Showing 36001 words to 39000 words out of 226733 words

Chapter 13 - Alkalamin Kaddara ta Complete Hausa Novel

Sajida   

11 Sep 2025

7946

kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.


*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618


Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰


Tana kallonsa da expression na mamakin ganninsa a irin wannan lokacin a cikin falonsu haka ta ce" You?"

Kure shin da ta yi da ido ya saka shi sakar mata lalausan murmushi yana fadin" Morning princess"

Juyowa NAHIDT dake cire safa ta yi tana fadin" Oh my baby ta farka? Zo zo zo nan"

SHUWWAR ta kasa daga koda kafarta daya ce bale ta je din da suke fadi har sai da Fauziya ta fito da plat mai dauke da dankalin turawa a soye da ta soyawa mutumen ta karaso tana ajiyewa ta ce" Shuwwa kin farka? Zo ki karya mutuniyar ta gasa maki"

SHUWWAR dake kallonsu da mamaki ta ce" Dama kun san wannan mutumen ne?......"
Ta juya tana kallonsa ta ce" Dama ka san yayuna ne?"

NAHIDT ta ce" ke wani irin dama ya sanmu? Dazu ne mun fito zamu je gidan su Sudais muka same shi a kofar gida, yake cewa jiya shi ya kawo ki, ya ce yana son ganninki dan jiya ya barki hankalinki tashe, na takaice maki dai ai da shi muka je gidan su SUDAIS , baki ga abinda Sudais ya so yi mana ba da ya ga Hamza, kiri kiri ya so kirta mana rashin mutunci bayan ya bamu akwatunnan da wata mata ke ta fadin a kan me zai bamu akwatunna ai bata ci akwatunna ba , ko sadakinsa ya ci mu maida masa in ji ita matar, shi kuma ya ce kennan dama jira muke ya sake ki shine muka zo masa da wanda ya mayr gurbinsa ya nuna masa shi wani ne a kasar nan? Dadin abin babu Wanda bai san waye Hamza giya ba, kin ga shirmen d'an adan ko? Sai ya fake da guzuma ya harbi karsana, shi a nan a tunaninsa wulakanta Hamza ya yi da laifin n da Hamzan ke aikatawa a yanzu, dan Adam kan mance laifin wani na yanzu na iya zamaa naka na gaba, shi kuma ka ga ya daina komai ya shiryu tamkar ba shi ba, wa ya ga SUDAIS na tatular giya????????????"

Fauziya ce kawai da ita NAHIDT din suka sheke da dariya banda SHUWWAR dake tsaye a labarin da suka bayar bata ga daya da zai iya sakata dariya ba, uwa uba a barcin safen nan da ta yi har suka je suka aiwatar da aikin nan banda ita suka amso mata hakkinta banda ita?, To shi kuma wannan din waye shi ne? Ba taimako bane? Ai ya yi ya gama me kuma ya zo yi nan?"

Hamza na kallonta ya ce" yar budurwa zo nan ki zauna mana"

Wajen da ya nuna ta bi da kallo, sannan ta sake binsa da kallo

Tsayuwarta ta gyara ta budi baki zata yi magana Baba Mai gadi ya yi salama
A nutse ya ce" Hajia Man Liman ne ke salama"

Sai da gaban Nahidt ya fadi, domin ta tabata zuwan nan da Liman zai yi harda tafiyarta tata ta ita kanta, tana kallon wajen da baba yake ta ce" Baba ce nai masa bama nan"

Fauziya ta kalleta tana fadin" Aa baba muna nan"

Ita da kanta Shuwwar sai ta rasa shin tana so Abanta ya shigo yanzu kuwa ko bata shirya fuskantarsa ba?

Shi dai Baba komawa ya yi ya sanar da Malan cewar sunna ciki yana iya shiga

Tun daga kan takalmin da ya gani na namiji a kofa ya dakata ya so juyawa
Sai dai tunawar da ya yi a message din NAHIDT tana nufin SHUWWAR ta dawo gida da wani tukiten sakin ne ya saka shi tunkaro gidan kai tsaye tun bayan dawo da su da ya yi ranar da aka kai SHUWWAR dakinta
Ya sani sarai irin yadda jama'ar anguwar ke mamakinsa, wasu a cikinsu sukan ce anya kuwaa malan?, Wasun kuwa gwa da gwa suke nyna masa cewar yana iya zubar da mutuncinsa idan har ya ci gaba da dorar da mu'amalarsa da wadinnan yan matan, dadin abin ba su kadai yakr bawa kulawa irin haka ba , kasancewar akoy wasu gugun samari da suka kafa zama irin na rashin da'a suke shuka abubuwan da suka ga dama, sai ya kasance yana shiga cikinsu yana jan ra'ayinsu cikin hikima, domin takanas zai je ya ce da shi za'ai zaman, zai zuba kudi a yi dahuwa a ci sai ya ce me zai hanna yau a yi tilawa koda ta sura biyar ce a cikin Alkur'ani ? Hakan zai sa ko me bawa ke yi Allah zai karre shi
Cikin hikima yake tafiyar da su, cikin dabara suke yin komai su wanye lafia, a yanzu ci gaban da aka samu a wajen samarin nan ba kadan bane, domin sun zubar da makamansu sannan sun daina cutar da y'ayan mutane, uwa uba a yanzun idan wani na cikinsu ya aikata aiki na lalata sunna za'a hukuntashi ne, sannan da abinda Allah ya hore masa yana taimakawa wanda ya ga da gaske zai nema, haka kuma yana kwadaita masu hannu da shinin anguwar sunna talafawa matasan sosai, hakan ya sa yanzu anguwar matasan nan sun zame mata garkuwa, ba dai ba a shigo masu da wani tsageranci, sace sace kuma ba dai a cikin anguwar ba,
Bai san ko dan su NAHIDT na mata bane ake nuna kar ya talafa masu? An cika zurfafa tsanarsu a bayane, fatansa suma su samu mafaka
Sai dai abinda yake tsorata shi she ne ALKALAMIN KADARRAR SHUWWAR din, Allah ya saka mata son yin auren a ranta, samun mazan take yi ta azalzala kan sai an aura nata kamar fitar rai, yanzun dai da kannanun shekarunta aure auren hudu, kuma ana sakinta ne da saki irin na son zuciya

Gyaran murya ya yi kadan ya sake yin salama

Muryar da ta amsa masa ta sake saka shi zubawa mutumen dake zaune wanda ba zai kireshi kai tsaye da saurayi ba, kun san idan farin mutun ya dan fara kwana biyu baya buya, ko yayane ana ganewa shi yasa a bayane ake gane shekarun HAMZA domin Hamza dama ba mutun bane mai kula da lafiyarsa da irin sport da sauransu

Murmushi ya sakarwa Malan yana mikewa hadi da tarbo shi yana mika masa hannu yana fadin" Masha Allah masha Allah, NAHIDT bako muka yi ne?"

Da NAHIDT din, da SHUWWAR din, da Fauziya du sai suka sha jinnin jikinsu jin furucin Hamza, uwa uba kallon da Malan ya sauke masu su su dukansun hakan ya sa Shuwwar yin kiri kiri tana tunanin kar dai ya cr a gidan giya suka hadu da shi, bata san me Aba zai ce ba

NAHIDT kanta sai da ta dan karkata kai sannan ta turo baki tana cire kanta a kuretan da ya yi da kallo kasa kasa sosai tana fadin" Allahn da ya sa mutun ba ubana bane!"

Kallonta yake yi, shi yasa dukan furucinta ya gane ba na zaman lafia ta yi ba, duda ba zai ce ga abinda ta fada din ba domin shi dai bai iya karanta furucin kan lebe ba

Dan Murmushi ya yiwa Hamza yana fadin" Masha Allah, sannu fa bawan Allah"

Hamza abinda yake fadin a kasan zuciyarsa shine'Allah ka sa wannan dai ba saurayinta bane, domin bana tunanin idan wannan a gabana wannan yar budurwa zata dube ni' sai dai a bayane sam bai nuna ba, ya dauke hirar da wasa da daria ta yadda har Malan ya kai zaune yana amsa gaisuwar su biyun dake gaishe shi bai daina dan yiwa malan din sannu da zuwa ba

Bayan zamansa bakinsa ya ja ya dinke kamar yadda ya dakatar da komai da yake yi
Ido ya zuba masu ta yadda ya karanci kowanensu
Shi dai namiji ne sannan mutun ne mai mu'amala da mutane, hakan ya sa a irin abinda Hamza ke yi ya gane inda akalarsa ta dosa
Sannan ya gane halayan Hamza a dan kankannin lokaci
Warau Hamza irin mutanen nan ne da waje baya masu wahalar shiga, sannan sukan saba da mutun koda yanzu suka hadu
A irrin masu halayan hamza akoy mugwayen cikinsu, daje shiga cikin mutane da dariyarsu da hakaya irin na sabonsu su cutar da mutanen su yi tafiyarsu ta yadda sai dai idan an je lahira ne wata shara'ar zata tabata,
Sannan akoy wa'inda haka suke, su kowa nasu ne, kuma da zuciya daya suke tare da kai
Hakan ya sa ya zubawa Nahidt ido da ya kula lalle lalle wannan bako ya gama siyan yardarta ta yadda take bashi amsa da zarar ya budi bakinsa sannan ta yi daria a dukan shirmen da zai fitto daga bakinsa

SHUWWAR dake tsarge har yanzu ta ce" Aba, wannan Hamza ne"

Malan ya kalli Hamzan a Karro na ba adadi a nutse ya ce" Na gani "

Daga na gannin bai kuma furta komai ba, sannan ya hade fuskarsa ta yadda shi da kansa Hamzan jin ta ce Aba duda da kamar wuya ace wannan mahaifinta ne, aman sai ya sake kama kansa , harma ya ringa sada kansa irin ka zo gaban sirikinkan nan

A tausashe kamar yadda ya iya mu'amalantar mutane ya kalli su NAHIDT yana nunin alamu na son karrin haske ya ce" ABA ne?"

NAHIDT ta hadiye yawu ta ce" Eh to Abanta ne, shine wanda yake........."

"Eh abanta ne ni" ya fada a tausashen shima yana katse bakin yar neman sannan ya sake kure yannayin Hamza da kallo, abin ya dawo daidai da namiji a namiji ne

Daga saman kujerar da yake zaune ya dawi kasa yana sake sada kansa ya ce" Masha Allah, Aba barka da warhaka......am ka yi hakuri dan Allah, Ban sani ba kaine Aban, dama jiya nine na hadu da ita a cikin wani irin yannayin da ya sakata ta je gidan Giyar dake anguwar................"

"Ba ba sai ka fadi nan ba, Aba wannan shine ya taimake ni jiya ya kawoni gida, yanzun dai ban san meye mu'amalarsa da aunty ba na dai farka fitowata kennanma daga daki na same su a haka, daga haka ban san komai ba" ta fada da dan gagawar dake nuni da bata so Aban nata ya san daga ina ya samota, hakan ya sa Nahidt da ta zabura jin ta juye laifin a kanta ita da take ikirarin bata wani Tsoronsa ta ce" Ke ki ji tsoron Allah yarinyar nan a kan me zaki ce kika tardo mu bayan ta dalilinki muka sanshi? Fauziya dan Allah mun sanshi kafin yau ne?"
Daga Fauziyar, har Shuwwar, har Malan din sun yi mamakin gannin yau NAHIDT na gudun aa dora mata laifi har tana kare kanta da dukan karfinta

SHUWWAR kam sai ta sada kanta tana hade yan hannayenta tana sauke ajiyar zuciya

Shima Hamzan sai ya samu Kansa da jin sha'awarsu, ashema sunna da alkibla? Ba kwata kwata bane suka bace? Ashema sunna da wanda ke tsawatar masu?

Malan ya maida dubansa kan Hamza ya yi dan gyaran murya yana fadin" Bismillah malan ina sauraronka a wani gidan giya?"

Sai da cikin Shuwwar ya juya, ta karra sada kanta sosai tana sauraronsa ya dora da fadin" bata sha ba, ta siya aman ta kasa sha, domin koda ta saurari shawarata bata yi niyar shan bane, domin da ta yi niyar sha din ba zara iya tsayawa dan wata maganata ba, daga nan ne na daukota na kawota gida, sai kuma tun da safe da na yi safiya na dawo"

A tausashensa ya ce" Wani abu ka manta ne?"

A hankali ya girgiza kansa ya karra sada kan nasa ya ce" Ka yi hakuro Abanmu, idan har shi ya saketa ni ina sonta, zan kuma aureta na zauna da ita da zuciya daya"

Murmushi NAHIDT ke yi tana gyada kanta ta ce" Kai abu ya yi kyau"

Harare Malan ya maka mata yana cire kansa ya maida kan SHUWWAR ya ga bata dago kanta a yadda yake ba, ya sake kallon Hamza ya ce" Ko zan iya sannin dan tarihin malamin?"

Hamza , mutun ne da bai iya boye waye shi ba, haka kuma baya jin kunyar hakan, Hamza bashi da boye boye nema sam a rayuwa, hakan ya sa ya ce" Ni dai sunnana Hamza, Ni haifafen garin Tanus be, Aba ni dai shege ne, domin bani da uba a yadda marikina baban sojan nan da ya yi retaya aka fada masa da na matsa masa ya fada min gaskiyar lamarin ana cewa ba shine ubana ba bayan ni kadai ya malaka? Ana cewa ni din ai shege ne, sai yake ce min....................



Tunda ya ce shi shege ne, gaba daya dakin kowa ya dago yana masa kallo irin wanda ya zo cikin zuciyarsa, ba ga Malan din ba ba gaa y'ayan nasa ba, shi kuma a nutse yake basu bayani ya ci gaba da fadin"

Shi kuma a nutse yake basu bayani ya ci gaba da fadin" a ranar da na dagawa Babana hankali da rigima da tashin hankalin wai an ce ji shege ne? Sai ya samu ya zauna da ni shi da mamana dake rike da ni ya ce, Hamza ka daina kiran kanka da shege, domin ba wanda aka samu ba aure bane shege a adinance, shege shine wanda akai ratsen samunsa a cikin zamantakewar matan mutun Idan ya ziyarci iyalinsa ba ranarta......., 'A fa tasa fahimtar kau?' Sai babana ya ci gaba da ce min Hamza ni dan da ka ganni a nan a lokacin ina te ke da bada tsaro a garinku aka tsinto ka, wanu manomi ya tsintoka ya kawo mana kai, mun hau bincike mun saka ka a hannun masu kula da kai sosai, a tsayin sati daya da kwana hudu muka samo labarinka, Mahaifiyarka haifafiyar garin Tanus ce , ta sameka haka ne ba da aure ba kuma aka koreta a gidansu dan sun ki yarda su amsheka, uwa uba saurayin nata ya ki ya amsheka, kai dai wahala ta isheta ta samu wata mata ta ce zata yi mata hanyar zuwa Saudiya Neman kudi, da zarar ta je ta bada kai da fata ta biya kudin jirgin da akai mata itama ta bata naira dubu dari biyar, in ta yarda su yi, idan bata yarda ba karma a fara domin yadda sukai dalilin zuwanta sunna iya yin na dawowarta ba tare da sun bari ta dauko ko tsinke ba, wannan dai shine dalilin da ya sa mamana ta kawo ni gonar Baba Augui ta ajiyeni ta tafi saudiya, maganar da nake yi maka dai har i zuwa yau babu ita babu labarinta, dangina kuwa ba ni ba su Gaskiya dan na kurce su kamar yadda suka ki daukana!"

Shiry falon ya dauka na dan lokaci
Yan matan nan tunda ya yi maganar mahaifiyarsa ta je saudiya sai ya kasance sun sake kura masa ido
SHUWWAR ta ce" Dama haka suke yi ne? A biya masu su zubar da bayansu ba ruwansu su yi tafiyarsu su je su haifa su kuma mutu su bari?"

Malan ne ya yi dan gagawar fadin" Ehm, ki yi shiru, bawan Allah kai kuma me ya kaika gidan giyar?"

Dan dagowa Hamza ya yi ya dan kalli Malan sannan ya maida kansa ya ce" Sha nake yi, an yi an yi na daina abin ya gagara, yanzu haka dai ta jiya ce kadai ban sha ba, aman in sha Allah ni na san watarana zan daina, na fada a shaye shaye ne sanadiyar abokannan banza, aka taki rashin sa'a babana a duniya yanaimin makauniyar soyayar da ba zai sakani kuka ba koda dan sanadiyar hannani shan giya, mamana kam na iya bakin kokarinta, a wajenta na gane ilar shan giyar kafin na gane haka da kankin kaina, domin sanadiyar ina shan giya na ga wulakancin rayuwa kala daban daban, na nemi aure sau biyu abinda yake faruwa da neman auren nawa ke sakani a kuncin zuciya, Malan ka gaa dai yada nake , ina aiki, ina karantun islamiya har yanzu, aman a haka kuma nake zuwa na sha, ban sani ba, ko kuma zaku hanna min mata?"

Wani shauki ke diban Fauziya da ta kure shi da ido, a hankali ta sada kanta a lokacin da ya dasa aya tana mai tsintar zuciyyarta da mangarinsa wa kanwar tasu, tana ji a ranta wannan din ai bashi da aibu, shan da yake yi kuwa idan har Allah ya nufe shi da dainawa zai daina ne in sha Allah, ita ba abinda ya birgeta da shi sai halayansa na fadin gaskiya kai tsaye, duda basu da tabacin gadkiyar ya fada, aman mutumen da zai fadi laifinsa kai tsaye ba tare da jin kunyar d'an Adam ba, gaskiya abin a duba ne

Malan ya lumshe idannuwansa yana tunanin mizanin dora wannan lamari

A hankali ya furta" Astgfrullah "

Ya sake yin shiru sannan ya dubi fuskar Hamza da ta NAHIDT, sai kuma ya kore da gagawa abinda fuskokinsu ke fada masa yana mai tunanin kaye kaye ne irin na tunanin mutun
A nutse ya ce" Malan Hamza, na gode, na gode matuka da ka ceci yarinyar nan ta hanyar nuna mata ilar saka kanta a rayuwar da ta so sakawa, ka sani daga yau, daga yanzu zan ringa sakaka a adu'ar Allah ya kawo gagarumin dalilin da zaka fita a harkar shaye shaye, domin shaye shaye bashi da anfani, bashi da kyau ga kiwon lafiyar dan Adam, kai ka san shaye shaye yana hadasa rayuwa irin ta wulakanci, sannan uwa uba shaye shaye laifine ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login