Showing 150001 words to 153000 words out of 226733 words
kennan da ya daina masu anfani da maganin dogon barcin da yake yi masu, domin su dukansu cikin ikon Allah jikinsu ya yi yadda yake so, balema namijin a yanzu baya kubtayar nan, sai dai shirunsa ya fi maganarsa yawa, domin a jiya matar yasa ce ta bukaci a bata abin aski da kanta ta bashi madubi ya rike ta yi masa askin da ya bamu mamaki, domin kamar wata mai aski haka askin ya yi kyau du ta kwashe duguzar nan
Aman baya cewa ummm, bale umum, ko rubutun da na fitar a frij na yau ya bashi ya amsa ya sha da kansa sannan ya shige bayi ya sake yin wanka , wai mutumen ba dai ba tsafta da ibada, ya nuna cewar sunna iya tafia gida domin Matar na ta tambayar ina y'ayanta ne? Ko mafarkinsu ne ta yi? Aman wani irin mafarki ne haka ? Ita sai tace sojan da ya dauketa wajen yarenta ya kaita, shin ina sojan yake da suaransu dai, to shine nake cewa Aba a bude gida guda a saka masu kula da su a kaisu kafin na dawo na ga idan na samu zama da mutumen ni ko zai bani amsoshin tambayoyin da ake masa baya cewa komai?......"
Ya fan sasauta dan maida numfashi, Mama ta ce" Ina jinka"
Muhay ya ci gaba da fadin" Shine Aba ya ce bai yarda da a kaisu wani wajen ba, wai idan mai binsu na tare da su fa? Komai na iya faruwa ciki harda siyan masu kula da su din, a nan gida akoy waje wadatace da zasu iya zama har komai ya daidaita .....to Mama da ni......."
"Kai me MUHAY?" Mama ta fada itama a sanyaye💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 5️⃣3️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
A hankali ya ce" Dama bana so Hakan ya hadasa wata fitina ne a gidan duba da na kawo Yarinyar nan da yayarta, sannan na karro iyayensu kar............"
Mama ta dan yi tsai ta ce" Kar a ga ka kawo mutane ka zuba?"
MUHAY ya dan gyada kansa hadi da fitar da fan sautin dake nuni eh yake nufi
Mama ta yi dan murmushi ta ce" Wani ya taba nuna maka wani abin ne Son?"
Dan tsai ya sake yi yana sauraronta, gaba daya yanzun Mama bata hawa kan fada a kan abinda ya shafe shi, sai dai ta saurara sannan ta bi abin a laluma, Hakan ya sa shima a yanzun yake doguwar magana kamar sunna a gabanta idan har zai yi mata magana ko wata iri ce
Mama ta yi dan murmushi ta ce"To ai sai dai ka yi hakuri, domin ka ganmu nan mun gama kimtsa bangaren da Abanku ya ce a gyara harma ga matarka cen tana saka ruraran wuta, kai din sai yaushe zamu ganka a gari ne?"
A hankali ya ce" Wani case ne na tarrar a nan sun, sun shiga kotuma, jibi ake yin zaman karshe, matsalar wani mai kudi ne ke son juya abin , in sha Allah da an gama zan dawo Mamah"
Mama ta gyada kanta tana mai yi masa adu'a sannan sukai salama ta sake maida hankalinta kan wajen labulayen da aka cenza da komai tana mai sake kula da tsaftar wajen da komai, sannan tana cike da farin cikin gannin yan matan murna ta ki ta boye kanta a saman fuskokinsu, ci gaba ta yi da taya su aikin itama cike da kula tana mai raya lalle lalle zata shirya tarewar Shuwwa ne, domin itama tana so yaron nata ya tare da iyalinsa wannan karron a ga yaya tafiyar zata tafi ne?
A nutse suka gama gyara ko'ina, sannan suka rufo suka koma bangaren Maman suka shiga girke girke, dama yau girkinta ne, hakan ya sa suka yi zama daya, da kansu sai masu aiki dake dan dauko abin daukowa su mayar da na maidawa suka yi tsararun girke girke, ciki harda favorite girkin da mahaifinsu ya fi so suka gabatarwa da Mama ta kuwa basu hadin kai suka girka masa , watau cus cus da boulette din naman kaza, sai jus na kwakwa mai sanyi , kai abincin saima da ya shiga cikin kwanoni na alfarma ya karra daukan kalla, ba'a cewa komai domin tabas ana iya ciza yatsa wajen dandanonsa
Da yama , wajen karfe shida Dad ya sanarwa Mama cewar sun kusa karasowa ya same su a bangaren bakin gaba dayansu, ashe har sauran matansa ya fada masu cewar su hadu dan tarbar bakim da yake tafe da su
Kasancewar babu wanda ya san wasu bakin ne? Domin basu san cewa wai mararsa lafiyan nan ne za'a tarba haka ba, ya saka su zuwa din
Sai dai sun yi mamakin gannin Matar MUHAY cikin shiga ta bak'ar abaya har kasa, ta yane kanta da mayafin abayar, sannan da bak'ar safa a kafarta, hakama yar uwarta irin shigarta ce a jikinta sak, hakan sai ya fitar da kamaninsu tamkar wasu y'ayan larabawa, kalar fatarsu ta sake amsar shigarsu, nanadewar da suka yiwa dan kwalinsu kuwa ya amshi yannayin fuskarsu, kowace da kamar wanda take yi a cikin iyayensu, sai dai jini da baya karya ne ya sa tashi dayama kana iya tunanin lalle kamarsu daya, sai in ka zauna da su ne zaka gane jinni ne mai karfi a tsakaninsu
Tabas sauran sun yi mamakin ganninsu haka dare dare a falon da ya dauki kaya ya yi wani irin kyau, ga kanshi ga sanyin AC na tashi ta ko'ina, ga lalausan capet ga tsaftar waje, sai dai babu wace ta fitar da mamakinta, aman kuma sun baza ido su ga abinda zai faru, domin shi ai kishi kumalon mata ne, kowace na da kalar nata kishin, bale uwar gidansa da ta gama daukarwa niyar in dai mijin nasu wasu bakin alfarma ne da shi bai tashi saukarsu ba sai yau ranar girkin uwar dan gwal walahi za'a yita kuwa a gidan nan, ita fa ta fa kai makura fa!, Walahil azim ta kai makura
Sunna nan zaune , ba wata hira suke yi ba, TV ce aka kunna aka rage amonta sosai a tashar da basu da aiki sai karatun alkur'ani, shi yake tashi a tausashe hakan ya sa kowace ke abinda ta ga ya fi mata zaman shirun, wata na waya ne, wata na karra harare harare ne, wata na shaaninta hankali kwonce ne, yan matan biyu kuwa kowace a cikin zulumi da kallon hanya suke, zuciyarsu na cike da tunanin yaya jikin iyayen nasu ne?
Wani soja ne guda ya bude kofar ya shigo bayan ya yi salama sannan ya sake bude kofar da kyau
Gaba dayansu ne suka mimike sunna kallon hanyar shigowar
Father ne ya fara bayana kadan , kafin ya sake rike mutumen dake bayansa da kyau dan ya taimaka masa ya shigo da kyau
A lokacin da ya bayana babu wanda bai tsura masa ido a cikinsu ba
Tabas rama ta samu wajen zama a jikin magaifinsu, sai dai abin mamaki annuri ya fara samun wajen zama a yanzu a tare da shi, haka kuma ramar ba kamar wace take hade da muguwar dati da duguzar gashin fuska da na kai din nan bace, a yanzun harda hiraminsa da ya dora a saman kansa, ga manyan idannuwansa farare kal yana kallon mutane da su , haka kuma kamaninsa tamkar ba ciwon ne kadai damuwar rashin maganarsa da saurin sakin fuskarsa ba, kamar a cikin lamarin nasa harda wani abu mai shige da iza, ko nace mulki dake fita a tare da shi
A hankali ya sauke idannuwansa a saman fuskar iyalinsa a karro na biyu kennan bayan sun shigo ta samu shigowar itama ta zubawa yan matan ido bayan ta ja ta tsaya a wajen da take , itama a jikinta sutura ce ta doguwar riga, sai dai tata fara ce sannan budadiya ce sosai hakan ya sa ba'a iya gannin girman ramar tata itama, aman ta fuskarta ana iya gane itama ba jikin ne da ita ba, du ya zube
A hankali ta juyo wajen da yake tsaye ta zuba idannuwanta cikin nasa, sai kuma ta sake waigawa ta sake kallon yan matan da tsoron laifukansu ya hanna su sake dankarowa a guje jikin iyayen nasu, tun bayan zuwan da suka yi na farko
A hankali ta maida kanta kan matan dake tsaitsaye bayan sauran yan matan nan da ta gama yarda cewa nata ne, Harma ta idasa bambance kowace a cikinsu
Muryarta cen ciki tana rawa ta ce" Asalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu"
Hawayen dake cikin idannuwan yan matan ne ya bale da kansa
A hankali Shuwwa ta dan daga kafarta bayan Mama ta amsa salamar a bayane da fara'a kwonce saman fuskarta ta nufota ta kamo hannunta harma tana mai yi mata marhabun ta waiga wajen mijin nata da ya ba wannan bawan Allah damar gama fahimtar wajen da yake, tare da wa yake, da mutanen dake gabansa a tsanake ba tare da ya azalzala shi zuwa wajen zama ba ta ce" CHIEF, a karaso shi ya zauna, kar tsayuwar tai masa yawa......"
A nutse CHIEF OF ARMY ya ce" Bismillah , mu je wajen zama........."
A hankali ya sake lumshe idannuwansa yana kallon yarinyar da a da sai tana saman kirjinsa take iya yin barci, wace ya tafi sallah masalaci ya barta zata ci abinci ita da yar uwarta, itace ta zama cikakiyar budurwa haka a gabansa a tsaye
A raunane ta ce" Abuiiiiiiiiii "
Sai da zuciyarsa ta buga da wani irin karfin gaske, irin mai motsa soyayar nan ta uba da y'ayansa
A hankali ya sake kallon fuskarta da hawaye suka gaba wankewa, ba ko diz din abin shafe shafe na kwaliya na mata a fuskar tata, aman yadda take walwali zai nuna maka a cikin nutsuwar zuciya take
A cen kasan zuciyarsa ya ringa taslima ga ubangijin talikai, zuciyarsa ta fara sanyaya da kuntacen kuncin da ta dauka na shekara da shekaru, ya fara yarda da maganar matarsa cewa ya yi kokari ya samu y'ayansa da ransa, ta tabata Allahn da ya dora masu wannan jarabawa shine zai zamto gatansu
A hankali ya sake fuskantarta sosai, yana ta kallonta kafin ya sauke idannuwansa a saman fuskar yar uwarta
Oh Nahidt dinsa
Yar matashiyar yarsa mai cike da kamala da fada da ilimi da wayau, yarinyar da ta tashi da zafin nema danma baya bari, itace ta zama wannan budurwar? Ya Allah alhamdulilah y'ayansa ne a hade gasunnan a gabansa?
Mama ce ta raka uwar gidan Dad da kallo a lokacin da ta yi gaba sanann ta sake fadin" Abansu ku karaso mana"
Sannan ta fuskanci Mama dake kallon bayan y'ayan nata, wa'inda sai su kalli mahaifinsu, sai kuma su kalleta a sanyaye ta ce" Ki kirayesu mana Hajia....."
Mama ta dan kure fuskar Maman Muhay da kallo kafin cen ciki ta furta" Sun gane ni?"
Mama ta sakar mata Murmushi itama kasa kasa sosai ta ce" kina tunanin ke Allah bai haska goshinki bamban da na wasu iyayen a idannuwan y'ayanki ba?"
Muryarta kasa kasa sosai ta dago hannunta tana kallon fuskar Mama da yadda ta zauna daf da ita haka ba kyama ba komai ta ce" Na kasa gane yaya aka yi su dake saudiya yara kannana suka samu zuwa nan? Sallah kika je kika taimaka masu? Kece kika rike min y'ayana da mutunci haka! Ashe da na cewa babansu gaba faya duniya kar ya yarda da kowa daga ni sai shi na tafka kuskure, yana iya yarda da daidaiku irinku?"
Mama gannin Mamansu ta rikice, gashi su din kansu a wajen nan da suke yanzun sun jimke hannayensu waje daya sun sada kawunnansu , domin daga mamansu har babansu babu wanda ya yi kiransu, su kuma basu je da gagawa ba dan sun gama tsoratar da kansu, Maman Muhay ta dubesu da tausayawa ta ce" Me kuke jira haka ne? Me kuke jira ne yan matana?"
Ai dama kam jira suke, kiris suke jira a ce, so suke a basu damar aikata hakan
Maganar ta saka kamar ta kunna su da rigai rigai suka kawo kansu wajen mahaifiyarsu da har ta dan fara cirawa zata mike suka koma gaba daya suka zube a saman kujerar suka saka kuka irin mai karfin nan har y'ayan da ita din kanta
A hankali ya bude idannuwansa bayan ya rufe ruf yana tunanin a duniya anya ko harbe wanda ya masa yankan kaunar nan ya yi ya huce kuwa?, Ya raba shi da abinda ya haifa bayan shi ya yi nesa ya bara masa komai da komai?
A zabure ya sauke idannuwansa a kansu gaba dayansu a lokacin da suke fadin" umah, wayo Umanmu, Mamah har kabarinku aka kaimu"
Da karfi Shuwwa ke sake shigewa jikinta tana fadin" Ni dama na san baku mutu ba, ina kuka tafi? Ina kuka je kuka barmu? Ina kuka je?"
Zurbat ya mike daga gefen Dad, da karfin zuciya ya karasa wajen da suke kafin shima ya kai inda suke rukunkume da junna ya rukunkume su da karfi yana rintse idannuwansa
Nahidt ta juya gareshi itama ta rike shi kam tana girgiza kanta ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, mu kuwa da muna da gata menene hukuncin da ya dace da dukkan wanda ya aikata maku haka?, A yanzu na fara tunanin ba da kafarku kuka barmu ba, domin a gidanmu Jaddah baku bari ko kuda ya rabe mu........, shuwwa take cewa baku mutu ba, sai na ce ta yi hakuri kun mutu ta yi hakuri, sai Mama ta nanma ta ce tana ji a jikinta baku mutu ba"
Tunda aka fara kayaniyar nan CHIEF OF ARMY ya samu ya fitar da dayar matar tasa da dukan wani sojan dake iya kallon abinda yake faruwa kafin ua dawo shima ya zauna kusa da matarsa sunna kallonsu zuciyoyinsu a karye gaba dayansu
Kamar an ciro a bakinsa, tunda ya samu lafiya kamar da karfi aka budi bakinsa, domin maganarsa ta yanna cikin ihun a kaishi nesa da kasar nan da ta yanzu ba iri daya bace ya budi baki ya ce" ku yi shiru"
Sai kuma ya yi kitttt da bakinsa, kafin ya sake daukan furucinsa yana fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une....... Nahidt, Ebtisemmmmmmmm, ashe zan ganku a duniya?"
Gaba daya sai da zuciyar kowa ta karaya a dakin nan, sun kasa sakin junna haka kuma sun kasa daina aikawa junna tambayoyi kowane so yake dan uwansa ya fada masa abinda ya same shi bayan baya nan,
Da kyar Mamansu ta sasauta nata kukan tana rike da kumatun Shuwwa ta ce" Me kuka gani a rayuwa y'ayana?, Ina da ina kuka je? Me ya same ku a wannan katuwar duniyar da ta yiwa yaro girma?, Abansu kana kallon jaririyarka yadda ta girma ?, Oh Ebtinahhhhhhhh"
A hankali IBTISAM ta sake komawa cikin jikinta ta lafe tana ta sauke ajiyar zuciya tana jin a yau bata tunanin idan akoy abinda zai nisantata da kirjin nan na mahaifiyarta, komai girmansa kuwa, itama riketa ta yi tana ta shafa bayanta da kanta a sanyaye idannuwanta a lumshe tana ta jin bugawar zuciyarta ta sake budar bakinta tana kallon Nahidht ta ce" Yar gidan Papanta, ku fada min, ku fada min abinda ya same ku , duda na ganku a hannu mai daraja a gida mai daraja, aman na kagu na san kafin nan me ya same ku, na kagu na san me da me kuka gani na rayuwa koda na rana daya ne na tabata kun san abubuwan rayuwa sosai, oya telll me "
Gabanta ne ya kwonci kwonci ya fadi, dogon hancinta kuwa da ya jajajir sai ya done , watau ta rasa wadataciyar iskar ja ta shi du irin girmansa
Jiki a mace ta sada kanta ta kasa furta masu koda A ne,
Hakan ya sa Mahaifiyarta tsatsareta da idannuwa gabanta na faduwa
Zata sake yi mata magana Maman Muhayta dan yi gyaran murya a sanyaye ta ce💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 5️⃣4️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA