Showing 96001 words to 99000 words out of 226733 words

Chapter 33 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

7982

kwankwasa a hankali sannan ta bude ba tare da ta tsaya an bata izinin shigowa ba, abinda ya sakata kwonkwasawar ta san yanzu du inda yake ya dawo daga masalaci ai

Da salamarta ta shiga ta dora da fadin" Gafara dai mutan nan"

Tsai ya yi da turaran da yake fesawa yana kallonta sannan ya samu kansa da kallon wajen da ta ajiye kayan aikin nata harda dan yin dadage , ya dawo a hankali yana bin dakin da rabonsa da gannin koda yar kura ce Tunda ta fara gyaransa

"Barka da safiya yalabai" ta fada a hankali tana dan murmushi sannan ta juya ta shiga bin dakinsa da kallo har ta sauke dubanta a kan fitilun da sak irinsu ne da ita a dakinta, sai dai a nan din babu camerar nan da aka makala mata a nata dakin

Dan tsare fuskarsa ta yi da kallon tuhuma domin a lokacin ya kawar da kansa a bangarenta , aman kasancewar ta riga ta kamu da rashin yarda na gidan gaba daya sai ta samu kanta da nufowa wajensa tana sake dan lura da dakin dan tana neman wajen da zata ga wata camerar

Kasa kasa yake kallonta a kansa Yana tunanin me kuma yau ta raya mata aikatawa ne?

Hannayenta ya ga ta bude a bayane sannan a sanyaye , ga wani murmushi irin na zata raina masa wayau ta ce" Oh 🫂 hug me husband"

Ido ya zarro ya samu kansa da dan yin baya yana kausasa dubansa a kanta yana kallonta

Sarai ta ga cenjin mood dinsa, sannan ta ga yadda ya hade girar sama da ta kasa, aman gaba daya bata yi nigar dakatawa ba domin idan yana mata kallon mashayi bayan bata daga kwalba gwara ta yi anfani da damar ta yi masa aikin mashaya koma zai ji haushi ya saketa su gudu tun kafin a sakata a cikin fadan neman rai, hakan ya sa gadan gadan ta karra nufarsa duda jan da ya yi a mamakance baya yana sake kallonta da son gane shin a bige take ne ko mutanen nata na kusa ne?

Gannin da gaske rungume shi ne take nufin zata yi a irin lokacin nan da ya tashi ba kanta da kuma azuminsa a bakinsa gashi singileti ce a jikinsa bai riga ya dora rigar kakinsa ba, duda ya riga ya sani cewar babu abinda ta isa ta yiwa azuminsa ko yannayinsa , aman kuma ya san cewar shi dan giya kawai ka kiyayi lamarinsa dan yana tare da matsaloli irin na mashayi a kansa
A dake , sannan magangannunsa a hade ya ce" Hey stop 🛑!"

Dakatawar ta yi tana kallon fuskarsa a sanyaye , sannan a shagwabe ta ce" Why?"

Gefe ya kauda kansa kafin ya juyo yana kallonta da mamakin tambayarsa da take a kan wani dalili ya dakatar da ita

Idannuwana ya kankance ya ce" Kin sha wani abu ne?"

Ido ta dan zarro da yannayi na mamakin karya da ta dora a saman fuskarta ta ce" Sai na sha wani abu zan so rungume mijina da safiya dan na gaishe shi? Bama wannan ba yanzu kai ka san mutuwa garemu civil ma yaya ta kare yanzu kana iya tafiya ka dawo ka iske gawata, bale ku sojoji kana iya fita wani dan ta'ada ya labe ya daukeka shikenan sai haduwarka da mai sama, so kake karamar magana ta zamto maka baba ne? Ka ga fa kai a ganninka kawai ka dakatar da matar da ka tsana wa zuwa rungumeka ne, aman a wajen ubangijinka abin zai bada wani abin ne daban, matarka nake, ina dauke da dukan haki a kanka nawa, ciki kuwa harda idan na rungumeka kiya......" A sanyaye ta dauki maganar, a sanyaye ta direta, ta yi maganar ne a hade kamar dukkan damuwar dake cen kasan zuciyarta take amayarwa, tamkar idan bata rungume shin ba wani abu na iya samunta, gaba daya ta yiwa fuskarta kalar tausayi da kalar dake nuni da gaskiyarta iya abinda ke ranta take so a barta ta yi, hakan ya saka shi sake zuba mata ido da mamakinta a ransa
Bai kuma ce mata ufan ba , haka itama daga wannan din bata kuma cewa komai ba sai dan daga kafarta da ta sake yi da niyar nufarsa tana mai adu'ar Allah ya sa ya hannata, domin a cen kasan zuciyarta ita da kanta tunani ne cike da Tsoron abinda take son aikatawa, shin wai zata iya aikatawar kuwa?, Zata iya zuwa ta rungume shi kai tsaye kuwa? Aman gannin da farko ya dan ja baya sai ta karra matse masa waje har dai ta ga yanzun bashi da jiyar motsawa bale ya tareta ya hannata fada masa a jikinsa hakan ya sa ta dago tanai masa kallon da kaima haka halinka? Ka ga yyar mutane zata afka maka ai sai ka gudu kau?

Gaba dayanta ne yake karantarta, kwarai ya tsaya ya gani wai da gaske rungume shin ne zata yi? Kai da ya ga tsaurin idonta walahi, aman da ta tsaya din sai yake son karantar kamar wace ke jin kunyar aikata hakan ba jin tsoro ba

Watau Tsoro daban, kunya daban, idan jin tsoron aikata haka ne ya bayana a fuskarta hakan na nufin shine take jin tsoron rungumewa kamar yadda sauran matansa ke nuna tsoronsa karara a bayane, hakan na nufin ba wai saba rungume rungumen wasu kartin bane bata yi ba, aa, tsoronsa ne ya dakatar da ita
Idan kuma kunyar hakan ne ke dawainiya da ita kamar yadda yake karanta a yanzu lalle lalle da ya shiga cikin tunani mai girman gaske, dan bariki da kunyar runguma? Bale ya san halalinsa zai runguma din? Kai da ya afka a cikin tunani gaskiya mai girman gaske

A nutse ta dan sake jimke hannunta tana murzawa tana kallon damtse hannunsa a ranta tana ayana' Allah ya taimakeka ni ba yar iska bace yau da ka ga gani gannin idonka, wayo Allahna to ni ta yaya zan iya rukunkume kato kai tsaye ne? Gaskiya sai na je NAHIDT ta sake min karatun fari fari, sai da ta fadan cewa mijina ne idan na aikata ba laifi bane ba aman kuma na zo na kasa aikata hakan

Da kyar ta iya aro jarumta ta dago kanta tana kallonsa ta ce"💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥


*The Hero writer*


*SAJIDA*


_Bismillahir rahamanir rahim_


PAGE:. 3️⃣2️⃣



*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*






*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*


*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*



*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*



*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*


*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618


Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰











Da kyar ta iya aro jarumta ta dago kanta tana kallonsa ta ce" Ita camerar da ka saka min a dakina na sirri menene anfaninta?"

Fuskarta wannan karron da bakinta ya kure da ido cikin kallo na hankalta
A hankali ta ga ya dan kalli gefen irin a kiyayencen nan, kafin ta jita gaba daya wani lalausan hannu ya janyota da dan karfi ta fada jikin nasa da ta ja dunga take jin kunya
Duka bata tantance aimahin abinda yake faruwa ba sai ji ta yi yana dan tafia da ita a hankali a cikin kirjin nasa ba tare da ya furta mata ufan ba, domin shi muryarsa bata da sirri du irin tarin maganar dake cikin bakinsa na tambayoyin da suka cika masa baki da mamakin Camera kuma? A dakin barcinta kuma? Subahannalah, subahannalah, hakan na nufin a dakin da take cenza suturarta, dakin da take dukan sirinta kanta tsaye ba tare da tunanin komai ba, a cen take nufin ta ga camera? Lalle ya yi sake, shi ya san da ta dakinsa wace aka boyeta a karkashin gadonsa gefen damarsa, hakan ya sa dukan abonda zai yi ya san takunsa, bai taba tunanin har an iya shiga dakin dake jikin nasa a kakafa ba, ya san da uku dake cikin gidan, daya a corido, daya a falo, daya a kicin, gaba dayansu ya san da su ne sakamakon amintacen abokinsa da ya saka massa camerorin nan, mutumen takadari ne, mugun mai ilimin da ya san kansa ne, caméra ko wace iri ce ya san kalarta sannan idan an yi dabara an boye yana iya ganeta da zarar ya kalleta, shi ya sheda masa wajen da kowace take harma ya nuna masa yana iya cire su, a nan ya hanna shi ya ce ya barwa mai son ganni ya sha kallo abinsa, bai taba tunanin da wata a dakin sirrin macen da zata amsa kiran sunnan tasa ce ba

Jikinta gaba daya rawa yake yi, hankalinta a tashe yake, gabgabgabgab tamkar zata saki fitsari haka take ji
Ki gane bata saba ba, sunnanta ne ya je wajen da bata je ba, bata san irin wannan aikin na, fitsararta a bakinta ne a cen din ba husssss domin ita ba sannin irin haka ta yi ba, gashi a jikin Soja, sojanma wanda ya saka aka maka mata saki a ofishin sojoji kawai dan yana tunanin sato kudi ta yi ya yi kiranta ya maido maganar dan ya tabatar, yau gata a jikinsa gaba daya jikinta ya mutu ta yadda bata iya anfanar da kanta komai harta da motsawa yana yi ne da ita a jikinsa domin bar kafarta daya ta haye saman tasa dayar kuwa ga dukan alamu janta ake a kas

Sai da ya tabata ya wuce wajen camerar corridor din nan sosai sannan ya ci gana da acting like soyaya ce mai sunnan soyaya ya kawo bakinsa wajen kunnenta ya maida muryarsa shakakiya sosai domin bai iya magana irin ta sirri ba in dai ba shake muryarsa zai yi ba, idan ya shake muryarsa kuwa takan bada wani yannayi ne daban, takan bada yannayi ne irin na wadda yake cikin wani hali na bukatukar mace a gefensa, koma nace a cikin jikinsa, aman yaya ya iya da wannan yarinyar da ta fada masa maganar nan haka? Allah dai ya sa ba tumbur take yi a dakin nata tana yawo tsirara ba, kai da ta ba masu nema abin kallo kuwa

"Yaya aka yi kika ga camera a dakin cen, kin ga idan shirme kika fada min komai na iya faruwa" ya fada kasa kasa sosai, hakan ya sakata jin kamar yanai mata tafiyar tsutsa ne a jikinta har cikin kwakwaluwarta, wannan dalilin ya sa ta rukunkume shi da karfi tana rintse idannuwanta

Idannuwansa ya rintse yana sauraronta har ta dan sasauta masa tana sauke ajiyar zuciya muryarta a wani kala na shagwaben da ita dai bataa yi da wata manufaa ba domin batama san anfanin hakan ba ta ce" To ni dai ba na gani bane ba kawai, a ciki ne mana "

Shiru ne ya wanzu na dan lokaci kafin ya sake maidata cikin jikinsa dan baya so abinda ya faea sakawa masu kallonsa a ransu ya fita a ran nasu

Tunda suka shiga ya kai bakinsa wajen wuyanta ya lumshe idannuwansa ya sake riketa a jikinsa sosai ya kai wajen sajensa a hankali ya shiga dan gogaa mata a wuyanta yana dan juyawa da ita yana hankalta da yannayin dakin yana ta dube duben camerar

A zabure taa janye jikinta jikin nata naa bari tana kallonsa da mamaki da tsoron meye haka kuma

Hannunsa ya saka ya maidota jikinsa muryarsa a shake ya ce" oh plz dea"

Gabanta banda dukan dari dari babu abinda yake yi a lokacin da idannuwansa suka sauka a kan abinda ke nanade da wani bakin abu wanda ya tabata lafiya maginan gidan nan ba zasu aikata haka ba, haka kuma wa'inda suka yi gyaran gidan ba zasu saka abu haka ba
Cen kasan zuciyarsa ya shiga tunani da wani dan baci bacin ran dake dan bijiro masa na tunanin ashe a dan sika suka dauke shi mutanen nan? Abin nasu har ya kai nan? Zai iya rantsewa bacin ransa bai taba ji yana hauhawa ba irin na yau, sai ya samu kansa da tunanin ta yiwu ko a sauran dakunnan da yake ajiye iyalinsa sunna saka camerar da zata ringa hasko masa har tsiraicinsu

Tsigar jikinsa ne ta ringa ta tashi na bacin rai hakan ya saka shi rintse idannuwansa da karfi sannan ya juya a taku biyu ya hade bayanta da jikin garu daidai saitin camerar, irin ya tabata abinda camerar ke harska masu a yanzu ba net bane, aman duda haka yana so su saka wani abu a ransu wanda basu taba sakawa ba, duda ya san zai iya jazawa yar mutane wata fitinar itama ta kasance cikin abinda zasu yi hako, aman kuma ya zama wajibi ya kwatanta masu cewar yana aikata sunna da ita ta yadda zasu sake daukar aniya, gaba daya ransa kuwa ya gama yin bakinkirin da tunanin cen, ya kasance mutun mai matukar kishi a kasan zuciyarsa, yana kishin iyalinsa kamar me, baya hada maganar iyalinsa da wani abun, shi din bai taba yin zam da mace mai sunnan zama ba, aman ya gama tsarawa kansa cewar du matar da zai zauna da ita zaman aure to fa ko yan yatsunta ba zai bari wani kato ya ringa gani ba, dan zai ringa kwaso mata safar hannu da ta kafa da na fuska ne yana cika mata dakinta abinta

Sai da ya gama yarda lalle camera ce sannan ya daga hannunsa ta kasanta ta inda ba'a gani ya daka mata dukan da ya saka ta karkace ta cire hakan ya sa ta lalace kennan,

Sakinta ya yiita kuma ta fice daga karkashinsa da gudu ta tsaya tana haki tana kallon bayansa

Dan dage ya yi kadan ya idasa cirota daga jikin garun gaba dayanta ya riketa a hannunsa yana jujuyata,

Pant din dake jiki ya warware ya cire ya bude shi dan gannin ko menene ta ninka ta rufa

Ido ya tsurawa Pant din mau kalar baki, haka itama idannuwanta ta tsurawa Pant din tana kallo tamkar bata san ko menene ba, haka kawai sai ta ji ta tsargu harma ta ji kamar ita din yake kallo da yannayi na harare

A hankali ta dago dubanta ta sauke a kan fuskarsa, a nan ta ga ita din kuwa yake harare da mugun kallo irin na neman fitina ido rufe ba ji ba gani

Ajiyar zuciya ta sauke , dama ba wai hayacinta ta idasa dawowa daga rungumar kato da ta sameta yau ba, sai ga kuma wani tashin hankalin yanai mata kallo kamar ya kama barauniya koma me zata ce oho

A hankali ya taka ya je bakin bed dinta ta zauna yana dafe gaban goshinsa da karfi da hannunsa na dama yana ta danne dacin dake taso masa a cen kasan zuciyarsa

Da yan yatsunsa ya mata nuni da gabansa bayan ya dago da jajayen idannuwansa ya sauke a saman fuskarta

Wajen da ya nuna ta bi da kallo, sannan ta juya da sauri ta kalli hanyar fita ta kuma juyowa tana kallon sawayensa da bai riga ya saka safa ba
A yan sekwani ta gama auna cewar idan ta ce zata fita daga dakin nan kafin ta je infa zata je dan samun malaba ba haufi ya kamata a hannunsa ba tare da ya sha wahalar hakan ba, idan kuwa ta samu ta gudu Wajen yayar tata bai zama wajibi ta tsira ba, domin ta tabata wannan mutumen ba tsagen kunya a tare da shi yana iya hada su ita da yayar tata ya masu dakan danyen mangwaro da kuli tasss ya kirbe har sai sun fitar da mai
Hakan ya sa a hankali ta kawo kanta sannan ta zauna a kasa ta dago kanta tana kallonsa

A gajiye a hankali ya ce" A gaban camerar kika cire wandonki?"

Tsuru tsuru ta yi tana kallonsa, ita dai ta san a gaban camerar nan dake hannunsa ta cire wandonta, aman kuma bata gane tambayarsa ba sam kai bata fa gane tambayarsa ba hakan ya sa a sanyaye ta ce" Ban gane tambayar ba ai"

Kasancewar ya riga ya yi waje ya ajiye yarinyar nan ya kuma san cewa babu yarinyar da za'a yi wace zata masa irin rainin da wannan ta yi masa a duniya ya sa ya dauki tambayarta da sauki harma ya bata damar bashi amsa ba tare da ya sake furta mata ufan ba

Dukan Alamu na jikinta zai daku a yau sun gama bayanar mata a fili, hakan ya sa ta dan fara lumshe ido tana dan mar da Idannuwanta

Wandon ya ajiye a saman kafarsa a sanyayensa ya ce" Kin san wani abu?, Idan kika tada aljannun nan naki yau? Da duka zan sauke maki su , duka irin na wulakanci zan maki na sauke maki su!"

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonsa tana karkace kai a sanyaye ta ce" Dan Allah ka min rai mana ka ganar da ni tambayar taka kar a je na bada amsar da ba ita ba, ni dai a sanina lokacin da na ga camera a dakina sai na ce lalema aiki irin na mai doka ya take dokarsa , sai kawai na cire wandon na naka a jiki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login