Showing 63001 words to 66000 words out of 226733 words
GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
Da baya baya take tafia zata fito daga falon, daidai Malan ya zo shigowa daga sallar la'asar yake an gama saukar alkur'anin da ya saka a wuni yi ana ta sadakar waina sai ya dawo ciki dan ya ga ko ta farka domin tunda akai fatiha Hamza ya koma dan sunna gudun ta farka daga su sai su
Dan gefe ya tsaya yana gyaran murya dan NAHIDT ta gane yana wajen
Sarai ta jishi harma ta gane aman sai ta ki ta tsaya din domin Shuwwar ce ta fara alamun motsawa ita kuma bata so gaskiya ta motsa tana kusa ta fara sauke kwondon balakin dake ranta a kanta, dan ta san a yau mai sauke guguwar haukan Shuwwar sai Allah
"Nahidt ki kula mana" ya fada a tausashe yana dan sake komawa baya
Juyowa ta yi tana murguda bakinta ta sake binsa da kallon ka ji kunyar nan da take masa tun bayan fitar matarsa ta ce" To wai me na maka kuma ni? Ka ga fa farkawa ne take yi"
Bakinsa ya tabe kasa kasa ya ce" Ita kadai kike tsoro, kin ji kunya ni ki sakani gaba ki min tasss aman kina tsoron kanwarki, ko me na maki ni din?"
NAHIDT ta zarro ido tana biyo bayanshi ta ce" haba dai wace mai tsoron kanwar tata? Ba dai ni ba NAHIDHT na rantse, kuma da kake cewa me ka min me kuwa zaka min a duniya? Abin kunya ne ka ci gaba da rabawa ba komai duniya ce, ai ba sai kun zo gaban mutane kunna abu kamar wasu makafi ba za'a gane ita matarka ce, kai kuma mijinta ne, itama ta fadi ba nauyi ko meye abin biyo miji cikin mutane?"
Har ga Allah abubuwan da ta wuni da su kennan na bacin rai a zuciyarta, domin fargabar Shuwwar ta maidata gefe ta ajiye domin abinda ta riga ta sani ne ko ana ruwan muzuru sai ta tare a gidanta a yau din nan, ai ba zata taba yin sake Shuwwa ta sake aikata wani haukan ba, ko daya walahi!,
Tsittt ta yi tana kallonsa sakamakon juyowa da ya yi yana kallonta
Shi da kansa sai ya samu kansa da manta a inda yake a hankali ya shiga nufo wajen da ta yi tsaye tana ta cicira ido kamar ta yiwa sarki karya
A hankali ya ce" Kamar ranki ya bace dan matata ta bani kulawa?"
Ido ta zarro tana kallonsa da tarin balagar rashin kunya ta budi baki zata zuba rashin kunyarta muryar Hamza daje rike hannayen Shuwwar da ta bude idannuwanta da adu'a a bakinta sannan ta shiga muzgutawa da alamu na son mikewa ya kamata ya taimaka mata ya tayar da ita zaune
Ido ta dan zarro ta yi raf da gaban rigar Malan muryarta kasa kasa ta ce" Kur'ani ta farka, ka wa Allah jeka ka tofeta ka fa san bata da hankali"
"Ya Salam ki cika min rigata to meye haka wai?" Ya fada da dan gagawa yana janye rigar shadarsa mai ruwan blue sai maiko take na sabontaka
Da dan karfin da suka saka dan mayar da ita zaune Hamza ya budi bakinsa yana fadin" SHUWWA, look, SHUWWA zauna mana kar ki jima kanki ciwo bakya gannin jikinki bashi da karfi?"
Idannuwanta ta rintse ta yi muimuimui da bakinta a hankali ta bude zazafar muryarta mai shige da sarewa idan tana fada ko tana dadadan kalamai ta ce" Ka ga ka sake ni haka, Hamza ka sake ni haka"
Fauziya ta dan zarro ido tana fadin" SHUWWA yayanki ne fa , ko a da ba ce masa kike yaya ba shine yau Hamza sak?"
SHUWWA ta saka hannunta tana bambare hannunsa ta juyo wajen da Fauziya take ta mika hannunta da yannayin zata warto wuyanta tana fadin" Bara na fara wancakalar da ke ko zaki fahimci ba sani ba sabo, na ce Hamza idan tai maki zafi ki nada min duka! Ku sakeni na ce na tarda shi ku sake ni!"
Wajen ya juyo ya nufo da sauri ita kuma tana bin sawunsa du inda ya dauke har suka karaso kusa da kujerar
A nutse ya ce" Ku saketa "
Hamza ya dube shi da dan mamaki ya ce" Mu saketa Malan?"
Malan ya gyada kansa yana sake kallon Shuwwar a kasan zuciyarsa yana ta adu'ar Allah ya dora shi saman kanta da karfin adu'a da Nasiha
A hankali ya cikata yana mai kallonta cike da tausayi
Tabas shi da kansa a yau ya dace ya samu a rarashe shi, a yi masa nasiha mai ratsa zuciya, sai dai gaba daya ya maida dukan wani firgici da damuwarsa gefe ya fuskanci na kannensa, ba shine abin tausayi ba, ba shine abin a rike ba, ba shine abin a zauna a fuskanta ba, shi mema ya gani? Abinda ya gani daya tak ne na rashin uba, bayansa ko me ya ganni shi ya saka kansa a ciki, iyaye ne a gefensa masu sonsa kamar ransu, a yau ya tabata kaf duniya ba zai yi kukan maraici ba koda waye mahaifinsa, aman su fa? Su fa?
"SHUWWAR zauna, ki zauna domin Allah" ya fada a sanyaye yana kallonta
Da muryarta mai tafe da ciwon da take ji tun daga kasan zuciyarta ta fuskance shi a sanyaye ta furta" Mafarki ne na yi ko Abah?, Abah ku ce min mafarki ne na yi, Abah ina hadina da mutun irin wannan? Hasalima namiji irinsa baya birgeni, na fi son namiji mai sanyi , mai sakani dariya, like yayanmu haka, ko kuma mai saurin kuka kamar Abdul Mutalab, ko a samu wani dan tawalwalin da zayana hakuri da halayana mu zauna kalau, aman ba irin wannan mutumen ba, Abahna ka ga sam ne ban ga alamun zamu iya jituwa da shi ba, tunda muka fara haduwa mutunci bai hadamu ba, ka ce da ni ya sakeni ka ji Abah?"
NAHIDT kasa kasa ta tabe baki tana fadin" Ki ce dai Dan daudu kike son aure ba namiji ba, hana malan yo wace mace ce zata ga mazaje irin wannan ta ki yabawa?"
"NAHIDT?, NAHIDHT? NAHIDT?, Sau nawa na ambaci sunnanki? Sau uku kau? Idan baki fita a harkata ba yau na rantse da Allaj sai na fara yaga fuskarki da faratunana kafin na tarda shi, ke kika ga namiji a nan, ni bai min ba na ce ya barni ya sauni ba zan iya zaman aure da shi ba!" Ta fada da karfi tana zazarowa NAHIDT ido wace ta sake labewa a bayan Malan
Sai dai kayan haushin Malan din kansa sai ya ji wannan ai wulakanci ne NAHIDT ke neman yiwa mazan da shirga shirga ba!, Me take nufi da kiran mazan da ba irin MUHYIDEEN da sunnan yan daudu ne? Lalle yarinyar bata san ba daga nan abin yakr ba ko?
Shima a fusace ya juyo yana fadin" Kin ga fice min a nan"
Ido ta dan kura masa zata yi masa tambayar me ta masa ne? Sai ta ga ba fuska kwata kwata kamar ba malan mai yi mata nasiha a sanyayen nan ba, hakan ya sa sumui sumui sumui ta juya ta nufi kusa da kofa tana zaunawa kasa kasa tana fadin" Bilahilazi ku yi ku gama ba za'a saketa ba, tap yo hakan na nufin na ga samu na ga rashi ne fa? Sai ta zauna zaman aure da shi wollah!"
A sanyaye ya sake matsawa dan kusa da ita kadan yana daukan hijab dinta dake yashe ya mika mata a sanyaye ya ce" Saka Hijab dinki sai mu yi maganar yar Akbarka kin ji?"
Hijab din SHUWWAR ta bi da kallo sannan ta kale shi, a sanyayenta ta ce" Abah, ni da za'a saka kuma me yasa zan saka Hijab ?"
Dan murmushi ya yi yana kallonta ya ce" Ki saka din dai mana yar arziki shin kin manta suturta jiki dabi'a ce ta musulmin dake anfani da fadar ubangijinsa, shi hijabi ai kariya ce ga yaro ko baba matsawar mace ce, ta suturara jikinta, ta kame shine alkhairi a gareta da sauran al'uma baki daya"
Nahidt ta kalli jikinta tana bin rigar jikinta ta madubin dakin da kallo
Gaba daya sai ta ji kamar habaici wancen mutumen ke yi mata wollah
Aman sai ta daj rarasa ta janyo daj kwalinta ta koma wajenta tana warwarewa ta yafa a jikinta a ranta tana ayana' Allahn da yasa muma muna tsoron Allahn kuma ba mu bane kafuran karshen zamani in sha Allahu!'
Hijab din Shuwwa ta laluba tana dan sake sadda kanta a hankali ta saka ta sada kanta kasa tana murza dogwayen yan yatsunta da suka sha jan kunshi da sukai mata kyau sosai hakan ya sa hannayen sai daukan ido suke sun dauki kunshi ba karya
Kanta dake sade ta sake sadawa a hankali ta fashe da kuka irin mai cin ran nan tana fadin" yaushe ne za'a daina auren hadi a kasar hausa? Yaushe ne za'a daina daukan mutun a ce an masa miji a mika shi? Abahna ina matukar yi maka biyaya, na san da ka ce baka son hadani da soja da babu wanda zai hadani domin koda a yanzu an ce ga dangina ni kaine dangina, ban sansu ha, rana tsaka basu isa su ce zasu min dole ba, Aman Abana me yasa zaka hadani aure da soja ne?, Abana ya sake ni dan Allah, idan ka min haka Abana an shiga hakina sosai kuma ina tsoron na hadiyi zuciya na mutu"
"Hehehe ka ji wani bakon iskanci a wajen IBTISAM, ke ba zaki shiryu ba? Yanzun du abinda muka tsalake bai saka kin hadiyi zuciya kin yi musai ba sai da aka dauko dan gata gangaroya kyankyasar inji aka baki shi a ledarsa dan cikin AC ne zaki hadiyi zuciya ki mutu? Ki yiwa Allah ki hadiya mu gani? Na ce tak ki hadiya dan uban babanki!" NAHIDT ta samu kanta da fadi bayan ta mike zurbat a lokacin da ita kanta bata shirya ba ta kuma nufosu taa tsaya ta fada
A tare suka mike da Hamza da Shuwwar inda Malan ya dafe gaban goshinsa yana mai binsu da kallo
A guje ta nufeta ita kuma ta zagaya da gudu ta yadda suka saka Hamza a tsakiya
Kikikikikiki suka shiga dima dambe dan jan Hali irin na Shuwwar tana ihun a miko mata NAHIDT tamkar itace karamar ita kuma itace babar
Sun yi juyi ya kai sau uku da kyar Hamza ya iya damkar hannun Shuwwar da karfin gaske har ta yadda ta dan saka ihu tana cin tirjiya da ihun bara ta fara nunawa Nahidt ainahin bata da hankalin da take fada
A dan kausashe Malan da ya mike ya ce" Ka ga sakar min ita saketa, ka kama ita wannan babar kwabom ku je waje ka bara min ita, ina kokarin nusar da ita na sanyayar mata da zuciyarta ita kuma tana neman rikita min ita babar kwabo kawai!"
Tun kafin a yi wajen da ita yanzun ita ta fara fita tana ta gyatsine da bakinta
Hamsa ya bi bayanta hakama Fauziya dake tsaye ta bisu sum sum sum
Yana tsayen ya fara magana da fada fada yana mai nunata da yatsarsa yana fadin" Godiyar Allahn kennan?, Na ce Godiyar Allahn kennan? Ke da zaki yi sujada ki fashe da kuka ki fadawa Allah cewar kin gode sannan ki kara fada masa idan alkhairinki ne ya baku zaman lafia da mijinki, idan kuma ba alkhairinki bane Allah ya sanyaya mana kamar yadda ya saba sanyaya mana shine zaki tashi ki ringa ihu irin haka? Shuwwa so kike mutanen dake zaune har zuwa yanzu sunna jira su ga kai amaryar da aka ce za'a yi da gasken gasken ne za'a kaiki ko kuma abinda ya saba faruwa ne zai faru da ke cewar eh haka din ne?, Shuwwa ake ta yamadidin ke din bakya ji baki da tarbiya baki da meye meye ashe ba zaki ba maradanki kunya ba?"
Shuwwar da ta kai tsugune tana mai cike da mamakin ashe dama Malan ya iya fada jikinta ya fara daukan sanyi
Wai yaya kamar babu wanda ke fahimtarta ne? Yaya ba za'a iya fahimtar cewa ta tsani wannan mutumen ne? Wani irin zaman aure ake ta yi da shi bayan bata saka haka a tsarin jerin munanan mafarkanta bama bale har ta hau zuwa burikanta? Ita mamakin kirjinsama take yi, tun a haduwarsu ta farko ta ga wani irin halita tama zata aljani ne ita kadai ke ganninsa ashr kutun ne, shine haka zai faru da ita? Wai ace a zuciyartama da take kira cewar zuciya mai bata hadin kai a dukan soyayar da zata nemi hadawa da kowani irin namiji cewar zuciyarta ba zata taba bata kunya ko ta bada mata kasa a ido ba itace a yau tana ganninsa tsanarsa ce ta shiga ruhinta fakat daya?
"Ki gane, Allah baya abu irin na mutun kai sake, ki gane tsanarsa da kike ta bayanawa a bayane babu alkhairi a haka, ba kyau tsananta tsana ko soyaya, IBTISAM ke baiwa ce ta Allah, ubangijin da ya halice ki ya baki rai da lafia yana iya amsarsu a dukan lokacin da ya ga dama, shin zaki ce min ne gwara ki mutu ki je ga ubangijinki dan zafin kunnar ya sako MUHYIDEEN a matsayin miji a cikin zanen kyakyawar kadararki ko akasinta ko kina so ki kwatanta min cewar kina da wayon da zaki zagaye wannan dan bau maki ba ki samo daidai da ke dan ke kin isa da wani isa naki wanda ke kika santa, SHUWWA ko so kike ki ce min na maki shishigi da na yarda da kirana da kike Abanki har na mika ki ga auren da na ga ya dace da ke ne? Shuwwa ko.............." Sai shiru ya dauki wajen, Muryar Malan ta yi kasa sosai da yadda take a da
Shirun da ya yi yawa ya saka SHUWWA dago kanta a sanyaye da hawayen dake zuba a saman fuskarta dan gannin ko ya ji haushinta ya fita ne? Domin shirun ya yi yawa sosai
Sai dai abinda ta gani sai da ya saka gabanta faduwa
Da sauri ya saka hannunsa yana share hawayensa ya ce" Kowani bawa da kika gani a gidan duniya yakan hadu da jarabawar da Allah ya daidaita ya bashi daidai da kansa wada kansa zai iya dauka ne SHUWWA, kin ga ni.....nima ina cike da zulunmin rashin mai kirana da Aba a dubiya, sai aka wayi gari wata rana kina kuka kika ce min Abah..........Shuwwa, da kin san irin farin cikin da na yi a ranar nan da kin yi mamaki, haka na zo na ringa sadaka da kyauta ina fadawa matana cewar nima an ce Abah, abah ba na tsokana ba, Aba aka ce min da zuciya daya, da soyaya irin ta haihuwa, Allah nima ya bani Y'a, kin ga Ibti da kika ce bakya son sunnan IBTISAM sai na goya baya duba da ba haramun bane na zaba maki sunnan da bake mangari muka yanka muka dayiba, na jima ban ji abu irin na rashi d'a irin na yau ba, SHUWWA da ace Aban naki ne umarni ne zan baki ki kuma cika dan na isa da ke, sai gashi.........."
Ya sake sada kansa alamu na wani kukan na son tiko sh💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 2️⃣1️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
Bata taba tunanin hankalinta zai tashi da tashin hankalin wani dan adam a duniya dan kawai ya shiga hali na tashin hankali irin haka ba sai yau
Da rarafe ta karasa gabansa tana karra dukawa ta hade hannayenta tana girgiza kanta tana fadin" Walahi ka isa da ni, kuma kai, kai Abana ne, dan Allah ka yi hakuri, ban yi haka dan na saka ka kuka ba ko kadan, walahi nima a Abana na daukeka kaf duniya bani da wani uban da ya daraka, Abahna me ka rage min na uba da dansa? Kana tare da ni dukan abinda na kwaso