba domin abin a jirkice yake gaba dayansa
Irin robar da ta zo da su ne biyu ajiye kowace ba komai a ciki, haka kuma a dakin ba komai daa zai nuna maka sunna dan samun na ci a bakansu ko yayane
Ba abin sallah, kai datin dake tare da su din nan anya ruwan alwallah na hawa jikinsu kuwa?
Sake maida kallonsa ya yi jikinsu yana mai tabatarwa kansa cewa hali ne na rayuwa ya mayar da su haka, dan haka sai ya samu Kansa da fitowa ya tsaya yana sake kallon Wajen ya dora numbobin ambulance tasu ta sojoji ya danna kira
Magana ya yi a takaice daa kwatancen hanyar ya fada cewar zasu ga motar dake dauke da number CHIEF OF ARMY a wajen sai su masa magana
Dan zagaya wajen ya ringa yi yana hankalce da matar nan ta leko da sauri kuma ta yi wuf ta koma dukan alamu na tsoro na tatare da ita, haka kuma muryar mijinta duda a shake take kuma a kasa take sosai aman ta karra amo yana ta ihun dake nuni a tsorace yake shima, hakan ya saka MUHAY a matsanancin mamakin abinda ya tsorata su dan sun ga mutun ya rabe su haka
Motor ta karaso tana jiniya irin na ambulance 🚑, da gagawa suka fito , likitoci ne uku sai soja biyu, a cikin likitocin kuma harda mace daya wace ta hau yau itama sojan ce
Sai da ya yi dan tsam kadan kafin ya juya wajen da dakin yake
Ky din motar da ya fito da ita ya mikawa daya daga cikinsu ya masa umarnin ya bisu da motar , sannan ya saka suka fitar da gadon tura marar lafia suka nufi dakin, kowane cikinsu na mamakin waye ba lafiya a nan?? Me ya kawo Lieutenant Ganaral nan?
Bai tsaya wata wata ba ya yi salama kasa kasa ya shige
Yanzunma a cure suke waje daya sun yi tsuru tsuru
Hakan ya saka shi bada damar a dauke mijin nata da ita din kanta a shiga motar da su
Zo ka ga dambatuwa, domin yaki ta shiga yi ba ji ba gani tana sambatun kalaman da basu gane makamarsu ba, fada take yi ba ji ba gani tana doke doke ido rufe kan ba zasu tafi da su ba
Hane hakan da suka yi sai suka fi bada hankali kan mijin suka gigibe shi suka dora saman gadon nan
Kwarai sun yi tunanin samun zaurin fitsari a jikinsa, sai dai du uban datin nan na jikinsa karnin dauda ne kawai ke tashi a jikinsa irin mai saka juwar nan, haka itama matar
Sunna fara tura gadonsa a hankali ta ringa binsu dan kanta tana kallon yadda aka daure shi a jikin gadon watau hannayensa da kafafuwansa fan kar ya fado ya raunata kansa ko ya yi ta doke doken da zai raunata kansa
Tsananin tashin hankali ya saka ta fara gannin dishi dishi
Tsoronta Allah tsoronta kar tafiyar da suka jaba kafin su yi nesa da garin ne ta tashi a banza yau tsal aka gano inda suke, tausayin mijinta da halin da yake ciki ya fi karfin tunaninta
A hankali take jan numfashi tana sake bin motar har suka kusa karasawa sai kuma luuuuu ta tafi da niyar jirtuwa a kasa sakamakon sumewar da ta yi
Dama a daf da ita yake, tunda aka fito da mijin yakr hankalce da yada take layi, ga kuma kafa tana ja da kyar, kasantuwarsa tsoron ma'aikaci da ya jima yana damawa da mutane kala daban daban ya saka shi gane cewa abinda ya koro kura daga raminta ba karamin balaki bane, hakan ya sa yake ji a ransa ya zama wajibi ya mika su asibiti sannan ya san su waye su, ba kyankyamin datin jikinta da warin da take yi ya talabe faduwarta kasa ta fada a jikinsa ya cicibeta yana hanna likitar da ta zo dan amsarta, amsarta ya kaita cikin Ambulance din suka saka gadon nasa sannan suka rufe direban ya ja motar su kuma suka shiga kokarin fara fahimtar damuwar mutanen harma suka farfado da ita tun kafin su karasa
Sunna karasawa suka shige da su ciki
Da gagawa likitoci suka shiga basu dukkan kulawar da ta dace da su, da gwaje gwaje kala daban daban ciki harda na su HIV,