Showing 201001 words to 204000 words out of 226733 words
gaba da raka shirmenka ba Allah yafe maka zunubanka!"
Kunamar bindigar ya danna, a haukace Wajen ya dauki kabara wanda hakan ya sake tarwatsa zuciyar Khamis, har bai san lokacin da ya fara magana a haukace kamar haka ba" Wayyo Allahna wayyo kar ka kashe ni, kar ka min kissa irin na bindiga, kar ka kashe ni na aamsa laifina, na aikata nine nan na aikata dan Allah ka yafe min na aikata ba zan kuma ba, wayo Allahna na shiga uku ga zoben gayanaan zoben gashi na cire gaya nan, kar ku kasheni tunda ban kashe kowa ba, na san na aikata asiri na fitar da shi daga kasar, kuma na haukata kanina aman bayan wannan ni ban kashe kowa ba"
Muhyideen ya amshi zoben yana sakinsa ya ce" Damar kisan ne Allah bai baka ba, aman ai ka dauki niya"
Ya juya wajen yarensa ya basu umarnin a tafi da shi da dukkan wasu masu take mada bayan da bai yarda da su ba, idan aka gama bincikw kotu ta yanke masu hukunci daidai da laifukansu su dukansu
Sai da suka gama watsewa sannan ya fuskanci yan jaridar ya kuma basu damar yi masa taambaboyin da suka shafi hawan sabon sarki, inda ya bada amsoshin a takaice sannan a bude, yana gamawa ya yi masu salama sannan ya koma wajen da sojojin ke idasa daidaita wajen domin ci gaba da wunin biki
Ido cikin ido suka yi da Malan dake tsaye yana binsa da kallon al'ajabi
Dan murmushi ya yiwa Malan din yana fadin" Ni wollah idan na ganka sai zan gaisheka sai na tuna ashe nine Aban Nahidt har a saman takarda"
Ido Malan ya karra warawa kafin ya samu kansa da sakin murmushin shima yana girgiza kai, kasa kasa sosai ya ce" Wai yanzun shikenan ni mijin NAHIDT ne?"
MUHAY ya dan kankance idannuwansa sai kuma ya gyada kai yana fadin" to mu je ka gani eh ne ko aa ne, ka ga kidan cen yana sakawa du hankalina tashi ina son shiga ina tsoron abinda zan tarar"
Yar daria ya yi yana fadin" Ka amso rigarka ko ta cikin ce ka saka mu je ai da kunya ka shiga a haka ko?"
Sai a lokacin ya waiga wajen da ya zubar da rigar, sai ya rigunnan a saman cinyar Aban Shuwwa sunna zaune da shi da mutanen dake gefens sai Dad
Ajiyar zuciya ya sauke ya tafi amsa hankalinsa kwonce
Yana zuwa ya duka kasa kansa a kasa, a sanyaye ya ce" Ku gafarceni na zarce abinda aka tsayar, na san abu ne mai matukar wahala hadiye irin haka, aman da ba'a yi haka ba ba zai taba mika wuya ba, ku gafarta min"
Sai a lokacin hankalin Aban shuwwa ya sake kwonciya, domin shi du jira yake ya ga an ririke Muhay a yadda idannuwansa suka kade lokaci daya ya ringa surfa tashin hankalin nan kwarai ya tsoratar da shi, shi da kansa Dad a lokacin da yaron nasa ya danna kunamar harbin nan sosai ya tsorata dan tabas ya dauka zai yi harbin ne, duda ya san da wahala ya dauki doka a hannunsa kai tsaye ya tsartar, aman kuma irin yadda abin ya nuna na ci masa tuwo a kwarya kowa ya sare , da wannan suka sake yi masa nasiha da fatan Allah ya tsare shi kafin ya amshi rigar tasa ya saka abinsa ya yi gaba
Shi kam dama Malan tuni ya fara yin gaban yana jiransa, dan shi kam ba zai iya gwa da gwa da sirikin nasa ba, kunyarsa yake ji fa sosai da sosai
Baban get din suka nufa, duda irin yadda wajen ke hargitse suka kutsa sannan suka dauki dayar hanyar da sun tabata a cen ne kidan nan haka kuma ba shaka matan nan na cen
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce" Allah ka bani ikon hukuntata idan na sameta a cikin filin rawar cen, ya Allah kar ka sa na zamto tamkar gabo a gabanta maimakun nai mata fada sai dai na rarasheta ya Allahna"
Aban SHUWWA ya yi murmushi yana girgiza kansa ya ce" MUHYIDEEN, yanzun idan sunna wajen cen ke zai faru? Kai fa da dama kanama iya yin ido, ni kam sai yadda Allah ya yi da ni, tsorona daya kar ta maimaita kwatanta aikata aikin da ta aikata a asibitin nan"
Me Muhyideen zai yi banda daria, dariar da sai da Malan ya ji mahaukacin mamaki har ya dan tsaya yana kallonsa
Sai kuma shima ya yi dariyar suka ci gana da tafiya
Malan ya ce" Idanfa matan mutane ne a wajen cen da muke nufa?"
MUHAY ya tabe baki ya ce" Inaga ai muma mazan mutanen ne, ka ga fa a gaskiya idan zaka koma ne ba damuwa aman ba mai sajani juyawa bayan ina ji a jikina tana wajen cen, kuma mai kwasarwa makadan kudadensu namiji ne! Ni na ganshi namiji ne!"
Ai kam shima yana jin hakan ya samu kansa da yin gumm ya bi bayansa suka karasa wajen
Daga nesa kadan suka tsaya sunna kallon ikon Allah, wajen ba zai shigu ba domin mata ne sun zagaye wajen ana kidan da aka kira na sarautar masarautarsu
Ji ya yi hankakinsa na neman sake tashi dan haka ya laluba aljihunnan jikinsa domin a sanninsa akoy karamar wayar da ya saka dan kira
Kira ya tura ya koma gefe ya saka a kunnensa
Ta jima tana ringin kafin aka daga
A hankali ya ce" Mamah, kunna ina ne?"
Mamansa dake cen wajen nadin gimbiya ta sheda masa ai sarkin ya shigo ana nadin gimbiya
A dan gagauce ya sake tambayar su IBTISAM fa?
Mama ta ce" Sunna bangarenka dan jama'ar ta yi yawa sai na tura su cen harda matan MUHAMMAD "
Ajiyar zuciya ya sauke yana dan murza gaban goshinsa a hankali ya kashe ya juya yana fadin" Sun tsira, sunna bangarena"
Muhammad ya sauke ajiyar zuciyar shima ya ce" Ko dai mun tsira ba"
Da wannan dan barkwoncin suka kuma nufar bangaren nasa, ba dan komai ya nace kan sai ya je ba sai dan ya dan kwatanta mata kar ta je cen din, dan ya kula wajen karra daukan harama yake yi, matan zuwa suke kansu da kafarsu
Shi ya fara shiga bayan ya yi salama an bashi damar shigowar
Kasa kasa Shuwwa ta furta" Katona ne"
Nahidt dake zaune taa hakimce Shuwwa din na mata gyaran akaifu ta yi dan murmushin da ya sake yanke gaban Furera ya fadi kasa kasa itama ta ce" Allah ya sa banda Abanki, Shuwwa sai nake ji kamar ina jin kunyar Abanki, kar dai an shiga gabana ban sani ba"
Shuwwa ta yi yar dariya ta mike tana rike dan kwalinta dake son faduwa ta wuce ta gaban Furera dake zaune kauyenta daban bata cikin mutane, fuskar nan tata tamkar an aiko mata da sakon mutuwa, tabas da Malan ya ce ta nemi abinda zai tareta bai yi karya ba, domin a lokacin da jarababiyar makeriyar ta budi baki take fadin maganar da kowa sai da ya girgiza ita kasa ta yasu, tun daga lokacin kuwa du inda suka nufa idannuwanta a kansu, a kasan zuciyarta kuma fata take yi kamar haka.....inama idan aka dauki amarya a motar rakiyarta motar ta juye da su su kone kurmus ta yadda labarinsu zai shude a doran kasa? Ota ta san wani hadi ne dan a wulakantata, ta san wannan maganar karyar karya ce, ina hadin biri da gada ? Wulakantatun nan ne za'a nemi rufawa asiri a wani hada magana tamkar saukar aradu? Sarautar garinsu mai karfi a africa itace ta hayo kan wadinnan?, Tana kallonsu ne dan ta ga iya gudun ruwansu
Tana karasawa daga wajen da yake ta zubawa fuskarsa ido da kuma jikinsa
A hankali ta ce" Ina babar rigar?"
Jikinsa ya bi da kallo sai kuma ya kalleta, itama ba abayar sai doguwar rigar kadai a jikinta ta cake daurin nan na tsokana
Dan gyaran murya ya yi irin zai yi kasa kasa sosai din nan ya ce" Tana wajen Aba, ina abayarki?"
Dan murmushi ta yi ta ce" Ka daina yin kamar zaka yi rada, ana jinka ko a hankali ko da karfi MUHYIDEEN"
Kikifta ido ya yi yana kallon bakin da ya ce MUHYIDEEN din, kasa kasan ya sake fadin" Ba ko sakaye, irin sunnayen nan da ake fadawa ababen kauna?"
Kunya ce ta kamata, ta dan sada kanta sai kuma ta dago ta kashe ido daya ta ce" Irin su my kankanar saudiya? My atarugun italiya? My fari masar Parissss?"
Daria ce ta subuce masa har sai da ya saka hannunsa ya rufe bakin nasa ya dan dara a cikinsa kafin ya saka hannun nasa ya dangwale hancinta ya ce" Kece kankanatah..........."
Ido ta zarro tana fadin" Ana jinka fa"
Bakinsa ya sake tabewa ya ce" Inace matan Abanki ne a ciki ko da wasu bakin ne?"
Kai ra girgiza dan haka ya sake tabe bakinsa yana fadin" Je cen kurya ki labe da katon Nahidt muke , ban san me yake so da ni ba, ba zai iya hakurin na kika masa matar bane ko menene? Sai na ji kamar na hanna masa anya wannan ba zai yi zalammmmmmm......." Dif ya dauke wuta sanadiyar hade bakinta da ta yi da nasa bayan ta yi dadage sosai ta cafke lebensa ta rike damatsunnan hannunsa kafin a hankali ta shiga tsotsar bakin nasa, wanda hakan ya saka shi yin baya baya kamar zai kifa sai kuma ya damke bayanta da hannunsa daya ya cika duwawun a hannun nasa ya matsa da dan karfi yana sake rintse idannuwansa
Da sauri ta cire bakin nata tana shigewa kirjinsa tana maida numfashi sannan kasa kasa ta ce" Aban nawa kake cewa zalamame? Kuma fa matansa duka sunna ji, idan suka kulaci abin fa? Ka san mata abin kishi baya masu kadan, kai kuma muryarka bata da sirri My alawar gwongwaninah......."
Idannuwansa dake rintse ya ringa hadiye yawu da kyar ya iya fadin" Mu tafi gida Ibtinah kin ji?"
A hankali ta dago fuskarta tana kallonsa, a sanyaye ta ce" Da gaske kake ba zan raka Nahidt dakinta ba?"
Shima kurre fuskar tata ya yi da kallo yana tunani yana cewa sun gama maganar nan kau? Sai kuma ya maida kanta saman kirjinsa ya dora a hankali yana shafawa ya ce" Kin ga jirgin da zai kaisu nan da awa daya zai sauka , zasu juya da yan rakiyarta mutun hudu da Dad ya wakilta kuma a dawo da su a yau yau, Ibtinah muma a jibi zamu koma na koma bakin aikina, sshikenan gaki gata, za'ina kaiki da kaina gidanta ina dauko abina, aman yanzun ki min uzuri ki zauna da ni itama ki ba Abanki daman ya zauna da ita na yau da gobe kawai.............." Ya karashe a hankali yana sake kallonta, ya kuma dago habarta ya ce" Na kamu, na kamu da yawa.......ba zaki fahimta ba, aman baban tashin hankali motsawa daga kusa da ke, aman idan hakan zai tayar maki da alkhairi hankali zan yi hakuri"
Idannuwanta ta lumshe a hankali tana kallonsa na yan dakiku, ya kamu da me? Ya kamu da mene?
Sai kuma ta saki murmushi a sanyaye ya sake maida kanta saman kirjinsa tana fadin" Allah ya nuna mana jibin in sha Allah"
Sosai ya yi mamakin yadda ta yi saurin yarda da abinda ya fada din
Bai san lokacin da ya rukunkumeta a jikinsa da dan karfin da sai da ta yi dan karra kafin ya sasauta mata ya sake dago fuskarta yana kallon fuskar tata
A fuzge ya ce" Ke fa idan kika tsufa a haka aljannar nan da kanta zata zabe ki Ibtin MUHAY, Allah ya yi ya matso min awanin nan na mika wancen hannun wancen na jaki mu je inda ya dace muryata ta bude hankali kwonce".....
Da sauri ta sake sada kanta tana cike da kunya ta juya da gudu ta shige ciki tana yar dariyar da ta saka Furera sake binta da kallo har ta karasa wajen da suke zazaune ta dauki jug din tsumin Nahidt ta kafa kai ta sha sosai ta ajiye tana yiwa Fauzy muzurai ta ce " Abinda ba zai barni ba gwara ya kasheni a huta!"
Haka suka tuntsure da dariyarsu sunna tafawa wanda hakan ya saka Malama sauke ajiyar zuciya tana cire tunanin cewa wai Malan ya kasa zama da hakurin har a mika masa ya zo gani? Aman gannin shiru bai shigo ba sai ya saka ta ware ta ci gaba da tsoma bakinta a hirarsu sunna shan dariyar tare, inda Furera take kutuntuma ashar kala daban daban a zuciyarta tana tsitainema kowa dake wajen, sai dai ba halin nunawa domin bata manta zaneta da wannan mai shige da baby dol din ta yi ba, zasu koma ne zasu zuba kishin da yayarta ba ita ba! Su zaaiwa karyar sarauta ?💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 7️⃣1️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
Da wannan tarin taron farin cikin aka kusan wuni ana tarbar baku ta ko wani bangare, domin auren ba na Nahidt kadai bane aka daura, kowa daga bangarensa yana abinda zai gyara shi har lokacin tafiyarsu ya yi
A lokacin da akai masu rakiya aéroport ya kasance sun cike filin jirgin ne, domin Aba da yan rakiyarsa ciki harda su Dad da Mama, domin sai Mama ta mika Nahidt dakinta zata dawo,
A daidai lokacin da zasu daga ne Shuwwa ta fashe da kuka, da kyar aka rarasheta domin tunda take bata taba rabuwa da yar uwarta na kasa da kasa ba sai yau sanadiyar darajar aure, ita kanta Nahidt din kukan take yi kamar ranta zai fita domin ta fi tausayawa kanwarta a kan kanta, sai dai yaya zata yi, dole zata tafi, idanma ta yi hakuri ai Shuwwa din ta ce Zasu dawo suma tare
Da wannan suka dawo wajen da zasunna hangen tashin jirgin duba da ba'a bari a matse waje idan baka cikin masi dagawa, danma sojan dake tare da ita ne ta yi rakiyar ciki
Tana jingine a kirjinsa har jirgin ya fara tafiya a doguwar hanyarsa , sunna hangensa har ya cida ya tashi, hakan ya saka ta fashe da wani kukan tana rungume tahi a jikinta hadi da fadin" Ta tafihhhhhhhhhh"
Ajiyar Zuciya ya sauke a sanyaye ya ce" Zan fa taya ki kukan nan, kuma kin san za'a shiga tashin hankalin kallo a wajen nan, ke na kula bama kukan su Aba sun tafi kike ba, na wancen y'ar kike, kuma ni du a banza ko?"
Kanta ta dago tana ta shashekar kukan ta kalle shi ta ce" Nahidt ce fa, Nahidt dina ce fa"
Fuskar ya kurawa ido yana ayana' Na shiga uku, wabilahilazi shagwababiya ce ta karshe, yanzun rarashi fa zan yi dole fa, ko ta ringa tale bakin nan har kartin cen su kalla'
A bayane kuwa sai ya riko hannayenta yana fadin" Kin ga in yauma kike so mu bisu kawai sai mu bisu, saima mu je mu yi waya da Aban naki tunda dai bangaren na Nahidht din dakunna hudu ne kawai a gyara mana daya gamunan zuwa ko? Share hawayen mana haba anmatana"
Yana maganar yana janta ne suka nufi cen balbalin da ake ajiyar motocin ya bude mata da kansa ta shiga ya rufe ya zagaya yana karra muzurai da gannin sojojin sun wani zuba masa ido da tarin mamakinsa
A hade ya ce" Kowa ya tafi gidansa ya huta tunda kun ga karshe"
Sumui sumui kowa ya nufi motar da ya zo da ita ya shiga kowane na kunshe dariyar rigimar rigimamensu a gaban hajia babarsa, wai dama haka ya iya kula da Matarsa ne?
Bayan ya shige da aka bude masa ya sake janyota jikinsa ya kwontar , da gudu bodyguard din nasa ya zagaya da direban suka shiga jan motar
Shashekar kukan da take yake ta sauraro yana sake shafa bayanta
Sunna isawa tun kafin Bodyguard din ya iya bude masa motar ya bude sannan ya duka ya taimaka mata ta fito
Dauketa ya yi cimak a hannunsa ya juya ya shige ciki bakinsa daidai kunnenta yana fadin" Kukan nan kam saura kiris na saki nawa, saura kiris Ibtinah"
IBTISAM kam ta jima da dangana, ta dore da shagwabar ne dan ta ga ta karbu, shagwabar tata na sakata nishadi ita da kankin kanta, inda masu bashi tsaron suka sake mutuwa da mamaki kafin General Almustapha ya furta" Alhmdulilah, yanzu barikin sojoji ta yi Uwa, Allah ya sa ta kasance mai kwontarwa oga hankali, dan kar ta ringa tada masa mu kuma yana jijiga mu!"
Du da amen suka amsa sannan kowa ya koma bakin aikinsa, bi ma'ana masu hawa suka hau , masu sauka kuma suka sauka
Kasancewar cikinsu du a cike yake, haka kuma sun yi sallah sunna shiga da kansa ya yi bayi da ita yana cire mata dukkan abinda yake