Showing 105001 words to 108000 words out of 226733 words

Chapter 36 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

7943

yi yana kallonta ya ce" Shuwwan Abanta idan fa da gaske take? Idan tana tsoron auren wanda baya haihuwa ne?"

"Subahannalah Abanah , subahannalah, dan Allah kar ka saka haka a ranka, na rantse maka tana sonka kuma zaka ganni gannin idannuwanka" Shuwwa ta fada jikinta na yin sanyi sosai

Wani murmushin ya sake yi yana kawar da zancen ya ce" Menene yake damunki? Na tabata akoy damuwar dake damunki"

Kwarai ta so ta bar maganar sai ko zuwa gaba, aman wannan maganarma mai mahinmanci ce, ba zata iya barinta haka ba, kuma ita dai a yanzu shi ne mutumen da zata iya fadawa wannan maganar, dan haka ta fuskance shi a sanyaye ta shiga fada masa dukan abubuwan da suka faru ta dora da fadin" Abahna, gaba daya na shiga hali na zargin kowa da kowa, wanene mai aikata haka? Koma wanene yana da dama a gare shi sannan Yana da kusanci fa shi ta yadda har aka ita shiga dakina aka saka camera, shin kafin ni sauran matansa da haka a dakunannsu? Matarsa dake garinsu itama an kirayeta ne? Ta amince da haka ne? Da wata maganar aka jinginata ne? Shin menene dalilin dake rabashi da mata? Abana gashi mai taurin kan tsiya bale a tambayeshi ya bada amsa cikin sauki, shi yasa na ce kawai mu zo, Nahidhtma ta ce gaskiya mu zo"

Gaba daya abin ya daga masa hankali ta yadda ya yi shiru yana nazari, "Ya salam" shine abinda yake ta furtawa a sanyaye kafin ya dunkule hannunsa ya ce" Mun shiga a cikin tsaka mai wuya IBTISAM, mun shigo a cikin yannayin da ya zama wajibi mu ringa kaye kaye a cikin kwakwaluwarmu, mu ringa zargin kowa, muna duban kowa, sai dai mu tuna cewar zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne........"
Ya sakue ajiyar zuciya ya sake fadin" Hasbunnalahu wani'imal wakim, shin tun yaushe hakan ya fara samunsa? Waye abokin hamayar dake neman ransa? Kisa? Me yayi da zafi haka?, Na san cewa ko a sanadiyar kujerar da ya taka , watau matsayin da ya haura yana iya samun abokin hamaya, ta yiwu kuma wani ya taba hukuntawa hakan bai masa ba, subahannalah koma menene me ya kai na shiga hurumin iyalinsa? Wani namijin da a taka lamarin iyalinsa gwara ka kashe shi ya san kashe shin ka yi"

Shuwwar ta dan tabe bakinta ta ce" Ni wollah Abana du sai abin yake min wani iri, wai shi iyayensa da rai kuwa?"

Makan ya kaleta da dan mamaki ya ce" SHUWWA, shin baki zauna da shi ba har yanzu?"

Rashin gane tambayarsa ya sakata tabe baki ta ce" Kai Abana wannan ake wata magana da shi? Shi fa kulun kashedi yake min, dazuma dai ya ce ba'a saka shi magana na kiyaye na ce ka ji dunkum!"..........sai da ta gama zubar kuma ta rufe baki tama fadin" Ba dunkum nake son cewa ba Abana"

Malan ya sauke ajiyar zuciya yana girgiza kai a nutse ya ce" kina jina?, Ina so ki fuskanceni da kyau sannan ki fahimci abinda nake son fada maki, SHUWWAR ko wanene, ko me yake tare da shi ina so ke ki zamto wace zata gagaresu da karfin adu'a fa gujewa daga wayarsu, SHUWWAR kina jin abinda nake nufi da ke?, Ina so ki ji tsoron Allah, ki sani mutumen nan yana da hakki a kanki, ki kiyaye dukan wani abin da zai zamto cutarwa ne a gare shi, zan je na samu manyana da nake maganar sirri da su na sanar masu damuwarmu ba tare da na basu sunna ba, dan su tayamu fadawa Allah, zamu hanna kanmu barci na tsayin sati biyu mu ga yadda Allah zai yi, idan kuma suka ci gana da kiranki ki yi kirana ki sanar min ko ki zo ki sanar min domin mutanen nan babu abinda ba zasu iya yi ba sunna iya sauraronmu ta waya su gane kin fadawa wani Maganar su maki ila, ki taso ki zo ki sanar min ni kuma na samu mijin naki mu yi maganar in sha Allah, Allah zai toni asirinsu ko su waye da izinin Allah, fatana ba hakinsu ya ci ba suka taso masa"

SHUWWAR ta ringa amsawa, sunna haka Hajia Rabi'atu ta dawo, daidia ana kiran sallah a dole ya mike itama ta dauki Nikaf dinta ta fice tana fada masu gidan Hamza zasu wuce

A lokacin da ta zo cikin motar wani fadan ne suka bude sabo, har suka isa gidan Hamza
A nan falon Fauziya suka baje bayan su masu yin sallar sun gabatar suka shiga hira , a nan Shuwwar ke fadawa Fauziya abinda Nahidt ta yi, ai kuwa suka sakota a gaba tamkar zasu cinyeta danya tana kare kanta , har sai da ta gaji ta ce" Ke Shuwwar da Fauziya ku tashi ku ci uwani mana wai? Na ce ba zan auri Muhamadu ba na ga ubanda zai min dole yai ga jaraba ba zan aure shin ba, iskancin banza iskancin wofi , ba zan aure shin ba!"

Ai fa summa suka sameta wannan ya fadi gaskiyarsa, wannan ya fadi tasa, SHUWWAR ta dire magana da fadin" Shi kadai nake da shi ubana a duniya walahi sai kin aureshi dan ba zaki hada masa ciwon zuciya ba ke muguwa!"

Sunna tsakiyar musun ne wayar SHUWWAR ta dauki kuka

Cirota ta yi tana dubawa , lokaci daya ta zarro ido tana masu alamun su saurara sannan da hannunta ta nuna masu mai kiran ko wanene

Saurarawar suka yi gaba dayansu suka nutsu sunna sauraro

Da irin wancen muryar aka ce" Muna fatan kin gama yin tunani, kin gama yanke hukuncin zaki bamu hadin kai mu hadu mu kawar da shi a doron kasa domin zuwa yanzu mun gama sannin cewa har rapping dinki yake kokarin yi a cikin gida, shin zaki amince mana mu cin masa a lokacin da bai yi zaton haka daga garemu ba?"

SHUWWA ta yi dan murmushi ta ce" To wai su wanene ku? Yaya zan yi baban aiki irin haka da ku bayan ban sanku ba?"

Amsa aka bata kamar haka " Ba sai kin sanku ba da zarar mun samu burinmu gaba dayanmu a lokaci daya, kawai ki bamu dama mu kuma zamu ajiye maki abinda zaki masa anfani da shi ki kawar mana da shi ba tare da likita ya gane kashe shi muka yi ba"

SHUWAR ta gyada kai tana kallon Nahidht dake miko mata hannu kan ta bata wayar domin tare suke sauraro gaba dayansu
Ta ce" To ga yayata zaku tatauna kan abin"

Bata tsaya jiran ta cewarsu ba ta saka amsa kuwa sannan ta a
ajiye

Wani bahagumen , lankwasashen ashar ne NAHIDT ta nado ta nadawa mai maganar bayan ta bambance cewar mace ko namiji da mai maganar take ta dora da fadin" La'anane sai mun ci ...............dinka!"

Tana rufe baki Fauziya ta dauka itama ta bada nata mamakin harda kyatsewa ta dire tana firfito da idannuwanta sannan Shuwwar ta shafa fatiha.........domin a dogon da ta daukoma aka katse kiran sai karan kashe kiran da suka ji ne ya shaida masu an katse

Shiru suka yi sunna kallon kallo, a sanyaye Fauziya ta ce" Yanzun kuma mu duka zai kashe kennan..........mun shiga uku"

Nahidt ta ce" ke bari tsinane, babu abinda ya isa ya yi da mu dan iska, kadanma ya ji na so na masa zagin mahaukata na ce da shi kai Uwaka!"

SHUWWAR ta yi daria tana kwontawa ta ce" Baku da mutunci yan matannan ko kadan............
Da wanna suka shantake, da hira tsakaninsu wace suka jima basu yi irinta ba suka nemi shashancewa sunna shan dariya a tsakaninsu sallar la'asar ta sake tashinsu yi, daga nan suka shige kicin dinta tare suka dafa sasaukan dahuwa ta dauki uban kifi da nama sannan suka baje suka ci aka ringa fitarwa da sojojin da suke tare, wa'inda basu yi tunanin zasu samu abinci a wajen matar uban gidan nasu ba, sai dai fitowar abincin ya saka su maida hankali suka ci abinsu sunna masu jin dadin hakan da tunanin lalle ita din zata zamto uwar sojoji

Ba su su tashi a gidan Hamza ba sai da magariba ta sanyo kai sannan suka shiga kimtsawa suka tarkata sukai mata salama suka kama hanyar tafiya,

Sunna tafe SHUWWA na fadin ta rantse da Allah sai an yi auren nan kwana kusa ma kuwa, in kuwa tsoron Furera Nahidt ke ji ta fito a mutun ta fadi cewar tsoronta take ji

Ita dai ta shaka ta yi mata gummm dan ta fahimci so take ta kaita makura su daku a motar ta yadda zasu bar abin fada

_____________________________________


Tunda motarsu ta sanyo kai a makeken tsakar gidan na LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN MUHAY gaban dukansu ya yanke ya fadi

Ba komai ya ja haka ba sai gannin jerin motocinsa da ya fita da su, kafin shi dake zaune saman kujera hannayensa rike da jarida ya dora kafa daya kan daya ga Dukan alamu karanta jaridar yake yi, sai ko Wajen kofar da sojoji hudu ke tsaye sunna kikitu da kofar sun rasa ta yadda zasu budeta gashi mai banbare kofar an tafi a dauko shi aman ba'a karaso ba, gaba dayansu jinninsu a akaifa da tarin mamaki da tsoron aikin da matar oga ta aikata yau na kile bangarensu ta tafi da ky, gashi ya dawo a kadan ya yi minti talatin yana jira

"Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, SHUWWAR dan baban babanki hala ky din kofar cen daya tak ne muka kule muka tafi da shi!?"

Shuwwar din kanta cikinta sai da ya juya ta kaleta a zabure ta kada bata amsa, da kyar ta iya yarfe hannunta ta ce" Walahi da na sani da ban aikata haka ba, shi kadaima masifa yake bale an tabo shi, yau Nahidt dukan sojoji ya wajabta a kanmu wayo Allahna"

Nahidt ta zarro ido tana fadin" Ya wajabta a kanki dai kece matarsa, kuma ke kika rufe gidan ai kau? wai tsakani da Allah mema ya dawo da shi gidan nan yau da wuri?"

SHUWWA ta rintse ido gannin motar ta tsaya, sannan ta ji an bude mata bangaren da take kafin ta ji ana magana kamar haka" Barka da dawowa Madame, a kawo ky na bude kofar "

Hannunta na rawa ta wurgawa Nahidt jakar, Nahidt ta bude ta ciro ky din ta mika masa sukai tsuru tsuru sunna kallonsu aka je aka bude masa sannan ya dakatar da su ya amshi kayansa ya masu maganar da ita dai bata jin me yace kafin ya ga gaba dayansu sun sara masa sun fice, nan da nan harta direbobin mazan suka fice suka barsu daga su sai ransu

Gwauron numfashi SHUWWA ta sauke ta fito a motar tana nufar ciki ta shiga ADU'A a bayane tana kallon Nahidht da ta biyota aman ta ki ta bita ciki ta zauna a saman kujerar nan tana saurare

Yawu mai daci ta hadiye ganninsa zaune yana fuskantarta a lokacin da ta shigo

A hankali ta nufo shi, shi kuma kallonta yake yanaa ta maimaita kalaman da suka yi ita da mai kiran nan a waya har lokacin da ta ba yayarta wayar cewar toh ga yayarta zata masa magana suka ringa bada bada da dayar muryar da bai san ko wacece ba sunna durawa mai kiran ashar, har ta karaso gabansa ta zuba gwuiwoyinta a kasa ta hade hannayenta ta ce" Ka mana rai ka yafe mana, bamu san yau da wuri zaka dawo ba, aman gaba idan zan je gari zan tambayeka lokacin dawowarka , ka san abindama ya tsaida mu Nahidht ce, Nahidt ce miji ya fito mata ta masa wulakanci ta ce bata so, an rarasheta, an mata nasihar ta ce bata so, dan Allah ka taimaka ka mata ihu na tabata tana tsoron soja zata maka biyaya, ko auren dole ne a mata da Abanmu yana sonta shi, yadda akai min auren dolen nan itama a yi mata shi dan Allah ........"
Ta karashe tana hade hannayenta biyu har tana kokarin zama a kan kafafuwansa sannan tana tare Nikaf dinta dake son dawowa ya rufe fuskarta tana kuma hankalce da hannunsa koda yaka so marintan nan, sai ta yi ta kanta!


Tunda ta fara maganar yake sauraronta, haka kuma yana karantarta har ta dasa aya
Sarai ya san dan ta mantar da shi rufe masa faki da ta yi ne ta sako shi a maganarta , aman fa ta ce a aurawa yayarta abansu sai ya samu kansa da mamakinta harma da maimaita kalmar ABANSU?

kafafuwansa ya janye gannin so take ta fada masa a kausashe y💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥


*The Hero writer*


*SAJIDA*


_Bismillahir rahamanir rahim_


PAGE:. 3️⃣6️⃣



*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*






*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*


*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*



*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*



*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*


*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618


Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰


Kafafuwansa ya janye gannin so take ta fada masa a kausashe ya ce" Ki kula mana ".................sannan ya sake jan bakinsa ya yi gumm yana kallonta

Nikaf din ta cire itama tana kallonsa da kikifta ido, irin alamu na gaskiya da gaskiyar dake tare da ita,

Ajiyar zuciya ya sauke ya sake kallon wajen diner ya ga wayam, yau babu komai, bayan kwana biyu yakan taba dukan abinda ya samu na tabawa, sannan ua dora shayinsa , sai dai yau matar nan ta yi aiki irin na mata bata yi girki ba

Mikewa ya yi ya dauki kayansa ya juya ya shiga haurawa sama, ita Kuma sai ta samu kanta da raka shi da kallo har ya bacewa ganninta tana hangen hanyar da ya bi

Wani gwauron ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da NAHIDT ta ce" Ke Shuwwa"

A dan firgice ta juyo tana kallonta

Murya ciki ciki ta ce" Yaya kuka rabu? "

SHUWWAR ta sake kallon hanyar da ya haye din sannan ta juyo wajen Nahidt tana sauke wata ajiyar zuciyar again ta ce" Cewa ya yi ki kula mana, shikenan ya tashi ya yi tafiyarsa, bayan na barshi da gidansa yana jirana a waje, ya shigo ban yi gyare gyaren komai ba, uwa uba ban yi girki ba, Nahidt anya ba dana min tarko zai yi ta yadda ina shiga sama zan ji kaina ba a jikin jikina ba?, Kin san fa sojoji dukan matansu suke yi, anya ba tarani yake yi ta yadda laifina zai kai na ya batar da ni shikenan kowama ya huta?, Zuwa yanzu na fara tsoron kyaliyarsa da kawar da kansa a kan neman fitinata"

Nahidt ta shiga kwabe hijab din jikinta tana fadin" Yanzun dai tashi kike yi ki fada kicin, ni kuma bara na yi sallah na fito na shiga gyaran falon, Shuwwa an fada maki kowani namiji ne bai san darajar mace ba kuma bashi da ilimin adini ne? Dan kawai yana Soja baa hakan na nufin yadda yake da tsauri da tsagera da mararsa ji a waje zai kasance mai aikata haka wa iyalinsa, mau be kina auren namiji mai daraja, mai mutunci , wanda zai koya maki son kanki da kanki , mutunta kanki da kanki, uwa uba ya koya maki zama da namiji mai daraja , ya karyata hasashenki, ya birkita zuciyarki da dumin kaunar Soja!"

Tunda take kalaman ita kuma kallonta take yi har ta dasa aya
Ajiyar zuciya ta sauke tana dan girgiza kanta ta juya ta nufi hanyar kicin din tana tunanin me ya dace ta girka masu sasauka a gidan duba da sun yi dare?

Mayafinta ta cire ta ajiye da jakarta mai dauke da wayarta sannan ta karasa wajen frij mai dauke da danyan nama da su kifi, da su naman talo talo

Naman talo talon ta samu ta ciro da kyar ta nufi wajen ruwa ta dauki roba ta saka shi ta kunna masa ruwa sannan ta barshi ya saki da kankarar da ta dafke shi
Wajen dankalin turawa ta koma ta debo mai yawa sannan ta kawo abin bare bayan shima ta ajiye da wata robar da zatana zubawa idan ta bare

Harhada kayan jajage ta yi su tarugu, koren tatasai, da tafarnuwa ta jajaga su sosai sannan ta zuba su a cikin kwalba ta zuba masu Mutarde da mayonaise da garin magin tafi da gidanka da bakin poivre da fari da dan mai ta cakude su sosai sannan ta kawo su ta ajiye wajen kayan aikinta

Naman nan ta cire a ruwan nan ta sake masa wani ruwan, ta samu ta wanke shi tass sannan ta zuba shi cikin abin tsanewa ta sake komawa wajen dankalin nan tana ferewa tana sakawa cikin ruwa da sauri da sauri
Sai da ta kusan rabi sannan ta koma wajen naman nan , zuwa lokacin ya tsane ruwansa tassss, hakan ya sa ta shiga tsatsaga jikinsa duba da manyan yanka ne sosai har uku ta ciro, bata cicira shi kannanu ba sai dan tsatsaga jikinsa da ta yi sosai ta kawo wannan jajagen da ta yi ta shiga shafa masa lungu da sako sosai tana shafe shi da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login