Showing 135001 words to 138000 words out of 226733 words
kuma a irin wannan lokacin ya kula ta samu tabuwar hankali
Sai da ya gama duba ko'ina kafin ya rufe ya fice da ky din falon ya nufo bangarensa dan shima yana so ya cenza kayansa
Ta jima a dakin nata sai da ta gama shiryawa cikin bak'ar abaya da nikaf dinta a hannunta, da kyar ta iya fitowa daga fakin dan wata irin kunya da tunanin yaya zasu iya hada ido da shi ya hannata fitowa kanta tsaye har sai da ta ga lokaci na karra tafiya gashi ko karri basu yi ba sannan ta iya fitowa daga dakin nata
Tunda ta fito kanta sade ta nufi wajen table din da aka jera abinci
A hankali taa ringa bubudewa tana dubawa, har sai da ta gama gannin wanda zata tafi da shi sannan ta shiga warewa gefe tana dan satar kallonsa
Gannin tamkar bai san da ita a wajen ba ya sakata sauke ajiyar zuciya ta dan saki karinta harma ya ware plat ta zuba masa abincin ta dauki ruwa ta dora ta karasa ta ajiye masa ta mike ta yi cikin kicin din dan dauko abinda zata zuba abincin
Da ido ya rakata har ta bacewa ganninsa kafin ya maido idannuwan nasa kan abincin
A hankali ya samu kansa da jin mararin cin abincin domin ba yinwar bace baya ji dama, hakan ya sa ya dauka ya shiga dan ci yana kuma hankalce da shige da fitarta da irin kayan da ta jibgo tamkar wace zata kaura asibitin ko a tunaninta zasu barta ta kwana a cen ne?
Bakinsa ya tabe bai ce komai ba, ya dai kula tun dazu bata kuma kallon fuskarsa ba, bayan ita din ba kunya ce da ita ba, bale jikin nata yau aka fara ganninsa ne ba komai a jiki da zata ringa masa wani iya yi? Dadin abin shima kamar yadda ya rike kansa shekara da shekaru a gaskiya ba zai yarda yar hannu ta bude shi a ledarshi ba, gaskiya sai sabuwa.....a kai kasuwa baya so!
Bayan ta gama daga inda take tsaye a kusan table tana hangensa dan bai gama cin abincin ba ta afka a duniyar tunani, shin a ina ya gansu?, Yaya aka yi ya gane sunne? Ya sanmu ne? Dama yana iya gannin mutun ya taimaka masa?, Dama soja na taimako ko menene ? , Tana ta tunani da sakar zuci har ya gama ya mike ya fita, kafin ta gane ta tabe bakinta ta fita ta kirawo masu aikin Maman sauka dauko mata kayan sannan suka fito ta rufe bangaren tanaa sakawa a yar jakarta sukai ido hudu da matar da aka yi dambe da ita jiya a matsayin matarsa
A hankali ta cire dubanta a kanta tana maidawa bakin hanyar da zata bi ta yi gaba, abinda ya tsaye mata a rai irin abinda ta ji a kan matar wanda ta rasa gane me ta yi mata ita kuma da ta ji haushinta haka?, Sai dai ta ajiye hakan a irin kallon wawancin da matar ke yi mata, dama ita ta tsani irin kallon nan sosai, dan bata ga anfanibsa ba gaskiya, kallo kamar na mahaukata a tsareka da ido har a saka ka fadi?
Da wannan suka koma asibitin, yana ajiyeta ya yi tafiyarsa wajen aikinsa, ita kuma tana dawowa Nahidhma ta tafi ta kimtsa din ta dawo , hakama Mama, wace suka dawo da mijinta domin sai da ta koma ta tarda ya dawo kuma yana ta kiranta wayarta a gida hakama MUHAY ya shige cikin aiki tasa bata tare da shi , a dole ya yi jiransu domin mutan gidan sun nuna su basu san inda suka je ba
Ai kuwa tana yi masa bayani al'ajabin abin ya kama shi, bai yi kasa da gwuiwa ba ya biyota suka koma tare, suka samu yan matan a nan suka wuni abinsu ga abincinsu a gefe da abin sallarsu
Shi ya fahimtar da su ko zaman nan da suka yi ya tabata dan MUHAY ne ya kawo su, domin asibitin nan basa bari ka yi sama da minti talatin a ciki, da zarar ka zo ka ga marar lafiyanka to fa sunna kwatanta maka cewar ka tafi, domin su aikin da suke basa son wannan shige da ficen, Idan wani abin ya taso dole zasu nemeka, aman a yanzu ka basu dama su kula da marar lafiyanka yadda ya dace,
Sunna nan MUHAY ya dawo tare da yarensa uku
Sun shigi sun gaisar da su Mama suka ajiye kayan dake hannayensu suka juya, a nan suka sake gaisawa da Father da MUHAY
Sai da ya je ya gama bayani da likita sosai ya sake jadada masa ba zasu kwana ba , sannan ya dawo ya kwatantawa Mama ya yi masu salma ya yi tafiyarsa gida
Da rarashi, da ban baki su Dad suka fahimtar da su kafin suke iya binsu zuwa gidan
Ko da suka koma gidan kadaice kawunnansu suka yi sukai kuka tsakaninsu bayan sun rungume junnansu
Nahidt a tsorace ta ce" Shuwwa, iidan Mama ta san na yi karuwanci ina tsoron idan wahalar da ta mayar da ita haka bata kasheta ba wannan maganar ta kasheta"
SHUWWA ta girgiza kanta a sanyaye ta ce" Ba zata kasheta ba, da izinin Allah ba zata kasheta ba, sai dai tabas ranta zai bace, kuma kin san cewa daga ita har Abui sun nuna mana soyaya aman ba wai sunna kyalemu bane idan har muka yi abinda zasu horamu, shi yasa a kulun nake ce maki, ki fa ji tsoron Allah ki daina, to kin ce Allah zai yafe maki a yanzu kin daina kina nemansa gafara ba ji ba gani, itama zata yafe maki in sha Allah....."
Da wadinnan hirarakin suka yi dare sosai kafin kuma su zarce da nafilolinsu sannan suka cude waje daya suka yi barci
Tunda sasafe suka wuce asibiti, yau harda matan Dad su biyun dukansu domin a jiya da dare yake fada masu cewar su je su ga narar lafiya, iyayen Matar MUHAY ba lafiya
Kowace da tambaya a ranta , sai dai kasancewar bai bada damar hakan ba sai kowace ta rike abinta suka kuma bi motocin suka je duba su,
Uwar gidansa da wuri ta dawowarta, mai dakin tsakiyar ce ta zauna ta dan jima kafin itama ta tafi , babu wada ta ga mararsa lafiyan haka suka je suka dawo
Sai kusan karfe goma aka basu damar gannin iyayensu na tsayin mintunna talatin, aka shaida masu cewar baci suke kar su yi hayaniyar da zasu iya tashinsu a barcin nan fa, kafin aka barsu suka shige
Su dukansu sun kasance ne a tsaye a gaban gadajen iyayen nasu da kauna da soyaya, da hawaye irin na soyayar iyayen nasu da tausayin abinda ya mayar da su haka
Daya bayan daya suka je suka gansu sannan suka dawo dakin da aka ware masu
Daidai ana kiran sallar azahar a cikin asibitin, ya kasance cikin gari har sun yi salolinsu , a daidai lokacin ne kuma summa suka fito dan gabagar da alwallah a cen wajen pampunnan balbalin asibitin dan ra'ayi
Motarsa ce ta dano kai, ba tare da yan tsaro ba, domin sai da ya sauka a wajen aiki ya je ya dauko Malan da ya sauka shima yanzu yanzun
Tunda suka fito a motar suka gansu, haka suma,
Malan na sanye ne da gari da yar ciki, ya kafa hularsa a kansa hannunsa rike da carbinsa fari kal , haka kuma kafarsa sanye da taklmi sau ciki bakin kirin
MUHAY kuwa yau kaki ne gaba daya a jikinsa babu bambanci sama da kasa hakan ya sa yau ya karra cika sosai yake cika ido
Dan tabota ta yi ta sake nuna mata shi, hakan ya sa gabanta sake balewa ya fadi, kuma abinda ya fi saka su kure su da ido shine kamar wa'inda aka dakatar da su bayan sun baro wajen motar kowane na kallon yar uwarsa
Malan ne ya dan kula da yannayin MUHAY, sannan ya tuna cewa shi fa sirikin MUHAY ne kar bege ya saka su mace su lalace a gaban yan yara guni guni haka, hakan ya sa ya dan yi gyaran murya da dan baza babar rigarsa ya daga kafarsa ya shiga gaban MUHAY din irin da karfin halin nan, irin ai shine baban baba a wajen nan dai kau?
Turus ya yi sakamakon gannin NAHIDT ta taho da dan saurinta, sannan ta dan wara hannayenta, uwa uba ta fashe da tabararen kukan da nan take shedan ne? Ko kuma banzan tunaninsa ne? Ya sheda masa cewar idan ta karaso wajen nan babu abinda zata aikata sai rukunkume shi a cikin bainar nasi, a irin wannan rana da ya dauki azumi , sannan ya zo a matsayin siriki watau mutumen da ya dace har ya bar wajen nan ana dubansa da daraja da mutunci, sai dai kasshhhh, wannan lamari da ya fuskanta ya saka shi jin kamar cikinsa zai juya masa
Yanzun fisabililahi wannan aikin na adalci ne? Da girmansa da darajarsa?
Ba shiri ya dan tatare babar rigar da sauri ya zagaya ya labe a bayan MUHAY dake kallon ikon Allah shima yana jira ya ga wai me zata yi ne haka?
Yana labewar da yaren larabci ya ringa maimaita kalmar sunnanta yana girgiza kansa yana lekenta har ta karaso da mamaki shinfide a saman fuskarta ta ce" Yah habiby yaya haka?"
Ido ya dan rintse dan hanna zuciyarsa fitowa, a hankali ya ce" Yah khalb me zaki yi ne?"
Muhay bai taba jin abinda ya tuko masa dariya ba shiri ba irin na wannan ranar, a hankali ya dantse lebensa na kasa ya baza idannuwansa yana kallon soyayar larabawa a lokacin da Shuwwa ta kyalkyace da dariya har tana dukawa tare da dafe cikinta tana kallonsu, daidai Doctern nan ya fito nurse na rike da takardunsa ga dukkan alamu gida zai je ya hango Shuwwa a duken nan tana kyakyata dariyar nan , hakan ya saka shi sakin murmushi yana sake kallonta kafin ya samu akalar tafiyarsa da juyawa yana nufarta , hakan kuma ya sauka a kan idannuwan MUHAY wanda shima ita din yake kallo harda bin mayafinta da ya fadi dan dariyar ketar da take yiwa Abanta da ya labe, hakan ya bayanar da gashin kanta da yau ta dan caje shi ta saka masa dan ribom, sannan ya sake maida dubansa kan likitan nan dake karasowa daidai NAHIDT ta budi baki tana leken MALAN da ya labe kansa da kafarsa baya so su yi hadewar nan da ta zo masa a kwakwaluwarsa da azuminsa a bakinsa ta ce"ALKALAMIN KADARRATA
PAGE
Na
Sajida
4️⃣7️⃣
*ZO KI JI, KE DAI DAMUWARKI RASHIN SHA'AWA ? KE TUNDA AKAI MAKI AURE KIKE FAMA DA SHI? KIN RASA GANE KANKI?, KE KAWIAI KALLON MUTANE KIKE DU KIN RAME KIN TSOTSE SABODA BAKYA SON ABINDA AKE MAKI MAI SUNNAN JIN DADI?, KE KUMA YAR UWA TUNDA KIKA HAIHU KIKA HADU DA WANNAN DAMUWAR, WATAU TUNDA AKAI MAKI AIKI KIKA RASA WANNAN JIN DADI DA KIKA SABA DA SHI KAFIN AI MAKI AIKIN??????, MAZA JE KI KASUWA HARHADO KAYAYAKI KAMAR HAKA : SOBO JA, GIMJIMBER, QUATRE CÔTÉ, POIVRE SELIM, da Copin ruwa biyu ( ku yi hakuri duk mai so zan turo mata da hotunnan abin domin ni ban sansu da hausa ba gaskiya, ko ku dora a google za'a baku su)....... Zaki hade su ki dafe su gaba dayansu ne, sai ki ringa sha karfe daya kafin lamura su kankama, ko tun da magariba................... Itatuea ne basu da wata matsala, idan kika ga lamuranki sun daidaita kina ita dakatarwa..........*
Ta ce" Ya habiby, me zan yi kuwa? Zan fada maka ne irin halin da Abanmu yake ciki da mamanmu fah"
Kansa ya dan girgiza ya ki ya fito din,
MUHAY dake ta binsa da kallo har ya karaso gannin Nahidt ta dan kare masa sai ya daga kafafuwansa da kyau ya matsa masu ya shiha takawa ya karasa wajen da take kyakyata dariya daidai lokacin da docter ke fadin" Dariya ta fi kayatar da fuskarki yar budurwa"
Da sauri ta dago dubanta kan docter, shi kuma komai ya sauka a cikin kunnayensa
Bai ce komai ba ya dan rage tsayinsa ya mika mata hannunsa na dama hakan ya sa ta juyo da wani saurin tana kallon fuskarsa
Gannin fuskar tasa a hade ba alamun ya taba yin dariya ta saka hannunta a cikin nasa, ya cicibeta ya mikar da ita sannan ya jata suka nufi ciki ko kallon likitan dake kwatankwacin abokinsa bai yi ba dan takaicin yarinyar
Yana shigowa da ita ya saki hannunta yana kallonta ya nunata da yatsarsa daya ya ce" Ki kula, kina wasa da igiyar dake wuyanki bayan har yanzu bata tsinke ba, ki kiyaye ki iya bambance igiyar aurena da ta sauran banzayen da kika aura, abayoyinki da hijabanki gaba daya munafukan abin lulubi ne, ban san a kan wani dalili kike son rayuwa irin ta bude jiki!"
Ya karashe a kausashe yana dan juyawa ya dafe gaban goshinsa hadi da rintse idannuwansa ya ce" Kin ga, me zai hanna ki rufawa kanki asiri ki kama mutuncin kanki ne? Har hanyarmu ta rabu da ke?"
A hankali idannuwanta dake kallon kasa ta ringa dagosu har ta sauke a saman fafadan bayansa da ya bata baya
Kalmar har hanyarmu ta rabu ta ringa maimaitawa a kasan zuciyarta har ta samu ta gane ma'anarta
A hankali ta sake wara manyan idannuwanta a saman bayan nasa daidai lokacin da ya juyo ya sauke dubansa a saman fuskarta
A nutse yana kallon fuskar tata da furucin dake karyata abinda yake son fada, domin ya dace furucin au fito a kausashe da ihu, sai dai gaba daya ya same su da sanyi a gareta yana kallon fuskarta ya ce" Ki yi kokari, ki koyi kilace kanki, ita mace daraja gareta, banzatar da kanta idan ta yi ba shine zai sa a ga kimarta ko a ga kyanta ba, ki kiyaye hulda da kowani namiji har ki samu yancin kanki....."
Ya karashe maganar, aman kuma fuskarta yake kallo sosai ya matse mata waje sosai
A hankali ta ringa hadiye dukan abinda take ji mai kama da tsoron jin furucinsa
Menene a ciki? Kar ta manta itama baban burinta bai fi ya sawake mata ba, da farko shi din ba zabinta bane, na biyu shine mutumen da ya wulakantata ya raba mata aurenta, na uku soja yake, wanda bata so ko a hanya su hadu da junna, so meye a ciki?
A hankali ta dan sakar masa sasaukan murmushi tana dan kawo hannunta dan ta tare kirjinsa domin ji take kamar kirjin nasa zai hade goshinta ne irin ya maki goshinta ne
A dan sanyaye ta furta" Ba damuwa........"
Daga haka ta juya ta nufi ciki wajen Mama dake zaune tana waya da yar uwarta tana sheda mata an rike iyayen matar MUHAY a asibiti tun jiya ta mata whatsup ta ga ta bude aman bata ce komai ba?,shine take ce mata ta kwontar da hankalinta yanzu haka ta kusa shigowa asibitin ta taho ai
A hankali ta zauna a gefen Maman tana lumshe idannuwanta
Baki ta tabe a kasan zuciyarta tana ayana' Irin gashi dan gwal din nan, to a kaina za'a fara ko a kaina za'a rufe? Dama me zan yi da namiji irinka?, Allah na tuba na dangana da masu nunan so ma bale mai nunan kiyaya? Kai zanma rokeka ka sakeni da wuri dan na samu wanda zai iya soyaya ba halaya na kiyaya ba!'
Shi kuma a lokacin da ta yi gaba da ido ya rakata har ta bacewa ganninsa kafin ya samu kansa da jan wani dogon tsaki ya juya ya fita ya nufi hanyar da zai iya gannin likitan cen, ya kuka dakiki ne ashe? Ya nuna masa a jiya ashe bai gane ba? To ya bari idan ya saketa sai ya nemeta, aman a yanzu ta fi karfinsa walahi!, Baban abinda ya fi bashi haushi da yarinyar girman kai da nuna ita wata ce, to in takamarta kyau sai ta baza ido ta ga irin matan da ya ringa aura yana saki, dukawa suke yi har kasa sunna kukan ya dawo da su ya kiya, zata yi bayani ne!
Sai da Aban Shuwwa ya samu wajen da ya tabata akoy al'uma dake yawan kai kawo kafin ya iya samun nutsuwar fuskantarta yana murmushi ya ce" Bismillah me yake damun amaryar Muhammad ne?"
Dan murmushi Nahidt ta yi tana dan kawar da kanta dan har ga Allah ta ji kunyar abinda ya fada , sai dai ita bata so ya gane ta ji kunya dan haka sai ta juyo tana fuskantarsa ta ce" Aban Shuwwa a tunaninka a nan din ba zan iya rukunkumekan bane hala?"
Ido ya zarro yana dafe bakinsa ya yi gagawar fadin" Astagfrullah, subahannalah, yah Nahidt ya dace ki karra rike istigfari a dukkan motsinki, sannan ki guji aikata aikin da bashi da kyau komai kankantarsa, fisabililahi wannan aiki ai bashi da kyau, gashi ni azumima nake......"
Murmushi ta sake sakar masa ta gyada kai , kafin ta yi yannayi na hankakinta ba a kwonce ba ta ce" Muhammad, ka san wani abu? Abanmu anya ba ya haukace ba?, Ka ga jiya kafin likitoci su saka shi a cikin barci daga inda muke muke jiyo muryarsa yana ihun shi a fitar da shi daga kasar nan, subahannalah gaba daya tamkar ba mahaifinmu ba mutun mai nutsuwa da izza a jikinsa, mutun mai tarin kamala a tare da shi, a yanzu haka tun barcin nan basa bari ya yi doguwar farkawa domin da ya farka hakan yake ambata......" Ta karashe tana mai sadda kanta
Shima dan tsura mata ido ya yi kafin ya girgiza kansa ya ce" MUHYIDEEN ya ce yana tsantsamin sihiri, idan kuwa aikin sihiri ne in sha Allah zamu samu kansa kin ji? Ki kwontar da hankakinki zamu je na gani idan har