Showing 102001 words to 105000 words out of 226733 words
sauke idannuwansa a kansu
Kuka ta fashe da shi daga wajen da Shuwwa ta makata da garu tana lankwashewa irin bayantan nan tamkar bayan nata ya kalle tana fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une me na maki?, Me na yi maki da zaki dakeni harda hadani da garu bayan kin zageni ta uwa da ta uba? Me na maki ne a rayuwa zaki zo har cikin gidana ki wulakantani da min ikirarin mijin da nake takama da shi kun gama da shi kun shanye shi?"
SHUWWA ta yi murmushi tana juyawa wajen mayafinta da ta cire ta ajiye ta dauka tana maidawa a kan gashin kanta da tuni ribom dinsa ya cire a kasa ta nanada da cazar dake hannunta sai da ta daure da kyau kafin ta juyo wajen da Nahidt ke zaune, ta ga a zaunen dai take tun zarro idannuwan da ta yi bata kuma yinkurin yin komai ba sai uwar gidan Malan ce ta ce" Ki ji tsoron Allah Furera, ki guji kafurin kishi Furera, idan kikai haka jin dadin na kankanin lokaci ne a cikin gidan duniyar, zaki je ki samu ubangijinki a kiyama, ki sani Furera koda jin dadin muzgunawa wani ya zame maki a duniyarki har ki je ga kiyamarki ne to fa da zarar kin mutu kin hadu da sakamakon abinda kika shuka kennan har zuwa tashin kiyama, shin yaya zaki yi idan ubangijinki ya tsayar da ke a gabansa ya tambayeki abubuwan da kika aikata a duniya bayan ya haliceki ne dan ki yi masa bauta me zaki ce? Ke ce hada wannan da wanan, kece zagin kadarar mutun, shin ke kin tabata kin isa ki juya salon rubutun ALK'ALAMIN kadararki ne?"
Malan ya sake furta" ASALAMU ALAIKUM "
Juyowa malama ta yi a nutse tana amsawa kafin ta matsa gaba daya ta bashi hanya ya shigo hakan ya sa Furera sake rakata da mugun harare mai zafi tana ji a cen kasan zuciyarta a duniya idan akoy makiyinta bayan matar nan ne, bata taba gannin mace mai kafurin hakuri da jarababen biyaya irin uwar gidan Malan ba, da ba dan ita ta san me take nacewa a zamanta da Malan ba da ko dan hakurin matar nan ta barshi ta yi tafiyarta nesa da shi, sai dai malan din ne duniya ne, ba zaku gane ba malan duniya ne
A nutse ya masu nuni da wajen zama gaba dayansu
Shuwwa ta cije baki da abin dukanta a hannunta tana jin haushin zuwansa bata farfasawa wannan tsageran jiki ba wai shari ne zata yiwa mutane ikon Allah, tabas sai ta koya mata hankali ko yau ba, wannan alkawari ne ( kai jama'a kamar irin zaka ladaftar da yaron da ka haifa din nan
Da sauri ta zagaye Shuwwar ta karasa wajen zama ta zauna a gantsare dan so take malan ya ganewa idannuwansa cewar mahaukaciya yake neman yin taraya da ita ko me?
Sai da suka zazauna su ukun, dama Nahidt a zaune take, sannan ya karaso saman kujera ya zauna yana dan sauke ajiyar zuciya kafin ya sauke dubansa a kan Nahidt
Ido hudun da suka yin da junna ne ya saka shi sake saka idannuwansa a cikin nata
A hankali yake rage girman💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 3️⃣4️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
A hankali yake rage girman nasa idannuwan a cikin nata, dukkan abubuwan dake cikin zuciyarsa sunna bayanar da kansu a bayanne a cikin nata idannuwan, karara halin da idannuwanta suka nuna tana ciki yake neman kasara dukan tunaninsa da dukan wani yannayi na jarumtarsa
A hankali idannuwansa ke isar mata da sakon rarashi duda bata budi baki ta yi magana ba, bata kuma yi rigima da wada ke zaginta ba ji ba gani ba
A hankali ya lumshe idannuwan nasa yana kawar da kansa a bangarenta ya maida kan Shuwwar wace ta tsatsare su da ido tana jin wanu farin ciki a kasan zuciyarta
Kakausan kallon da ya mata ya sakata sada kanta kasa tana boye bulalar a cikin mayafin abayarta a kasan zuciyarta ta shiga ayana' kai, ashe ashe itace na daka kuma ya ganni'
Ya maida dubansa kan uwar gidansa da kanta ke sade , ya samu kansa da yi mata lalausan kallo mai saka Nutsuwa a zuciya sannan ya maida kan Furera
Ido hudu sukai da ita, tunda ya fara kallon Nahidht take kallonsa haka kuma take fasara shi a cikin zuciyarta har ya sauke dubansa a kanta
Ta so ta yi kisarta da kisisinarta ta hanyar sake lankwashewa, sai dai duban da yake yi mata a bayane yake cewar sam bai yarda da abinda take son nuna masa ba, hakan ya sa ta samu kanta da tsarguwa harma ta kasa kallon cikin kwayar idannuwansa
Ajiyar zuciya ya sauke a nutse ya ce" Abin alkhairi na ga ana ta shigowa da shi, IBTISAM ashe kece tafe?"
SHUWWA ta kasa cewa komai sai sake sada kanta da ta yi, hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya yana yin murmushi ha ce" Allah ya karra budi, Allah ya saka da alkhairi"
Uwar gidansa ce ke amsawa a nutse da ladabi da biyaya
Sake yin dan Murmushi ya yi yana kallonsu aa sanyaye ya ce" Ban ji dadi ba, gaba daya sai Tsoro ya kama ni, na fara tunanin yaya iyalina zasu kasance zuwa gaba ? Bale idan ban yi tsayin rai ba yaya zumunci zai kasance a ahalina?"
Zuwa yanzun gaba daya gaban jikinta idasa mutuwa suke yi, haka kuma karra kallonsa take yi
Irin yadda zuciyarta ke bugawa kuma abin nema yake ya fi karfinta bil haki, hakan ya sa a hankali ta ringa ambaton sunnan Allah
A tausashe ya ce" Irin haka babu abinda zai haifar mana sai bacin rai, da tabarbarewar zumunci, da mugun sakamako a wajen Allah, domin kuwa Allah na yafe laifin da ka yi masa ne kai tsaye aman baya yafe wanda ka yiwa bawansa, idan har ka zalunci bawansa ya zama wajibi ka nemi yafiyar bawan nasa koda zai yafe maka ne shima da kansa, hakan na nufin Allah baya so a zalunci bawansa ta kowani siga, sannan ya haramta bawa ya ringa yankewa bawansa hukunci ko yayane..............., Fisabililahi kun kyauta kuwa?"
Gaba daya shiru ne ya sake ratsawa, kafin Furera ta bude bakinta ta ce" Allah ya gafarta Malan , shin da adalci a cikin lamarin nan da ake son nuna min kuwa ? Mata ta tardoni har gidana ta dakeni?"
Kansa ya girgiza a sanyaye ya ce" Ba adalci a hakan ko daya, asalima dukan bashi da anfani, to aman ke me kika yi ne?"
Ido ido suka shiga yi , a dab hade ta ce" koma me na yi ai ban cencenci haka ba"
Shima a dan haden ya ce" Dan su ba mutane bane ya saka basu da zuciyar dake iya hasalasu s Idan suka samu kansu a hali na bacin rai dake iya tunkuda su aikata kowani irin aiki kike nufi ko me?"
Gaba daya sai ta dawo jifansa da kallon dake nuni kamar tana mai tuhumarsa ne da goyon bayansu, shi kuma ya sake daurewa ya ce" Haba Furera, a zaune na fada maki, haka kuma a tsaye cewar koda abinda kike hasashe gaskiya ne ko karya ne baki da hurumin hanna su ziyartata koda a wani irin lokacine, shine zaki wulakantar da kanki har kanwarki ta daga hannu a kanki? Kin san da ba kowa yaa janyo ba sai ke da kanki? Ga yayarki nan, da ta kama girmanta ta mutunta kanta hakan ya sameta ne? Subahannalah yaya kike so na dube ki bayan tun farkon fara furucinki na sanyo kai zan shigo wajen nan nake jin kalamanki na rashin da'a kina furtawa wa yar uwarki? Me ta tsare maki? Idanma abinda kike jifanta da shi ta dawama a ciki Allah ya ce ki ringa jifanta da shi ne? Idan zaki yi mata nasiha ki kwatanta, idan zaki yi mata fada ta sigar nasiha ki kwatanta aman zagin nata da kike yi Furera kin saka hankalina ya tashi bayan na manta cewar Nahidt ta yi rashin ji na ajiye gefe na guji abinda zai daga min hankalina sai gashi kin tuna min kin fada min fisabililahi wannan aikin ilimi ne ko jahilci?"
Kanta ta sake sadawa domin a zamanta da shi, bata taba gannin ya yi mata fada da kakausar murya da dogon zango irin na yau ba, gashi kuma a bayane ransa ya gama baci ne domin abin a bayane yake ba a boye ba, ta gama yarda cewar sai ta tashinwa kanta a kan matan nan, ta gama yarda cewar an shanye mata mijinta malaminta ustazunta
A sanyaye ya kalli gefen da Uwar gidansa take ta sake sanyayar da muryarsa ya ce" Allah ya saka maki da Alkhairi, ya kara shiryar da ke , ya yi maki albarka, ya baki aljannar firdausi ya ke Rabiatu"
A sanyaye ta ringa amsa adu'o'insa tana sake sadda kanta a sanyaye da matukar sannin waye mijinta ta ce" Allah ya huci zuciyarka Allah ya baka hakuri"
Karra cika Furera take tana batsewa tana kallonsu, shi kuma ya sakar mata murmushi a sanyaye ya ce" Dan Allah ki taimaka ki idasa rokar min ita cewa bayan dakinta dake jiranta a gidan nan wanda ya fara tara yanar tautau, ni da kaina na fara gajiyawa da Zaman jiranta, Rabiatuna ki ce mata ta ji tsoron Allah ta dube ni tun kafin karfina ya gaza"
A zabure du sula sake kallonsa, banda ita Hajia Malama Rabi'atu, wace maganar nan irin haka sau uku kennan yana fadarta a gabanta, ta farko ita ce ta tayar masa da balin rigimar ta gaji da ganninsa cikin bacin rai da yawan hadewar fuska sai ya fada mata damuwarsa, ya yi ta kaucewa, ya yi ta kiyawa har ta yi yar dariya ta ce da shi a da dai shi din ba rago bane , aman a yanzu ya kasa fuskantar Nahidt ya fada mata cewar yana sonta? Ita fai ta san mijinta ba rago bane dan haka gaskiya ya daina wannan fargabar a gaban Nahidt ya yi kokari ya fada mata ya taimaketa ya ceceta, ta yiwu sanadiyar haka Allah ya bude masu haihuwarsu, domin su dukansu babu mai matsalar haihuwa sun ga asibiti ba'a ga dalilin da ya tsayar da haihuwarsu ba, sai na biyun ranar da sukai wayar nan ta dare da ta kashe da safe Hamza ke fada masa bata nan ko gidansa ta yi? Ya fice a fujajan ya je tsohon gidanta ya samu gidan a garkame, daga cen wajenta ya yi hankalinsa tashe yake fada mata, daga wannan ranar ta kara daukan aniyae gabatar da tsaftatacen kishi, ba dan bata kishin Nahidt ba, itama mace ce, tana kishin mijinta sosai, aman kuma zata gabagar da tsaftatacen kishin da zai karra mata daraja da soyayar mijinta, shi yasa ta bashi goyon baya a gaban idannuwansa da kuma bayan idannuwansa
A sanyaye ta sakar masa murmushi ta ce" In sha Allah, zata amince ta zama yar uwata, matar mijina, abokiyar tafiyar da zaman lafiyar gidan MALAN Aban SHUWWA"
A hankali Shuwwa ta furta" Muhamadu rasululahi sallalahu alaihi wa salam" tana kallon Matar malan baki hangame
Furera kuwa a lokaci daya kanta fa idannuwanta suka kwashi zazafan ciwo
Da gaske abinda take gani kuma take ji cewar Malan ne ke neman auren wannan karuwar?
A birkice ta mike tana fadin" Malan, anya kuwa kana cikin hayacinka?, Rabi kina cikin hayacinki kuwa?, Ka gane wa kake cewa zaka aura kuwa? Matar da ta gama rabar da dukan wani mutuncin dake tare da ita? Matar da kila wa kala tana dauke da cutar h................""""""
Tsit ta yi tana rufe kumatunta da sauri sakamakon mikewar Da Nahidt ta yi jikinta na dan rawa , dukan gaban jikinta a mace ta tsatsareta da idannuwanta da suka dauki ruwa sosai
A hankali ta lumshe idannuwanta hawayen dake ciki suka zubo saman kumatunta
Muryarta a sanyaye tana kallonta ta ce" Daina rufe fuskarki, idan SHUWWA na waje ba zan zane tsageran dake zagina ba na tabata ta fini zafin hannu dan ta taba zabga min mari da na kirayi kaina karuwa, walahi fitsari na yi a wandona a ranar sai daga baya ta bani hakuri na kuma yafe mata, Furera ban san me na yi maki ba, nakan daukanki a matsayin wace ya zama wajibi ta tsaneni dan kina tunanin ina bin mijinki sannan nakan dauki tsanar da kike min da sauki domin a rayuwa babu bawan da zai ce shi lalle kowa dai ua so shi, kin ga dole zaka rayu da wa'inda zasu tsaneka ba tare da ka tsare masu komai ba, bale ke da kike gannin nice damuwarki, Furera bari ki ji, farkon fara masha'ata ya samo asali ne da rashin ci, rashin sha, rashin muhali, da ace da irin mijinki muka fara haduwa da na tabata maki da yanzu ba haka nake ba, da farko tabas kadarar rayuwa ce ta sameni Furera, sai dai shi sabo fara shi ne da sauki, fitarsa Yana da matukar wahala domin daga baya mun samu budi sosai sai dai gaba daya na riga na shiha sai fitar ta gagaremu, aman ki yi hakuri dan girman Allah, kuma ni na yafe maki, hakama kanwata zata yafe maki ko ba yanzu ba, ke zan iya ce maki idan ta kasa yafe maki zaki ganta ta dawo ta nada maki wani dukan dan ta huce domin bata so ta rike mutun a ranta, ta fi gane a yita ta kare da ta rike mutun a zuciyarta, Furera abinda kike yima din fa ni ba zan aikata ba, Furera me gareni da zan iya zama matar sa? Shi din adali ne, ya amshe mu, ya zala uba a garemu, ina zuba masa hauka dan ma ture shi daga rayuwarmu aman shi aikin Allah yake yi, da zuciya daya yake yi, yanzuma abinda ya kawo mu kin ga y'arsa ce ke son ganninsa, ni gabana faduwa yake idan na fiskance shi, bayan wannan sha kuruminki ba zan iya aurensa ba, ba zan taba aurensa ba, ki huta abinki?"
Daga haka ta juya ta fice da gudun tsiya wanda hakan ya saka shi rintse idannuwansa fa karfi ya sada kansa yana sauke numfashin dake fita da gagawa a kirjinsa
Ido SHUWWA ta zarro tana raka Rabiatu da ido wace ta bi bayanta da gudun itama tana fadin baki isa ba walahi! A bayane ta ce" Lah " tana firfito idannuwanta gaba daya da mamaki
Dubanta ta maido kan Furera, kafin kake cewa tak, ta fice itama da dan gudunta har tana waiwayen Shuwwar din, domin ita yanzu ta fara tsoron yarinyar nan, shegiya mai karfin aljannu (😒)💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 3️⃣5️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
Sai ya rage daga Malan sai SHUWWA
Kansa shi kuma a kasa ya kasa dagowa har sai da Shuwwa ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Abana "
Idannuwansa ya lumshe kafin ya dago a hankali yana kirkirar murmushi yana kallonta ya ce" Na'am Shuwwan Abanta"
SHUWWAR ta ce" Ka san wani lokacin Aunty kan haukacewa kau? Kawai ka hada sadakinmu mu je mu kaima Hamza"
Dan murmushi ya